Showing 111001 words to 114000 words out of 126765 words

Chapter 38 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf

numfasa cikin dabara ta ce "Ka taɓa ganin ayi aure ba a san mutum ba? Iyaye
family e.t.c?" A hankali ya ce "Me kike son sani a kaina?" Ta ce "Ur Father, country da sunan
mahaifiya" Murmushi kawai taga ya yi, tare da yin baya ya kwantar da kansa yana rufe idanun,
bottle ɗin hannunsa ya matse nan take ta fashe juice ɗin ya zube hannunsa ya fara zubar da
jini. "Khalil" ya yi mata shiru tana danne tsoranta ta ce "Abraham" Idanunsa ya buɗe tare da
zuba mata su, wani irin ja taga yayi wanda bata taɓa ganinsa ba, a nan kuma ta ƙara tabbar da
zuciyarsa rauninsa kuma iyayensa. Murmushi taga ya sake yi wanda ya fito da kyansa duk da

baya yanayi na jin daɗi cikin sauyin murya ta ji ya ce "Mother? Uhm" A hankali ya sunkuyar da
kansa ya ce "I don't know her, ban santa ba, she's alive or not I don't know" Kallonsa kawai take
a hankali ya sake cewa "Idan an ce uwa ke nake kallo, kece mace ta farko data kula dani ta
nuna mini soyayya ta uwa, wacce na rayuwa da wannan soyayyar har yanzu, Bayanke maza ne
kawai suke tare dani Gang team ɗin nan su ne ahhalina, ina da 10yrs na gama secondary
school na fara University a wata ƙasa" Ya yi shiru ta ce "Wacce ƙasa?" Calmly ya ce "Germany"
Ta ce "Ohk ina jinka" Ya ƙara lumshe idanunsa wanda duk suka rine ya ce "Daga nan na sauya
University, har dai na kammala" Ta jinjina kai ta ce "Ur Father?? Mahaifinka fa?" Ya ce "I hate
him" Da mamaki ta ce "Why? Me ya sa me ya yi maka?" Murmushi kawai ya yi yaƙi ce mata
komai. Ta ce "Ok Shi ne ya biya maka kuɗin makaranta?" A nan ya yi wata kalar dry sosai yana
girgiza ya ce "Funny, ina yaga kuɗin kai ni Germany? Kuma Karatun Likitanci, Welder fa yake"
shi kansa ya san ya yaudari kansa sai ya ji kansa ya masa girma na ƙaryar da ya yi. Majeederh
ta ce "Kuma ina kai kke samun kuɗi? Me haɗinka da Gang team ɗin nan?" Ƙuri ya yi mata da
idanu ta ji ya saki dry ya ce "you're asking too much, are you trying to change me? use your
chance on me" Ya ƙara yin murmushi kawai idanunsa jajur jijiyoyin kansa duk sun fito kallo
zakai masa kasan ba daɗin hirar yake ji ba, ya watsa hannunsa tare da cusa yatsunsa cikin
suma ya birkitata ya zuba idanu ya ce "You can because I love you, kawai dai Gang team is my
happiness in bani da lafiya sune, suke iya ɗaukan haukana" Idanunta ta ji ya ciko da hawaye
sbd tausayinsa ya yi kamar bai gani ba ya ce "Me kike so?" Ta ce "Bana son Debeka" Da wani
irin sauri ya ɗago ya kalleta bai ce komai ba, ta ce "Bana son Shaye-shaye, yawon banza, kula
matan banza, bana son faɗa da kowa ka koyi controlling kanka, kana zuwa wajan mahaifinka
bana son gajeren wando ka maida hankali akan sana'arka, idan ba wani doke ba bana son
shiga cikin Gang team ɗin nan" Tunda ta fara magana yake kallon bakinta da idanunta ta ce
"Kana jina?" Calmly ya ce "Ohk" A wannan karan da ƙyar muryarsa take fita ta miƙe tsaye zata
ta fi ya bita da idanu ya saka remote ya cire password sai da ta je bakin ƙofa ta ji ya ce "Zan
aureki dole, Abraham baya ƙarya" Da sauri ta fice daga cikin gidan tana sauke numfashi. Akan
idanun Bar Aliyu ta fito da sauri ta shiga motarta tare da yin key, dake ya sauya mota bata sani
ba, kuma bata hayyacinta hakan yasa sam bata gansa ba. Kifa kansa ya yi a kan hannun motar
yana jin zuciyarsa kamar ta fito gabaɗaya ya rasa yadda zai yi da rayuwarsa, he want
Majeederh in his whole life, amma tsoranta yake sauya masa take a ko wanne lokaci, duk
sanda ya yi attempting faɗa mata he loves her sai yaga kamar ba ita ba, nan da nan ransa ya
ɓaci. He couldn't sleep, eat, everything komai nasa ya tsaya ya yi asarar contract da yawan
gaske. Failing a Shari'a ba a magana. A hankali ya kunna motarshi kai tsaye gidansu ya nufa,
lokacin Hajia da Almustapha na zauna a parlour. Tunda ya shigo Hajia ke Kallonsa har ya nemi
waje ya zauna yana mai da numfashi ta kasa daurewa ta ce "Aliyu lafiya?" Ba tare daya buɗe
ido ba ya ce "Good, ina yini Hajia?" Ta yi shiru ta kasa amsawa. Wayarta ta ɗauka ta kira Dije ta
ce "Ki haɗawa Babana abinci yanzu" Dije ta ce "Done Hajia" Ta ɗauke kallonta ga Aliyu ta ce
"Almustapha ya matar taka?" Ya ce "Da tare zamu zo ma, bata jin daɗi ne" Ta ce "Ohk, Allah ya
sauwaƙe" Ya ɗan juya ya ce "Papa fa?" A nutse ta ce "Ya je meeting, kasan an fara
shirye-shiryen tsayar da ɗan takara" El ya ce "Kai, Shi Papa mene haɗin sa da wani takara ne,
ban son ya tsaya wata siyasa wlh" Ta yi Murmushi kawai El ya ƙara cewa "Ohk i understand,
jam'iyyar su ai ke kan mulki a yanzu, baya so mulki ya fita daga hannunsu" Almustapha ya yi
dry ya ce "Kuma wallahi na ji jam'iyyar hamayya da ƙarfinta ta fito, suna da ƴan takarkaru har

biyu dole sai sun yi primary election zaɓen cikin gida kafin fitar da gwani, amma da ina zaɓe
Abuturab zan zaɓa, he's a kind of person that i have never seen before, a dai ƴan siyar nan
tamu, ya taɓa neman takarar ko house of representatives or assembly na manta, yanzu na
kamar ya yi aure wai, amma baya ƙasar jinya yake" Aliyu zancen ya ji yana hawa kansa haka
kurum kuma Abuturab ɗin bai masa ba. Hajia ta ce "To Aku, duk ina kake jin wannan labaran?"
Almustapha ya ce "Hajia media, a twitter a nan nake ganin latest news na ƴan takarkaru,
musamman wanda suka ke viral suna trending in the world" Almustapha ya ce "Kuma
ƙyakƙyawa da shi so Masha Allah" Sai a lokacin Aliyu ya buɗe ido tare da kallon Almustapha ya
ce "To kai mace ne? Da zaka na description kyan ɗan uwanka namiji?" El ya ce "Kai ban taɓa
cewa kana da kyau bane? Idan kaga abu mai kyau ka yaba shi ne kawai, day before yesterday
na je gidanka ai" A tsorace Aliyu ya ce "But baka faɗa mini ba?" Almustapha ya dinga kallon
Aliyu, shi kuma Aliyu tsoro da kunya ya kama shi "Na je, matarka ta iya girki sosai fa, na ganta
tare da wata kamar munafuka mai liƙab" Wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Aliyu ya sauke,
Majeederh ce ta yi girkin. Suna zaune Dija ta kawo Hajia ta saka Aliyu a gaba sai gashi ya tashi
da abincin cikin babban plate Kallonsa kawai take tayi tambayar duniya ya ce "lafiya"....
Abuturab na zaune feeling better gabaɗaya kwanan shi biyu da dawowa ƙasar daga
Switzerland. Idanunsa ya buɗe da ƙyar jin Maysoon na cewa "Ka fita duba lafiyarka, ka dawo
and you're still sick wai meke damunka ne Yallaɓai? Ina ta ƙoƙarin ganin na kyautata zamana
da kai but i couldn't, ka hana ni duk wata dama da zan kafa soyayyata a zuciyarka" Hawaye na
zubu mata hannunta dafe da cikinta wata tara ta ce "Nasan baka so na, amma ni ina son ka,
bani da tabbacin zan haife cikin nan lafiya, inma mu mutu tare inma na mutu na barsa ko ya
mutu ya barni, don Allah ka nuna mini soyayya a kwanakin nan kafin cikar EDD ɗina na roƙeƙa
Haydar" Kuka Maysoon ta saki sosai tana dafe cikinta, Abuturab ya zuba mata Idanu a hankali
ya miƙa mata hannu ya ce "Come" Ta ƙarasa ya zaunar da ita saman cinyarsa idanunsa akanta
ya riƙo fuskarta ya ce "Maysoon" Tana kuka ta ce "Sir" Ya ce "Ina da ƙulafuci ina da naci,
zuciyata nada kafiya akan abinda take so,ki yi mini uzuri ki amsheni a yadda nake, first love
ɗina tana wani wajen ke kuma Allah ya ƙaddara zan zauna dake matsayin mata, ina baki ci sha,
suttura ina saka miki kuɗi a bank duk wata, Maysoon ina jin zafi a zuciyata ina jin raɗaɗi ki
taimaka mini na samu abinda nake so ta hanyar addu'a, yadda nake son ta ko mulkin nan dake
tunkaro ni bana so haka, mene matsalarki?" Kuka take sosai ta ce "Are you going to insulate
me? Kana faɗa mini ƙarara baka so na, dole akai maka, me ya sa ba zaka duba irin son da
nake maka ba Yallaɓai? Ni bani da matsala kaso ko wacce kawai kulawarka nake nema lokacin
ka nake buƙata, hatta wannan cikin na jikina Ubangiji ne kawai ya ƙaddara samuwar shi,
yaushe rabon daka raɓeni?" A hankali ya ce "Sorry Maysoon" Kuka take ta ce "Please ko sau
ɗaya ne" Ya ce "Am not in the mood, ki je" Za ta yi magana ya daka mata tsawa tare da
hankaɗeta ta faɗi ƙasa saman ƙaton cikinta, wata ƙara ta saki tana runtse Idanunta Abuturab ko
ta kanta bai bi ma ya nufi part ɗinsa, ƙarar data kuma yi ya ya jawo hankalin Mama da mai
aikinta suka shigo parlourn a guje jinin dake malala a ƙasan Maysoon ya sanya Mama rikice
Maysoon tuni ta fara kokawa da ranta, Mama ta fara kuka sbd tausayi cikin ikon Allah kuma
suka fara jin kukan jariri da sauri Mama ta ɗaga Maysoon ta matsar da babyn Salati Maysoon
take tana kiran sunan Abuturab tare da yin wata jijjiga idanunta na rufewa, Abuturab Mama ta
shiga ƙwalawa kira yana ji ya yi shiru ganin numfashin Maysoon na tafiya baya dawowa yasa
Mama fara kalmar shahada,idan ta kira sunan Maysoon sai ta faɗi kalmar shahada cak

numfashinta ya tsaya jikinta ya saki idanunta ya yi sama rai ya yi halinsa Maysoon died.


Ban yi Edited ba.. bear with meDa hannun bibbiyu Abuturab ya riƙe kansa yana kallon
ƙyakƙyawar jaririyar da matarsa ta mutu ta bari. Mama dake Kallonsa tayi jigum ta ce "Ka yi
haƙuri, ko wanne mai rai mamaci ne, damuwata har yanzu ban san mene ya samu Maysoon
har ya yi sanadin Ajalinta ba" Abuturab ya yi shiru yana jin wani iri a ransa. Kallonsa kawai
Mama take kafin ta ce "Na yarda da kai na aura maka ƴar mutane ta zauna dakai a yadda ta
sameka, Ali wallahi muddin ka saɓawa yardar da na yi maka Ubangiji ba zai barka ba, zaka
samu jarrabawa ta yadda baka yi tsammani ba, gwara tun wuri idan akwai wani abu ka faɗa
mini" A hankali Abuturab ya ce "Are you accusing me, Mom?" Ta girgiza kai ta ce "Ba zarginka
nake ba, kawai dai tunatarwa na yi maka" Ya jinjina kai ta ce "A sakawa jaririyar sunan uwarta
Maysoon" Da sauri ya ce "No Mama" Ta ce "Why? I don't think it's a crime to inherit her mother's
name, no matter what, we'll always remember her" Cikin rauni da siga ta tausayi ya ce "Mama
zan dinga jin kamar zata dawo gareni ne, ni kaɗai na san abinda ke damuna, ko a saka sunanta
ko ba a saka ba, she's always be on my mind, she's a kind and nice person da ban taɓa ganin
irinta ba, so Please Mama ki yi haƙuri kada a saka sunan Please" Mama ta tsora masa idanu
kafin ta ce "To wanne sunan kake so?" A hankali ya ce "Hawwa'u, we can call her Jidderh"
Mama ta ce "Hawwa'u?" Ta tambaya da mmki ganin ka kaf Familynta babu mai irin sunan ya yi
shiru. Ta ce "Ubangiji ya rataya, ya bata haƙuri irin na mahaifiyarta" Miƙewa ya yi zuwa part
ɗinsa sbd jin muryar ƴan gaisuwa duk da ya hana zaman makoki for no reason. Kwanciya ya yi
yana lumshe idanunsa tun auren su da Maysoon bai samu nutsuwa ba, gani yake kamar ya ci
amanar wacce zuciyarsa take so da ƙauna da muradin kasancewa da ita, yanzu kuma wani irin
sauƙi yake ji da nutsuwa ko babu komai she's pass away frm his life,She was out of his life, He
will live without constraints, he will live from him only what his heart wants. Ajjiye babyn ya yi
yana jin son yarinyar har ransa musamman idan ya tuna sunan data mallaka. Wayarsa ce ta
fara ringing a hankali ya duba ganin mai kiran ya sanya ɗauka. A nutse ya ce "Barka" Daga
cikin wayar aka ce "Ka duba news kaga meke faruwa?" Ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce "Bana ce
ba, kasan am not in the mood" Mutumin ya ce "Motar ƴan boarding school dake tafiya zuwa
wani abu na makaranta aka cinnawa wuta, ɗalibai sama da 500 sun ƙune ƙurmus ga kabari
mutane wajan goma da aka tune aka kwashe gawarwakin an rasa waye, Hon ina jin tsoro baka
tunanin jam'iyyar hamayya ta aikata wannan abun sbd kawai taci mulki? Ko wani asiri suke ki
tsubbu?" Miƙewa Abuturab ya yi zufa na yanko masa ya ce "Yanzu Sir al'amarin har ya kai sbd
son mulki a sanwaltar da rayukan al'umma wanda basu ji ba basu gani ba? Me ake son zama
ne?" Mutumin ya ce "Calm down Hon, ina tunanin we can do something about that" Ya ce
"Kamar m" Ta cikin wayar aka ce "Mu je makarantar mu jajanta lamarin mu bawa iyayen ko
wanne yaro haƙuri da kuma ɗan wani abu, tare da al'ƙawarin yin bincike idan jam'iyyarmu ta
samu mulki" Tattaunawa sukai kana suka sauka akan layi.
After 1weeks
Majeederh na zaune tana duba wasu files da aka turo mata na Human rights akan wani cases
da ake son ta taimaka kamar daga sama taga Abbu ya shigo cikin sauri ta ɗago kanta ta dube
shi jikinta duk rawa yake ta kasa cewa komai Abbu ya ce "Hawwa'u me ya kai ki Bristol Palace
Hotel?" Wani irin bugawa ƙirjinta ya yi ta ce "Hotel Abbu?" Hannu ya ɗaga ya zabga mata mari

ya ce "Are answering my questions with a question? How dare you?" Yatsunsa ya fito sosai
akan fuskarta sosai idanunta ya shiga fitar da hawaye ta ce "Abbu ban taɓa zuwa Hotel ba, don
Allah..." Wani marin ya kuma sauke mata idanunsa sukai jajur kamar zasu fito waje yama kasa
magana sai pointing ɗinta da hannu da yake "Ban haifi yarinyar da zata ɓata mini sunan family
da nawa ba, kin yi kadan zaki san cewa ni na haifeki ba kece kika haifan ba wallahi lokaci kawai
nake jira" Kuka take sosai kamar ranta zai fita ta ce "Why should i do that Abbu? Wallahi ban
taɓa zuwa Hotel ba mene ribata bayan nasan illar hakan don Allah Abbu...," Hannu ya ɗaga ya
ƙara sauke mata wani marin kafin ya ce "Idan ba ki ki Hotel ba to wace wannan? 1week ago
wacce ta je gidan ƙartin maza? Past week's waye ya dinga hauro mini gida yana shiga ɗakin ki?
Ko shi ma bake bace baki san anyi ba? Shekaran jiya kin ce mini zaki wani meeting a Abuja
daga nan mene ya kai ki Lagos?" Wani irin kuka take sosai bakinta na rawa ta ce "Abbu zan
maka bayani wlh ba abinda kake tunani bane" Jin hayaniya ya saka Mami fitowa Main parlour,
Raihana ta fito itama da sauri Mami ta ce "Meke faruwa ne?" Da hannu Abbu ya ce
"Hawwa'u zata saka mini ciwon zuciya, tana sane ta ƙi yin aure take yawo tarbiyyar dana baki
kenan? Na yarda dake na amince miki shi ne zaki aikata mini haka? Kin san bana iya bacci sbd
damuwarki, burina kawai na ganki a ɗakin mijinki kamar sauran ƴan uwanki amma abin ya ci
tura, ashe haka zurfin ilimi ke jawowa?" Mami ta ce "Take ur heart please Alhji baka da lafiya ka
dinga bin komai a sannu Please, kada ka yanke hukunci ba tare da bincike ba" Abbu ya ce
"Wanne irin bincike bayan wanda na yi? Komai nake idanuna yana kan Majeederh bani da
cikakkiyar nutsuwa private Investigators nawa na saka akanta?" Da wani irin tashin hankali
Majeederh ta ce "Zargina kake Abbu? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un na shiga uku, wallahi Abbu
ban taɓa aikata sabon Ubangiji ba, ba zan taɓa cutar da tarbiyyarka ba da nayi haka gwara
mutuwata, taimakon al'umma musulmi kawai nake" Wata zabgegiyar bulala ya ɗakko ya nufi
Majeederh zai daka da sauri Mami ta shiga tsakani idanunta na zubar da hawaye ta ce "Haba
Alhaji idan rai ya ɓaci nutsuwa ake samu, hankali ke nemo shi, idan ka yarda da Majeederh tun
farko bai kamata ka zargeta ba yanzu, zargi haramun ne a musulunce wlh" Yana huci sosai ya
ce "Leave, Asabe ki matsa daga nan ko na haɗa dake" Mami na kuka sosai ta ce "Wlh sai dai
ka dake mu tare, na fara gajiya wanne irin mutum ne wai kai? So kake a zageni ace sbd bani na
haifeta ba? Ka sassautawa zuciyarka, kabi komai a sannu faɗa baya magani idan ba kangarar
da yaro ba, ko ƙaddara ce fa ta faɗa mata dole ka zauna da ita ƴarka ce jininka ce hannunka
baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar" A wannan karan hatta Raihana sai da ta ji tausayin
Majeederh, babbar mace mai shekaru ilimin addini dana boko kuɗi hankali nutsuwa amma ita
ake doka kamar Ƴar shekara biyar. Zubewa Abbu ya yi dafe da kansa dake juya masa yana jin
kamar zuciyarsa zata fashe, shigowar Abraham cikin main parlour ya sanya Abbu miƙewa da
sauri ya ce "Ban hanaka shigo mini cikin gida ba? Ban hana mara tsafta me yawo da datti ya
dinga shigo mini cikin gida ba? Ban hana mara gata da ƴanci wanda bashi da mara da almajirin
kan titi shigo mini gida ba?" Abraham kallon Majeederh dake durƙoshe yake wacce gefen
bakinta ya fashe, ta kasa ɗago kanta ta kalli Abraham sbd gujewa ganinsa da take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login