Showing 114001 words to 117000 words out of 126765 words

Chapter 39 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf

rabon data
ganshi ma ta mance ta rufe duk wata hanya da zata haɗata da shi ba da son ranta ba. Abbu ya
ce "Da kai nake magana?" Abraham ya zame idanunsa ya kalli Abbu, sauyin idanun Abraham
ya kaɗa hantar cikin Mami. "What brought you into my house?" Gently Abraham ya taka har
gaban Abbu ido cikin ido ya ce "Ƴar ka nake so" Hatta Mami ta jijjiga da wannan maganar ta
Abraham, Abbu kuma ji ya yi zuciyarsa ta tsaya na wani lokaci cikin rashin fahimta ya ce "Me ka

ce?" A takaice Abraham ya ce "Zan auri Mamina" Abbu ya ce "A sbd kai Mahaukaci ne?"
Shortly ya ce "Akan ta, ni Mahaukaci ne Grandpa ya turo ni wajanka just to ask ur permission
na aurenta" Abbu ya juya ya kalli Majeederh wacce kanta ke sunkuye sai numfashi take da ƙyar
ya dawo kan Abraham ya ce "Ka zo gidana, a gabana ka kalli cikin Idanuna ka ce kazo auren
ƴata?" Abraham ya ɗan watsa kafaɗa tare da fito da Teller ya ce "Daga 1m zuwa ko nawa ka
faɗi kuɗin da kke buƙata yanzu ka bani ita mu tafi" Mami ta ce "Son ta kake?" Ba tare daya
kalleta ba ya ce "I don't know, kawai ina son auren ta" Abbu ya ce "Mara addini kamar ka shine
zan bawa auren ƴarta? Wanda bashi da gata, Ahhali mai yawo da ƴan iska suke fashi da
bindigogi zan bawa auren ƴata? Mai Shaye-shaye da yawo da mata wanda yake gidan kansa
maimakon na iyayensa shi zan bawa auren ƴata?" Abraham kallo Abbu kawai yake ba tare
daya damu ba ya ce "Yanzu ma kuɗin auren nata ai fashin su na yi" Majeederh dai ta kasa
motsi zaka iya ɗauka bata cikin hayyacinta ne Abbu ya ce "Ban yi mamakin hakan ba, bari na
faɗa maka abinda baka sani ba, wallahi tallahi dana aura maka ƴata gwara naga gawarta, dana
aura maka ƴata gwara ni na mutu, dana aura maka ƴata gwara duk me zai sameta ya sameta,
dana aura maka ƴata gwara naga ta zube mini shego gwara ko wacce ƙaddara ta faɗa mata"
Da wani irin tashin hankali Majeederh ke kallon Abbu sbd jin furucinsa wanda ya gigita ta ya
sauya mata lissafi tunaninta ya tsaya, kalmar shego ta nemi tarwatsa mata zuciya da sanya wa
ta jita kamar matacciyya. Mami ta ce "Alhaji kasan me kake cewa kowa? Kada ka jawa
Majeederh masifa da bakinka" Abbu ya ɗagawa Mami hannu ya ce "Ki daina saka mini baki
cikin maganata Asabe" Mami ta zaune tana rushewa da kuka. Abraham jijiyoyin kansa suka fito
tare da yin raɗa raɗa saman goshinsa silently ya ce "Ohk, ka shirya ganin babies" Yana faɗin
hakan ya juya tare da ficewa daga cikin gidan a hanya suka haɗu da Latifa dake shigowa
Murmushi tayi masa ta ce "Our son kana ta girma abinka wajan Mamin taka ka je?" Ko inuwarta
bai kalla ba balle ya bata amsa shi duk duniya da Majeederh kawai yake duguwar magana.
Yana zuwa mota Taj ya buɗe masa ya shiga gidan baya, Salamon na gaba shi kuma Taj ya nufi
mazaunin driver bayan sun fice daga cikin gidan Taj ya ce "Bad boy ya amince?" Abraham ya yi
shiru Salamon dake danna waya ya ce "What did i miss?" Taj ya ce "Bad boy ya je neman
auren Mami" Da wani irin sauri Salamon ya juya ya kalli Abraham dake bayan mota idanunsa
rufe ya dunƙule hannayensa ya birkita sumar kansa ya dawo da ganinsa kan Taj ya ce
"Shawarar wace wannan?"Taj ya ce "I, to me zai zauna jira kawai ya aureta" Salamon da wani
irin yanayi yake kallon Taj kafin ya ce "Wai mene ruwanka da rayuwar Abraham ne? Me yasa
kake sawa ya aikata abinda bashi kenan ba? Daman haka ake neman aure a musulunci? Kawai
ya tunkari mahaifin Mami ya ce he wants to marry his daughter ko me?" Taj ya ɗaga shoulder ya
ce "Is just a suggestion, kawai na duba yanayinsa baya bacci cikin kwanakin nan kullum kiran
sunan Mami ni kuma i can't take it anymore" Salamon ya ce "U can't take it a matsayinka na
ubansa ko uwarsa ko kuma me?" Taj ya ce "A'a kada ka zageni bafa fini son Bad boy kayi ba,
ina yin komai sbd farin cikinsa da kwanciyar hankalin sa ai shi ya sani idan kai baka sani ba"
Tuni zuciyar Salamon ta fara kaiwa ƙarshe ya ce "Farin cikinsa ko kuma ɓata shi? Ka bashi
ƙwaya ya sha ka saka masa maganin felling da burin ya yi wa Maminsa Fyaɗe Allah ya taƙaita,
ka kirata har gidansa ta da burin ta ganshi kwance da Debeka, ka haɗa plan da Engagement,
yanzu ka sanya ya je wajan mahaifinta wai ya bashi aurenta are you mad....," Da ƙarfi suka ji
Abraham ya ce "Stop the car" Taj ya tsaya bakin titi cikin ƙara ji Abraham ya ce "Salamon get
out of the car, bana son ganin fuskarka har abada" Murmushi kawai Salamon ya yi yana kallon

Taj ya ce "Wannan shi ne abinda kake buƙata?" Taj bai ce komai ba, Salamon ya buɗe ƙofa ya
fita tare da matsawa can gefe da gudu kuma Taj ya ja motar sai Club. Wine yake tsiyayawa
Abraham yana zubawa cikinsa sai da ya sha ya yi tatul kafin Taj ya ce "Bad boy ni zan tsaya
maka ko kowa zai gujeka ka mini halacci a rayuwa, Salamon son Maminka yake" Sai a lokacin
Abraham ya buɗe rinannun idanunsa ya kalli Taj wani irin kallo yake masa kafin can ƙasa ya ce
"I'll kill you Salamon" Taj ya ce "Ganin yana son ta shi ya sa nace bari kawai mu fara da neman
auren amma tunda Abbu yaƙi kawai ka tafi gidan Uncle Isma'il yanzu kafin Abbu ya bata auren
wani a daren nan" Cak yaga Abraham ya miƙe yana tangaɗi daga shi da three quarter ya zari
key ya nufi hanyar fita daga cikin Clun ɗin da ƙyar, murmushi Taj ya yi ya ce "Well-done
Abraham Daniel David"
Uncle Isma'il da Uncle Bello sai Abbu na zaune a compound na gidan Uncle Isma'il su kaga an
buɗe gate wata dalleliyar mota ta shigo, gabaɗaya suka kalli motar banda Abbu da kansa ke
ƙasa, Abraham ya buɗe murfin motar da ƙyar ya fito yana layi da tangaɗi ko idanunsa baya iya
buɗewa sbd wine ɗin da Taj ya bashi mai ƙarfi ce, bibbiyu haka yake ganin su Uncle Isma'il,
Uncle B ya gyara zama ya dinga bin Abraham da kallo har ya ƙarasu ya zube akan qiwwoyinsa
ya lumshe idanunsa. Uncle Isma'il ya ce "Khalil lafiya?" Abraham ya yi shiru, Abbu ya miƙe zai
bar wajan Uncle Bello ya ce "Ka zauna plx" Ya koma ya zauna daman alrdy ya shaida musu
everything daya faru. Dafa shoulder ɗin Abraham ya yi ya ce "Khalil me kake so?" Kansa a ƙasa
a hankali ya ce "Mami" girgiza kai kawai Uncle Isma'il ya yi ya ce "Mamin take kake so yanzu
kuma?" A hankali ya ce "Yes, ina so Mami" Ya ce "Khalil bana jin ko ka kasance Musulmi
Majeederh zata amince ka aureta, ta raineka da hannunta ta kula da kai da ace tayi aure babu
mamaki ta samu ɗa kamarka, addininmu da naku ba ɗaya bane, babu yadda za a yi ka auri
Majeederh, yau da ace kai Musulmi ne ita Christa to da sauƙi, amma kana Christa tana
Musulma kuma Malama? Ba zai taɓa yiyuwa ba, ka yi haƙuri Ibrahim" Abraham baya fahimta
bai kuma san haƙuri ba ya ce "Uncle Mami, ina son zama da ita" Ganin kamar zai basu matsala
ya sanya Uncle Bello cewa "Ohk, ka turo iyayenka sai a saka muku date na bikin" Da ƙyar suka
lallaɓa shi ya shiga mota yabar gidan. Uncle Bello ya kalli Abbu ya ce "Wai lamarin Majeederh
ke damunka ne Alhji Abdul'aziz?" Abbu ya ce "Me ya sa ba zai daman ba?" Uncle Bello ya ce
"Gaskiya bai kamata ya dameka ba, sbd komai ya faru kai ka siya da hannunka, akwai ƙaddara
amma tana zuwa da sanadi, tun Majeederh na da 20yrs a duniya ta nuna aure take so, amma
kayi burus ka nuna kamar baka sani ba, kamar baka san meke damun ƴarka ba, Imran ya fito
aurenta ta kure shi sbd kawai cikar burinka, bata san karatu amma haka ta daure ta maida
kanta kamar namiji ta tafi wata ƙasar tsayin shekaru Takwas, ta dawo ka tilasta mata fara aiki,
yanzu kuma ka samu abinda kake so shi ne zaka damu sbd ba tayi aure ba? Allah zaka ma
wayo ko ka nuna masa dabara kenan? Muna rayuwa da ƙaddararmu wacce Ubangiji ya tsara
mana, ƙaddarar jinkirin aure ta samu Majeederh sai ka tayata amsa kayi mata addu'a, kuma ka
bar ƙaddara ta yi aikinta" Abbu kallon Uncle Bello kawai yake, Uncle B ya ɗora da faɗin "Yanzu
da kake zargin Majeederh a matsayinki na mahaifinta mu kuma da jama'ar gari mu ce me? Da
Majeederh zata lalace to da tun a Misira hakan zai faru, ka gode Allah ka masa mubaya'a akan
yadda ya tsara lamuransa, komai ya sameta a rayuwa kai ne sila, sannan daza ka yi wannan
lalataccen furucin akan Abraham shi me ya yi masa zafi? Mutumin da yake da zuciya na ci, da
taurin kai ka zafin rai, baka tunanin kalamanka su haifar da wani abu? Kai fa uba ne komai ka
faɗa akan ƴarka Immediately Mala'iku za su amsa su rubuta, idan Allah ya ƙaddara Abraham

mijinta sai kaga ya musulunta kuma ya aure ta" Abbu ya ce "Har abada ba zan taɓa bawa
lalataccen yaron can auren yarinyata ba" Uncle Isma'il ya ce "Idan da rabo mai zafi sai kaga ya
kashe ka, rashinka a duniya babu abinda zai hana, ka karɓi ƙaddara a yadda tazo domin allon
lauhil mahfuz baya rubuta abin da ba daidai ba, komai ta faru da sanin Ubangiji, zanen
ƙaddararta kenan"
After 2 yrs. Lokacin Majeederh nada 33yrs a duniya Abraham kuma 18 Abubuwan sun faru,
tashin hankali fiye dana baya, Majeederh ta gujewa Abraham ya haukace baya iya ci baya iya
sha duk wani abu da ta hana shi baya yi amma ya fita daga hayyacinsa, ganin hakan yasa
Abbu barinta tafiya aikin Hajji bayan an kammala Azumin Ramadan. Fitowarta kenan daga
bathroom ɗaure da towel duk ta rame tana daga tsaye taga kamar gilmawar shadow da sauri ta
ɗauki hijabi ta saka tana juya idanunta ya sauka cikin na Abraham wanda ya sauya mata ya
ƙara yin wani girma na ban mamaki kamar ana ƙara shi kyansa na baƙin ɗan America ya sake
fitowa a fili. A kallo ɗaya da tayi masa ta fahimci bashi da cikakken nutsuwa walking slowly ya
nufeta da sauri ta ce "Karka zo nan" Ya yi mata banza kamar ana jansa haka ya nufeta kafin ya
ƙarasa ta ɗauke shi da mari ta ce "Mahaukaci, to addinina ba irin naku bane, ɗabi'ata tasha
bambam da taku kada ka sake mafarkin taɓa jikina, ni ba Maminka bace ok fine ni ma ban
haifeka ba, ba zan taɓa haifarka ba ka fice mini daga....," Caraf ta ji ya cafke lip's ɗinsa da
bakinsa tare da manneta da jikin bango ya shiga....Zare idanu tayi alamar ya haka? Banda
bugawa kuma babu abinda zuciyarta take. He was kissing her passionately, the kiss coming
from the land of his heart with all love and affection. Takaici ya sanya Majeederh runtse
Idanunta wani irin hawaye mai zafi ya shiga gangaro mata ta gefen idanunta, jikinta ya saki ta
kasa koda motsa hannunta, tunda ta zo duniya bata taɓa jin wani abu mai kama da wannan ba,
ji tayi jikinta ya shiga rawa da ɓari kamar ana kaɗa mata gangi, wani abu ke tsarga mata tun
daga kan babban yatsar ƙafarta har tsakiyar kanta. Tsigar jikinta ya shiga tashi yana zubewa
ganin yadda jikinta ya ɗauki rawa da ɓari numfashinta na neman ɗaukewa sbd kawai yana
kissing ɗinta ya sanya Abraham buɗe idanunsa da sukai jajur yana jin kansa na masifaffen sara
masa sbd baƙon lamarin daya ziyarce shi ba tare daya shirya zuwansa ba.
This is the first time in his life that he kissed a woman and the woman he looked upon as his
mother. A hankali ya zame bakinsa ganin tayi baya zata faɗi ƙasa ya yi saurin saka hannu ya
dawo da ita saman chest ɗinsa hannunsa ɗaya a waist ɗinta, idanunsa ya ware sosai cikin
mutuwar jiki ya kasa cewa komai yadda take sauke numfashi haka shi ma yake ganin babu mai
ƙauri a cikinsu ya sanya ya ƙara riƙeta sosai a jikinsa yana riƙe kansa da ƙoƙarin ganin ya dawo
cikin nutsuwarsa. A hankali ya zame daga inda take yana matsawa ta yi baya zata kifa sbd ta
gama tunanin tana jikinsa ta gama sakin jiki bakiɗaya, cikin sauri ta riƙe kanta da kyau tana jan
breathing ɗinta da saukewa a hankali, har lokacin jikinta kuma bai gama daidaituwa ba rawa
yake still. Idanunta ta buɗe da son nuna masa ko a jikinta ta ce "Ka fita daga cikin bedroom
ɗina" Ta faɗa ba tare daya kalli direction ɗinsa ba, shi kuma ya zubawa yatsun ƙafarta idanu
yana karantar yanayin da kike ciki, a hargitse ta ƙara cewa "Khalil get out of my room,i Said"
gently ya ɗaga kai ya kalleta da rikitattun idanunsa wanda sukai laushi calmly ya ce "Bayan
kasancewata Christa mene hujjarki?" Wani irin murmushi ta yi ta ce "Waya faɗa maka sbd kai
ba musulmi bane ya sa naƙi amincewa? Da ace ina sonka da na ja ra'ayinka kan musuluncin ai"
Ta gyara tsaiwa ta ce
"Ba zan taɓa son ka, ba zan taɓa son yaron cikina ba, ba zan taɓa auren under age irinka ba,

kayi mini ƙanƙantar da ba zan iya cewa kai mijina bane, infact i don't love you, wani gwanini da
kai a gabana" Tunda ta fara maganar yake kallonta da wani irin yanayi wanda ba zaka iya
tantance shi akan fuskarsa ba, ya nufeta da niyyar riƙe hannunta ta yi saurin matsawa ta ce
"Ya zama last time da zaka ƙara gigin riƙe wani sashi na jikina, addina da naka akwai tazara
mai yawan gaske" Rai ɓace kamar Mahaukaci! ya ce "Wanne irin addini ne wannan for God
sake? Komai ba kyau" ta fizge hannunta, kau! Ta ɗauke shi da mari ta ce "Mahaukaci, addinina
ya fi ƙarfin cin mutuncinka sai a yanka wuyan wanda duk zai aibata Musulunci" idanun Abraham
sukai jawur ya ce "Shi addinin ya haramta auren macen data girmeka kenan? Shekaruna 18
mene abun yarinta a jikina? Me ya sa ki ka raina ni? Kawai saboda ni yaro ne, saboda kin
girmeni da shekaru goma sha biyar?" "Kai yaro ne"
"Zan wadataki da komai JEE, don kin rai ne ni a lokacin dana rasa iyayena bashi ke nuna ba
zan iya zaman aure dake ba, ina soyayyar da kika nuna mini ina yaro? Okay fine, i have a
solution! Your father doesn't like me kawai muyi auren Choci ko kuma wallahi mu haifi ƴa ƴan
banza kuma shegu, ko kuma na wulaƙanta addinin Musuluncin naku" Yana faɗin hakan ya fice
daga cikin bedroom ɗin. Zubewa tayi saman gado tana riƙe kanta wanda yake juyawa mata,
tama rasa wanne irin tunani za ta yi da matakin da zata ɗauka, Abraham na neman zame mata
ƙarfe ƙafa. A hankali ta lumshe idanunta da sauri ta buɗe jin tsigar jikinta na tashi har yanzu
while bakinta na mata wani iri, Abraham ya bar mata wani irin moment da memory mai wahalar
mantawa a zuciya, ya yi abinda babu wani namiji daya isa ya yi shi ya kafa tarihi a rayuwar
Majeederh. Shuɗaɗɗan abinda ke damunta shekara da shekaru wanda tayi maganinsa ya dawo
mata sabo fil. Gabaɗaya ta hargitse tare da yin luf saman gado ta rungume pillow addu'a take
Allah ya kawo mata ko tsoho ne wanda ya girmi Abbu ta aura ku ta samu sauƙin maganganun
jama'a ta kaucewa rashin kunyar ɗan cikin nata.. Uncle Isma'il ne zaune a parlourn baƙinsa ya
dubi Pasto David kana ganinsa kaka cikakken Christa gaba da baya. Uncle Isma'il ya yi
murmushi ya ce "Sir Please ga ruwa nan" Grandpa ya yi murmushi ya ce "My pleasure sir"
Uncle Isma'il ya gyara zama cikin nutsuwa da harshen turanci ya ce "Kafin na ce komai zan su
nasan waye kai, kuma na yi maka some of questions akan Abraham" Grandpa ya jinjina kai
yana yaba nutsuwar Uncle Isma'il kafin ya ce "David sunana, shugaban church, business man
with experience, sai wani secret aikina, kuma Abraham's Grandfather" Uncle Isma'il ya watsa
hannu ya ce "That's good and i like it, amma Sir daman can Abraham Christa ne?" Kallo Uncle
Isma'il kawai Grandpa ke yi kafin ya ce "Maybe, Abraham gaba da baya Christa ne kamar
yadda ka ganni ɗin nan, muna ganin kima da matar tabar addininmu kamar yadda kuke ganin
naku, muna ƙarfafa al'adunmu mun san muhimmancin hakan sosai, sai dai Abraham rayuwarsa
ta samu bambanci da tamu kasancewar a nan Naija aka haife shi tun yana da 3yrs baya ƙaunar
zama cikin gidan iyayensa, akwai wasu Neighbor ɗin su da suke Musulmi kullum yana gidan,
yana da masifar wayo na ci da taurin kai, idan su kai alwala haka shi ma zai yi, ko sallah sukai
haka shi ma zai. Bayan mahaifinsa ya fahimci hakan ya fara dukansa san bai gwadawa
Abraham tausayi ba, ya tashi cikin mugunta yau zai dake shi ya fasa masa jiki haka zai wayi
gari babu shi ya koma gidan Musulman nan, daga bisa ni ya kulle shi a wani ɗakin duhu babu
abinci ya gana masa azaba sbd kawai ya daina zuwan gidan mutanen, kai har farcen ƙafa dana
hannu Denial ya cire Abraham yana ɗan ƙaraminsa, shi yasa zuciyarsa ta ƙeƙa shi bashi da
tsoro ko kaɗan, watarana kawai aka wayi gari babu shi neman duniya, shi kuma Denial ya yi
tafiyarsa tunda daman ba a ƙasar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login