Showing 12001 words to 15000 words out of 126765 words
Chapter 5 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf
tsoro ya kama Majeederh ta runtse
Idanunta cikin rauni ta ce "Ni za a kashe"
"What? Kisa wake shirman haka" ya ajjiye babyn ta É—auke É—anta da sauri ta duba hijabin dake
gefe wanda yake sabo ta É—auka ta saka jikinta jiri na É—aukarta ta rungume É—anta tare da nufar
wajan domin ta miƙa kanta gare su.
His Excellency Abu-turab Alƙasim ya fito yana kallon Hammadala dake ɓoyewa cikin nutsuwa
ya shiga nufar wajan da harbin ke tashi Hammad ya ce "No Your Excellency, kada ka je wani
Mahaukaci ne da bindiga yake harbi kawo yanzu ya harbi securities guda uku"
"In my house? Mahaukaci?" Hammad bakinsa na rawa ya ce "Yes Sir, kuma wallahi riƙaƙƙen
Mahaukaci ne kayan jikinsa tamkar sun yi shekara É—ari a jikinsa, gabaÉ—aya jikinsa zane ne
kamar na tattoo gashi baƙiƙƙirin...
Na'ima Sulaiman Sarauta
08119237616*í ¼í¼ˆ MIJIN MALAMAí ¼í¼ˆ*
Nimcyluv Sarauta
*_Follow my accountí ½í±‡í ¼í¿¾_*
https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv
*6......*
His Excellency Abu-turab ya dubi P.a É—insa Hammad ganin yadda jikinsa yake ta rawa kamar
wanda aka ce masa ba zasu ƙara samun mulki ba. "Your Excellency abun nan yana neman
girmama, mu sanar da securities na Government house" Abu-turab dai bai ce komai a hankali
ya ci gaba da takawa har zuwa tsakiyar compound na gidan nasa, ya shiga ware idanunsa akan
securities ɗinsa da aka harba wanda suke kwance a ƙasa. Ya ɗaga kai ya dubi wanda yake
tsaye ya juya masa baya, cikin nutsuwa ya shiga ƙarewa yaro ko matashin saurayin kallo.
Cikakken namiji ne a tsaye, ya riƙe ƙugunsa da hannu ɗaya, ɗaya hannun riƙe da bindiga ga jini
yana zuba daga hannun, baƙi ne irin sosai ɗin nan fatarsa har sheƙi take gabaɗaya wuyansa
zanan tattoo ne kamar wanda aka zanawa macizai, sumar kansa a cure take ta wani murmurÉ—e
kamar indomie ta sauka har wuya, wani irin crazy jeans ne a jikinsa wanda ya yayyage ga wata
Armless É—in riga tayi fata-fata a jikinsa, siffofin mahaukaci bayyane a jikinsa. "Who are you?"
Abu-turab ya tambaya cikin kakkausar murya fuska ba wasa.
Wanda aka kira da Mahaukaci gabaÉ—aya ya juyo, kyakkyawar bugawa zuciyar Abu-turab ya yi
in his whole life zai iya cewa bai taɓa ganin kamar shi ba, zubin idanunsa ma daban yake
musamman yanzu da idanun suka sauya launi babu mai iya fassara abubuwan da suke
nunawa, wanda ya yi masa mugun sani shi ne zai iya me yake ji ko me yake buƙata. Sosai
yake da gashin gira a cunkushe, duk baƙin da yake da shi lips ɗinsa jajir yake. Ya lumshe idanu
ya buɗe akan Abu-turab,bai ce komai ba ya ci gaba da ƙare masa kallo sai kawai ya ɗauke
kansa.
"Ma ka ke buƙata?" Still bai magana ba. Sai a lokacin Hammad ya ƙara so wajan suka dinga
kallon mahaukacin kafin P.a Hammad ya ce
"Hi crazy man, who are you, What do you need?"
Nan ma ya daÉ—e yana kallon su still bai ce komai ba, Hammad ya kalli Abu-turab ya ce
"Your Excellency Wallahi Mahaukaci ne"
Abu-turab ya jinjina kai yana ƙoƙarin juyawa cikin gidan ya ji saukar muryar mahaukacin ya ce
"Hhhh kai... I want my Jee back, and my son" Hammad da His Excellency Abu-turab suka kalli
juna kafin Hammad ya ce
"Who's Jee?" Yaƙi cewa komai sai ƙirjinsa dake ɗagawa. "Your Excellency na faɗa maka
Mahaukaci ne, da alama ba a son ya hauro ta kadanga ba" Abu-turab ya yi jima kafin ya ce
"Call securities" yana faÉ—in hakan ya juya zai koma cikin gida wajan Majeederh. Da sauri
Mahaukacin ya sha gaban Abu-turab yana ƙare masa kallo idanunsa jajir kamar gauta cikin
gurɓatacciyar Hausar shi ya ce
"Ina so Jee, i want my babe" "Are you mad? Kai ma haukaci ne?"
Shi dai babu abinda yake cewa sai "Ina so Jee, i want my Jee back babe na" His Excellency ya
dubi sauran jami'an tsaron ya ce "Ku fita da shi" kafin su kama shi idanun Mahaukacin ya sauka
akanta, tana riƙe da jajirin kamar kullum jikinta rufe da hijabi ya zaro dara daren idanunsa waje
ya juya da sauri cikin ɗaga murya ya shiga faɗin "Jee, Jee!" Tazarar dake tsakaninsu ya sa sam bata ji ba. Ya ƙara sauri kamar zai kifa, yana ƙoƙarin haure
motar da ke parking lot aka cilla masa igiya ta ƙafa ya faɗo ƙasa, kafin ya yunƙura an sake cilla
masa igiya ta harɗe hannayensa, maimakon ya yi ƙoƙarin dukan securities ɗin sai ya fara buga
kansa da tarazon wajan yana faÉ—in "Bebe, Jee, Malumana"
Ya dinga faɗa yana buga kansa cikin ƙaramin lokacin jini ya wanke masa fuska ya fara gani
dishi dishi.
Majeederh na shirin ƙara sawa tsakiyar parking lot ta ji anyi saurin kama hannunta tare da janta
baya, a tsora ce ta juya suka haÉ—a idanu da Abu-turab baki buÉ—e take kallonsa, daman shi ne?
daman Gwamnan jihar su ne ya taimake ta? "Me ki ke?" Ya faÉ—a speaking calmly. Ta janye
idanunta tare da kame kanta tana son ɓoye fuskarta ta tuna ai bata da wata sauran ƙima da
daraja sai kawai ta É—an ja baya ya tattausa murya ya ce
"Baki da lafiya Jiddo, kina son hutawa" ta juya ta kalli yadda Hammad ke kallon su haka kawai
jikinta ya bata akwai wani abu ta ce
"Ni za a kashe?" Ta furta cikin kamilalliyyar muryarta. His Excellency ya buÉ—e ido ya ce
"No, wa zai kashe Jiddo, na samu baƙi ne da zamu yi meeting koma ciki ko?" Haka kurum ta ji
ta yarda da shi kuma ta san waye shi yana kyakkyawar mu'amala ta juya shi kuma ya bi
bayanta, tana ɗaga ƙafa zata shiga ƙofar ta ji an ce "Malumana" cak ta tsaya ƙirjinta na bugawa
zuciyarta na harbawa a ranta ta ce "Little Son"
Zata juya ya yi saurin faÉ—in "Meke faruwa?"
Ta É—an yi jam can ta ce
"Na ji murya" ya ce "A voice?" Bata saurare shi ba ta juya shi ma ya juya har ya sha gabanta ya
ce "Akwai jama'a, mu koma ba wata murya, ba wanda ya san kina ciki" ya lallaɓata tayi cikin
gidan tana shiga ya rufe ƙofar ya sanya securities a jikin door ɗin.
Yana komawa ya samu ana dambe da shi ya yi jina jina da jikinsa "Duk sanda ya ƙara zuwa
shoot him, kuyi masa duka" shigowar wata mota ya sa suka tsaya wasu ma'aikatan asibiti suka
fito da wani dattijo wanda yake sanye da ƙatuwar sarƙa mai zanan kurus. David ya haɗe hannu
alamar apologies ya ce "Sorry" Abraham sosai ya gane David domin shi ne babban Pasto ya
jinjina kai kawai. David ya ce "His name is Abraham Daniel David, My grandson ya samu
depression har ya zama taɓin hankali, na yi mamakin yadda na'urar jikinsa ta nuna mana nan,
duk yadda akai akwa abinda yake nema, baya zuwa waje babu dalili duk haukansa" Pasto
David ya faÉ—a yana sawa a kunce Abraham tare da sanya shi a mota.
Faɗa akai sosai kafin daga ƙarshe aka danna masa Allura nan take ya fara barci.
Majeederh ta zubawa jaririn nata idanu tana son ƙara fahimtar kamanninsa amma abun ya
kwanta mata gashi kullum ƙara juyewa yake kama da ita.
"Kin sanya masa suna ne?" Mama ta tambaya tana miƙawa Majeederh haɗin tea a cup ta
lumshe idanu ta buÉ—e a hankali ta girgiza kai. "To ai yana da kyau ayi masa huÉ—u ba, wanne
suna ki ke so?" A hankali ta ce
"Ibrahimul-khalil"
"Ikon Allah, Sarkin zuciya da faɗa kenan, ga ƙwazo shi kuma ba rago ba halin su ɗaya da Aliyu
Haydar Allah ya raya mana Ibrahimul-khalil" Majeederh ta saci kallon Mama so take ta É—an saba
da ita amma yanzu gabaɗaya zuciyarta na gargaɗinta da ƙara yarda da wani, tunda Latifa Omar
ta riga ta sanya mata tsoro ainun a zuciya ta gane babu Aminiyya, Abbu ya sama tabo na har
abada wanda ya sa ta fahimci babu wani masoyin ƙwarai ko true love.
"A beautiful name, but why Ibrahimul-khalil?" Ba tayi masa magana ba ya zauna saman kujera
kafin ya ce.
"P.a a shirya tsaro na musamman a gidan nan, a duba motsin kowa" Hammad ya rusuna ya ce
"In sha Allah, Allah ya taimaki Your Excellency"
Fita su kayi gabaÉ—aya ya rage daga Mama sai Majeederh da Kalil dake barci.
Aaliyyah na zaune a parlour farin ciki ya kamata gobe za a É—aura aurenta kamar yadda Uncle
Isma'il da Uncle Bello su kayi al'ƙawari.
Abbu taga ya fito É—auke da tarin takardun Majeederh na makaranta, da shaidar zamuwarta
mace ta farko data fara lashe gasar musabaƙar Alkur'ani ta ƙasa da duk wasu ducoment da
Award nata da tarin littafanta. Ta miƙe da sauri ta ce "Abbu me za ka yi da wannan?"
Ya yi mata banza tabi bayansa har zuwa tsakiyar compound gani tayi ya zuba musu fetur ta cilla
Ashana ta zare Idanu ta ce.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, me kayi haka Abbu" ya dubeta ya ce
"Har na koma ga mahaliccina ba zai taɓa daina yi wa Majeederh Allah ya isa ba, da haihuwarta
gwara ɓarinta Allah ya sanya ta ƙarasa lalacewa har abada,ta ɗakko cutar ƙanjamau Hiv har
tayi silar mutuwarta a wulaƙance" Aaliyyah kuka take sosai ta ce "Abbu kana sanya mini tsoro
anya kai ka haifi Anti Jeederh?" Ya yi murmushi ya ce "Kowa zai yi zaton haka, wallahi wallahi
ni ne uban Majeederh ni na haifeta amma yanzu kaf duniya ba Wacce na tsana sama da ita, a
kullum idan na ce ta fito da mijin aure sai ta ce Allah bai kawo ba har cewa take ba wanda ya
taɓa cewa yana sonta na zaɓa mata, na sha haɗata da maza daga ƙarshe su gudu ashe su sun
riga sun halinta sun gane Fasiƙa ce, Mazinaciyya ce, la'ananniyya ce, Allah ya isa Allah ya isa
Ubangiji ya tsine miki Albarka Majeederh" ya fashe da wani irin kuka Aaliyyah ma kukan take.
Bar Aliyu Sufyan Alhassan yini ya yi yana neman Malama Majeederh amma ko mai kama da ita
babu, yana dawowa gida zazzaɓi mai zafi ya rufesa...
Misalin 1:23 na dare tana zaune rungumeta da Ibrahimul-khalil da yaƙi barci yana ta rarraba
Idanu gashi so Ma sha Allah sbd kyau daman ance shegu masu iya kyau ba. Sai ya zame mata
abokin hira ta ce "Ina son ka Kalil, yadda na riƙe ƙa amana Ubangiji ya kawo sanadin da
gaskiya za tayi halinta, ina jin kamar na shiga duniya na kama hotel....," Gilmawar inuwa ta gani
kamar an shige ta É—an kalli wajan ta juya ta duba lokaci taga É—aya da rabi na dare saura kafin ta
san abin yi an fara buga ƙofar bedroom ɗin da ƙarfi ana faɗin "Jee Jee Malumana...
Na kusa ending free pages. Contact to subscribe.... 08119237616 Whatsapp only.*í ¼í¼ˆ MIJIN
MALAMAí ¼í¼ˆ*
Nimcyluv Sarauta
*7.......*
_Complete story Arewabooksí ½í±‡í ¼í¿¾_
https://arewabooks.com/chapter?id=6219d7896c0de838cd360960
Duk yadda Jeederh ta kai da son kamewa waje guda da riƙe kanta amma ka sawa tayi ta miƙe
tsaye hannunta riƙe da Khalil, amma ta kasa motsawa sbd bata ƙara jin saukar sautin da
kunnuwanta suka jiye mata ba. Shiru shiru sai kawai ta juya zata koma saman bed ta ƙara jin
ance "Jee, Jee Malumana" a wannan karan muryar da aka kira sunan bata fita sosai kamar bai
kiran yana cikin wani hali, ƙirjinta ya yi kyakkyawar bugawa, bugawar da sai data runtse
Idanunta, me ya sa muryar ke yi mata tsananin kama data Little Son? Me ya sa hatta sunan ya
zo ɗaya da wanda ya laƙaba mata sbd bashi da hausar da zai iya kiran complete sunanta
Majeederh kamar yadda kowa ke faɗa, iya ƙoƙarinsa da faɗar sunan sai dai ya furta kalmar
_Jee_ a sauƙaƙe?
"Yaa Allah" ta furta domin tasan har abada har gaban abada idan akwai he never comes to her,
amma meke damunta har haka me ya sa muryar ke mata amsa kuwwa a kunne? "Jeeeee!!!" Ya
sake furtawa muryarsa bata fita sosai kamar wacce aka tsikara tayi wajan ƙofa tare da sanya
hannu ta murɗa handle, tsaye ta gashi yana zabga ƙamshi daga shi sai wata kyakkyawar
Arabian jallabiya brown kallo wacce tayi masa kyau sosai, ya É—an sakar mata kyakkyawan
murmushi kafin ya ce
"Kina buƙatar wani abu ne?" Tayi masa kallo ta ɗauke kai ba tare data amsa shi ba, domin bata
da yawon magana Majeederh nada matsanancin aji sosai, wanda kuma halittar ta ce hakan.
Gani ya yi tana leƙa waje shi ma ya leƙa yana cewa "What are looking for? Me ki ke kallo?" A
raunane wanda kuma ba kowa take son yaga raunin nata ba ta riƙe kanta sosai tana sake rufe
jikinta da hijabi ta ce "Allow me to go"
"Where?" Ya amsata da sauri. "Ban son zaman nan, kuma ka bari na leƙa waje" Abu-turab ya
ware idanu yana shafa sumar kansa ya ce.
"Me Jiddo zata yi a waje yanzu? 2 saura ok" tayi shiru ya ƙarasa shigowa cikin bedroom ɗin tayi
saurin ƙanƙame jikinta waje guda lokacin Khalil ya fara kuka..
Sosai Abu-turab ya rufe ƙofar kana ya nemi waje nesa da ita ya zauna saman kujera ya harɗe
ƙafa. Malama Majeederh hankalinta ya rabo wajan kashi uku, ɗaya na waje, ɗaya na kan Khalil
dake kuka, É—aya na kan Abu-turab daya sanyata a gaba tare da kafeta da idanu. Sai ta zama ira
bata ƙaunar kallo yana takura ta ainun. Abu-turab yana ƙoƙarin magana su ka ji an daki ƙofar ya miƙe tsaye tare da kallon Jeederh ya
ce
"Sorry, na ce a kawo mini abin shur ina da azumi" bata ce komai ba ita dai.
Ya nufi ƙofa yana fita ya rufe ta, kokawa ake sosai da Abraham Daniel David wanda yake son ta
ƙarfi sai ya ɓalle ƙofar, gadai securities da yawa amma sun kasa controlling nasa ya jiwa kansa
ciwo amma yaƙi ya yi giving up, wani irin ƙarfi ke zuwar masa. "Abraham" Abu-turab ya kira
shi,ya juya kalli Abu-turab. "Me ka ke buƙata?" Da hannu ya nuna masa bedroom ɗin da Malama Majeederh ke ciki, kana
ya nuna ƙirjinsa wajan zuciyarsa ya ce.
"Jeena, nan" Abu-turab ya fahimci Abraham na son shaida masa Jee na cikin zuciyarsa ita
kuma yake nema. Cikin nutsuwa yana murmushi ya ce
"My friend zo ka ji" Abraham ya kafe waje guda domin babu na biyunsa a taurin kai. Cikin
tattausa harshe ya ce "Ita Jee É—in bata nan, amma ka dawo gobe zan kaita wajanta" ya faÉ—i
hakan cikin harshen Ingilishi yadda Abraham zai fahimci mai yake nufi.
"Promise?" His Excellency ya ce "Promise" Abraham ya sanya hannu a tsakiyar rigarsa inda ya
yage ya zaro wata kyakkyawar flowers sai ƙamshi take ya miƙawa Abraham yana wani irin
buÉ—e ido ya ce "Malumana"
Ma'ana the flowers is for her. His Excellency ya amsa deep down na zuciyarsa cike da
mamakina Abraham who is he to her?.
Securities É—in za su kama shi ya girgiza musu kai tare da yin gaba yana É—an tangaÉ—i yana yin
gaba ya ji saukar muryar Khalil na kuka ya tsaya cak, sai ya juya kawai sai su kaga ya yi
murmushi ya ce
"My pregnancy"
"An samu matsala" In ji Khamal. Abu-turab ya saka hannu ya tsige flower É—in tare da zubar da
ita ya ce
"Make sure baku sake sakaci ba, i hate noises"
"We're sorry Sir, Hakan ba zai sake faruwa ba, wallahi ta sama ya hauro mahaukaci ne daya
kama hannun Captain sai da ya ƙarya shi,ya sha duka sosai wajanmu amma bashi da haƙuri
yana da zuciya ban san wani abu giving up ba" His Excellency bai ƙara magana ba ya buɗe
bedroom ɗin har yanzu tana zaune saɓanin ɗazo Madara take bawa Khalil, Abu-turab ya jima
yana satar kallonta da tayi ƙoƙarin ɗago kai sai ya janye idanunsa ya basar
"Jiddo, we need to talk please" yadda ta ƙara nutsuwa ya san cewa ta bashi dama cikin
nutsuwarsa ya ce
"Majeederh kina da hankali, ko ban girmeki ba zamu iya zuwa age mate don haka duk abinda
zan faÉ—a miki ba zai zama cutarwa a gareki ba" ya sauke numfashi ya É—ora da "Don Allah kada
ki ji zafinki akan hukuncin da ya yanke miki, iyaye ba a taɓa fushi da su ki ɗauki hakan matsayin
jarrabawa kuma ƙaddara wacce babu yadda zaki iya dole sai ta kasance, ba zan miki nasiha
akan yarda da ita ƙaddarar ba domin kusan kin fini sani, sai dai na nemi ta barraki a wajanki" ya
ƙara yin shiru ya ce "I feel your pain, kafin na zama gwana na sha wahala,ina rayuwa da
mahaifiyata after my father's died, dangin mahaifina they are so selfish sun ƙwace komai dana
mallaka wajan Abbana, filaye, kadarori all the properties, mun fara yawo yawo a dangi kowa
yana gudunmu sbd babu ran mahaifina sun manta alherin da ya yi musu, dangin Mamana basa
kusa, na fara dako ina garuwa ban taɓa yarda ba zan iya ba, burina Mamana ta ji daɗi na zama
wani abu" ya É—an sauke numfashi kamar lokacin abin ke faruwa kafin ya zuba mata Idanu ya ce
"I was thinking mene ya sa mutane suke manta alheri? Kuma da yawan mutane suke sawa ka
zama mutumin banza, ko dana fito takarar House of assembly kin me ne ya faru?" Sai a lokacin
ta É—ago kai ta kalle shi some seconds kafin ta janye ganinta daga gare shi, tana É—an É—auke
numfashi sbd abubuwan da suka tukare mata bata san ranar faÉ—awar su ba. Abu-turab smile
yana jan idanunsa zuwa sama kafin ya ce
"Cewa akai kada a sake a zaɓeni wai bani da uba, ba wannan ya daman ba familyna sune kan
gaba wajan ganin na fasa kujerar da nake nema, kamar yadda suka so ban samu ba, gabaÉ—aya
deligate suka juya mini baya, cikin ikon bayan an cinye tenuwa huÉ—u cif na sake fitowa takara i
won the election, nayi shekara huɗu a lokacin ne na haɗu da ƙaddarata, wacce ta zame mini
Dafi a zuciya, ta zame mini wani tabon da