Showing 75001 words to 78000 words out of 126765 words
Chapter 26 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf
take jin tsoro?... "Majeederh"
Anti ta kira sunanta. Ta ɗan kalleta kana ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce "Kina son auren
Alpha?" Majeederh ta ce "Anti ai zaɓi ba nawa bane kamar taimakona ya yi" Anti tayi shiru sai
kuma ta ce "Shikenan jeki Allah yasa haka ne alheri a rayuwarki" Miƙewa tayi ta shige bedroom
amma deep down na zuwarta mamaki take anya shi yace zai aureta? Mai yasa bai fara neman
Soyayyarta ba? "Ke da za a taimakawa ina ruwanki da neman soyayya?" zuciyarta ta bata
amsa.
Da daddare bayan Majeederh ta gama dinner tayi sallar Magriba tana zaune tana azkar wayarta
ya yi ringing ganin sunan Alpha yasa gabanta faɗuwa har kiran ya katse bata ɗauka ba, wani
kiran ya sake shigowa ta yi bismillah ta ɗauka a hankali ta ji ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Me
kike?" A hankali ta ce "Azkar" Ya yi jim ya ce "Shi ne baki picking kiran farko?" Ta ɗan
marairaice ta ce "Kayi haƙuri" Ya share maganar ya ce "Majeederh" Ya kira sunanta ta kasa
amsawa ya ce "Wannan shi ne hukuncin dana yanke mana, ina fatan banwa rayuwarki
Shisshigi ba, idan kuma baki so na baki son aure let me know first" Ta yi shiru Ya ce "Kina son
Aurena? Majee?" Da sauri ta kashe wayar tana rufe Idanunta kamar yana gabanta, daga can
ɓangaren murmushi Alpha ya yi kana ya kashe wayar ya shiga Parlourn Mahaifiyarsa zaune ya
sameta ya ce "Sannu da dare Mama" ta ɗaga masa hannu ta ce "Ya isa" Tana faɗin hakan ta
miƙe tare da ficewa daga parlourn...... Ciki sati gudu wata muguwar shaƙuwa ta wanzu tsakanin
General Alpha Bello da Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Tana jinsa har cikin zuciyarta gashi
da masifaffen kishi, Anti ta kira mai gyara aka shiga yiwa Amarya Majeederh wani mahaukacin
gyara, sosai Alpha yake kashe kuɗi har kawo lokacin ko hannu Majeederh ta hana ya riƙe
mata..... Ana saura kwana ɗaya ɗaurin aure tun safe aka haɗa Family meeting gidan Uncle
Isma'il an cika sosai yara da manya maza da mata, Alpha ne kawai babu a wajan can Uncle
Bello ya ɗakko wayarsa ya kira shi yana ɗagawa ya ce "Wanne irin iskanci ne haka? Mu zamu
zauna zaman jiranka?" Muryarsa can ƙasa Ya ce "Am sorry" Uncle Bello ya kashe kiran babu
jimawa ya shigo kansa a ƙasa ya zauna can kujera, aka buɗe taro da addu'a Uncle Isma'il ya ce
"Ma sha Allah, a gobe In sha Allah muna da ɗaurin auren da zai kafa tarihi a Khan family" Cikin
sauri Alpha ya ce "Auren wa za'a ɗaura Uncle?" Gabaɗaya aka kallesa cike da mamaki Uncle
Isma'il ya kasa bashi amsa, Alpha ya ce "Me ya sa kowa ke kallona? Why are you staring at
the?" Anti ta ce "Gidanku General Aurenka mana" Ya ware idanu ya ce "Aurena kuma Anti?
Dawa?" Ta ce "Da Majeederh" Ya ƙara waro idanu ya ce "Wacce Majeederh? Ni zan yi aure
kuma Majeederh zan aura?" Innati ta ce "Ji wawa dilla kuyi abinda ya kawo ku" Uncle Isma'il ya
kwaso katin ɗaurin auren ya ce "Gashi nan It's too late ka bawa friends ɗinka" Alpha ya kwashi
katin da Shock ya dinga bin sunansa da idanu da kuma na Majeederh ya ɗago kansa ya ce "Ke
ni na ce zan aureki? Wai meke faruwa ne?" Uncle Bello ya miƙe ya zabgawa Alpha ya ƙara
zabga masa ya ce "Bana son hauka, lokacin da kazo da maganar aurenta kwana bakwai daga
shige uban waye ya yi maganar ba kai ba?" Alpha ya girgiza kai ya ce "Wallahi Abba ni ban
taɓa cewa ina sonta ba, ni me zai saka na aureta ƙanwata ce fa?" Innati ta ce "To da sauƙi
tunda ba nono ɗaya kuka sha ba" Alpha ya ce "Uncle,Abba this is misunderstanding wlh ni
bance zan auri Majeederh ba infact ina da wacce nake so kuma gobe zan kawota ku ganta don
Allah kada ku aura mini Majeederh.......
*BOOK 1 PAGE 32*
*MIJIN MALAMA*
_littafina na kuɗi idan kina so ki biya ki karanta.... 08119237616 ko yayane kada ki karanta free
without my permission please siyan littafinmu shi ne nuna soyayya a garemu_
*Ƙaddarar mace abace mai wahala musamman ƙaddarar za dinga maka gori da ita, ana ganin
kamar ganganci ne ko kuma kai ka ɗorawa kanka ba yin Allah bane Yadda da ƙaddara shi ne
cikar imanin mutum, Ubangiji bai baka abu ba hakan na nufin abin nan ba alheri bane a gareka
da rayuwarka, ƙaddara na tafiya da lokaci shi kuma lokaci ne abu ne da baya jira, hakan na nufi
ita kanta ƙaddarar ba tabbatacciyya bace, akwai lokacin da zai zo ta zama tarihi... Wani jinkirin
alheri, rasa abu baya nufin rasa rayuwarmu hakan wata dama ce da Ubangiji ya baka wajan
gane laifinka da kuskurenka, wasu suna sakaci da addu'a, wasu kuma rashin biyayya ga iyaye,
wasu kuma ruɗin ƙawaye, wasu kuma ƙaddarar ce dai.... Idan aka haɗa zamu fahimci
gabaɗaya lokacin kowa ne bai ba, da zarar lokaci ya yi komai zai zama shuɗaɗɗen, cimma
manufa bashi iyawa ma, cimma nasara da tsayawa akan ra'ayinki shi ne cikakken mutum.
NO MAN IS THE MAN WITHOUT A WOMAN*33
Murya na rawa ya ce "Don Allah ku tausaya mini wallahi ban taɓa son ta ba, balle na ce zan
aureta, why should I? Allah kuka aura mini ita mutuwa zan yi mana son ta, bana ƙaunarta, kada
ayi mini auren dole" Ya faɗa His voice was shaking. Yanayin yadda kowa ke binsa da kallon
mamaki ya sanya shi ƙarasawa gaban Uncle Isma'il ya ce "Kun sai dai ni ba mahaukaci bane?
Balle ayi mini uzurin taɓin hankali, I don't know what is going to happen to me, I don't know
when this happened.....," Tass! Mama ta ɗauke Alpha da mari, without letten him to recover ta
ƙara sauke masa wani wanda ya sanya shi yin baya sai kuma ya dawo ya tsaya da ƙafafuwan
shi dafe da kuncinsa tayi pointing ɗinsa da yatsa ta ce. "Idan ƙwayar ku ta sojoji ta faɗa maka
ba daidai ba, ko allurar da ake muku to gabaɗaya haukanka ya zama na banza a nan, kayi
kaɗan kayi tsararo bamu haifi ɗan da zai juyamu ko ya raina mana hankali ba, We are your
parents, you are the child we gave birth to, we have the power to pass the sentence on you...."
Mama ta ja ƙwafa ta ce "Let make it clearly for you, idan harni na ɗauki cikinka wata tara, na
haifeka na baka nono na, naci kashi da fitsarinka wallahi wallahi ko zaka mutu ka farko sai ka
auri Majeederh aurenka da ita a gobe babu fashi" Ta faɗa Sounding very angry. “.... Mam....” Alpha's Expression softened slightly as he looked at her ya juya ya kalli Majeederh wanda take
zaune kamar anda sata, bata ko motsi sbd tsananin tashin hankali ruɗu da fargaba, da kuma
tu'ajujjin abinda yake shirin faruwa da ita, An fasa aurenta? Kuma ranar ɗaya kasance saura
kwana ɗaya a ɗaura? Ko dai ba ita jin ake nufi ba? Fizgota da Alpha ya yi ya sanya ta dawo
daga hayyacinta ta dinga kallonsa kamar zautacciyya a hargitse ya ce "Kiji tsoran Allah
Majeederh ki faɗa musu gaskiya, tunda nake na taɓa cewa ina son ki? Yaushe na sameki nace
zan aureki kada ki bari a cutar dani ina da wacce nake so" Majeederh ta girgiza kanta tana jan
jikinta baya ƙirjinta na ɗagawa sama tana dafe saitin zuciyarta ta ce "Me ya sa zaka zaɓi
tuzartani a lokacin dana saka rai da samun ƴanci kamar ko wacce mace? Me ya sa zaka samun
son abin dana fidda rai da samun shi? Me ya sa ka dawo da kwaɗayin kasancewa ɗaya daga
cikin matan da zamu martabar aure bayan kasan ba haka bane? Me na yi maka a rayuwa daka
nemi ɗaukan fansa ta hanyar da zuciya ba zata iya ɗauka ba? Me ya sa ƙaddara zata juya ta zo
mini ta hanyar da ba zan iya jure mata ba?..." Ta girgiza kanta duk wannan abun jikinta ƙyarma
da ɓari yake kamar mai shirin yin jijjiga ta zube a ƙasa saman ƙafafuwanta tare da rarrafawa ta
riƙe ƙafar Alpha ta ce "Ko a lissafin ƙaddara ban taɓa lissafa zuwan wannan ƙaddarar ba, ka
tausaya mini ka aureni kuma aure zaɓin zuciyarka, zan zauna da kai a haka koda baka so na,
koda zan zama ƴar aiki a cikin gidanka dakai da matarka, wallahi ba zan iya jure wannan
ƙaddarar ba fasa aurena da zakai daidai yake da tsayawar numfashina" Majeederh ta ƙara
ƙanƙame ƙafafuwan Alpha ta ce "Tunda na buɗe idanu naga kana damuwa da duk wata
damuwata naji babu wanda ya dace dani sama dakai, zuciyata ta ƙauna ce ka Yaya, ƙauna
mara algus ina sonka zan zauna da kai komai wahala, ƙunci, damuwa,takura ka rufa mini asiri
kamar yadda Allah ya rufa maka kada ka muzanta ni kada ka sanya na sama abar kwatance a
dangi da kuma unguwa ka dubi girman Allah ka amince da aurena wallahi da bakinka kazo mini
da maganar da......,"
"Stop it, stop!" Alpha ya faɗa yana janye ƙafarsa daga gareta ya ce "Wallahi ba zan iya aurenki
ba, baki mini komai but i can't be your husband, i don't love you anymore ki barni na aure wacce
nake so ni ko zan takura miki ba zan iya aurenki ba ni ma kiyi mini wannan rufin asirin" Ya faɗa
yana riƙe kansa da hannu bibbiyu. Majeederh ta kallesa irin kallon ka rusa mini rayuwata kafin ta ce
"What have i done to deserve this from you?? Wallahi ina sonka ni" Aaliyah ce ta tashi tare da
ƙarasawa wajan Majeederh ta ce "Anti Jeederh ki barsa Allah zai kawo miki naki rabon, ya yi
haka ne domin ya kunyata ya sanya ƙaddararki ta ƙara tsamari" Majeederh ta girgizawa
ƙanwata kai ta ce "No Aaliyah ba zan iya jure gorin aure a wannan lokacin ba" Kuka sosai
Aaliyah take kamar ranta zai fita, tana tausayawa halin da yayarta take ciki. Anti girgiza ƙafa
kawai take lokaci zuwa lokaci take jan ƙwafa, Abbu tunda aka fara maganar ya sunkuyar da
kansa ƙasa baka iya gane yanayin da yake ciki, wai ƴar cikinsa take durƙoshe tana roƙan wani
ya aureta? Me ya yi mata da zata nemi tuzarta shi har haka? Mami ta yi jigum idan ranta ya yi
dubu to ya yi tsatsa ya lalace, kana ganin yadda idanunta ya yi jajur zaka san zuciyarta a kusa
take. Uncle Isma'il kallon Alpha kawai yake, Uncle Bello ya dubi ɗan nashi ya rasa me zai ce
masa he really disappointed him. Innati zare idanu tayi kana ta ce
"Komai yana da lokacin, lokacin bayyanar hakan ne ya yi kada ku damu, gaggawa aikin shaiɗan
nasan za rina ansaci zanin mahaukaciya na jima da ganin wannan rana" Ganin babu wanda ya
ƙara cewa komai ya sa Uncle Bello ɗaukan wayarsa ringing ɗin farko aka ɗauka cikin sauri ya
ce "Liman kayi haƙuri an samu matsala a invitation card ɗin nan, ɗaurin auren ƙarfe 9:00 na
safe sai a sanar a masallaci" A gigice Alpha ya kalli mahaifinsa ya ce "Abba me na yi maka da
baka son farin cikina? Wallahi kuka aura mini Majeederh zan kashe kaina" Wani Mahaukacin
mari Uncle Bello ya sauke Alpha kafin ya dawo hayyacinsa Mama ta ƙara sauke masa wani,
ganin haka yasa Widad fashewa da kuka sosai ganin yadda ake marin yayan nata Uncle Bello
ya nuna Alpha da hannu ya ce “General Ajzan-Alpha Bello Khan wallahi yau ko da gawarka ne
sai an ɗaura aurenka da Hawwa'u" Alpha ya juya ya kalli Majeederh ya dawo ya dawo ya kalli
Uncle Bello muryarsa bata fita ya ce "Sai a ɗaura da gawar tawa"
Yana faɗin haka ya fice daga cikin parlourn, Majeederh ta miƙe zata bi bayansa sai a lokacin
Anti ta ce "Kada ki kuskura ki bi bayan wanda bashi da imani" Uncle Isma'il ya miƙe da hanzari
ya ce "Kada Alpha ya cutar da kansa fa?" A takaice Uncle Bello ya ce "Rabo dashi daidai nake
da zamaninsa, he really disappointed me ya nuna bashi da biyya ban isa da shi ba" Kafin kowa
ya yi magana aka ji faɗuwar abu gabaɗaya suka juya Majeederh ta faɗi babu numfashi a
ƙirjinta.....
Duk da kiran asubar da ake bai sanya ɗaya daga cikinsu ya motsa ba, ko wanne ka kalli
fuskarsa za kaga tashin hankali musamman Dattijan mazan. Uncle Isma'il ya saka hannu ya
sharce zufar data gangaro masa yana cire hular kansa ya ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!"
Ya juya ya dubi Uncle Bello daya kasa cewa komai idanunsa ya yi jajur ya kalli Mama dake rusa
kuka sosai ya ce "Wai mene ya faru mai zafi har haka da yaron nan zai mana wannan cin
mutunci?" Mama ta share hawayenta ta ce "Idan ni na haifi Alpha da cikina to wallahi.....," "A'a
please" Anti ta tare ta da sauri wanda ya hana Mama ƙarasa faɗin abinda tayi niyya. Uncle Bello
ya ɗago kansa ya ce "Ɗan cikina? Ɗan dana haifa Isma'ila?" Uncle Isma'il ya sauke numfashi
ya ce "Dole akwai wani abu, yadda Alpha ya birkice kamar Mahaukaci sabon kamo zaka san
something is fishy?" Jinjina kai kawai Mama take kafin suyi magana motar Abbu ta shigo cikin
compound ɗin gidan Uncle Bello wanda aka baza rumfuna na ɗaurin aure, Abbu ya jima cikin
motarsa kafin ya buɗe ya fito da sauri Mami ta fito tana mara masa baya, tun a balcony kafin su
ƙarasa ƙofar parlour suka fara jiyo kukan Mama, Mami kamar zata kifa haka ta bangaje Abbu ta
shige "Ba dai an fasa auren ba?" Abinda Mami ta faɗa kenan tana binsu da idanu, Abbu ya
shigo tare da jingina da jikin bango can ya ce "Isma'ila, Bello na ji kira cikin gaggawa gashi ina
ƙoƙarin rasa sallar asuba?" Uncle Isma'il ya miƙawa Abbu white paper ya ce "Read, karanta"
Har Abbu yaƙi amsa sai kuma ya saka hannu ya karɓa tare da buɗewa hannunsa na rawa
idanunsa ya sauka akan handwritten ɗin Alpha da yake cewa....
DEAR PARENTS.
_Bani da baki ko kalmar da zan muku bayani wajan fahimtar daku abinda nake nufi, amma
na zaɓa mana hanya mai sauƙi da warware ƙullin da yake ƙoƙarin raba zumunci, ban kashe
kaina ba, ban kuma zauna a cikinku na ɓata muku sunan family ba, more especially mahaifina,
kayi mini komai a rayuwata ta duniya har kawo lokacin da nayi wayo na girma na mallaki
hankalin kai na, Ina son Majeederh a matsayinta na ƴar uwata wacce jinina da nata suke yawo
a jijiyoyin ko wannenmu, amma bana sonta ta aure bana ƙaunar zama da ita, akwai yarinyar da
nake so a duk sanda kuka amince mini zan gabatar muku da ita a matsayin matar da zan aura
kuma sirikar ku._ _Naso karɓarta matsayin mata kuma nayi muku biyayya, amma wallahi zuciyata ta kasa yarda
da wannan ƙudirin idan na auri Majeederh ba zan iya sauke hakƙin aurenta akai na, zanta cutar
da ita, zata zama bora a cikin gidana, zan wulaƙanta ta, wulaƙanci da human rights za su iya
hukantani, zan muzantata, muzancin da babu macen da aka taɓa yiwa irinsa, zata zama baiwa
a cikin gida, irin bayin da ba a samun su a yanzu sai ƙarnin baya irin bayin gidan sarauta ɗin
nan, zata zama almajira a cikin gidan mijinta, To idan zan iya aikata mata duk wannan gwara
ban aureta ba, nima ina mata fatan samun rayuwa mai ƴan-ci, ina gudun na tashi da ɓari ɗaya a
shanye rana gobe ƙiyama_
_Babban Dalilia na rashin aurenta shi ne, Ni mashayi ne, ni mazinaci ne Majeederh bata dace
da mutum mara tsafta kamar ni ba, ku yafe mini don girman Allah, kuji tausayina kada ku aibata
ni, zan dawo duk sanda kuka yarje mini idan kuma mutuwata ta riskeni ina roƙan kuyi mini
addu'a da samun dacewar Ubangiji!_
~G.A.B Alpha~
Abbu ya ɗauke numfashi lokacin da idanunsa ya sauka akan kalma ta karshe, date da time. A
sanyaye ya ce "Yaushe ya tafi?" Mama ta ce
"Ya tafi ko ya gudu? Wallahi ƙarya Alpha yake baya Shaye-shaye, duk mutum bai hali irin
wannan baya zama inda yake, ya tsani zin kamar yadda ya tsani fitar hawayena" Anti ta ce
"Me ya sa zaiwa kansa irin wannan tabon to?" Uncle Isma'il ya ce "That's what i was thinking
too" Wayar Abbu ce tayi ƙara ya ce "Ina zuwa" fita ya yi yana ɗaga kiran ya ɗan yi shiru sai
kuma ya ce "Thank you, na gode sosai" Ya kashe wayar kana ya dawo. "Yanzu mene abin yi?"
Uncle Bello ya miƙe ya ce "Ku san hanyar daza ku bi ku kwantar da hankalin Majeederh, ita
nake tausayawa wallahi da ina da wani yaron bayan shi da a yanzu ba sai anjima ba zan ɗaura
masa aure da ita, Allah ne shaidata, Alpha kuma sam ba zan masa baki ba, amma zan ga illar
bijrewa iyaye nasa kalar godiyar kyautatawar da mukai masa kenan" Yana faɗin haka ya fita
gabaɗaya mazan fita sukai domin gabatar da sallar Asuba zuciyoyinsu babu daɗi. Mami ta kasa
cewa komai domin ta girgiza da al'amarin, wani irin baƙon al'amari ne wannan? Only God
knows! Bayan Anti tayi sallar Asuba bata jira mijinta ba ta nemi napep zuwa gida...
Wajejen huɗu na rana ta fara buɗe Idanunta da ƙyar, wanda sukai mata nauyi har lokacin drip
ne manne a hannunta, ta juya kaɗan sbd ciwon da ɓarin kanta yake mata ga wani dishi dishi da
take gani kamar mai hawan jini, da sauri kuma ta buɗe idanun tare da yin shiru tana ƙoƙarin tina
mene ya kwantar da ita ciwo