Showing 63001 words to 66000 words out of 126765 words
Chapter 22 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf
ya ce "Ga ni fa... Call her" Ta tura baki ta ce "Gashi nan sai sallah take Allah don
kar tazo ne" Ya saka hannu ya zame hular kanta yana cusa hannunsa cikin sumarta bai ce
komai ba. "Ka zo muke part ɗin nata, ka ji Kalb my prince"
Ya waro dara daren idanunsa cikin murya irin ta masu mulki ya ce "Prince ɗin Saudiyya da zo
wajan wata? Ni Ajlaal? " Ta yi shiru tana kallonsa ya ce "Uhm, shi ya sa kike ta zubar mini da
ƙwayaye a hanya ƙasa ƙasa, kin kasa riƙe ko ƙwai ɗaya balle Sultaan ya saka ran samun
grandson?" Ta daki ƙirjinsa dake buɗe cike da yalwataccen gashi kafin ta ce "Ajlaal wayo zaka
mini, idan ka fara haka" Ya tsorawa lip's ɗinta idanu kana ya saki wayarsa a gadon ya ce
"Damn it...!"
"Me?" Ya miƙewa gabaɗaya tana wutsil wutsil haka ya cillata gadon yana kashe hasken ɗakin
gabaɗaya muryarsa can ciki ya ce "Yarinya ina zama lafiya wajan aikina kika saka rigima ashe
Allah ke sona da rahama"....... Cikin dare Majeederh ta kasa bacci sai juyi take saman gado
tana riƙe cikinta a hankali take kiran sunan Allah, jin azabar ta yi yawa ya sa ta miƙe a haukace
tana girgiza kanta tare da zubewa saman gwiwoyinta ta ce "Ya Allah ka ɗauke mini abin da na
ke ji har gaban abada wlh ban so, Ubangiji ka karkatar da halitta jikina zuwa ta jinsin maza" Ta
yi shiru duk da sanyin ac amma zufa take jikinta na ƙyarma da ɓari, ta zari hijabi tare da sakawa
ta nufi wajan part ɗin. Lokacin data fito yana zaune saman kujera a daidai corridor wanda zai
mayar da kai part ɗin Ƙhulud, daga shi sai wata Jersey fara tas faffaɗan ƙirjinsa a bayyane, ya
ɗora ƙafarsa saman table hannunsa riƙe da system yana dannawa, lokaci zuwa lokaci yake
yatsuna fuska yana ɗaukan green tea tare da sha a hankali, sumar kan nan nashi har wuya,
Prince Ajlaal Sultaan gabaɗaya mahaifinsa ya ɗakko sak. Yana zaune ya ji motsi ya juya kansa
ya hango mace durƙoshe ta cure waje guda tana yarfe hannu, taɓe baki ya yi tare da kwasar
system nasa ya na jan tsaki..... Washegari dai wajan 11 ta shiga Al-Azhar University tun kafin ta
nufi department ɗin su taci karo da babban malaminsu. Cike da tsantsar ladabi ta gaisheka ya
ce "Majeederh Abdul'aziz Khan?" Ta jinjina kai ya ce "Follow me" Yana tafe tana binsa kamar
bata son takawa har ya isa office ɗinsa, manyan mutanen data gani a office ɗin ya bata tsoro ta
zauna gefe guda. Malamin ya yi gyaran murya ya ce "Majeederh ga jakadan ƙasarku Nijeriya
dake zaune a nan Misira, bayan zaman tattaunawa da manyan ƙasar ku kama daga shugaban
ƙasar, gwamnan sauren jihohi da naku, shugaban malamai na ƙasa dana jiharku daga ƙarshe
sun bada sunanki matsayin wacce zata wakilci ƙasarku Nijeriya a gasar musabaƙar Alkur'ani ta
duk duniya" Majeederh ya zaro idanu waje ta shiga girgiza kai a raunace ta ce "Ba zan iya ba,
ba zan iya ba ni Ɗaliba ce"
Jakadan Nigeria ya ce "Zaki iya Majeederh, Malamin daya baki ilimi ya shaida hakan, mahaifinki
ya shaida" Muryata na rawa ta ce "Duk duniya fa? Ba zan iya ba please a sauya wata" Ta faɗa
a shagwaɓe Ajlaal Sultaan ya ɗago kansa dake naɗe da hirami ya ɗan kalleta kana ya taɓe baki
yaci gaba da abin da yake. "Ki nutsu wannan dama ce da ba kowa Allah ke bashi ba, abin
alfahari ne ko da baki nasara ba ace kina cikin jerin Ɗaliban da suka shiga, Nijeriya yanzu ke ya
zubawa idanu, jikarki, unguwarku, Malaminki, mahaifinki ke ce hope ɗin su, sun yarda dake don
haka ki basu mamaki" Majeederh ta yi shiru ta ce "Ina tsoran rashin nasara" Wani dake zaune
ya ce "Good, than sai ki miƙe ki tashi tsaye ki saka yaƙini sai Ubangiji ya tabbatar, kuma sai nan
da wata biyar za ayi kafin nan kin samu hurarwa" Ta ƙara yin shiru tabbas dama ce a gare ta ta
bawa Abbu abin da yake buƙata.
"Zan yi" Suka sauke ajjiyar zuciya kana suka sanya mata albarka ta miƙe a hankali ta fice Ajlaal
ya ɗan saci kallonta yana ɗauke ido.
Tun daga ranar Majeederh bata da lokacin kanta, manyan malamai suka sanyata a gaba, karatu
safe, rana, dare. Daman tuni haddar Alkur'ani sittin ɗin suna zaune a kanta daram, Tajwid da
mukarijin hurum ake tisa mata, da saita ƙira'a daman Ubangiji ya bata murya kamar haihuwar
Larabawa. Ya zamana a tsaye bacci take sbd karatu, Ƙhulud Arzaan ganin Majeederh ya yi
mata wahala idan tana bita da rigima Ajlaal baya ce mata kanzil. Majeederh ta goge harsu
malaman mamaki kawai suke idan tana karatu, hakan ya ƙara sa musu hope mai girma
akanta...
*5 Month later..... The day*
Ranar Musabaƙar Alkur'ani ta ƙasa ya tashi ranar watan tafiyar alhazzai, watan zul-hajj. Tun
ana sati ɗaya gabaɗaya Ɗaliban ko wacce ƙasa ta Muslunci suka sauka a ƙasar Misira, daga
nan kuma manyan mutane, shugaban ƙasar ko wacce ƙasa, da gwamnoni, hatta Sarkin
Saudiyya Sarki Sultaan ya halaccin Misira ana kwana ɗaya da shi da Mahaifiyarsa Zaytoon,
hadda. Babban hall ɗin ya cika da jama'a fal, ƙabila da yare daban daban farar fata da ɓaka,
jami'an tsaro kamar me. Saura minti ashirin a fara Ɗaliban duk suka shigo ko wanne da
tambarin ƙasar shi a jikinsa, kowa aka nuna masa wajan zama kana zama computer zata nuna
sunanka da kuma ƙasar da kake, gabaɗaya kuma ya kasance mata ke namiji ɗaya ne daga
Qatar. Majeederh kanta a ƙasa sbd jiri da faɗuwar gaban dake riskarta na rashin sanin su waye
a wajan. Zagaye biyar ne masu zafi, da kayi kuskure Computer zata tsayar da kai. Aka fara da
ƙasar Saudiyya ta tayi karatu yadda ya kamata, a zagaye na huɗu dana biyar ta samu matsala.
Abun kamar abin mamaki Majeederh ce ta zamo ta ƙarshe ma'ana Nigeria, Computer ta nuna
mata farkon shafin suratul Yusuf, kana malamin ya ja.
Kanta a ƙasa ba tayi kuskuren ɗago kan ba, lokacin da tayi Basmala shiru wajan ya ɗauka ya
zamana kamar ba a ji ƙira'ar kowa ba sai nata, sbd zaƙi da sautin muryarta daya zaga ko'ina na
hall ɗin, a tare Sarki Sultaan da Zaytoon suka ɗago kan su, tare da kallon inda Majeederh take
zaune fuska rufe, Zaytoon ya dubi computer gaban Majeed taga ansa. _“Majeederh Abdul'aziz
Khan, from Nigeria”_ Karatu take mai ɗauke da zallar ƙa'idoji na Kur'ani. Tunda ta fara karatun
idanunsa akanta ya kafeta da wani irin rikitaccen kallo yana mamakin yadda a ƙasar su Nigeria
aka samu mai daɗin murya da ilimi kamar Majeederh. Tunda ta fara karatun babu gyara ko tuni,
waƙafi, aya ko wasali har zuwa zagayen ƙarshe. Computer ta nuna mata Suratul Maryam
tsakiyar surah. Cikin rashin sa a ta ɗago kanta da nufin sauke numfashi nan take komai nata ya
kunce dalilin ganin dubban jama'ar da suke gabanta tare da kallonta suna kuma saurarenta. Ai
gabaɗaya neman duk haddar Alkur'anin dake kanta tayi ta rasa kaf, a tare kuma Aliyu-haydar,
Captain Alpha, Prince Ajlaal Sultaan da wani matashi dake kusa da Gwamnan jihar Kano suka
ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!....
MIJIN MALAMA
Paid book
08119237616
ALLAH ya nuna mana ranar Monday Monday Lafiya.... Have a nice weekend29
Da sauri Aliyu ya juya tare da fita daga hall ɗin, Alpha ya harɗe hannu a ƙirji zuciyarsa na
harbawa, Ajlaal Sultaan kowa numfashi ya sauke yana mai lafewa a bayan matarsa tunani fal a
zuciyarsa, kyakkyawan matashin dake zaune kusa da Gwamna ya runtse idanunsa. Tsoro da
fargaba ya cika zuciyar ko wanne haifaffen ɗan Nijeriya dake zaune a hall ɗin. Idanun dubban
jama'ar wajan ya sauka akan Majeederh da jikinta ya fara rawa ƙwaƙwalwarta ta tsaya cak
kamar wacce akaiwa formatting. Malaman da suke lura da musabaƙar suka dinga kallon
Majeederh cike da mamaki da tu'ajujji tunda ta fara babu gyaran da akai mata, babu shakka
mu'ujizarsa Alkur'ani ce ta sauka akanta, hakan ya sa ta mancewa komai. A hankali ta kifa
kanta cikin rauni ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ubangiji ka taimakeni kada na kunyata a
idanun ƴan ƙasata" Da sauri wani malami ya yi mata alama data ɗauki ruwa ta sha, kasa yin
musu ta yi ta ɗauki ruwan ta sha ta cikin liƙab ɗin fuskarta, a daidai lokacin kuma computer ta
Kaɗa wanda yake alamanta mata cewa ta fita daga cikin lokacinta. Jikinta jama'ar wajan duk ya
yi sanyi domin kowa ya ƙaddara Majeederh matsayin wacce za ta yi nasara ganin har zuwa
zagaye na biyar ɗin ba a cita gyara ba, makinta ya fi na kowa saɓanin sauran da duk zagaye aci
su gyara wajan biyu ko uku. Akai sanarwar tafiya break bayan an dawo za ayi Finally round
wanda shi ne zagaye mafi wahala aka umarci gabaɗaya ɗaliban da suje su sha ruwa su huta.
A sanyaye Majeederh ta tashi juwa na ɗaukanta Ƙhulud na ganin haka ta miƙe cikin sauri ta
ƙarasa ta ce "Mu je ki huta" Majeederh ta tsorawa Ƙhulud Arzaan idanu kasa magana tayi sai
jikin Ƙhulud data faɗa ta ƙanƙame tana sauke numfashi, da ace taga idanun wani ahhali nata da
babu shakka ta ji sauƙin abinda take ji a zuciya, amma ƙaddara ce haka babu kowa nata a
wajan da zata iya raɓar shi ta ji sanyi. "Ba zan iya fa, I alrdy told them"
Ƙhulud ta ce "Zaki iya, kina da cikakken lokaci"
Ta faɗa tana rungume Majeederh. Daga gefe suka ji an ce "Daman dai Nijeriya ai ta saba
samun failing, bata taɓa winning ba ko sau ɗaya, babbar matsalar sun ɗauki daƙiƙiya matsayin
wacce zata wakilce su" Ya taɓe baki ya ce "Goodness, please Maa step down for Juwaira ki
barwa Qatar domin baki da ilimin cin gasar Alkur'ani ta duniya, actually baki da shi, baki
cancanta ba"
Ba Majeederh ba, hatta Ƙhulud ta girgiza da jin maganar kai tsaye ta fahimci mamallakin muryar
ta juya suka haɗa idanu da Ajlaal ta ce
"Kalb, Majeederh ce fa? Ita ce Daƙiƙiya?? Duk ciki ita kaɗai ce ba aiwa gyara ba, me ya sa?"
Ajlaal idanunsa akan Majeederh da kanta ke ƙasa ya fahimci yadda maganarsa ta yi tasiri a
zuciyarsa musamman da yaga jikinta na rawa
"Ita fa, ni muryarta ce ma ta firgitar dani wallahi, karatu sakaka kamar zubar ruwan sama,
Asstagafirullah gaskiya Nijeriya akwai saura gashi sun saka hope kuma za su yi failing" Ajlaal
Sultaan ya sake faɗa yana lumshe idanu. Ƙhulud ta kafe shi da idanu ta kasa fahimta
yanayinsa, bata taɓa jin ya yi magana mai tsayin haka ba, a rarrabe yake yinta. "Me ta yi maka
da zaka jefe ta da wannan maganar Ajlaal Sultaan? Da zaka wulaƙanta ta?" Ya watsa hannu
irin ko a jikinsa ya ce "I don't know what comes over me, amma na ji kamar bata yi mini ba, ina
bala'in son mace mai tsayawa akan nasara wacce bata yarda da faɗuwa ba, Sorry Nigeria" Ya
yi gaba
"Meke damun Ajlaal?" Ƙhulud ta furta tana binsa da kallo ganin yadda yake tafiya kamar bai so.
Majeederh kasa motsi ta yi maganganun Ajlaal suka zauna daram a zuciyarta tare da yi mata
amsa kuwwa! Ta ji jarumta ya zo mata, komai na kanta ya dawo fresh, Ƙhulud za ta yi magana
Majeederh ta girgiza kai tana ɗan yi murmushi "Babu komai" Majeederh ta faɗa a taushashe tana nufar wani corridor, duk abinda yake faruwa akan idanun
Captain Alpha daya jingina yana kuma jin komai deep down na zuciyarsa godiya yakewa Ajlaal
yasan Majeederh ta tsani ace bata da ilimi ko a jefata da kalmar _“Kasawa”_ Ya yi murmushi
kawai yana ɗauke kansa gefe guda. Majeederh ta buɗe bottle water mai sanyi ta shanye tas, a
hankali ta shiga safa da marwa idanunta rufe, idan ta ja numfashi sai ta sauke. Tana tsaye Wani
malami ya ce "Ki nutsu, tunda kin fahimci weakness na ki sai ki kiyaye kallon mutane, mu je
lokaci ya yi" Ta jinjina kai har yanzu idanunta rufe yana gaba tana binsa a baya. Cikar da hall
ɗin ya yi har yafi na baya, kanta a ƙasa ta nemi wajan zamanta a hankali girgiza cinyarta
idanunta rufe. Rabin jama'ar wajan idanunsa yana kanta mamakin yadda sauran ɗaliban aka
rufesu malamai da jagororin ƙasar su, ita kuma ba kowa. Ɗaya bayan ɗaya aka fara gabatar da
final round babu ƙasar data tsallake sai da suka sha gyara, gyara kuma na ban mamaki har aka
zagayo kan Majeederh. Ta runtse idanu jin computer na gabanta ya yi ƙara kafin ta ji computer
ta ce. "الله"
"Ma hukumu?" Ma'ana hukuncin kalmar Allahu.
Ta sauke ajjiyar zuciya a taushashe cikin sanyin murya mai daɗi ta ce
"Tafkimun laámun ismul jalala" Computer ta nuna blue alamar “Mumtaz" ta yi daidai aka ci-gaba
da yi mata tambayoyi na Alkur'ani kafin daga bisani aja mata aya
“Allah taziru waá zirataán uƙƙurrah" Ba sunan sura ba number aya kawai ita ce zatai tunanin
wacce surah ce. Ta yi shiru ta rufe Idanunta tare da dunƙule hannu exlty yadda take yi idan tana
haddar Alkur'ani.
Ajlaal dake hakimce saman kyakkyawar kujera ya zubawa Majeederh Idanu, haka Aliyu da
shigowar shi kenan sai Alpha daya kasa Kallonta, matashin saurayi kuma ƙanƙame jikinsa ya yi
waje guda.... Daga can ƙasa Nijeriya gabaɗaya Khan family ne zaune a babban parlourn gidan
Uncle Isma'il, sun tisa plasma a gaba tsoro ya cika zuciyar kowa musamman Abbu. Ba iya Khan
family ba duk wani gida idan ka shiga kallon musaɓar suke live, wanda basu da t.v a rediyo
suke saurara. Abbu ya saka hannu ya share zufar data gangaro masa, ya kasa zama waje guda
ya gama tsara plan ɗin yadda zai yi da duk wata kyauta da kuɗin da Majeederh ta samu, amma
da alama yarinyar baƙin ciki take masa yana da tabbacin ta iya mugunta ce kawai. Ba zai iya
zama ya ji wannan abun ba ya nufi hanyar fita daga parlourn daidai nan ya ji sautin saukar
muryarta a cikin kunnenshi wacce ta wadatu da zallar ƙira'a Tajwid mukarijil hurum, ta fitar da
komai da karatun Alkur'ani yake buƙata ta saka komai cikin muhallinta. Cak Abbu ya tsaya yana
washe baki farin ciki fal zuciyarsa. Uncle Isma'il, Uncle Isma'il Bello, Maman Alpha, Anti, Mami,
Aaliyyah, Ruma, Raihana, Widad, Innati... E.t.c suka sanya kabbara.
Wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Ajlaal Sultaan ya sauke yana tasbihi a ransa, Aliyu ya yi ƙasa da
kansa hall ɗin tsit sautin ƙira'arta ne kawai yake tashi har computer ta tsayar da ita alamun
lokaci ya yi. Lokacin daya shiga cikin kundin dairy ɗin Majeederh Abdul'aziz Khan, ta kasa tashi
a hankali ta durƙoshe a wajan jikinta na ɓari rawa da ƙyarma wani irin raunataccen kuka ya
ƙwace mata lokacin da alƙalai suka tabbatar da Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Matsayin
wacce ta zama Gwarzuwa a jerin ɗalibai sama da 100 wanda yake nufin Nigeria ta ƙwace
kambon tarihi daga hannun Ƙasar Misira wanda sune su kai na ɗaya a shekarar data gabata.
Shugaban ƙasar Nijeriya riƙe kai ya yi ashe kafin ya sauka da rabon a teniwarsa uwa Nigeria
zata amsa wannan kambon? Sauran gwamnoni suka miƙe lokaci guda hadda gwamnan Kano
suka shiga ɗaga hannu da kabbara, da sarkin Misira dana Saudiyya Sarki Sultaan suka nufi
inda Majeederh Abdul'aziz Khan take durƙoshe, Zaytoon ta saka hannu ta ɗagota tare da
jawota ta rungume tana cewa
"Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar ma sha Allah" Majeederh daman waje take nema
domin ta kasa believing na nasarar data samu, ta ƙanƙame Zaytoon tana sakin wani
mahaukacin kuka, She just wished that her parents were here to see her suga nasarar data
samu, musamman Abbu burinsa ya fara cika. Ƴan jaridu gidan t.v da rediyo sukai kan
Majeederh ɗaukarta suke ta ko'ina, lokacin da aka ɗauki wata farar hula ta silver aka saka mata
tare da ɗaukan wani abu mai kama da Award na zallar tagulla aka bata wanda ya biyo ta
hannun Sarki Sultaan, yin duniya ta cire liƙab ɗin taƙi haka aka dinga yi mata photo wanda kai
tsaye ake watsa su a duniya, wasu mahaukatan kuɗi aka bata wanda ita kanta ba zata ce ga
adadin su domin hankalinta baya kai tunaninta yana ga mahaifinta. Aka rataya mata sarƙa gold
daga nan aka dinga mata kyauta wannan gwamna ya ce ya bata kaza wannan ya ce ya bata
kaza, Shugaban ƙasar Nijeriya har yanzu kasa tantance me zai bata matsayin kyauta, duk
abinda ya yi tunani sai yaga ya yi kaɗan. Kyautar kujerar Umara data hajji aka bata sarkin
Makka ya ƙara bata kyautar kujerar hajji. Kana aka dinga photo lokacin da aka sanya mata
albarka bata san mene ya faru ba, Majeederh ta samu kanta da wani irin jin girma wani abu mai
girma ya hau kanta daga nan taro ya watse sai walimar da za ayi da daddare. Ƙhulud ta
rungume Majeederh tana kuka murmushi kawai Majeederh ta yi tare da bubbuga bayanta a
hankali ta ce "Ina mijinki?"
"Yana wajan takawa" cewar Ƙhulud, Majeederh ta ce "Rakani" Da sauri Ƙhulud ta kama hannun
Majeederh suka isa wajan Ajlaal na tsaya rungume da Zaytoon da yake tsokanarta Majeederh
ta tsaya kanta a ƙasa Zaytoon ta ce
"Ba dai ita ce wacce kike bani labari ba?"
“.... Ita ce Grandma”
"Ma sha Allah, na yi farin ciki ina alfahari dake da ƙasarku" Murmushi Majeederh ta yi ta ce "Na
gode Mama" Zaytoon ta ce "Laa, wacce irin Mama bayan zan iya jika dake?" Ta yi murmushi
kawai Ajlaal dai yana lafe da bayan Zaytoon ya kasa Kallon Majeederh ya ji ta ce "Thank you"
"For?" Ajlaal ya tambaya yana gyara tsaiwa ta ce "Kai ne ka ƙarfafa mini qiwwa na kasa mance
kalmar Daƙiƙiya" Ajlaal ya ɗan shafa gemunsa ya ce "Congratulations"
Yana faɗin hakan ya bar wajan. Bayan sun fito tana ƙoƙarin shiga mota domin komawa gidansu
ta ji ance "Hawwa'u"
Cak ta