Showing 3001 words to 6000 words out of 126765 words

Chapter 2 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf

ya sa hakan? Zaka bawa Anti Jeederh tikiti shiga duniya da
hannunka,bayan komai ta aikata kana da kamasho akai ba ita É—aya ba, mene ya sanya zaka
hofintar da MACE MUTUM kamar Anti Jeederh,ita É—in haske ce, farin ciki ce ta ji da iya
jarrabawar da take ciki ta rashin aure da kallon da jama'ar gari suke mata, kayi bincike Abbu,
kada ka yi ladama a lokacin da bata da amfani"
Hannu ya sanya ya ɗauke Aaliyyah da mari yana huci ya ce "Ba zan taɓa ladama akan na rabu
da wannan shaiÉ—aniyyar yarinyar ba, wacce ta cuceni ta cuci tarbiyyar dana bata, babu abin da
zan iya cewa Majeederh sai Allah ya isa, ban yafe ba, ban yafe har na koma ga mahalaccina ba
zan yafe mata ba" ya juya ya kalli sauran yaranshi da matarshi ya ce "Ni Abdul'aziz Khan na yanke dukkan mu'amalar dake tsakanina da Æ´ata Majeederh Abdul'aziz
Khan, ko da wasa ta ƙara ambaton sunana a matsayin ni ne mahaifinta wallahi sai na tsine
mata, domin ni a wajena bata da maraba da gawa! Duniya ce ki je zaki gani"
Ba fatan gaskiya Majeederh take ba, ba kuma neman afuwar Abbu take ba, domin shi É—in kaifi
guda ne, amma tasan zai yi ladama a lokacin da bata da amfani kamar yadda Aaliyyah ta ce.
Burin Jeederh shi ne Allah ya bayyana mata uban Jaririn nan, ko itama zata samu damar tsine
masa, tayi masa Allah ya isa kamar yadda Mahaifin daya kawota duniya ya yi mata, ta yi masa
mummunan fata a rayuwarshi ta yi masa addu'ar É—aukewar dukkan wani jin daÉ—i walwala na

tsayin rayuwa, damuwa da ƙunci su mamaye farin cikinsa, duhu ya maye gurbin hasken daya
haska duniyarshi.
"Tashi ki ɗauki shegen danƙi ki bar mini gida" Aaliyyah kamar zata haukace ta ce "Mami ki
sanya baki don Allah, Abbu ina Anti Jeederh zata nufa? shin tana da gidan da ya fi wannan
ne?" Sai a lokacin Ruma ta ce "Aaliyyah kada ki sanya na fara zargin kema kin munafurci Abbu"
Aaliyyah ta juya ta kalli Ruma ta ce "Me kike nufi?" Ruma ta ce "Ina nufin abin da kunnuwanki
suka je yi miki, kin jima da sanin Majeederh nada cikin shege ki ka ɓoye"
Wani irin mugun kallo Aaliyyah ta watsawa Ruma ta ce "Ki ji tsoron Allah, kuma akwai ƙiyama,
Mami do something"
"Something?" Mami repeated. "Don Allah" Aaliyyah ta sake furtawa Idanunta ya kumbura sosai,
tausayin Malama Majeederh ya kamata tasan tunda Majeederh ta kasa cewa komai hakan na
nufin abubuwa da yawa.
Mami ta kalli Majeederh ta ce "Ki duba Majeederh babu alamar dana sani a idanunta, ni kai na
da nake uwarta ta yaudareni, sai yanzu nake mamakin abin da ya hanata aure ashe mu muke
hauka ita ta jima da sanin kan É—a namiji shi ya sa babu littafin aure a cikin littafan da take
wallafawa, kin ja mana abin faÉ—a" Da sauri Abbu ya ce
"Ta jawa kanta dai, domin ban haɗa komai da ita ba, ta je hakƙin Addinin Musulunci ma kaɗai ya
ishe ta, kafin na buÉ—e idanu ki fice daga gidan nan"
Zuciyarta tayi nauyi bata da hanyar kare kanta, fatan ta Ubangiji data yarda da shi,kuma take
bautawa ya bayyana gaskiya ya wanketa a wajan Mahaifinta ko da ba zai amsheta matsayin Ƴa
ba. Ta juya ta kalli Jaririn ko Jaririya domin bata san me ta haifa ba, amma tasan samuwar
babyn na nufin wani abu! Only God knows. Da hannu biyu ta ɗauki jaririn ta miƙe da ƙyar jiri na ɗaukarta, ga wani ciwo da cikinta ke mata
har yanzu mahaifa bata faɗo ba. Kanta a ƙasa cikin wata murya mai tsananin rauni wacce ko
fita ba tayi sosai sbd yadda numfashinta yake riƙewa ta ce.
"Me ya sa zaka mai dani Gawa bayan da rai a tare da gangan jikina? Bayan da numfashi a
ƙirjina? Me ya sa zaka bawa duniya ni Abbu wallahi bana da laifi ban san samuwar cikin ba, ban
san waye da wannan alhakin ba, ban san waye yake da sanya hannu wajan ruguza rayuwata
ba, ban san waye ya zama silar rabani da Mahaifina, dangina, haÉ—i da farin cikina ba, zan tafi
Abbu ina roƙan ka yafe mini a duk sanda gaskiya ta bayyana ko da ƙasa ta rufe mini Idanu, zan
raini kyautar ALLAH, zan raini Raba Gardama shi ne hujjar da zata iya fiddani daga zargi, Allah
ya haÉ—a fuskokinmu da alheri"
Aaliyyah ta cire hijabin jikinta ta sakawa Majeederh domin rigar barci ce kawai a jikinta, kuka
take sosai tana faɗin. "Kiyi haƙuri Anti Jeederh bana da ikon taimakonki na kasa aikata komai
kiyi...,"
Kuka ya ci ƙarfinta ta juya da gudu ta shige ɗaki ba zata iya ganin tafiyar yayarta ta ba.
Gently Malama Majeederh ta kalli Mami, ta juya ta kalli Ruma, da kuma Raihana wacce bata ce
komai ba har yanzu. Ta jima tana kallon Mahaifinta kafin ta nufi hanyar barin parlourn jiri na
ɗaukarta, tana jan ƙafa wacce ko takalmi babu ta buɗe gate tare da ficewa daga cikin gidan,
kamar yadda take barin gidansu haka numfashinta ke barin ƙirjinta, ganinta na janye wa, jinta
na raguwa, jaririn hannunta na neman ƙwacewa zuwa ƙasa.
Tafiya take jini na bin cinyoyinta, tafin ƙafarta na taka kan titi, tun tana jurewa har ƙafarta ta fara

rawa jikinta ya saki ta ƙanƙame jaririn a ƙirjinta, slowly slowly ta fara ganin duhu a Idanunta tayi
baya luuu! Zata faɗi a kayi saurin tare ta, ta faɗa jikin mutum ba numfashi a ƙirjinta.

Hospital
A hankali aka buɗe Ƙofar room ɗin tare da mayarda ita aka rufe slowly. Tsaye ya yi a kanta ya
zuba mata narkakkun idanunsa ya ɗauki almost 5 minutes yana kallonta kafin ya ɗaga ƙafarsa a
hankali zuwa gaban bed É—in, ya ja kujera tare da zama akai, cikin nutsuwa ya sanya hannu ya
É—auki jaririn dake kwance yana motsi cikin tattausan showel É—in da aka saka shi. Soyayyar
Jaririn ya samu gurbi a zuciyarsa musamman da bai taɓa samun ɗan kansa ba, bai taɓa ganin
gudan jininsa ba. "Ohh baby, your Dad is here" ya furta can ƙasa gudun kada ya tashe ta.
"His Dad?" Ta furta cikin magagin barcin dake É—aukarta domin allurar bai gama sarkinta ba.
Ya ɗago kai da sauri ya kalleta ba ƙaramin harbawa zuciyarsa tayi ba, this is the first time da
yaga fuskarta babu liƙab iya tsayin shekarun daya santa.
Kasa magana ya yi domin duk yadda zuciyarsa ke fasalta masa kyanta abin ya shige haka,
musamman da tayi maganar kamar wacce bata hayyacinta idanunta rufe gashin idanunta sun
kwanta luf luf gwanin sha'awa fuskarta ta ƙara haske.
"Kin farka? Ya jikin"
Muryarsa ta daki dodon kunnenta yanzu kam allurar ta gama sakinta ta buÉ—e manyan Idanunta
da suka kumbura tare da sauke ganinta akan Aliyu Sufyan Alhassan. Ta runtse idanu yau ƙarya
ta ƙare fuskarta available, Allah ya rufa mata asiri jikinta a rufe yake.
"Sorry, In sha Allah komai ya zo ƙarshe zan wankeki wajan Abbu be patient" bata kalle shi ba,
domin ƙirjinta ya yi mata nauyi babu wanda ya sake magana har Aliyu ya ce "I love my son, i
love both"
"Ka barni" ta furta a kame cikin sanyin harshe. Aliyu ya gyara zama idanunsa akan fuskarta duk
da bashi take kallo ba. "You're dreaming, ba zan sake kuskuren baya Jidderh,ba zan sake ba,
ina son rayuwa da yarona tare da mother's of the son"
"Ni guba ce, zan iya zama illa ga kowa" ya tari numfashinta ya ce
"Ban dani Aliyu Sufyan Alhassan, ban dani Jeederh" ta juya ta kalle shi kallon daya kusa zautar
da shi hannunta ɗaya a ƙirjinta ta riƙe sosai cikin nutsuwarta da kamilalliyyar muryarta ta kame
kanta sosai ta ce. "Baka da haÉ—i da É—ana, kada ka yaudari kan ka ka duba kusancinmu da Latifa
ka barni" "Jeederh idan na barki ki É—auka na bar duniya, Latifa kuma ta bani full opportunity na
aurenki" cikin gajiya wa ta ce "ba zaka saman ba"
"Koda na halattawa kai na zama Uba ga danƙi? Wallahi Majeederh na shirya ɗaukan ko wanne
ƙalubale akan ki, kuma idan wannan yaron zai sanya ki aureni zan je court ta mallaka mini
shi,wanne Irin mallakawa ma? Bayan blood grp É—ina da na shi É—aya ne, ko DNA text za a yi zai
tabbatar da ni ne uban shi" Wayarsa ce ta fara ringing sunan Wife ya fito ya É—an ja tsaki har
kiran ya tsinke aka sake kira lokacin Jaririn ya fara kuka, picking call É—in ya yi tare da saka
wayar a hands free.
Muryar Latifa na rawa ta ce "Sweetheart kana ina? 3days without you ina ka je ina ta kiran
number ka a kashe" ba yabo ba fallasa ya ce.
"Ya akai Latifa?"
"Wani abu mai kama da almara ya faru, na kasa sanin babin da zan iya sanya Malama
Majeederh"

Aliyu ya ce "Just go to the point Wife" cikin damuwa Latifa ta ce "Majeederh ta haihu,na goya
mata baya amma ta bani kunya ta sanya ina yawo da ita har ina kare cikin shege?" Ya tare ta
faÉ—in
"Who told you that?"
"Ruma, ta kirani tun a daren da abin ya faru lokacin na tashi naga babu kai babu motarka,
kwana uku kenan yanzu haka Majeederh ta gudu da É—an gudun surutun jama'a kuma ta shaida
É—an shege ne, Ruma ta ce Majeederh ta bayyana musu cewa daga gidan Abbu ba inda zata sai
gidan uban É—an taci gaba da zaman karuwanci da shi" Duk maganar da suke Majeederh na ji, tuni ta amshe É—anta daga hannun Aliyu ta rungume
shi,tana jin kawo yanzu shi ne kaÉ—ai ya rage mata, shi zata kalla matsayin wani nata kuma zata
kula da shi da dukkan iyawarta har kawo lokacin da gaskiya zata kure ƙarya.
"Ke yanzu kin Yarda Malama Majeederh Abdul'aziz Khan zata iya aikata ZINA?"
"Me zai hana Sweetheart? Tunda ga gaskiya ta bayyana kuma Allah ya isa tsakanina da ita, na
gode Allah da ya sanya baka aureta ba, balle mu haÉ—a iri da shege" "Ba shege bane"
Da ƙarfi ta ce "Wallahi shege ne" cikin tsawa mai firgitarwa ya ce
"Latifa Omar idan ki ka sake sheganta mini yaro zaki sha mamakina, zan miki hauka zan nuna
miki true color na" Majeederh ta dafe kanta a hankali ta miƙe bayan ta zare ƙarin ruwan da ake
mata, ganin Aliyu ya juya baya yana masifa jijiyoyin kansa na motsawa ta sulale a hankali ta bar
room É—in rungume da jaririn nata. Kamar mahaukaciya haka ta zama, Latifa ta hargitse tamkar zata cinnawa kanta wuta ta ce
"Aliyu Sufyan Alhassan kasan me ka ke cewa? Mene haÉ—inka da yaron?" Cikin rashin damuwa
kuma daman ya shirya amsar ko wanne ƙalubale ya ce.
"Yes that's my name Aliyu, kuma baki taɓa jin nayi hauka ba sai dai ina dab da shirin manna
bikin haukan ke, tunda ba soyayyar gaskiya ki ke nunawa Majeederh ba"
Latifa ta zari key É—in motar ta ce "Don't Tell me kana tare da Majeederh tsayin kwanaki ukun
nan?" Ya ware hannu irin he don't care É—in nan ya ce.
"Yhh, Ina tare da ÆŠana da matata, Majeederh is my wife....



08119237616*🌈MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv Sarauta
*_Arewabooks@Nimcylub_*

*3.....*
Maganganun Aliyu suka kusan tarwatsa mata zuciya, idanunta ya rufe kafin tayi magana ya ce
"Ko a lokacin da nake yaro, ban taɓa kuka saboda wahala ba, ba kuma zan yi kuka saboda abin
da zaki aikata ba, ki sawa ranki ba a haifi Aliyu domin sadaukarwa ba, amma an haifi ni domin
bautawa Ubangiji da kuma cimma burukana, bana da burin daya shige zama da Malama
Majeederh Abdul'aziz Khan!" Ya fesar da numfashi ya ce
"Ban taɓa neman abu na rasa ba, kin san yadda nake zama mahaukaci akan abin da nake

so....," Da ƙarfi Latifa ta ce "And so what Aliyu? Ni kuma zan tabbatar a wannan karan na zama
sanadin da zaka rasa abin da ka ke nema, ka yi ta farauta wacce bata da amfani har zaki ya yi
gaba da abin farautar taka, zaka san kuma kaci amanar matarka ni Latifa Omar zaka sani" tayi
hanging off na kiran. Tsakanin ita da Aliyu ba a san wanda ya fi wani shiga damuwa da baƙin ciki ba, shi yana jin
baƙin ciki idan ta shegenta ɗan gidan Jeederh, yana jin tamkar gudan jininsa ta shegenta. Latifa
Omar tana ganin Majeederh ta munafurceta tayi mata kyakkyawan zato ta ci amanarta, Allah
kaɗai ya san lokacin data ɗauka tana bin baza, ko komai nata zai ƙare ba zata taɓa barin Bar
Aliyu Sufyan Alhassan ya kasan inuwa guda da Jeederh ba.
Ta dunƙule hannu tare da kaiwa iska naushi cikin zafi ya juya yana faɗin.
"I can't take it any longer Majeederh, dole kiyi haƙuri mu zama abu guda" shiru not respond.
Ya riƙe ƙugu cikin sauke numfashi yana son ya saisaita kan shi ya kasa ya ce. "Ina son na je
wajan Dr Jamal, i have something to discuss with him" nan ma shiru sai a lokacin ya juya zai
sake kiran sunanta yaga wayam! sai gado da drip yana ɗiga a ƙasa.
Baki buɗe ya tsaya cak yana ƙarewa room ɗin kallo kamar ƙungi.
"What?" Cikin sauri ya buɗe ƙofa ya fita suka ci karo da wata nurse ya ce
"Heee Nurse" "Yes, Sir how can i help you?"
Ya juya idanunsa ya yi ta kallon wajan yana son yaga ta ina zai gano Jeederh. "Sir!" Kiran ya
dawo da shi hankalinsa ya ce "Kinga wata yanzu da baby a hannu ta fita?" Ta shiru alamar
tunani sai kuma ta ce.
"Yanayinta?" Ya ce "She's beautiful, fara tas yar yellow take tana da jiki zata kai 35 yrs going to
36" Ta kalli hanya ta ce
"Oh Malama Majeederh Abdul'aziz Khan?" Ya É—aga ya ce "Exlty, where she's?" Ta ce "She Left,
alright"
Ya yi baya a fili ya ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, why? why Jeederh mun shiga uku daga ni
har ke" da gudu kuma yabar world É—in ya nufi reception har zuwa parking lot na hospital É—in
amma babu ko mai kama da ita.
Motarshi ya shiga tare da yi mata key kamar zai tashi sama haka yabar cikin asibitin bakiÉ—aya
wanda ya yi kwana Uku ciff a cikinsa.
Dr Jamal na zaune a office É—insa yana operating system sai gumi yake duk da sanyin A.cn dake
office ɗin. Bell aka danna ya ce "Come in" buɗe Ƙofar akai tare da shigowa.
"Dr Jamal wai meke faruwa da kai ne, kwana uku baka cikin hayyacinka" ya share zufa ya ce
"Tajju ina cikin damuwa"
"Problem?" Tajju ya maimaita. Dr Jamal ya gyara zama ya ce "Ka san Malama Majeederh
Abdul'aziz Khan?" Gaban Tajju ya faÉ—i hakan ya tuna masa da wasu memories ya ce "Uhm, ina
jinka" kai tsaye Dr Jamal ya ce "Ta haihuwa, kuma yanzu an nemeta an rasa, kwana kenan
bana barci kullum sai na duba all scanning da na taɓa yi mata, wallahi tsayin shekara biyu result
bai taɓa nuna mini Majeederh nada ciki ba ko da wasa, infact results ɗin na nuna she's Good,
sai a satin nan dana sake mata wani ya nuna mini ƙari ne a cikinta shi ne ya haddasa kumburin
Cikin, sai gashi kuma wai ta haihu harta gudu" cikin wata kalar hausa Tajju ya ce
"Innalillahi, subuhana"
Ya yi ta maimaita wa kafin ya ce "Amma tayi aure?" Dr Jamal ya ce
"Ko engagement ba tayi ba balle aure, bata taɓa aure a zahiri ma babu wani ɗa namiji daya

taɓa cewa yana son ta"
Tajju ya miƙe ya shiga kai kawo cikin office ɗin da sauri kuma ya fice yana cewa "ina zuwa"
Yana fita mota ya shiga ya nufi gidan shi dake cikin Nassarawa. Tun da ya shiga bedroom yake
tunani,akwai muhimmin abu da yake son tunawa amma ya rasa mene? Dr Jamal abokin Tajju
ne gabaÉ—ayansu likitoci ne.
A hankali ya ce "Malama Majeederh Abdul'aziz Khan? Ya Allah!"
Kwanciya ya yi nan take barci kuma ya É—auke shi.
Can cikin barcinsa ya ci wasu maganganu na tashi a kunnenshi a firgice ya farka yana haÉ—a
zufa jikinsa na rawa ya ce.
"Gang" ya miƙe ya ce "Gang team!" a haukace Tajju ya dinga fito da kayan wardrobe nasa cikin
sa a wata envelope ta faÉ—o ya É—auka da sauri yana dubawa, har yanzu wani sassan yan
ƙamshi ke tashi jikin envelope ɗin, ya duba da kyau idan har ba zai manta ba shekaru biyu
kenan da bashi saƙon ya bawa Majeederh, shi kansa ba zai iya tuna abin da ya mantar da shi
ba. A hankali ya duba jikin envelope da aka rubuta.

*_No words to explain, no words to describe, no words to as your forgiveness, Wait for
me, I'll be back sooner or later, Please Jee_*

Tajju na gama karantawa ko gyara bedroom É—in bai ba ya zari key É—in mota tare ficewa daga
cikin gidan, tana ina zai fara? Ina zai ga Malama Majeederh har ya bata wannan saƙon? A fili ya
ce "Allah na tuba, ban san me ya mantar dani ba" haka yaci gaba da driving.
Tun safe Majeederh take tafiya fuska rufe babyn ya yi shiru a jikinta, kamar mahaukaciya haka
ta zama bata gane komai bata bambance komai, kiran sallar Magriba ya yi daidai da tsayuwarta
a gefen wani shago a lokacin kuma babyn ya kama kukan yunwa, ta samu waje ta zauna ta
shiga kallon fuskar jaririn ko Allah zai sanya ta gane dawa yake kama, amma abin mamaki
komai nata ne, kamarsa É—aya sak da ita idanunsa ne kawai da bai fiya buÉ—ewa ba yasa bata
gama gane ƙwayar tawa ba, ganin kukansa zai sanya hankalin jama'a ya dawo kanta ya sa ta
zura shi cikin hijabi bata san me zatai masa ya daina kuka ba can ta tuna abincinsa yana jikinta
ta É—aga rigar asibitin dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login