Showing 54001 words to 57000 words out of 126765 words
Chapter 19 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf
ɗaya hadda ɗakko waya
yana danna vedio yana cewa "Lallai bikin Widad da Mansur ya yi albarka, hadda su
mahaukaciya a wajan?" Ta ƙarawa tafiyarta sauri harta shigewa bayan ƙofa ta shiga gidan
Uncle Isma'il tana dafe ƙirjinta. Her heart broke, she hugged her knees even righter. She felt
warm tears running down her cheeks, nothing hurts like they words, ta wulaƙanta kanta akan
neman mijin aure sai gashi buƙata bata biya ba mazan ma kallon mahaukaciya ce suke bata, a
wancan karan ance Aljana yanzu kuma suna kiranta da mahaukaciya. Ba abinda ke bata tsoro
ganin hatta Aaliyyah da suke ciki guda bata ganeta ba. Ta ƙara ƙanƙame jikinta waje guda.
Hannunsa duk biyun ya sa ya rufe kunnenshi wanda sautin kiɗan ke neman fasa masa dodon
kunnen, a hankali ya juya yana buɗe idanunsa cikin sauri kuma ya sakko daga kan gadon yana
jan tsaki, gabaɗaya ƙaddara ce ta kawo shi gidan Uncle Isma'il ya ɗauka a gidan Uncle Bello za
su yi Shirman abun nan, gashi daga dawowarsa garin ba a bar kunnenshi ya wuta ba, idanunsa
sun ƙanƙance sbd bacci ya buɗe ƙofar ya fito daga shi sai wani 3gauter, tunda ya fito ta tsora
masa idanunta da suke ɗauke da jiƙaƙƙun hawaye tana mamakin yaushe ya dawo shi kuma?
Harya gama watannin kenan, yana zuwa ya fice ta gefen ƙofar kai tsaye kuma wajan M.c ɗin ya
nufa "Hi" M.c ya ce "Hi" Ya kame fuska sosai ya ce "Kwashe kayanka kabar wajan nan yanzu,
duk wanda ya yi magana ka ce Alpha Bello khan ya saka ka ok" Yana faɗin hakan ya juya,
Ruma ce ta fara magana ta ce "Kai Dj ya haka? Yanzu fa abokan ango za su zo, kawai sai ka
shiga kwashe kaya" M.c bai magana ba sai Dj ne ya ce "Wa nine ya ce mu kashe yanzu" Ruma
ta ce "Kan uba waye?" Ya ce "To gashi nan dai, amma kamar Soja yanayin jikinsa" M.c ya ce
"Sunansa Alpha Bello khan" Da sauri Ruma ta rufe baki tana zare idanu daidai nan Widad ta zo
tana complain me ya sa ta ji shiru, Ruma ta faɗa mata Alpha is back, wani irin rushewa da kuka
ta yi shikenan ta shiga uku, yanzu dinner ɗin gobe hanata zai yi ta dinga kuka, Anty ta zuwa ta
ce "What did i miss?" Sahar ta ce "Captain ya dawo, Alpha" Anty ta ce "Na gode Allah, ya dawo
a daidai".... Majeederh na zaune ta ji an saka hannu tare da miƙar da ita tsaye da sauri ta buɗe
ido ganinsa tsaye a gabanta ya harɗe hannu a ƙirji yasa ta haɗiye sauran hawayen, ya dinga
kallonta frm head to toe ya girgiza kai ya ce "Follow me" Ya juya zuwa bedroom ɗin daya fito, a
hankali ta tura ƙofar ta shiga yana zaune hannunsa riƙe da waya yana magana a hankali ya
nuna mata toilet "Clean your face, now" Za ta yi magana ya haɗe dole ta shige, ya daɗe zaune
kafin ta buɗe ƙofa ta fito a hankali take takawa zata bar bedroom ɗin ta ji ya ce "Come,
Jiddatul-khairy" Ta juya tare da zubewa a ƙasa ya ce "Meke faruwa?" Ta girgiza kai, ya ajjiye
wayar tare da juyawa gareta bakiɗaya ya saka hannu ya tallafo haɓarta ta yi saurin ja baya zai
ƙara ta ɓata ta marairaice fuska cikin shagwaɓa wanda daman ita halittace a jikinta ta ce "Don
Allah Yaa Alpha kar ka sake ta ɓani" ta faɗa har zuciyarta domin daya ta ɓata ji tayi kamar an
watsa mata wani abu, tsigar jikinta ya miƙe, ya nuna mata ƙofa ya ce "Out" ta fice da sauri....
Bayan gama bikin Widad aka zauna family meeting amma rawar bata sauya zani ba, har su
Uncle Isma'il suka zare hannunsu daga kan al'amarin Abbu, har lokacin Alpha bai san meke
faruwa ba, shi ne babban ɗan Uncle Bello, daman jininsa bai haɗu da Mami ba shi ya sa bai
damu da zuwa gidan Abbu ba, Ranar monday aka gama komai na batun tafiyar Malama
Majeederh Abdul'aziz Khan, daman tana yin dashi kuma ita ce ɗaukan ƙarshe aka bata kuɗi ta
siyi kayan sawa sabbi da taimakon Latifa, sosai ta yi mamakin yawan Abayas ɗin data tambaya
sukai mata shiru kawai, ta siyawa Abbu buhun shinkafa, katan na tafiya dana makaroni, ta siya
musu masara ta Tuwo, ta bawa Aaliyah kuɗi ta ce ta riƙe a hannunta kana ta bawa Abbu ya
dinga murna yana cewa "To gashi ɗan ƙaramin albashi ya yi rana, ina ga idan ta fara aiki a
Misira ai shi Allhamdu lillahi, Majeederh ta wanke masa zuciya" Kanta a ƙasa, a daren ta shiga
sallama da ƴan-uwa Innati kuka sosai, Majeederh na zaune a gaban Anty tana mata faɗa suka ji
an shigo ɗakin ganin yadda yake huci kamar an maciji yasa Anty jin tsoro ta ɗauka ko wani
abun ya faru domin tasa duk wani soja kullum cikin shiri yake ta ce "Alpha lafiya??" Idanunsa
jajur bai kalleta ba, ya saka hannu ya damƙi hannun Majeederh tare da janta zuwa ɗaya
bedroom ɗin yana shiga ya juya ya sakawa ɗakin sakata tare da harɗe hannu a ƙirji ya shiga
takawa zuwa inda take tsaye.....
MIJIN MALAMA
Paid book
08119237616
Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv sarauta
Ba posting weekend, mai buƙata mu haɗu a arewabooks da special grp25
Huce ta ya yi tare da neman waje ya zauna, a hankali kuma ya sake miƙewa cikin ƙasa da
murya Alpha ya ce "Why Majeederh?" Majeederh ta yi shiru ya sake juyawa a fusace kamar zai
daketa ya ce "Don't let me to repeat myself Jiddatul-khairy" Ya faɗa yana hargitsa sumarsa.
Majeederh ta ɗago kanta suka haɗa idanu ta yi saurin yin ƙasa da nata idon, ya san halinta da
kafiya da rashin son magana ga shegen zurfin ciki, ya saisaita murya ya ce "Yanzu kina jin
tafiya wata uwa duniya ya dace dake a matsayinki na mace? Duk ilimin da kika samu baki gode
Allah ba? Idan karatun kike so me makarantunmu suka rasa? Bakya tunanin aure Ke??" Baki ta
buɗe za ta yi magana ya daka mata tsawa yana ɗaga mata hannu ya ce "You have nothing to
say, Ai na je wajan Abbu ya faɗa mini komai everything, bai san lokacin da kika nemi
scholarship ba, sai form kawai ya gani kina kuka kika bashi uzurin tafiya karatu wannan dalilin
ya sa kika kuri wancan that stupid Imran, akan karatu? Me kika rasa?" Tunda Alpha ya fara
magana Majeederh ta yi ƙasa da kanta amma jin abinda ya furta Abbu ya shaida masa ya sa ta
ɗago kanta da sauri ta shiga kallon bakinsa dake motsawa yana mata faɗa da ihunsa na sojoji.
Baya ta yi tana riƙe ƙirjinta tare da nufar hanya zata fice daga cikin bedroom ɗin duk da ya sa
key amma ita ta riga data mance, kafin ta ƙarasa wajan ƙofa Alpha ya ƙara yi mata wata
mahaukaciyar tsawa wacce bai bata taɓa jin irinta ba, hakan ya sa ta rikice ga ƙirjinta da ya yi
mata nauyi a hankali ta fara gani dishi dishi, sama-sama kuma take jin muryar Alpha daya riƙe
kafaɗunta yana girgizata tasan ta faɗa jikin mutum kuma ya rungumeta daga nan bata sake
sanin komai ba.... A hankali yake tafiya a cikin wrld ɗin hannunsa zube cikin Aljihu, yana sanye
da wani floral jacquard one button suit, black colour sai necktie ɗin daya kasance red, ƙafarsa
cikin Loafers mai kyau, sai fidda ƙamshi yake a nutse yake sauraran Latifa Omar dake gefensa
tana cewa "Wallahi ban san meya sameta ba, ni ina gida ita kuma taje sallama yanzu nake
samun labari wajan Aaliyyah ina ƙoƙarin tafiya kuma kace na jiraka, ashe hadda su kwanciya
asibiti??" Aliyu ya fesar da iska ya ce "Allah sarki" Daga haka bai sake cewa komai ba, Aaliyyah
Latifa ta kira ta fito zata nuna musu inda aka kwantar da Majeederh, su kaci karo a hanya ta
durƙosa har ƙasa ta gaida Aliyu-haydar, ya bita da kallo yana yabawa da nutsuwarta, ga sahihin
kyan da take da shi, ya fara tunanin ko ya Majeederh take? Idan babu wannan abun na
fuskarta? Ya yi saurin cire tunanin a ransa har suka ƙarasa ƙofar room ɗin suka samu Anti,da
Mami, sai mahaifiyar Alpha da kuma Uncle Isma'il da Ruma, Aliyu ya durƙosa har ƙasa ya ce
"Ina yini Uncle ya mai jiki?" Uncle Isma'il ya yi murmushi ya ce "Jiki Allhamdulillah, sallamarta
ma za ayi" Ya jinjina kai ya ce "Allah ya ƙara afuwa" Ya juya ya gaida sauran jama'ar wajan, Anti
sai kallonsa take sbd abinda ta gani kwance akan fuskar shi ta ce "Aliyu ka shiga kaga jikin nata
mana, Latifa raka shi" Latifa Omar ta yi jim ta ce "Ba kowa a ciki?" Uncle Isma'il ya ce "Da kowa
ba kowa, Soja ne yayanta Alpha shi kawai a ciki" Latifa Omar tayi kamar karta shiga haka
kurum jininta bai zo ɗaya dana Alpha Bello khan ba, baya kulata ko gaishesa ta yi, sai kuma ta
miƙe tsaye daman tuni Aliyu ya miƙe tayi gaba ya bi bayanta a hankali ta murɗa handle ɗin
Ƙofar tare da shiga bakinta ɗauke da sallama, ta matsa gefe Aliyu ya shigo idanunsa ya sauka
akan Majeederh da kanta ke cinyar Alpha sai kuka take rusa masa mara sauti wanda ya fi ko
wanne cin rai, yadda idanun Alpha ya yi jajir zai baka tabbacin kukan na Majeederh yana taɓa
masa zuciya. Aliyu ya dinga kallon yadda Majeederh kewa Alpha kuka kana gani kasan kukan
data jima tana tarawa a zuciyarta ne, ya rasa kukan na mene? Hannunsa ya sauka akan
hannun Alpha da yake ɗan shafa kan Majeederh da sauri Aliyu ya juya har yana birgewa da
ƙofa jiri na ɗaukarsa ya fice daga room ɗin, Latifa ta biyo bayansa, Uncle Isma'il dake tsaye shi
da Dr ya dubi Barrister Aliyu ya ce "Badai har kun gaisa ba?" Ya daure murya can ƙasa ya ce
"No, zan dawo" Yana faɗin hakan ya nufi harabar asibitin tare da shiga mota ko Latifa dake
kiransa bai saurara ba yaja motar da gudu yabar asibitin...
Alpha ya ɗago Majeederh ya kasa cewa komai can ya sauke numfashi ya ce "It's okay, stop
crying" Ta kasa daina kukan harda shassheƙa daman kuma Alpha ne kawai ke iya jin zurfin
cikin na Majeederh tun tana yarinya, ya sa hannu ya riƙo fuskarta ya kalleta ya ce "What again?
Kina so ni ma na shiga damuwa ne?" Ta girgiza kai ya ce "Gashi kina ta kuka, 20 yrs kamar
yarinyar goye" Ya sa hannu ya share hawayen fuskarta a hankali ya cire hannunsa ya yi shiru,
Majeederh ta ce "Kada ka faɗawa kowa abinda nace please" Ya kalleta kawai ta ƙara
marairaice fuska ta ce "please" A hankali ya ce "Ok" kasa ci-gaba da ganinta haka ya yi a
hankali ya fice daga room ɗin yana jinta tana wani kukan. Anti ta tsare Alpha da idanu ta ce
"Har yanzu bata ce maka komai ba? Na yi mmki" Maman Alpha dai kallonsu kawai take da
idanu dake magana bai dameta ba, Uncle Isma'il ya ce "Lallai al'amarin babba ne tunda har ta
kasa cewa Alpha komai" Alpha bai tsaya ba ya nufi wajan Dr ya biya bills na komai kana ya
dawo ya ce "Uncle zamu iya tafiya" Anti ce da kanta ta shiga wajan Majeederh ta bata hijabi ta
zura kanta a ƙasa suka shiga motar Alpha kai tsaye kuma Gidan Abbu ya nufa, lokacin Abbu
yana zaune saman kujera yana duba littafi Anti ta yi sallama hannunta riƙe dana Majeederh sai
Maman Alpha, Uncle Isma'il da Aaliyyah da sauran napep suka shiga shiyasa tafiyar bata yi
daidai ba. Bayan sun gaisa da Abbu suka nufi ciki har kan gado Anti ta kwantar da Majeederh ta
ce "Ki kwanta ki huta sosai, Kinga ace 7 jirgin naku zai ta ce" Ta juya ta kalli ɗakin ta ce "Kin dai
gama haɗa komai?" Majeederh ta ce "Na ji sauƙi fa, na gama" Ta ce "To Allah ya ƙara afuwa,
bari ni ma duk na gaji kwana biyun nan" Mami ta yi musu godiya suka samu Alpha zaune da
Abbu Maman Alpha ta ce "Kai fa?" Ya ɗan yatsuna fuska ya ce "Momi kuje kawai, ga kuɗin
napep" Ya zaro dubu biyu ya bawa kowa duba ɗaya suka tafi, Abbu da Alpha suka ci-gaba da
magana har aka kira Magriba suka nufi masallaci a tare. Mami na haɗa abincin dare Alpha ya yi
sallama ya shigo parlourn Mami ta ce "Soja mazan fama, sai da ranka akan na wasu" Ya shafa
kai kawai bai ce komai ba ta ce "Ga abincin dare zauna ka ci" ya ware idanu ya ce "No thank
you, am full" Mami ta haɗe fuska ta ce "You're always full dama" Ta ƙara cewa "Tana ciki ai" Ya
nufi ɗakin Majeederh ya sameta zaune saman ladduma tayi wanka ta sauya kaya kanta a ƙasa,
shi kuma ya tsareta da idanu kamar zai magana sai kuma ya ajjiye takeaway ɗin hannunsa tare
da fita.
Har aka kira sallar Issha Majeederh na zaune tana azkar, turo ƙofar ɗakin aka yi Mami ce ta
shigo ta kalli Majeederh ta ce "Kizo inji Abbu" Tana faɗin hakan ta juya tabar ɗakin, sosai gaban
Majeederh ya faɗi ko sunan Abbu aka kira sai ta ji faɗuwar gaba, gudun kada ta yi laifi ya sa ta
ajjiye azkar ɗin ta nufi waje ta samu su Raihana a parlour suka dinga yi mata sannu, ta samesa
a zaune yana wanke hannu zai ci tuwo ta yi sallama ya amsata ta nemi waje ta zauna. Cikin
ɓacin rai ya ce "Ni mahaifinki Majeederh zaki tuzarta? Sbd ki nunawa duniya forcing naki nayi
zuwa Misira kika kwanta ciwo? Na haifi yarinyar da zata haɗa da ƴan-uwana Majeederh ni zaki
saka ciwon zuciya? Sbd na nemi alfarma a wajanki? Ko riƙonki nake ban cancanci ki wulaƙanta
ni ba irin wulaƙantawar da ki kai mini yanzu ba, babu komai ki je na soke tafiya Masar ɗin"
Majeederh ta zube akan ƙafafuwanta ta shiga girgiza kai idanunta cike da hawaye ta ce "Ka
yafe mini Abbu, na tuba na bi Allah na bika, wallahi ban san na faɗi ba gani na kawai nayi a
gadon asibiti, kuma bance bani da lafiya ba, bance kai kace naje karatu ba, ni nake son karatu
nina zaɓi tafiya Egypt ba kai ba, na shiga uku idan kalamanka su ka yi tasiri a gareni, ka yafe
mini na tuba na bi Allah na bika Mahaifina, ka yi mini komai yanzu ya kamata na baka farin ciki
gwargwadon yadda zan iya" Abbu ya haɗe rai ya ce "You surprised me, as your father you will
humiliate me, ni Majeederh? Har kin yi girma hakan? Ba zaki iya sacrifice akaina ba?" Jikinta
duk rawa yake ta gigice da kalamansa wani irin kuka take kamar zata haɗiye zuciya ta ce "Ka
yafe mini don Allah, ni mai laifi ce na yi alkawarin zan yi karatu zan yi aiki duk acan ƙasar, har
sai mutuwa ta riskeni ko ka bani umarnin dawowa?" Abbu ya sauke numfashi ya ce "Kin yi mini
alƙawarin zaki aiki a can?" Ya jinjina masa kai sbd kuka ya ci ƙarfinta ya ce "Allahamdu lillahi,
idan ki kai hakan kin gama mini komai Allah ya yi miki Albarka maza jeki kwanta kada ki
makara" Ajjiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa tabar ɗakin ta nufi nata tana jin kamar zuciyarta
ce zata faɗo......
A can Darmanawa a rikice Aliyu ya shiga cikin haɗɗen gidansu lokacin Hajia da Almustapha da
Papa suna zaune a parlour Almustapha ya ce "Papa amma Gwamnati mai ci a yanzu tana
ƙoƙari, na ji ɗalibai wajan ɗari biyar aka ɗauka scholarship shi, hadda allowances every month"
Papa ya ajjiye remote ɗin hannunsa ya ce "sosai ga hukumar jakadanci ta jiha ta saka hannu,
haka na tsaro, hukumomin fikira, da tawaga ta musamman duk an zuba idanu akan ɗaliban
gudun samun matsalar rikicin ƙabilanci, ko wani abu" Almustapha na ƙoƙarin yin magana Aliyu
ya shigo babu ko sallama hannunsa riƙe da kansa, Hajia ta miƙe da sauri ta ce "Zakina Lafiya?
Baka da Lafiya ne? Meke damunka?" Aliyu ya kasa cewa komai sbd parlourn dake juya masa a
hankali ya ce "Hajia lulluɓeni san yi nake ji" Hajia da bata jure rashin lafiyar yaran nata
gabaɗaya ta rikice ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Aliyuna mene ya sameka yanzu ka fita
lafiya lafiya fa?" Papa ya kalli Almustapha ya ce "Kira Dr" Almustapha ya juya da sauri zuwa
ɗakko waya, Papa ya kama Aliyu ya kwantar saman duguwar kujera sai rawar sanyi yake
idanunsa rufe jijiyoyin kansa duk sun fito, Hajia ta fashe da kuka ta ce "Na shiga uku mayu sun
kama mini yaro, yarana kwaya biyu kacal a duniya shi ne za a ga bayan ɗayan?" Papa ya dinga
kallon Aliyu shi kansa ciwon ya bashi mamaki, Aliyu dake cikin ciwo ya kama hannun Hajia ya
riƙe ya ce "Ki danna mini ƙirjina Hajia, zuciyata zata fito waje" Hajia ta ƙara saka kuka, daidai
nan Almustapha ya dawo babu jimawa Dr ya zo allura ya yi masa tambayar duniya ya faɗi meke
damunsa amma yaƙi. Suna zaune har bacci ya ɗauke shi a cinyarsa Hajia yana sauke numfashi
a wahale.. Har gari ya waye bacci baiga idanun Majeederh ba, ana kiran sallah ta tashi tayi wanka tare da
yin Sallah ta jima tana addu'a sosai kafin ta shirya cikin wata duguwar riga Maroon tayi rolling
kanta. Tana tsaye Latifa Omar ta shigo idanunta ya yi jaa taci kuka son ranta ta ce "Wai ki fito
ba lokaci" Murmushi Majeederh ta yi ta ce "Haka aka damu dani? Irin wannan kuka" Latifa ta
sake fashewa da kuka, bata hanata ba don dai itama taiwa kanta al'ƙawarin daina kuka ne, da
babu shakka sai tayi nata kafin ta tafi, safiya ce amma ƴan-uwa sun cika gidan Abbu kowa
yana son ganin tafiyar Majeederh, tafiya