Showing 87001 words to 90000 words out of 126765 words

Chapter 30 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf

ya ce "Bata jin daɗi, shi ne nayi
takeaway" Ta ce "Allah ya sauwaƙa" Parking Aliyu ya yi a ƙofar gidansa bayan ya kashe motar
ya fito yana zube hannu a aljihu wani irin baiwar kyau Ubangiji ya zubawa Aliyu, domin ko Ajlaal
sai dai ya nuna mana hasken fata da suma mai yawa da kuma launin idanu, gashi da wani irin
haƙuri da kawaici amma idan ransa ya ɓaci kamar Mahaukaci haka yake yana da ƙulafuci da
saka abu a rai. Ya ce "Kamar an rufe gidan ko?" Ta yi masa shiru yana mmkin yadda Majeederh
ke feeling kanta da yawa, tsayin shekaru bai taɓa ganin munafukar fuskar da ake rufewa ba. Jin
shiru ta ɗago kai suka haɗa idanu ta kame fuska tana jan jakarta zuwa hanyar gate domin tuni
gatekeeper ya buɗe tana jinsa yana magana amma ta yi shiru a gareta haramci ne babba da
ɗaukar ƙaton zunubi ga yin magana da namiji baligi sai ya zama dole. Tana shiga cikin gidan
taga Abbu tsaye a Balcony ta zube har ƙasa ta gaishesa ya amsa a wannan karan ta yi mamaki
da ya ce mata "Congratulations" Ta nufi cikin gidan tana shiga Aaliyah ta rungumeta tana ihun
murnar ganinta, Majeederh ta cire liƙab ɗinta bayan ta tsuguna ta ce "Barka da dare Mami"
"Yawwa" Ta ce tana binta da ido, Raihana ta ce "Allah mai iko! Ana ta shiga rigar Muslunci ana
ci da addini" Aaliyah ta kalleta ta ce "Idan fitsari banza ne kaza ma ta yi mana" Raihana ta
watsa mata harara tana cewa.
"Ji saƙarya, ana maganar kan giwa wake jiyo ƙamshin zomo? Mai da wuƙar ni ba tsararki ba ce"
Aaliyyah ta riƙe haɓa ta ce "Hooo ƙaasa, to aini walkice daidai da ƙugun ko wanne lalatacce,
kuma Majeederh kuturwa uwa ce zama da ita dole murucin kan dutse bai fito ba sai daya
shirya" Raihana taja tsaki ta ce "To ai ga sararin subuhana ɗin nan, sai a zuba muga idan za a
kwashe daidai, ba girin girin ba ta yi mai" Majeederh dai ikon Allah kawai take kallo domin ita
bata ma iya karin magana da habaici ba shi yasa ta rasa fahimtar me suke cewa, Mami na
zaune watching all of them. Aaliyyah ta saki dariya ta ce "Ai gurbin idon ba idanun bane, ni
masallacin kurawa ce bawa kare limanci daidai yake da datse iskar dake shaƙa, kiyi a hankali
domin na kawo kai nasan fari na san baƙi kada ki ja nayi miki wankin babban bargo, domin
naga fahimtar ki daidai yake da fahimtar yaron goye, bana son kuma ya kasance duk kun far
bakinki kiyi haihuwar guzuma" Raihana ta ce "Me kike nufi da haihuwar Guzuma? An faɗa an
ƙara faɗa idan Majeederh tayi zuciya gobe muji loud speaker Liman na sanar da ɗaurin aurenta,
waye bai san cewa Majeederh ba auren ne a gabanta ba? Office ɗin data buɗe na mene? Gari
gari da take zuwa da sunan kaiwa marayu taimako bayan ƙarya ne na mene? Ke yarinya
wahainiyarki ta kiyayi ramata, ta dauwama ba tayi aure ba har Mahadi ya bayyana" Aaliyyah
idanunta a cicciko da hawaye ta ce "Bar gaigaye za kici tumu ne, ƙaddara zane gwara ita tata
ƙaddarar ya fito sarari mun gani, kuma komai ya yi farko zai yi ƙarshe" Ruma ce ta fito daga
ɗaki ta ce "Kaza uwar tune tune mene ya faru kuma?" Kafin Aaliyah tayi magana Abbu ya shigo
gabaɗaya suka nutsu ya dinga binsu da kallo kafin ya ce "Kun kyauta, ko wacce ta fice mini
daga cikin gida" Raihana ta ce "Abbu ka yi haƙuri baya nan fa, gidan shiru tsoro nake ji" A
fusace ya ce "Ya kashe ki, kuzo ku fi ce mini" Jiki na rawa suka ɗauki mayafi da handbags ɗin
su ya ce "Shashai, ku dinga faɗa kamar ba jini ɗaya ba zan yi maganin ko wannenku kada ɗan
banzan yada dake dawo mini gida" Ya juya kan Aaliyyah ya ce "Dage, basu girmeki ba?" Ta ce
"Kayi haƙuri Abbu Anti Jeederh sukewa gorin aure hadda sharri" Ya kalleta ya ce "To kashin
awakai, ita Majeederh Ubangiji bai bata baki bane? Sai ke rasai? Ba ita ta sake musu ba da
tana cin ubansu tun farko za ayi haka?" Mami ta dinga kallon Abbu sai bata ce komai ba, ya
dawo kanta ya ce "Asabe kin kyauta,na kuma gode" Ya kalli Majeederh ya ce "Da safe ki same

ni"..... Washegari da safe bayan Majeederh ta shirya cikin wata tsadaddiyyar Abaya Marron irin
turkies Abaya ɗin nan ta samu Abbu a parlourn shi yana zaune ya yi shiru bayan sun gaisa ta
ce "Abbu gani" Ya ce "Hawwa'u, Hawwa'u, Hawwa'u" Ya yi pointing nata ya ce "Sau nawa na
kira sunanki?" Ta ce "Uku Abbu" Ya jinjina kai ya ce "To wallahi Allah na gaji da ganinki a gidan
nan" Da wani irin Shock take kallon Mahaifinta tashin hankali ya bayyana akan fuskarta tsoro da
wasa fargabar Abinda zai biyo baya ya wanzu a zuciyarta Abbu ya ce "Shekararki 31 a duniya
kina gantali,duk sha'aninki suna gidan mijinsu harda yara uku wasu huɗu amma ke kina yawon
neman abin duniya? Yaran da aka tsuguna aka haifa akan idanunki duk suna ɗakin mazajan su
banda ke, kina jerawa da Majaufiarki kamar sa'arki? Ka kaf Family ke ɗaya ya rage idan kika
ɗauke Aaliyyah da Sona? Wallahi wallahi idan ina ganinki a gidan nan zuciyata zafi take
daurewa kawai nake idan kuma na ci-gaba da ganinki tabbas zuciyata bugawa za ta yi sbd
baƙin cikin ki......


Littafina na kuɗi ne, biya ki karanta cikin kwanciyar hankali da salama da fitar da hakƙina.......

MIJIN MALAMA it's a paid book, pay before you read...... For me information via WhatsApp
number 08119237616Ya gara zama ya ce "Allah ya na gani na ga ji da ganinki a cikin gidan nan
ba aure, gorin dangi ya Isheni ba zan jure ba, ba kuma zan lamunta ba, shekaru 31 kina haɗa
kafaɗu da mahaifiyarki? Gabaɗaya ke ɗaya ya rage a dangi ƙannen bayanki suna gidan mijinki"
Da tashin hankali kawai take bin Abbu da idanu ta kasa koda jan numfashi domin a ƙirji komai
ya tsaya mata, zufa na yanko mata all over herself, kullum tana jin ciwo a zuciyarta, bata da
burin daya shige tayi aure amma kuma bata da ikon aurar da kanta ai? Ciwon dake damunta
kullum ƙara yawa yake This pain was different, it was draining and excruciating painful, and
soon it stopped abruptly. Abbu ya ce "Kina ji na?" Ta ɗaga masa kai a hankali ya ce "Good, Tun
kafin na nuna mini The other side of me ki shiga hankalinki, ko mazan auren ki ka rasa? Kawai
kin tsaya zaɓe da ruwan Idanu" Majeederh dai bata ce komai ba, domin sama sama take jin
maganganun mahaifin nata rai ɓace ya ce "Get out, ki fari na sake miki maganar fito da mijin
aure" A sanyaye ta ce "Kayi haƙuri Abbu" Zata miƙe ya ce "Sit down"
Ya kalleta sosai sosai cikin magana ta fahimta tsakanin uba da ƴar shi ya ce "Mene matsalarki?"
Ta yi ƙasa da kanta, tsayin shekaru 31 bai taɓa zaunar da ita ya ce meke damunta ba, sai
yanzu da komai ya ƙare mata “When all is gone” to yanzu ta ce me? Bayan faɗar bata da wani
amfani, it's too late to cry. Cikin tsawa Abbu ya ce "Ina magana kina ji na?" Ta girgiza kai ta ce
"Lokaci ne bai ba Abbu, ka yi haƙuri" Abbu ya ce "Eclty, ni ne kike cewa lokaci ne bai yi ba? To
buɗe kunnenki da kyau ki ji" Ya gyara zama ya ce "Wallahi wallahi ki fita daga idanuna, dana
matsa miki a shekarun baya ki yi karatu ai saboda rufin asiri mu ne nothing more, yanzu i have
what i want, kin rufa mini asiri yanzu kema ki rufawa kanki kiyi aure hankalina zai fi kwanciya,
Hawwa'u am telling you as your father lokacin da zan ƙara miki maganar aure zaki sha
mamakina wallahi Allah" Yana faɗin hakan ya miƙe tare da shigewa bedroom ɗinsa ya barta
zaune kamar gunki. "Majeederh!"
Zuciyarta ta kirata, ta yi saurin ware idanunta tana dafe ƙirjinta. Zuciyar tata ta ƙare cewa "Nutsu
Majeederh, think about that, wai kina da saurayin ne ma?" Waya taɓa cewa yana son ki? Balle
ya yi tunanin sanyaki a gidansa matsayin matar aure ta sunna?" A razane Majeederh ta girgiza

kanta, cike da tashin hankali tana sauraren abinda zuciyarta ke faɗa mata, ta yi shiru jin ta ce
"To kenan yanzu ya zaki? Shelar kan ki za ki yi ko yaya? Kinga dai bakya son ɓacin ran Abbu
ya zame miki dole neman mijin aure.....," Da sauri ɗaya zuciyar ta buge ɗayar ta ce "Ji banza,
ke dai ƙwaƙwalwarki bata aiki kamar mai shan miyar kuka, banda awon igiya ce ke kamar
Malama Majeederh ce zata yi shelar kanta? Kuma shi Abbun bai san ƙaddara bane? Waye ya
jefata wannan halin tun farko? Ba son zuciyarta bane da neman abin duniya? Do what is right
not what's easy, yadda ya dama zaka zai shanye abinsa, tsuntsun daya ja ruwa, shi ruwa akan
doka! Dole abu ya yi haƙuri domin shi ne silar faruwar komai shi ne ya haddasa mata jinkirin
auren, by the way Ubangiji hakan jarabta mu, kuma shi aure lokaci ko ita Majeederh ce zata
aurar da kanta? A wannan zamanin bafa ita kaɗai ce take da wannan matsalar ta rashin aure
ba, jarrabawa ce! Kuma zurfin cikin ki ya yi yawa Majeederh You have to do something, do
something Majeederh! Biyyar da kikewa Abbu is too much....,"
Kamar zautacciyya haka Majeederh ke sauraren shirar zuciyoyin nata guda biyu, da mai faɗin
gaskiya da mai kushewa tana ɗora ta a tubalin da zai kai ta halaka. Kyakkyawar zuciyar ta ce
"Oh! Kina nufin ta wulaƙanta mahaifinta kenan? Daman haka ya dace ɗan halak ya yi wa
iyayensa? Ba Abbu da yake mahaifinta ba, ko Mami idan ta yi magana dole Majeederh ta yi
mata biyayya, mai haƙuri shi ke da riba a wannan rayuwar, na tabbar Ubangiji ba zai taɓa barin
Malama Majeederh ta haka ba, dole akwai wani rabo da tanada mata albarkacin biyayyar da
takewa Mahaifinta, rabonta yana ta wani ɓangaren" Majeederh ta yi zuru domin tafi gasgata
maganar kyakkyawar zuciyar, muguwar zuciyarta ta ce "Hoo ƙaaasa! Yau ga bikin zuwa babu
zanin ɗaurawa, waya hanata auren tun fil azal, lokacin yana wagairawun bai ajjiya ko sisi ba, a
matsayinsa na uba wanda zai fita ya nema ya ciyar da iyalansa amma ya jingina ƴar cikinsa mai
tsafta da kamala matsayin jarinsa, ya sadaukarwa duniya ita idanunsa ya rufe, kuɗi kawai yake
so arziƙi yake nema ta ko'ina sbd yanzu ta tara masa ya shiga jerin masu kuɗin Kano shi ne zai
ce ta fito da mijin auren? Ya ja mata ƙaddara sai su amsheta da hannu bibbiyu, rayuwar
Majeederh ta shiga cikin lack of parents careless, Takaicin Uba zai iya kai ruhinta zuwa
kushewa, yanzu daya tilasta mata kawo mijin aure idan zuciyarta ta buga fa? Kawai ki share
mahaifinki ki ci-gaba da sabgar gabanki ya je ya ci kansa, Allah kaɗai ya san yadda zai da shi"
Da hannu bibbiyu Majeederh ta toshe kunnuwanta, sosai maganganun da zuciyoyinta suke,
suke mata amsa kuwwa a kunne! Jikinta har ɓari yake yana wata jijjiga. Kyakkyawar zuciyar ta
ce "Amma ke baki da lissafi, da kina da shi ba kya ce haka ba, komai yana da sanadi Ubangiji
ya ƙaddarawa Majeederh Jinkirin aure, amma Abbu shi ne sila, idan mutum ya kauce hanya
addu'a ake masa idan da rabo ya dawo, abu ɗaya Majeederh za ta yi ta ci-gaba da addu'a,
sadaƙa da yawaita azkar, kuma shi Imran ƙilan ƙaddararta da tashi daban shi ya sa a lissafin
ƙaddararta babu auren shi, abu guda ɗaya ne ke ɓata mini rai da Majeederh yadda take yin
shiru shirun nan, yaran cikinta na rainata ta ci uban kowa ta tattaka kowa, ta kuma cigaba da
kare mutumcin kanta..." Ceceku ce aka shiga yi tsakanin zuciyoyi biyun! Kowa yana son
Majeederh ta ɗauki shawararsa, ta saka hannu ta rufe kunnenta tare da sakin wani irin
gigitacciyar ƙara ta zume wajan a sume.... Misalin 12 na rana, ta shiga buɗe Idanunta wanda
sukai mata nauyi, a hankali ta saka hannu ta dafe gefen kanta dage barazanar tarwatsewa.
"Sannu Hawwa'u" Muryar Anty ta sauka a kunnuwanta. Ta ya motsa fuska a hankali ta miƙe
zaune tana jingina da jikin frame ɗin gadon bedroom ɗinta, cikin son nuna ta ji sauƙi ta ce "Ina
yini? Yanzu kika zo"

"I haven't been here long" Anti ta bata amsa cikin ƙasa da murya sai kuma ta ce "Meke faruwa
dake har haka?". Majeederh couldn't speak sai da Anti ta ce "Kina da ilimi, kuɗi, hankali, kyau,
amma duk da haka da sauranki baki gama cika mace ba". Anti ta yi shiru can ta kuma cewa "I'm
starting to get tired of seeing you in this situation,It is good that now you are married and you
are in your husband's house, Majeederh duk wani ɗaukaka da da iliminki a banza yake, macen
da bata san komai ba wacce take gidan mijinta sai anfi ganinta da girma da daraja, sai anfi
martabata fiye da komai, Abbank Uncle Isma'il shi ne ya turo ni ya ce na faɗa miki ya gaji idan
ya haɗu dake ba zaki ji da daɗi ba, You're a darling ke abar so, kina da kyau" Murmushi kawai
Majeederh ta yi wanda ya fi kuka ciwo ta kalli Anti ta ce "Mene amfanin kyau? Wallahi ban taɓa
fariya sbd ina da kyau ba, ina tausayawa duk wata mace mai kyau"
"Kyau abin so ne Majeederh" Majeederh ta runtse Idanunta ta ce "Bai ƙare ni da komai ba,
wallahi da na san inda ake sauya fata daga fara zuwa baƙa da tuni na yi, na gaji da duniyar nan
Anti" Ta faɗa tana riƙe ƙirjinta hawaye ma ya gagara fito mata. Anti ta ce "Kin gaji da duniya ga
shi duniya na son ki, Majeederh mazan aure kika rasa ne?" Kanta a ƙasa ta kasa cewa komai
Mami dake zaune looking so worries ta ce "Ta yani tambayarta Maryama, ni dai ba ruwana dole
na ja baya idan ina matsa Majeederh za ta yi zaton dan bani na haifeta bane wallahi,to me ma
zan ce? Nan nan wata Neighbor ɗinmu ta zo ta mini ta tas kamar uwata, zagi kala-kala tunda
uwata ta haifeni ban taɓa ganin tashin hankali irin na ranar ba" Ta yi jim! Sai kuma ta ce "To
akan me"
"Uhm, ta tsuniyar gizo ai bata shige na ƙogi, cewa ta yi wai bata yarda da Majeederh ba, gani
take gantali kawai take a duniya shi ya sa bata damu da aure ba" Anti ta ce "To fa, ita wa
kenan? Ina cewa akwai zabga zabgan ƴan mata a gidan wata ma ta yi Arba'in kamar uwata
wallahi, amma ita ba taga na gabanta ba sai munafurci a ɗaure a ƙugu? Mutane basa kashe
wutar dake ci a gabansu sai na wani? Baka da gadon mutum yana da gadon maganarka, to da
izinin Ubangiji ba zamu ga wannan mummunan ranar ba, wani hanin ga Allah baiwa ne" Mami
ta ce "A to, munafurci ne kawai irin na mutane wallahi Maryama, nan ta zo ta wata
yaƙunanniyyar atamfarta duk gansa kuka, ai kana ganin wannan matar kaga zubin munafukai
Inyami take kowa?" Anti dai bata ce komai ba. Ta juya kan Majeederh ta ce
"Ki tausayawa kan ki, ki tausayawa mana dan Allah Majeederh, zaɓen miji yanzu ba naki bane,
duk wanda ya fito da niyyar aurenki kawai ki amince masa As long as you trust his morals, his
behavior, his mind and his religion"
Kallon Anti kawai Majeederh take domin bai ɗaki shiyasa inda yake masa yayyu, wai ba a yarda
da ita ba? Babu wanda ya taɓa riƙe hannunta sai Ajlaal shi ma kuma ta yi Asstagafirullah! Ta ja
masa Allah ya isa kuma har azumi za ta yi bisa hakan wani ƙato ya riƙe mata hannu. Ta rufe
Idanu "Ban ya fe ba Ajlaal" Anti ta ce "Waye haka?" Ƙasa magana ta yi sai a lokacin ta kifa
kanta in between her legs ta shiga rera kuka kamar ƙaramar yarinya takaici da baƙin cikin Ajlaal
ya cika mata zuciya.
Ta riga ta manta da wani Alpha domin shi ne mutum na farko daya tuzarta ta a duniya, She laid
back down to rest but couldn't. Tears of fear, betrayal and sadness streamed down her cheeks,
and she knew that her life had been altered completely......
ZAZU Restaurant, Sultan Road Giginyu Nasarawa.
Suna zaune saman wasu haɗaɗɗun kujeru wajan wani gefen ruwa dake gudana, su wajan biyar
ne kana ganinsu kaga tantiran marasa jin magana, wanda suka gagari kowa, abu mafi jan

hankali a gare su ko wanne yana da class ɗinsa, ka taɓa ɗaya goma su hau kan ka, basa
ɗaukan raini basa gudun abin magana, sun mai da jami'an tsaro kamar abin wasan su, Police
station kamar shiga restaurant suka mayar da shi ko beach ko club... They're all education
natured enough, gabaɗaya kuma a Gang team ɗin Bad boy Abraham shi ne ƙarami, amma yafi
ko wanne girman jiki da tsare idanu, baya ɗaukan raini baya son munafurci, idan ya faɗi
magana haka ne domin baya ƙaunar ƙarya yafi son gaskiya ko zata kashe sa ko ta ja masa
wata masifar, wani irin masifaffen jan aji ne da Abraham Bad boy, basu taɓa ganin dariyarsa
ba, gashi da wani irin fikira ya ƙware wajan yin zane..... Abinci ne birjik a gabansu da difference
types of drinks a gabansu, ga Shisha ga wine. Taj ne ya ce "John yarinyar ta ci banza kenan?"
Ya faɗi hakan cikin turanci. Nan da nan fuskar John ta sauya ya ce "How do you think I will
forgive her?" Taj ya yi dariya ya ce "To You didn't take any action akanta" Wani lalataccen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login