Showing 18001 words to 21000 words out of 126765 words

Chapter 7 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf

kenan?" Idanunsa akan ƙofar toilet ya ce
"Daman ai bance Mahaukaci ba ne ni, let me warn you kada ka takura kada ka matsanta,kada
ka zurfafa domin You can take it"
"I love her" cewar Abu-turab.. "I am the one who raped her" Abraham ya bashi amsa, yana
matsowa dab da shi.
"Zan iya komai a kanta" Wani irin murmushin mugunta Bad boy ya yi kafin ya ce.
"Ita ne dalilin ya sa aka kai ni gidan mahaukata"
Abu-turab ya faÉ—a shi ma yana matsowa wajan Abraham suka haÉ—e ko wannensu yana huci.
"Mara tsafta, wanda ya dulmiyya cikin yadanci ha zai taɓa samun Malama Majeederh ba"
Wata dariya sosai Abraham ya yi yana É—ora hannunsa a shoulder ta Abuturab ya ce.
"Ƙarshen samu ni na amshi budurcinta, na ɗauka abinda nake kwaɗayi ne sai dai ko mintuna
arba'in ba ayi ba na fahimci ba budurcinta nake so ba,I want to end my life with her, I want to
take my last breath on her shoulder,I lived with her love, I will die on her lap with a smile on my
face" Abraham ya faɗa a hargitse. Abu-turab ya ce "Idan ka dauwama a gidan yari har ƙarshen
rayuwarka, sai mu gani ko zaka sameta"
"Kai ka ke tsoron prison, ka duba record, da report na Abraham Daniel David ni criminal nan"
Abu-turab ya É—aga hannu zai mari Abraham kafin His Excellency ya sauke hannun ji ka ke
ƙasss! Abraham ya ƙarya hannun. Wata ƙara ya saki da sauri kuma ya danna wani abu daman
Hammad na waje don kada ya shigo ne, yana jin ƙarar ya shigo da sauri ganin Abraham ya sa
ya ja da baya. Securities É—in da suke cikin gidan gabaÉ—aya suka shigo part É—in Malama Majeederh daidai
lokacin itama ta fito Idanunta jajir da alama ta saurari komai dake faruwa.
Zufa ce ta dinga yankowa Abu-turab, Majeederh ta tsaya tana kallon Abraham day taso ya
tsaya a gaban baki ya buÉ—e ya ce.
"Malumana, shi ne....,"
Marin data sauke masa yasa ya kasa magana, ta ƙara sauke masa.
"Ka tarwatsa mini farin cikina, jin daÉ—ina kwanciyar hankalina, ka rabani da iyayena i hate you"
Abraham ya zare ido domin shi ya ɗauka for now bashi da wani laifi, idan har ta karanta saƙon
daya bari before he leave the country.
"Na raineka da hannuna, na baka kulawa kamar yaron dana haifa,daga baya na rasa ka, nayi
kuka na shiga damuwa, ban cancanci haka ba, kaci zarafina ka ci mutumcin addinina, ban san
ya akai hakan ta faru ba amma zan so ka bayyanawa duniya gaskiya domin na samu sassauci,
Abraham Daniel David...". Ta ɗauke kai shi dai yana tsaye gabanta kamar idanunsa za su faɗo ƙasa, yadda ƙirjinsa ke
É—agawa kai sai sanya a gane zafi da tasirin maganganunta a zuciyarsa.
"Allah ya isa, na tsaneka adadin tsanar da mahaifina ya yi mini zan so ka samu tabbataccen
taɓin hankali na har abada" sai a lokacin Abu-turab ya zo ya kifawa Abraham mari amma ko
motsawa bai ba Malama Majeederh kawai yake kallo.
"Ku kakkarya mini shi a kuma kai shi prison har ending rayuwarsa"
Securities suka rufe Abraham da duka ta ko'ina da ƙasan bindiga. Da ace babu Majeederh
wajan ko kalamanta ba su yi tasiri a zuciyarsa ba da tuni dambe ake da shi. Ana dukansa yana

kallonta. Ya miƙe tsaye tare da ɗaukan hijabinta yaje har gabanta ya sanya mata, shi kansa bai
san dalilin sanya mata hijabin ba, amma yana lura da idanun Abu-turab akanta. Wani securities
ya sakarwa Abraham ƙasan bindiga akansa nan take kan ya fashe, Majeederh ta runtse
Idanunta. Daidai kunnenta ya ce.
"Jee kin jima da sanin Abraham baya giving up, azabar nan babu inda zata, idan baki yafe mini
mun daidaita har mun yi aure babu shakka zan baki ciki na biyu, i don't care" "take him out"
Cewar Abu-turab, Hammad tausayin Abraham ne ya kama shi.
Da ƙyar yake jan numfashi sbd wahala amma bai fasa kallonta ba, har suka isa bakin ƙofa za su
fitar da shi idanunsa ya kawo ruwa sai kuma ya yi dry domin ya hango rauni a cikin idanunta
kawai bata sani ba ne, da ƙarfi ya ce
"I love you Malumana, I'll be back"

Not editing.
Littafin MIJIN MALAMA na kuÉ—i ne, kuyi magana a wannan number domin biyan kuÉ—in
08119237616... Na kusa gama free pages



*Ina Mata 'yan gayu masu son kayan gayu kuzo ga dama ta samu*. _BY JAY_ *ta kawo maku
Kayan masu kyau da inganci indai mace tasan gayu to* _BY JAY_ *ne gurin siyayyar ta.*
We have
*Laces* _(Dubai laces, london laces, Switzerland laces,)_ dan uban su
*Atampha of all kinds*
*Veils*
*shadda*
*shoes*
*qualitative handbags*
*Jewelries* etc
Abun sha’awa ana shine Kayan mu ba a jikin kowa zaku gansu ba dan kaya ne unique na mata
yan gayu da suka san kan gayu ku dai kawai ku mana magana ta Wannan no din
*09060450181*
Ko kuma ku danna Wannan link din domin samun damar ganin kayan mu

https://chat.whatsapp.com/IBD74Cka3X2E2AqZyg0Nfo*🌈MIJIN MALAMA🌈*

Nimcyluv Sarauta
*9......*
Yadda suka ɗaure Abraham a jikin sarƙa zaka ɗauka wani tantirin ɗan fashi ne ko kidnaper, ko
irin mutanen nan masu muyagon harƙalloli. Suna zuwa suka cilla shi a mota tare da yiwa motar
key.
"Ku daka ta" P.a Hammad ya faɗa yana ƙara sawa inda suke ya dubi Abraham wanda kansa
yake sunkuye jini ya ɓata masa fuska.

"Mene matsayina?" Kai tsaye Captain ya ce "Kai P.a ne a wajan His Excellency" Hammad ya
jinjina kai ya ce "Good, kamar matsayin P.a ya fi na mataimakin Gwamna, idan ya tabbata haka
ne la shakka zaku bi nawa umarnin" suka kalli juna
cikin kuma rashin fahimta Captain ya ce
"Me kake buƙata?"
Ya ce "Ku kai Abraham gidana, ya zama sirri ni da ku kada ku kuskura akai shi Prison idan ba
haka ba, ku ne zaku tabbata a can har ƙarshen rayuwa"
"Cin amana?" "Shi ma ita ya yi" cewar Hammad. Captain ya ce "I can't, dole mu kaisa prison
kamar yadda ya umarta"
"Nawa ya baku?"
"Mu ai ma'aikatan gwamnati ne, wannan shi ne aikinmu" Hammad ya yi murmushi mai kyau
kafin ya ce "Mu ne Gwamnati ai, baka san inda rana zata faÉ—i ba gobe" "Kowa ya san ta yamma
take faÉ—uwa" Captain ya tari numfashin Hammad da faÉ—in hakan.
"Zan baka 10Ms, zan faÉ—a maka yadda za kayi" ya yi shiru alamar tunani kafin ya ce "Sauran
securities É—in fa?" Hammad ya watsa hannu ya ce "ÆŠauke shi, lokacin ya fara" Captain ya dubi
abokan aikin nasa, ganin sun yi nesa da su hakan ya tabbatar ba su ji abinda suke tattaunawa
ba. Tunaninsa ya rabo gida biyu shin ya amshi kuÉ—in? Idan ya amsa kuma ya ci amanar
Gwamnansa, da ƙasar shi da kuma aikinsa. Amma miliyan Goma ai ba nan ba ce, babu wanda
kuma zai sani.
Ya shiga motar, sauran securities ɗin ma haka kai tsaye suka fita daga cikin keɓantaccen gidan
na His Excellency Abu-turab.
Hammad ya yi murmushi a fili ya ce "Kaci amnar maci amana kamar babu laifi? Ba zan jure
ganin hakan ba, am sorry Best friend"
Abu-turab ya na tsaye da hannunsa wanda aka karya ya dubi Majeederh dake zaune tayi shiru
ta sanya hannunta tsakanin cinyoyinta hakan na nufin tunaninta ya girmama har ya kasa
ɗaukan ƙwaƙwalwarta. Abu biyu ya fi tsaya mata, kalaman mahaifinta Abbu, da kuma kalmar
Abraham "I am the who raped her" hakan na nufin Abraham yaga surarta na É—iya mace? Ya
gama kallonta. Ta rutse idanu tana kiran sunan ALLAH. Yaron cikinta? ÆŠan data raina? Ya yi
mata FyaÉ—e? Ya samar da cikin Khalil, ta ya ya hakan ya faru? Rabonta da shi shekara biyu,
shin ciki yana shekara biyu ne? Ya akai har ya yi mata FyaÉ—e bata sani ba? Yaushe hakan ta
faru.
"Jiddo" Abu-turab ya kirata a ruÉ—e ganin yadda jikinta ke rawa kamar wacce take shirin yin
jijjiga. "Ka da ki sawa kan ki damuwa wani ciwon ya kama ki, don Allah Jiddo listen to me ki bani
dama, ki bani dama just one chance, please Jiddo Give me one chance"
Ta É—ago kai a nutse ta faÉ—aÉ—a kyakkyawar fuskarta speaking calmly ta ce "Your Excellency"
"Yes, Jiddo"
"Don Allah ka bani waje" ta faɗa murya can ƙasa idanunta na lumshewa.
Ya jinjina kai ya ce
"Zan fita,idan zaki farin ciki" yana faɗin haka ya yi waje yana zuwa wajan ƙofa ya juya ya kalleta
sai kawai ya fice yana rufe ƙofar bedroom ɗin. Yana fita ta zame ƙasan lallausan carpet na
ɗakin, zuciyarta tayi mata zafi ƙirjinta na ɗagawa sama. Tsoron t ɗaya kada bakin mahaifinta ya
kamata ya sanya ta lalace kum ta bi duniya kamar yadda kalamansa suka bayyana haka, mene
ya sa ya kasa yarda da ita ya kasa fahimtar ba zata taɓa aikata zina ba, ya kasa amincewa

ƙaddara ce ta faɗa mata.
Kuka take son yi ku zuciyarta za tayi mata sanyi amma ta kasa sai ma wani abu daya tsaya
mata a ƙasan maƙoshi da ƙyar take jan numfashi. A raunace ta ɗaga kai sama ta ce
"Allah na gode maka, Allah na gode maka da wannan jarrabawa, yadda kayo ni a Musulma mai
yadda da ƙaddara Ubangiji ka sanya na cinye wannan ƙaddarar, zuciyata ta kasa jurewa Allah
kai kasan abinda yake ɓoye Ubangiji idan rayuwata a wannan duniyar shi ne alheri ka tabbatar
dani a raye ka bani haƙurin jure ƙalubalen cikinta, idan mutuwata ita ce hutu a gareni Ya Allah
ka É—auki raina a wannan lokacin, ka yafe mini kurakuraina ka kula mini da abinda na haifa" Ta
rufe idanu tana ƙanƙame jikinta tana jan numfashi da ƙyar ta ce
"Asstagafirullah Ya Allah, Asstagafirullah, Asstagafirullah Ubangiji kana kallo,kana ji, kana gani
albarkacin imanin da nayi da kai, albarkacin kare addininka da nayi, Ya Allah ka bani haƙuri
kwatankwacin haƙurin da Annabi Luɗ ya yi da mutanensa, ka bani ikon jure yanayin rayuwa
kwatankwacin juriyar da Annabi Yusuf ya yi, Allah ka bani ƙarfin zuciya wacce zan fuskanci ko
wanne ƙalubale, kwatankwacin Yadda ka bawa Annabi Sulaiman ƙarfi ikon, Allah ka kula dani
kwatankwacin kulawar daka bawa Annabi Musa a cikin gidan Fir'auna... Ya Allah
Asstagafirullah!"
Jira take taga ta inda mutuwarta zata fara, amma shiru hakan na nufin rayuwata ita ce alheri a
gareta.
Abu-turab na zaune ƙasan carpet ya sanya Mama a gaba hannunsa naɗe da bandeji cikin
kulawa ta ce "Abu-turab me ka ke so?"
"Majeederh nake so Mama" ta ce "Nemi Soyayyarta idan ta amince ba zan hana ba"
Ya yi shiru ta ce "Idan baka da abun faÉ—a jeka, ka sani a gaba" ya kalleta ya ce "Kamar ba zata
amince ba" Mama ta dube shi sosai tana duba yanayinsa ta ce
"Idan har baka sanya son zuciya cikin lamarinka ba babu shakka zata amince, ka yarda da kan
ka shi ne kawai" tana kallon T.v ta ce
"fight for the truth, fight for your love, idan har ka faÉ—a mata wahalar daka sha akanta Majeederh
zata ji tausayinka, sai dai bana son ta aureka don jin tausayi sai don cewa tana Son ka"
"Tausayi yana zama so"
"Inji ku Hausa ba, babban kuskuren da kuke kenan, gurbin tausayi daban na So daban go and
search"
"Mama please ki....,"
Cikin faɗa ta ce "Abu-turab ba zan tilasta ƴar mutane ba, fita ka bani waje" ya miƙe jiki a
sanyaye yabar bedroom É—in, Jidda na nufar inda yake ya daka mata tsawa. Mama ta ce "Na
gode Allah tunda Æ´arka ce" yarinyar ta fashe da kuka sosai da gudu kuma ta nufi bedroom É—in
Majeederh ta sameta zaune inda take.. "Mami" Majeederh ta zubawa yarinyar idanu sai ta É—an saki fuska ta ce "Call me Jidda"
"Dady ya ce Mami" Majeederh ta jingina da bed ta kallon yarinyar sosai tayi kama da
mahaifinta. Jidda ta ce
"Ina son Daddy, kema kina son shi?" Majeederh shiru ba amsa ta ƙara cewa "Zaki zama
Mamina?" Sai a lokacin ta ce "Ai ni Mamin kowa ce come here"
Barrister na zaune looking so worries ya ƙara ramewa ya yi baƙi kamar ba kyakkyawan
matashin nan ba mai jini a jika. "Aliyu Meke damunka?" Ya dubi Hajia ya ce "Me kika gani
Hajia?" Ta haÉ—e rai sosai ta ce "Why are you asking my question with a question?"

"ÆŠan Najeriya ne fa?" Almustapha ya bada amsa yana hararar Bar Aliyu Sufyan Alhassan.
"Lafiya nake" "ƙarya ka ke, na san halinka dole da abinda yake damunka" Aliyu ya rasa me zai
ce, ya faÉ—awa mahaifiyarsa damuwarsa tamkar ya tona sirrin aurensa ne, kuma zata tsani
Matarsa Latifa Omar, amma seriously yana cikin damuwa ya mance when last da ya yi
mu'amalar aure da Latifa, ya manta rabon da ya ji ƙamshin girkinta kullum abinci da ƙauri ya
manta rabon da yag kitso a kanta, ya mance rabon da ya ji kalmar adawo lafiya daga bakinta.
Yana buƙatar kasance da matarsa haƙurinsa ya fara gazawa.
Ya riƙe kansa, da mutuncinsa sbd gudun faɗawa halaka, amma irin su Latifa sune suke sanya
maza neman mata da aikata zina.
"Ni banga abinda ka rasa a gidanka ba, amma ka sanya wa kanka damuwa akan wata Æ´ar iska
haba Aliyu" Barrister ya kalli Almustapha ya ce
"Mai É—aki ai shi yasan inda yake masa yoyo, ba zan hana ka aibata Majeederh ba amma ba
kowa ake halinsa ba" Almustapha ya kalli Aliyu sai kawai ya miƙe tsaye. A tare suka fice daga
cikin gidan nasu, Bar Aliyu ya yi Lodge Road wanda dalilin Majeederh ya kama haya a
unhwhaty, shi ma Almustapha ya nufi hanyar gidansa. Maimoon na zaune ita da ƙawarta wacce
suke neighbor da ita. "Maimoon kin ji daÉ—i, Allah ya baki miji wanda yake wada taki da komai na
rayuwa" Maimoon tayi dry sosai ta ce "Allah sarki, wallahi bani da matsala da mijina saɓani bai
taɓa haɗani da shi ba, yana da haƙuri sauƙin kai, sometimes na fisa rikici ma, gaskiya samun
miji kamar Almustapha da wahala, yana da kare hakƙin aure da nasa, kullum cikin kyautatawa
iyalansa yake" Maryam tayi murmushi ta ce
"To Allah ya bamu irin taki" "Haba ya bawa Æ´an gaba dai, ke kina É—akin mijinki ai ki ce kawai
Allahamdulillah,kin san duk wani kwanciyar hankalin aure shi samun daidaito tsakanin
ma'aurata, yarda da juna, haƙuri, tausayi. Ni kam i trust my husband" Shira suka ci gaba da yi.
Suna zaune Maimoon ta ji anyi horn ta miƙe da sauri ta ce "To ga ɗan halak nan" Maryam ta ce
"A'a zama bai ganni ba, lemme have my way" sukai dry kana sukai sallama.
Maryam na fita compound na gidan Almustapha na fitowa ya dinga kallonta domin bai taɓa
ganinta ba. Ya shafa kai lokacin da take cewa "Sannu da zuwa"
"Thank you, can i know you?" Ta ce "Matar maƙocinka ce Habib"
"Oh, you're too beautiful" Mamaki ya kama Maryam sai tayi É—an murmushi ta ce "Harna kai
Matarka Maimoon?" Ya yi murmushi yana kashe mata idanu guda ya ce "Haba waccar
Dabbar?" Maryam ta zare ido ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un Matarka ka ke kira da
Dabba?" Ya watsa hannu ya ce "Yes, Kinga bani number ki please" Number ta bashi ta shige
tana KaÉ—a masa jiki, ji ya yi kamar ya bi bayanta domin ya tabbatar mijinta baya gari.
Cikin dare Abu-turab na zaune ya samu sanarwar gaggawa an samu motar jami'an tsaron shi a
wani gefen hanya, gabaÉ—aya jami'an sun mutu guda É—aya ya yi saura Captain shi ma yana
gadon asibiti. Misalin 2 na dare Uncle Isma'il na harabar gidansa yana duba jaridar ranar inda
yake ganin cewa Governor yana asibitin Cameron domin duba lafiyar shi, kamar yadda aka
samu sanarwar ta bakin mai kula da lafiyarsa. Ji ya yi an tsaya gabansa ya miƙe da sauri da
ƙarfi ya ce "Abraham innalillahi,mene ya sameka...

MIJIN MALAMA
Book1 500
Book2 500

Mutum zai iya biyan book1 kafin a fara book2... Idan kuma yana da hali zai iya biyan 1k É—in
bakiɗaya. 08119237616 kuyi magana ta nan.*🌈MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv sarauta
*10...…*

Masu Arewabooks follow my account👇🏾 akwai gift ga wanda suka fi kowa share da comments
acan
https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv


Abraham ya zube gaban Uncle Isma'il ya ce "I want to convert to Islam, I want to become a
Muslim, how much will I give" Uncle Isma'il da mamaki yake kallon Abraham É—in, Yaushe ya
dawo? Mene ya same shi yaga jikinsa da wannan raunin? Mene ya ja hankalin shi zuwa ga
addinin Musulunci duk da sauri irin na mahaifinsa Denial, duk da kasancewar Kakansa Pasto a
church É—in da tafi ko wacce girma.
"Lafiyarka É—aya? Mene yaja hankalinka zuwa ga Musulunci? Yaushe ka dawo?" Uncle Isma'il ya
jerawa Abraham tambayoyin cike da mamakin domin kansa ya riga cushe. Abraham ya kasa
cewa komai domin bashi da kalaman da za su iya fahimtar da Uncle halin da yake ciki,
But speaking the truth, he wants to be a complete, pure Muslim. Na gartaccen mutum mai
tsafta. Al'amarin daya wakana akan idanunsa sun bashi malam tsoro da tu'ajujji wani abu mai
sunun tsoro Abraham bai sani ba. that is the first way he will take to surprise Majeederh.
Uncle ya kalli ko'ina kafin ya tattausa murya ya ce
"Ka bari zuwa gobe sai muyi magana mu shiga ciki" Sai a lokacin cikin gurɓatacciyar Hausar shi
ya ce "Uncly, Jee"
"Jee?" Uncle Isma'il ya maimaita kenan bai mance da ita ba?
"Abraham Maminka Majeederh bamu san inda take ba, we lost her" Ya faÉ—a cikin damuwa.
Abraham ya É—ago kansa tare da saka hannunsa ya dafa cinyoyin Uncle Isma'il ya ce
"She slapped me, insulted me, said she hates me, babu ni rayuwarta abada" Baki sake Uncle
Isma'il ya ce
"Ita Majeederh? Wait a ina ma ka ganta? Mene ya sanya harta mareka?" Ya É—aga gajiyayyun
idanunsa wanda babu ladama ko kaÉ—an a cikin su ya ce "Tana wajan Governor na garin, his
prvt

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login