Showing 72001 words to 75000 words out of 126765 words
Chapter 25 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf
ba tare da iyaye ko wani
nata ba, ta ɗaukan zai sanya mata albarka bisa namijin ƙoƙarin da tayi na zama Gwarzuwa a
musabaƙar Alkur'ani ta ƙasa, ta ɗauka zai albarkaci rayuwarta bisa burinsa data cika sai ta ji ya
ce "Na haifi ƴar da bata san girma da ƙimata ba, na haifi ƴar da take son tuna mini asiri a cikin
al'umma, na haifi ƴar da take son saka mini ciwon zuciya...,"
A gigice Majeederh ta dakatar da Abbu da faɗin "Me na yi Abbu, me aka ce nayi idan zuwa
gidan Latifa ya ɓata ranka don Allah ka yafe mini" Jikinta duka rawa da ɓari yake sbd tsoran
ɓacin ran mahaifin nata. Abbu ya dubeta sosai kana ya jawo laptop ɗinsa ya shiga Gmail ya
nuna mata wani saƙo ya ce "Hukumar makarantarku ta ƙasar Egypt take ƙorafin sun nemi
alfarmar ki zauna musu domin zama malama amma ki kaƙi bayan sun yaba miki ba za su samu
wata ɗaliba data kai ki ba" Majeederh ta ce
"Ka yi haƙuri Abbu" Ya ɗaga mata hannu cikin tsawa ya ce "Haƙuri? Kin manta al'ƙawarinmu
dake?" Ta ce
"Ban manta ba" Cikin zafin rai ya ce "Ok isa ce ban ba? Anya zaki albarka kowa Majeederh?
Kina son wanyewa lafiya?" A ruɗe ta ce
"Ka yi haƙuri Abbu, rayuwata a wata ƙasar da bani da kowa akwai hatsari ba zan iya zama ba,
na yi ƙoƙarin cika al'ƙawarin amma na kasa ka yafe mini, bana da kowa a Misira bana da mai
mini faɗa, bana da wanda zai kalla a matsayin wani nawa, bana da wanda zan zauna nayi fira
da shi" Abbu ya dinga kallon Majeederh cikin tarin tsana da ƙonar rai ya ce "Shi ɗan uwanki Alpha ba mutum bane? Da yake tafiya cikin jeji sai ya yi shekara bamu sa shi a
idanun ba, ba kuma mu san halin da yake ciki ba, gwara ke mun san inda kike...,"
Ta ce "Abbu taya zaka haɗa ɗiyarka mace da namiji? Namijin daya kusa tun karar shekaru
arba'in? Kuma zai iya kula da kansa?" Ta ƙare maganar tana sakin kuka sosai. Abbu ya ce "Ok
ke yarinyar goye ce kenan ba zaki iya kula da kanki ba? Kinga tashi maza ki bar mini parlour
idan na ci-gaba da ganinki zuciyata bugawa zatai mu zauna mu cinye ƴan kuɗaɗen da suka
rage kinga ma dawo gidan jiya talakawa" Zatai magana ya ƙara daka mata tsawa kamar ba
Mahaifinta da take mutuwar so kamar rai ba ta miƙe jiki na ƙyarma da ɓari ko kallon gabanta ba
tayi ta nufi waje ga idanunta da suke mata wani masifaffan ƙaiƙayi nan da nan sukai jajir ta
shiga susawa tana yin main parlour kuka na cin ƙarfinta, karo tayi da mutum tsaye wanda
shigowarsa kenan cikin garin Kano tana ƙoƙarin yin compound a tunaninta main parlour ne sbd
idanunta rufe yake caraf ya sa hannu ya riƙo nata hannun....
*BOOK 1 PAGE 31*
MIJIN MALAMA
LITTAFIN KUƊI NE WANDA YAKE SO YA YI MAGANA 08119237616
Ina godiya bisa ta'aziyyar da akai mini ta babban rashin da na yi na wan mahaifina Alhaji Musa
Zakari sheka ( Dagacin sheka) Na gode sosai Allah yabar zumunci marubuta da yawa wasu ma
ban san su ba, sun nuna mini kara ƙwarai makaranta ina alfahari daku kune silar kai ni inda
nake kune kuke goya mini baya ta hanyar siyan littafaina, ina fatan ba zaku gajiya ba32 Janta ya yi har tsakiyar main parlour yana zuwa ya saki hannunta yana binta da wani irin kallo
kafin ya ce "Baki da hankali?" Ta buɗe idanu wanda sukai jajir ta ce "Me na yi?" Da idanu ya
dubi shigar dake jikinta da kuma kallon fuskarta dake buɗe, itama tayi saurin kallon kanta tana
ɗan marairaice fuska zuciyarta duk babu daɗi ta kasa cewa komai sbd yadda ƙirjinta ke ɗagawa
ga zafin da idanunta suke mata duk ta sushe su. Ya gyara tsaiwa yana harɗe hannu a ƙirji shi
ma nasa idanun sun yi ja sbd abubuwan da suke masa yawo a zuciya can ƙasa ya ce "Kuma da
gaske fita zaki haka? Tsirara?"
“.... Tsirara!?” Ta faɗa da sauri cike da tsoro, Alpha ya haɗe fuska ya ce "Mene marabar dambe
da faɗa?" Majeederh ta yi shiru domin ita sam tunaninta baya nan wajan, zuciyarta ta Kaɗaita
da maganganun Abbu, lura da yanayinta ya sa Alpha bai ƙara magana ba ya bi ta gefenta ya
shige ya zauna saman kujera yana harɗe ƙafafuwan. Majeederh ta shige part ɗinta not too long
ta dawo sanye da rolling na vail a kanta, ta nemi waje saman kujera ta zauna, shiru ya biyo
baya can ta ce "Ina yini?"
"Lafiya" Ya bata amsa a taƙaice. Majeederh ta yi ƙasa da kanta cikin sanyin murya ta ce "Ance
an maka ƙarin girma congratulations" Alpha ya ce "Uhm" Yana ɗan kaɗa ƙafa kafin babu wasa
idanunsa ya kira sunanta ya ce "Majeederh!" Ta yi shiru.
"Zabiya?" Ta kwaɓe fuska tunda bata son sunan ya ɗan shafa kai daman He just wants to tease
her. Ta miƙe zata bar parlourn ya ce
"No, please" Ta zauna kamar zatai kuka ta ce "Tun ina ƙarama kake ce mini Zabiya Yaya, ni ban
so idan kai ma da Aljanar nake maka kama to"
"Stop it Majeederh!" Ya furta a tsawa ce, domin ji ya yi kamar ta caka masa nashi a ƙahon
zuciya, ya girgiza kai ya ce "Sorry"
Ta yi shiru speaking calmly ya ce "Sannu da dawowa ƙasa Nigeria, yanzu sai me?" Kanta a
ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta ce "Sai abin da Abbu ya ce" Alpha ya watsa hannu ya ce
"Kina sane da problem ɗinki, komai zaki ki fara tuna aure first" Kunya ta kama Majeederh sai
yanzu take dana sanin sanar masa da matsalarta, kuma yanzu da baya ai ba ɗaya bane tuni
Ubangiji ya ye mata "Kina ji?" Ta ce "Aiki zan nema" Da wani irin sauri ya ce "Aiki?" Ta ɗaga kai
ya ce "Shi ma Abbu ne?" Tayi shiru cike da tausayawa ya ce "Am sorry, zan masa magana ya
fara bari kiyi aure" Wani irin abu ne mai ɗaci ya tsayawa Majeederh a maƙoshi ta runtse
Idanunta tuni ta ji rauninta na son bayyana muryarta na rawa amma ta dake domin tayi
al'ƙawarin ko hawan jini zai sameta, ko zuciyarta ce zata buga ta mutu nan take ta daina yin
kuka ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Idan ya amince nayi auren wa zai aureni?" Alpha ya zura
mata manyan idanunsa ya ce "Kamarya? kina nufin tsayin shekarun da ki kai a Egypt baki
saurayi ba?" A hankali Majeederh ta girgiza kai ta ce "Even friend ban ba, shekaruna ashirin da
takwas 28 ban taɓa yin saurayi ba idan ka ɗauke Imran shi ma ya guje ni ba tare da sanin dalili
ba, baƙin jini ne dani Yaya na zama mujiya a idanun mazan duniya, hatta soyayyar ƙuruciya ban
san ya take ba, ban san daɗin soyayya da wahalar cikinta ba, ko saurayin da zai zo ya
yaudareni ban taɓa yi ba, balle wanda zai ji muradin aurena a zuciyarsa....,"
Ta yi shiru sbd numfashinta dake fisga kaɗan kaɗan kafin ta ce "Duk son da maza suke wa farar
mace, duguwa mai kyan fuska nawa ya tashi a banza, mummunar mace wada ta fini farin jini, to
idan ban yi aiki ba me zan Yaya? Shi ma Abbu fahimtar hakan ce ta sanya ya zaɓa mini wannan
rayuwar kuma ina farin ciki da ita" Duk rashin imanin Alpha kasancewar shi Soja, wanda yaga
masifu da yawa ya kashe rayuka da yawa amma a yanzu a gaban Majeederh sai dai zuciyarsa
ta karye ya miƙe tsaye ya shiga kaiwa da komowa yana bugawa hannayensa waje guda kafin
cikin sauri ya tsaya a gaban Majeederh ya ce "Majee ki minin wani al'ƙawari, do me a favor
please" Ta kasa kallonsa ya kai hannu zai riƙe nata tayi saurin janye nata tana ɗan yi murmushi
ta ce "Na maka"
Ya ja baya ganin bata son ya taɓa jikinta, numfashinsa na sauka ya ce "Kiyi accepting duk wani
abu dana yanke miki muddin ba cutarwa bane, ki yarda ba zan cuceki ba Majee" Ta ce "Me
zakai?" Ya bata amsa ya ce "Zaki ji, ki amince first" Ta jinjina kanta bai ƙara cewa komai ba, ya
fice daga part ɗin ya shige part ɗin Abbu ita kuma ta nufi Kitchen ta fara haɗa dinner harta
gama ta shige part ɗinta ba taga fitowar Alpha ba....
Washegari ya kama weekend ne, Aaliyah na zaune a parlour watching Ds t.v lokacin 10:10 na
safiyar Saturday jin ana sallama ya sanya Aaliyah ɗago kanta tana amsawa da faɗin
"Wasalamu Alaiki, Anti Latifa" Latifa ta zauna tana cewa "Ashe fa yau weekend da tuni kina
school" Aaliyah ta yi murmushi ta ce "Ina kwana?" Ta amsa da "Lafiya lou" Sukai shiru can
Latifa ta ce "A level nawa kike ne yanzu?"
“... 200" Aaliyah Said, tana ɗan buɗe Idanunta akan series ɗin _My heart knows_ da take kallo a
zee wrld. "All The best little sister, ina Malama?" Aaliyah ta nuna mata hanyar kitchen da hannu
ta ce "She's in the kitchen" Lura da hankalin Aaliyah nakan series ya sanya Latifa miƙewa ta
nufi hanyar kitchen ɗin tana zuwa ta samu Majeederh tsaye gaban sink tana wanke hannunta
tayi dariya ta ce "Sannu da aiki Madam koko" Majeederh ta ɗan yi murmushi ta ce
"Uhm" Latifa ta ce "Gasky am lucky na samu abinda nake so"
“... Kike so? Ko ya ke so?"
Latifa ta ce "Shi wa?"
Majeederh ta watsa mata harara tana ɗauke plate ɗin data wanke ta ce "Nasan ciki ne dake"
Latifa ta ce "A'a ba ciki ba, baya ne dani" Ta faɗa tana tofar da yawo a bakin kitchen ɗin har sai
dai Majeederh ta runtse idanu a ɓoye.
"Ni dai zuba mini breakfast yunwa na ke ji" Da mamaki Majeederh ta ce "Idan na baki mijinki
fa?" Latifa ta jima tana kallon Majeederh can ta ce "Na yi fa, idan ni nayi bana iya ci sai na
kwaɗayi" Bata ce mata komai ba, ta haɗa mata breakfast fal cikin warmer hadda kunun gyaɗa
mai kyau, tana bata tayi godiya ta fita a hanya taci karo da Raihan tana shigowa cikin
compound ɗin a haɗaɗɗiyar motar ta, bata kulata ba ta fita tare da shigewa nata gate gidan...
Lokacin da Raihana ta shiga gidan duk suna parlour suna breakfast ta cire mayafinta tare da
ajjiye hand bag ɗinta tana zama saman dining ta ce "Ki ce nazo a daidai" Aaliyah bata ce komai
ba haka ma Majeederh, sai da Raihana ta kai abinci bakinta ta ce "Majeederh ba gaisuwa?" Da
sauri Aaliyah ta ce "Wakike so ta gaisheki Anti Raihana?" Kai tsaye ta ce "Majeederh?" Baki
buɗe Aaliyah ta juya ta kalli Majeederh kana ta kalli Raihana ta ce "Anti Jeederh ce zata
gaisheki? Bama ke ki gaidata ba?" Raihana ta ce "Ai ni ya dace ta gaisar" Aaliyah da ranta ya
fara ɓaci ta ce "A sbd kin haifeta? Shekaru nawa Anti Jeederh ta baki?" Raihana ta saki dariya
hadda buga dining ɗin dake gabanta ta ce "Ji banza wake ta ƙama da shekaru? Ai tunda nayi
aure to yanzu ni ce gaba da ita, bayan nayi aure haihuwa zan yi Kinga durƙosawa wada ba
gajiyawa bane ko? Ai aure shi ne martabar ko wacce mace, kiyi ƙoƙari ki aure sai mu iya haɗa
kafaɗa dake"
Aaliyah ta miƙe tsaye itama tana sakin dariya ta ce "hehehe, matar na tuba bata rasa miji aure,
ai dake da Anti Jeederh da ke kwaryar sama ce take dokan ta ƙasa, mene marabarki da ita?
Sunan kinyi aure amma kullum kina hanyar barbaɗa na zuwa gida ana ƙarar da albarkar aure
akan titi, Anti Jeederh da izinin Ubangiji ba zatai auren barbaɗa irin naki ba, zata auri miji wanda
yake kishinta yake sonta wanda zai jure duk wani ƙalubale nata wanda zai sota fiye da yadda
take son shi zatai aure inda aka san darajarta, ba zata taɓa auren wanda zai sallamawa duniya
matarsa ba" Aaliyah ta riƙe ƙugu ta ce "Mema kika ce haihuwa? Ai sai dai kici ki haifi kashi ba
dai ɗan mutum ba, domin juma'ar da zatai kyau tun daga laraba ake ganeta....,"
Hannu Raihana takai zata kifawa Aaliyah mari tayi saurin ja baya, Raihana na huci ta ce "Zan yi
maganinki dan uwarki idan ni sa'arki ce" Aaliyah ta zare idanu ta ce "Ni na isa na haɗa kaina da
uwar mata mai aure? Wlh wani ya kalleki sai ya ɗauka kin yi shekaru 20 da aure duk kin
rakwaɓe kamar tsohuwar mota" Wani baƙin ciki ya turnike Raihana ta ce "Ni kike faɗawa haka?"
Sai a lokacin Majeederh ta tashi ta zabgawa Aaliyah mari ta ce "Ya zama ƙarshe" Aaliyah saka
kuka sosai ta ce "Na gaji Anti Jeederh na gaji da abinda suke miki, su basu da aiki sai gorin
aure? Kamar ke zaki aurar da kanki sun manta komai lokaci ne? Ita Anti Raihana da take yin
ɓari ta taɓa zama ta tambayi kanta me yasa cikin baya zama? Da aure da haihuwa da arziƙi
duka na Allah ne, wani jinkirin alheri ne kuma da aure irin nasu wallahi gwara mutum bai aure
ba, mata nawa suke aure amma baya zuwa ko'ina auren ke mutuwa" Majeederh na ƙoƙarin yin
magana suka ji gyaran murya a tare suka juya Alpha ne tsaye hannunsa harɗe a ƙirji fuskar nan
kamar an aika masa da saƙon mutuwa, yana sanye cikin wani jeans da Racing jersey ya saka
p.cap a kansa sai ƙamshi yake. Gabaɗaya sukai shiru jikin Aaliyah da Raihana ya ɗauki rawa
musamman Aaliyah domin tasan Alpha baya son raini da rashin kunya ga babba bakinta na
rawa ta ce "Ya...yaya A.b don Allah....,"
Hannu ya ɗaga mata, idanunsa akan Raihana ya ce "Ke dan kan uwarki Majeederh sa'arki ce?"
Raihana ta yi shiru ya ƙara sakar mata tsawa ya ce "Shegiya munafuk za kici ubanki daga ke
har mijin da kike tunanin kin aura wanda yasa kikewa wata gori akan haka, duk sanda na ƙara
ganin ƙafarki a gidan nan without any reason wlh sai na kusa karya ki" Ya nuna mata ƙofa ya ce
"Bar nan wajan kafin na karyaki na karya banza, shi ma mijin naki bashi da tunani bai san
ciwonki bane" Ganin ta juya zata shige part ɗin Mami yasa ya nufeta ta kwasa a guje tana
kurma ihu ta faɗa part ɗin Mami, tsayawa ya yi yana shirin komawa kan Aaliyah yaga wayam
babu ita sai Majeederh dake tsaye. Bai ce mata komai ba ya juya zuwa part ɗin Abbu. Mami ta
kalli Raihana dake haki duk tayi wujiga-wujiga ta ce "To shi haka ake bai ji ta bakin kowa ba sai
ya hau faɗa?" Raihana ta ce "Shi daman baya son mu ai, ya fi son Anti Jeederh da Aaliyah he's
so selfish" Mami ta ce "To ai shi ba Allah bane, kuma ke matar aure ce yana dokanki Shari'a ba
zata barsa ba, yabar ganin shi soja ne wlh garƙame shi za ai a bayan canter" Raihana tayi shiru
Mami ta kalleta ta ce "Kema bana son rashin ta ido, ina ke ina zabgawa Majeederh wannan
maganganun? Kar na kuma ji balle ki ja mini zagi" Raihana ta tura baki Mami ta ƙara cewa "Yau
kuma me ya kawo ki?" Ta ce "Jiya da daddare ya dawo, ya kuma da asubar fari a haɗa kayansa
wai wani aiki ke ya taso masa" Mami ta zabga tagumi ta ce "Shi kuma ƙaddararsa kenan
tafiye-tafiye? Wai aikin me yake ne?" Raihana ta ce "Ni ban sani ba" Ta ce "To Allah ya
kyauta"...... Kwana biyar kullum sai Alpha ya zo wajan Abbu ba tare da sanin meke kawosa ba,
da yamma liƙis Anti ta shigo gidan ƴarta Sona bayan sun gaisa da Mami ta ce "Ina Majeederh?"
Mami ta ce "Ta leƙa gidan Latifa daga nan ance sun fita" Kafin Anti tayi magana Majeederh ta
shigo bakinta ɗauke da sallama Anti ta amsa "Daga ina kike?" Majeederh ta ce "Mami gidan
Latifa" Cikin faɗa Mami ta ce "Ji munafukar ƙarya ba ance kun fita ba?" Majeederh ta ce "Oh na
rakata asibiti na sameta tana ta amai ne ashe ɓari za tai" Mami ta ce "Au ciki ne da ita?" A
hankali ta ce "Eh" Mami ta ƙara cewa "Yanzu ya ɓare cikin?" Nan ma Majeederh ta ce "Eh"
Mami ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah, wannan ɓarinta na uku kenan, mahaifarta ce bata da ƙauri
ina zato" Babu wanda ya yi magana tsakanin Anti da Majeederh, Mami ta gyara zama ta ce "To
me Likitoci suka ce kuma" sai a lokacin Anti ta ce "Haba Asabe wannan tambayoyi kashi da
kashi ita yanzu Majeederh me zata ce?" Mami ta ɗan yi murmushi, Anti ta ce "Daman abin
alheri ya same mu" Mami ta ce "Ma sha Allah" Anti ta kalli Majeederh kana ta ce "Alpha ne yake
son Majeederh yana son ya aureta" Da wani irin Shock mai kama da mamaki Mami ta ce "Shi
Alpha ɗin? Kuma Abbu ya amince?" Anti ta ce "Shi ne ma ya saka ranar auren ai" Da wani irin
Scorned expression Mami ta ce "Ikon Allah bani da labari Allah ya sanya albarka" Majeederh ta
yi shiru She couldn't say a word sai bin Anti da idanu take. "Majeederh kin amincewa da yayanki
kuma ɗan-uwanki Alpha? Kin aminci ya zama mijinki?" Buri Majeederh ta auri wanda ya san
kima darajar ta, wannan yasa take yawan kallon Alpha matsayin crush ɗinta take jin inama ya
aureta? Ganin bashi da interested akanta yasa bata taɓa sanyawa ranta ba, Majeederh ta tsinci
kanta cikin tashin hankali sbd babban burinta ta zama matar A.b Alpha Bello, It's her dream tun
sanda ta buɗe idanu ta gansa yana kula da ita, She can't afford to lose him, her life will be
incomplete without him, She's felling scared and restless me yasa