Showing 66001 words to 69000 words out of 126765 words

Chapter 23 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf

tsaya ta kasa tuna inda ta ji muryar ta juya, yana tsaye hannunsa zube cikin Aljihu sanye
da wani tissue ɗin farin yadi ƙal da shi ta yi murmushi ta ce "Aliyu"
Ya yi jim domin bai ɗauka ta san sunan shi ba ya ce "Congratulations Hawwa'u ko wani zai
nuna mini farin ciki ina tunanin bayan Abbu ne" Kafin Majeederh ta yi magana aka ce "A sbd kai
ne wa?" Majeederh ta ware idanu ganin Captain Alpha bakinta na rawa ta ce "Yaya?" Ya ware
mata idanu ya ce "Me kike? Yana da kyau ki huta" Ta ce "Ayya yau ai bana iya bacci, Aliyu baka
da lafiya?" Aliyu dai bai ce komai ba sai kafeta da idanu da yake ya ce "Congratulations once
again, take this matsayin nawa gift ɗin" Ya dubi hannunsa ta box ne ɗan ƙarami ta ce "No thank
you, hakan ma ma gode sosai" Calmly ya taka har inda take ya ce "Please, ki amsa kamar
yadda kika amshi ta kowa" Tana ƙoƙarin amsa Alpha ya karɓa ya ce "Mun gode, let's go"
Majeederh bata ji daɗi ba amma haka ta daure ta ce "Jazakallah-bil khair, ina Latifa Omar? Kun
yi aure hala?" Ta faɗa cikin muryarta wacce ta juye bai amsata ba ya juya kawai tare da barin
wajan. Majeederh ta shiga mota Alpha ya shiga baya kusa da ita, driver ya ja suna tafe ya buɗe
box ɗin wani ɗan ƙaramin ring ne mai kyau sosai, sai wani farin tissue da akai rubuta cikin good
handwritten a hankali ya fara karantawa da sauri kuma ya tura tissue ɗin cikin aljihu ya maida
ring ɗin yana tafe baki. Har Magriba Majeederh na tare da yayanta Alpha sosai tayi farin ciki,
har akai walima. Ƙarfe 12 na dare ta buɗe wayarta message kamar hauka musamman daga
wajan Aaliyah da Anti cikin sauri ta dinga dubawa ko za taga na Abbu domin tasan he's the first
person da zai cnrgt nata amma har ta gama dubawa babu nasa jikinta ya yi sanyi a hankali ta
danna number Abbu ringing ɗin farko ya ɗaga ta ce "Assalamu alaiyka Ya Abbu" Abbu ya ce
"Majeederh na ji labarin irin kuɗaɗen da kika samu, da na yi lissafi sun haura miliyan 20 banda
kujerar makkan " Sosai abin ya bata mamaki ta ɗauka zai farin ciki ya sanya mata albarka kan
nasarar data samu amma sai ta ji babu batun hakan a bakinsa maganar kuɗi kawai yake? Ta yi
murmushi mai ciwo ta ce "Ban san nawa bane Abbu, amma dai da yawa" Abbu ya ce "To da
kyau ai tuni na lissafa, a hakanma banda kuɗin albashinki" Ta jinjina kai idanunta cike da
hawaye wanda ya fara sakkowa saman fuskarta ta ce "Abbu ka shirya tafiya aikin hajji, ni ma
zani Uncle Isma'il da Mami su je Umara" Abbu ya yi zumbur ya miƙe daga zaune ta cikin wayar
ya ce "Ashe Majeederh baki da hankali baki da wayo?" Muryarta na rawa sosai ta ce "Me na yi
Abbu? Ka yi haƙuri don Allah" Ya ce "Daga ni harke har su Uncle Isma'il ɗin da ita Asaben babu
mai zuwa ko nan da airport balle aikin hajji, siyar da su za ayi a haɗe kan kuɗin tas" Majeederh
ta ware Idanu while hawaye na zuba a fuskarta ta rufe bakinta ta kasa cewa komai "Hawwa'u?"
Muryarta na rawa ta ce "Na'am Abbu?" Ya ce "Kuka zaki akan na ce haka? Shikenan riƙe

kuɗaɗenki" Da sauri ta girgiza kai tana zubewa saman gwiwoyinta jikinta na rawa ta ce "Ka yafe
mini Abbu wlh ba kuka nake ba, idan kukanne ma na farin ciki nake, na bar maka kuɗin halak
makal ko biyar ba zan ɗauka ba, amma don girman Allah Abbu ko kai ɗaya ne ka je aikin hajjin
idan ya so sai a siyar da sauran" Abbu ya girgiza kai ya ce
"A'a ai tas za a siyar da su, nan gaba sai ki sama mini kuɗin da zan je aikin hajjin hakan ya fi
ko?" Ta jinjina kanta ita gabaɗaya ba ruwanta da kuɗin ba shi take buƙata ba burinta kawai ta ji
ya ce "Majeederh Allah ya yi miki Albarka" Wannan kalmar ita kawai take buƙatar ji, babu uwar
da zata sanya mata albarka uban kuma bai damu ba. Abbu ya ce "To sai anjima aci gaba da
ƙoƙarin adana kuɗi banda ɓarnatarwa" Kafin ta yi magana ya kashe wayar, sakin wayar ta yi
tare da durƙoshewa ta shiga rera kuka kamar ranta zai fita tana buƙatar sanya albarka ko sau
ɗaya ne idanunta ya kumbura sosai da ƙyar ta iya kiran Uncle Isma'il ya yi mata addu'a haka
Uncle Bello ta kira Anti da Mama kana ta kira Mami sai Aaliyyah ji tayi duniyar ta yi mata zafi
komai ya jirkice mata bacci ya ƙauracewa idanunta...... Majeederh ta tattara komai ta ajjiye waje
guda karatu take sosai, shaƙuwa sukai sosai da Ƙhulud Arzaan Ajlaal kuma basu taɓa magana
ba tun ranar, duk wata sai ta turawa Abbu kuɗi bata san me yake da su ba, Majeederh kullum
cikin azumi take ta rame sai ɗan jiki fatarta ya goge sosai, zamanta da Ƙhulud ya ƙara sawa ta
zama wayayyiya sosai rashin magana ya ninka nata, tun a lokacin da Abbu ya ja mata kunne ta
cire batun aure a ranta, tun tana sha'awar yi har ta fice mata a rai, ta sanyawa ranta ba zata
taɓa yin aure ba, duba da cewa tun a lokacin babu wanda ya ƙara cewa yana sonta, a shekarar
ƙarshe ta zanna jarrabawa mai kyau ta samu first class tayi farin ciki sosai ta zama cikakkiyar
Malamar addinin Muslunci ga tarin magoya baya da take da shi a facebook ta fara faɗakarwa
akan maza da mata kamar yadda taga Fauziyya d sulaiman tana yi....

*After 8 year's.... Nigeria*
Aminu Kano airport...30
*After 8 year's.... Nigeria*
Misalin ƙarfe 6 na yamma jirgin sama na Emirates ya sauka a fili tashi da saukar jirgi na Aminu
Kano airport, mai ɗauke ɗaliban ƙasar wanda suka kammala karatun su na scholarship da
gwamnatin baya ta samar musu. Ɗalibai ne suka ta sakkowa maza da mata ko wanne fuskarsa
ɗauke da wani irin farin ciki bayan shekaru takwas yau sun dawo ga iyayensu. "I couldn't
believe Aunt Jeederh would come back from Egypt today" cewar Aaliyyah daga gefe aka ce "Me
ya sa?" Ta kalleta "Haka nan" Aaliyah ta bawa Widad amsa. Ko wanne banza idanu yake yaga
ta ina Malama Majeederh zata fito... Jawaad ɗan gidan Anti da Uncle Isma'il ya ce "Finally" Jin
hakan yasa gabaɗaya suka kalli direction ɗin jirgin inda ake sakkowa. A hankali take sakkowa
kanta a ƙasa tana sanye da wata Abaya ruwan sararin samaniya wacce akaiwa feshin dutsuna
na masu ruwan huda, tayi rolling kanta da vail sai liƙab ɗin data sanya a fuska da wani sirrin
farin photochromic ɗin Glasses a Idanunta. Hannunta ɗaya yana jan ƙatuwar trolley ɗinta ɗaya
kuma riƙe da hand bag a nutse take sakkowa, lokacin data sakko ta tsaya cak ta lumshe idanu
sbd wani daɗi daya ratsa, farin ciki ya wanzu a zuciyarta. Da ace tana da iko kuma zata iya da
buɗe fuska za ta yi ta shaƙi ƙamshin iskar ƙasarta wacce rabonta da ita shekara takwas kenan,
tun tana shekara ashirin a duniya yanzu kuma tana dab da cika shekaru talatin domin kaɗan ne
ya rage mata 28 take yanzu going to 29 tunda end of the year suka kammala Final exm.

"Ma sha Allah" Majeederh ta furta cikin lallausar murya. A hankali ta shiga rarraba idanu taga ko
akwai wanda ya zo tafiya da ita, domin komai ya sauya mata. Ihu ta ji an kurma tare da
ƙanƙameta ana faɗin "Wlcm back Anti Jeederh" Majeederh ta ware idanunta akan Aaliyah cike
da mamakin ganin yadda ta girma sosai ta yi murmushi tana hugging nata back. "Sannu da dawowa ƙasa Nigeria" Widad ta furta murmushi kawai Jeederh take sbd tsantsar
farin ciki. A hankali ta ɗaga kanta sai a lokacin taga tarin jama'ar da suka zo tafiya da ita, Anti,
Ruma da Raihana sai Jawaad da Uncle Isma'il da Innati. Ta dinga ware idanu ko za taga Abbu
amma babu shi sai jikinta ya yi sanyi. Tana zuwa Ta faɗa jikin Anti ta ce "Na yi kewa Anti" "Mu ma mun yi rashin yarinyar arziƙi barka da dawowa" A hankali ta dinga bin kowa tana bashi
hug Uncle Isma'il ya shafa kan Majeederh ya ce "Kin zama abin alfahari, Ubangiji ya baki zuri'a
masu hali irin naki" Majeederh ta kalli Uncle Isma'il a ranta tana maimaita kalamar "Zuri'a" Ganin
motoci har guda huɗu duk na familynsu ya bawa Majeederh mmki musamman da taga Ruma ta
shiga wata kuma matsayin driver, motar Uncle Isma'il ta shiga ita da Anti a baya sauranma duk
suka shiga mota, On their way back home, Majeederh kept looking at the road, everything has
changed for her since she went to Egypt until now, eight years after returning. Ta ɗan ware
idanu ta ce "Yaushe akai wannan a Government house?" Anti ta ce "Mefa?" Ta nuna musu
roundabout Uncle Isma'il ya ce "Bayan tafiyarki da shekaru biyu, gwamanti data sauka" Ta
jinjina kai Calmly ta ce
"Amma kamar ba hanyar gida ba, ko ni ce na manta?" Anti ta yi murmushi ta ce "Daman kam za
a sha tambaya, nan ai hanyar Lodge Road ne bari mu ƙarasa za kiga komai" Murmushi kawai
Majeederh ta yi tana jin sauƙi a ranta ganinta kusa da ƴan uwa shi ya sa bakin nata ya buɗe a
taushashe ta ce "Uncle yanzu ya yanayin garin yake, waye Governor da mataimaki?" Uncle Isma'il ya ce
"Engineer Dr. Muhseen Bagayya" Ta yi saurin cewa "A'a ai daman shi ne Governor har lokacin
dana bar ƙasar" Uncle Isma'il ya ce "Yes, ai shekara takwas ya yi yanzu ake ƙoƙarin yin zaɓe
duk sun tashi hankali" "Kenan wanne jam'iyyu ne?" Uncle Isma'il ya ce
"Yaushe Hawwa'u ta zama Talkative ne? zamanta a Egypt?" Murmushi kawai ta yi Anti ta ce
"A'a ka barta ta tambaya ai ta zama maƙowa, kuma tana da ikon sani ai" Majeederh bata ƙara
cewa komai ba har suka isa Lodge Road suka isa street ɗin da zai kai su har gida, Majeederh ta
waro idanu waje ganin sun nufi wani tamfatsetsen gida mai mugun kyau, ta kasa ɗauke
Idanunta daga gidan domin kaf unguwar babu na biyun gidan, gida ne iya gida 200by 200.
Uncle Isma'il ya danna horn gatekeeper ya miƙe da sauri yana buɗe musu, shi kansa jikinsa
rawa yake yau zai ga Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Mamaki bai gama sakin Majeederh
ba idanunta ya sauka akan wasu lafiyayyiyun motoci na alfarma har guda huɗu a rumfar ajjiye
motoci. Parking Uncle Isma'il ya yi yana fitowa Anti ta buɗe ta fito, a hankali Majeederh ta fito
tana lumshe idanunta tare da bin cikin compound ɗin da kallo, a hankali kuma sauran motocin
suka shigo. Aaliyyah ta kalli yadda Majeederh ke kallon komai ta ce
"Mamaki ko?" Ta jinjina kai Aaliyah ta ce "Ai zaki sha labari" Gabaɗaya suka shiga gidan a Main
parlour suka zauna ita dai Majeederh kallon komai take cike da mamaki. "Ya kamata a cire
mana liƙab ɗin" In ji Ruma murmushi ta yi ta cire liƙab ɗin, Gabaɗaya suka tsora mata idanu ta
waro nata ta ce "Lafiya?" "Wallahi baki da maraba da Balarabiya Anti Jeederh kin ga mahaukacin kyan da ki kai, sa maza

hatsari a titi" Majeederh ta ce "Kyau ya zama Annoba idan har za ai accident" Suka saki dariya
Mami ta ce "A bar mini ƴa ta huta haka nan, ta ci abinci" Innati ta ce "Azaba ji munari nabi abinci
da gudu ba wando" Aaliyah ta fasa ihu ta ce "Rufa mana asiri ki saka wando" Innati ta ƙanƙance
idanu ta ce "Da ubanki kike mara zuciyar nan, mai yawa ƙasa ƙasa yawan kasuwanci, ƴar
banza da idanu fiƙi-fiƙi kamar malafar kwaɗo" Aaliyah ta murguɗa baki ta ce "Bani da lokacinki,
Allah ya sa kiga fatalwa yau" Tsit Innati ta yi bata sakewa cewa komai ba. Anti ta sassauta
murya ta ce "Majeederh jeki wanka ki sallah kici abinci" Ta marairaice fuska ta ce "To ban san
ina zan shiga ba" Ruma ta ce "Zaman house ya dawo kenan" Ba wanda ya kalleta Aaliyah taiwa
Majeederh jagora zuwa wani part mai kyau sosai da tsari With so much surprise ya dinga kallon
komai kana ta cire kaya ta shiga bathroom a hankali ta saukewa kanta shower tana sauke
numfashi, ta ɗaura alwala wata duguwar riga mai sauƙin nauyi ta saka, ta saka hijabi bayan tayi
sallah ta ɗauki vail tare da rolling kanta kana ta nufi main parlour duk suna zaune saman dining
area ta ƙarasa tare da jan kujera ta zauna. Spoon ɗin kawai take juyawa ta kasa cin abincin can
dai ta runtse idanu ta ɗan ci kaɗan. Innati ta ce "Shi ya sa kike kamar kazar matsiyata firit a fige
ba tsiya ba arziƙi, tirrr" Hira aka dinga yi har su Anti suka yi sallama tare da komawa gida.

Misalin 12:30 na dare Majeederh da Aaliyyah na zaune saman gado Aaliyah ta ce "Bayan
tafiyarki babu jimawa Abbu ya ce za a rushe wancan gidan namu a yi sabo, ya ce kuɗi ya samu
sama da miliyan biyar, ni dai ban ce komai ba ban kuma nemi sani ba, sbd i don't have any
business with that, kuma ubanwa ya bani ikon tambayar inda ya samu kuɗin ma? Muka tattara
gabaɗaya muka koma Gidan Uncle Isma'il Mami Kuma da Ruma suka tafi can dangin Mami, ba
a ɗauki lokaci ba aka gina gida haɗaɗɗe aka dinga surutu a unguwa ina Abbu ya samu kuɗi shi
ba sana'a ba?? Ya yi burus dai a lokacin akai bikin Ruma da Imran sai Raihana......,"
"Amma na gansu gida?" Majeederh ta katse Aaliyah da faɗin hakan ta ce "I have no idea,
amma idan suka zo gida sai su yi wata gudu wai mazajan nasu basa gari" Majeederh bata ce
komai ba, Aaliyah ta ɗora da cewa "Daga nan kuma Abbu ya buɗe shago a kantin kwari ya
zuba kaya da yara masu kula da komai, ya ɗinka sutturu kamar yaƙi, lokacin da kika samu
nasara a Misira da bayan wata huɗu ya ce gabaɗaya tashi za mu yi daga gidan nan zamu koma
Lodge Road, haka muka koma bamu da wani option, shekarunki uku da tafiya akai bikin Anti
Latifa" Majeederh ta waro idanu waje cike da mamaki sosai kafin ta yi magana Aaliyah ta ce
"Wallahi anyi bikin bayan jinyar da Yaya Aliyu ya yi a ƙasar waje tsayin shekaru biyu, to bayan
ya dawo akai bikin" Majeederh ta sauke numfashi ta ce "Ikon Allah, ina aka kaita?"...... "Gata
nan kusa damu, ita ce neighbor namu fa" Majeederh kamar ƙaramar yarinya tai zuru ta ce
"How?" Aaliyah ta ce "Good, bamu san mene ya faru ba daman akwai gida kusa damu dake
duk kusan gidan haya ne na masu kuɗi kawai sai mu kaga ana fara gyara, daga nan ne Latifa
take cewa Aliyu ne ya ce nan zai zauna yafi kusa da wajan aikinsa, ana yin bikin ya ta tare,
amma a ranar auren ana ɗaura auren Aliyu ya tafi Cairo ƙaro karatu maganar da nake jiya ya
dawo cikin dare" A gajarce Majeederh ta ce "Allah ya sa albarka, ke fa?" Aaliyah ta zaro idanu
ta ce "Tab ai nayi al'ƙawari sai kin yi aure zan yi" Majeederh bata ce komai ba ta yi shiru da
sauri ta ce "Abbu bai dawo ba?" Ta ce "Kai ai tun 7 ya shigo gida, baku gaisa ba?" Majeederh
ta yi shiru kawai.
"Na manta ban faɗa miki ba" Aaliyah ta gyara zama ta ce "Bro Alpha an ƙara masa matsayi
daga Captain zuwa General" Majeederh ta ce "Ma sha Allah, Allah ya riƙa" Daga nan Aaliyah ta

nufi ɗakinta ba don ta so ba.
A hankali Majeederh ta miƙe tsaye tare da ɗaukan hijabi hankalinta yana kan Abbu shi kawai
take son gani, taga ya mahaifin nata yake? Kai tsaye part ɗin da aka nuna mata aka ce shi ne
nashi ta nufa, sosai part ɗin ya haɗu iya haɗuwa gashi parlourn farko ta gansa buɗe da dinga
kallon komai cike da sha'awa da mmki, ganin baya parlourn ta shiga wata ƙofa da zai kai ta
ɗaya parlourn wanda daga shi sai bedroom, ta tsaya cak tare da yin knocking ta ɗauki good 10
minutes tana knocking kafin cikin faɗa aka ce "Who is there?"
"Majeederh ce, Abbu"
Abbu ya maimaita "Majeederh?" Ta ce "Eh" muryarta duk rawa take gefe guda kuma farin ciki
take zata saka mahaifinta a Idanunta can ta ji ya ce "To ya akai?" Sosai tambayar ta bata
mamaki da tsoro ta ce "A'a daman tunda na dawo ban ganka ba, ina ta duba ka ina so mu
gaisa" Daga cikin parlourn Abbu yana zaune saman lallausan kujera watching TV hannunsa riƙe
da cup yana shan black tea ya ce "Ok bani da lokaci zuwa safiya" Majeederh kamar zata
zunduma ihu sbd abin da ya tsaya mata cikin rauni ta ce "Please naga kowa banda kai, shekara
8 ban ganka ba" A ɗan hassale ya ce "Ok na bar abinda nake na fito ki ganni kenan ko
Hawwa'u? Bani na ce ki bari sai safiya ba, ni ma ina da buƙatar ganin naki" A sanyaye ta ce
"Kayi haƙuri" Tana faɗin hakan ta nufi part ɗinta. Waje ta nema ta zauna a saman bed tana cusa
hannunta a tsakanin cinyoyinta tare da yin shiru tana girgiza ƙafa, ita kanta ba zata iya cewa ga
abinda take tunani ba.....
Washegari misalin 7 na safe Majeederh ta fito tana mustsike idanu sbd baccin daya ɗauketa
bayan sallar asuba, ta ci karo da Mami ta ce "Ina kwana?" Mami ta kalleta sosai ta ce "lafiya,
me ya samu idanun naki?" Majeederh ta ɗan yatsuna fuska ta ce "Sometimes ya yi ta mini zafi,
wani lokaci kuma ban fiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login