Showing 99001 words to 102000 words out of 126765 words
Chapter 34 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf
him, like that, Eh?"
Har ya juya ya tafi yaga dukan bai masa ba, ya dawo da sauri tare da kama hannun ɗan
karotan zai karya. A gigice ta ce
"Ibrahim-Khalil!" Bai kula ba sbd bai yi tunanin da shi yake ba, cak kuma ya tsaya dalilin
muryarta da ya ji. Ya ɗago jiki a sanyaye sbd shi bai ba san yaushe ne ya shiga dukan mutumin
ba, kallonta ya yi ya ce
"Sorry Mami" A fusace ta ce "Sorry for yourself Khalil" Ta kalli mutumin ta ce "Don Allah ka yi
haƙuri, yaro ne ina mai baka haƙuri" Ta juya ta kalli Abraham da ransa ya yi masifar ɓaci jin ta
ce wai shi yaro ne? Ta ce
"Say sorry to him, ka bashi haƙuri" Ya ɗauke kai tare da yin shiru.
Tun da aka fara faɗan yana zaune cikin mota, sanye da wata dakakkiyar shadda gezner sai
ɗaukan idanu take, komai na jikinsa da mugun kuɗi aka siye shi. Uncle Isma'il dake ɗaya side
ɗin ya ce "Majeederh's disappointed me, na kasa yarda ita ce cikin tsakiyar mutanen nan" Abbu
ya runtse idanunsa,wai ƴar cikinsa ce a nan wajan? Idanunsa ya sauka akan rigar Abraham
dake jikinta, a hankali ya dinga binta da kallo, frm head to toe ganin jini kwance a bayanta ya
sanya Abbu fara tari yana girgiza kai, Uncle Isma'il ya ce.
"Take heart Abdul'aziz,
Ka bi komai a sannu dan Allah, Please!" Shi kansa Uncle Isma'il idan ransa ya yi dubu to ya
ɓaci, he can't believe cewa Majeederh yake gani, akan idanunsu ta saka hannu ta jawo hannun
Abraham har zuwa cikin mota. Shi kowa Abbu tari ne ya sarƙe shi idanunsa ya yi jajur sosai, da
ƙyar yana jan numfashi ya amshi bottle water ɗin da Uncle Isma'il ke bashi ya shiga ja yana
komai ya fice masa a rai.
Misalin 5 na yamma wata ƙatuwar mota, Mercedes-Benz EQS Black colour ta yi parking a
compound na gidan Uncle Isma'il, Driver ya ce "We're here, Sir"
Abraham dake bayan mota, ya shiga buɗe idanunsa da suke always sleeping sbd ƙwayoyin da
yake sha, tar ya buɗe ganinsa akan harabar gidan, har ranshi ya ɗauka gidan zai ninka
tunaninsa sai ya ga ko kwatan na Grandpa bai kama ba, balle kuma nasa gidan da bai fiya zana
cikinsa ba. Sanye yake da Brown ɗin Armani suit, wacce ta kama jikinsa sosai dark black skin
ɗin ta fito sai sheƙi take, hannunsa maƙale da agogon wrist na Patek Philippe, ga wani takalmi
Half Cover Leather Shoe, komai na jikinsa designer ne. Fitowa ya yi daga cikin motar yana rufe
idanu tare da zuba hannu a aljihu, a hankali yake bin komai na harabar gidan Uncle Isma'il,
yana tsaye Uncle Isma'il ɗin ya fito cikin nagartacciyyar shigarsa tun daga nesa yake kallon
Abraham har ya ƙarasu ya ce "Oh har ka iso?" Abraham ya nufi wajan Uncle I zai rungumesa
alamar gaisuwa Uncle Isma'il ya miƙa masa hannu alamar musabaha bai musa ba ya amsa a
hankali ya furta "Good day Sir" Uncle Isma'il ya ce "Come in, bismillah" Suka shiga har Parlourn
baƙi. Uncle I ya gyara zama cikin turanci ya ce "Sunana Isma'il mahaifi ne ga Majeederh uwar
riƙon ka, Ban yi wahalar gane ka ba, a wancan lokaci Little ake ce maka, sbd yadda kake baƙi
ƙyakƙyawan mai ɗaukan hankali, ga saurin fushi da zafin zuciya,na lura har yanzu akwai ta
kuma" Abraham dai kallon Uncle Isma'il yake bai ce komai ba.
"Kana da shekaru 3 a duniya Majeederh ta tsince ka, ta raineka da hannunta, ta ciyar da kai da
albashinta tana hana cikinta ta baka, bata faɗa amma akan ka tana yi kamar wacce akaiwa asiri
da jininka, a haka har kayi shekaru biyar bi ma'ana kayi 2 years a wajanta, Tayi kuka sosai
lokacin daka sake ɓata a hannunta sai gashi yanzu ka bayyana a bayyanar da ban ji daɗi ba, ka
bayyana a wani addinin da ba namu ba" Uncle Isma'il ya gyara zama ya ce "Tambayoyi nake
son yi maka, ina fatan zaka bani amsa?"
Abraham ya jinjina kansa alamar yana jinsa.
"What's your real name?
And who are you?
Meme aikinka? Matakin karatu? Ina familynka suke, Father, mother, e.t.c" Abraham ya sauke
numfashi a ɓoye ya daɗe yana kallon Uncle Isma'il kafin a hankali ya ce "Abraham Daniel
David, that's my name, Who is me?" Ya yi shiru for a second kana ya ce "Bani da uba, but i
have a mother" Uncle Isma'il ya ce "Mene sunan mahaifiyar taka?" Abraham ya ɗauke shi fa
duk ya gaji da tambayoyin nan, kawai don Uncle ɗinsa ne ya ce "Ohk, Jee Malumana, i can't I
can't pronounce the name" Ya faɗa yana ɗan yatsuna fuska.
Uncle Isma'il ya ce "Ok, Ina son faɗa maka abinda baka sani ba, Majeederh uwar riƙo ce ba
uwar asali ba, ina nufin akwai aure tsakaninka da ita ba kamar yadda ba zaka taɓa auren wacce
ta tsuguna ta haifeka ba, yadda kake zuwa kana rungumeta itama tana biye maka is prohibited
in Islam. Ka saka a ranka duk sanda ka fara feelings na Majeederh to zaka iya aurenta, kasan
Developing feelings towards opposite sex shike kawo So ka ji kana son mutum ko kasancewa
da shi ko aurensa zama na dindin wani kuma sha'awa ce kawai take jan mutum ga abinda yake
gani, kasan mata komai nasu mai kyau ne Zasu iya attacking opposite sex ɗin su, su ja ra'ayin
namiji ya kwaɗaitu da su, Abraham I am telling you this as your Uncle, not as my guest" Tunda
Uncle Isma'il ya fara maganar Abraham ke sauraren shi cike da fahimta, nan take ya ji komai na
zuciyarsa na sauyawa. Uncle I ya ce "Think, U can marry Majeederh, but u can't marry your real
mother, maybe a duk sanda kke rungumeta kana jin wani abu a ranka baka saki jikinka ka
fahimci mene ba sbd tunanin Majeederh is ur mother amma yaudarar kanka kawai kake, itama
Majeederh takai matakin da zata iya haifar ɗa kamar ka shi ya sa ta manta cewa abin da take
kuskure ne, ina fatan ka fahimta za ku ka yi nesa da jikinta" Abraham was speckless da ƙyar ya
jinjina kai tare da miƙewa suka fito waje anan ya ci karo da Sona kamar ta san shi ta ce "Uncle"
Ya ɗan yi murmushi domin yana ana bashi girma ya ce "Sorry gashi bana yawo da kuɗi?" Sona
ta ce "Ba komai, kai ne mijin Anti Jeederh?" Bai gane ba sbd da Hausa ta faɗa ya yi al'ƙawarin
zai dawo mata da gift...
Majeederh ta share hawayenta kwana biyu duk ta zama raguwa mai saurin kuka ta kalli Latifa ta
ce "I'm tried Latifa na ga ji da rayuwar nan, tun ina son aure har ya fita akai na, yanzu wa nake
da shi wa zai aureni da za a ce mini na kawo miji nan da 2weeks wlh bana da kowa" Katifa ta yi
murmushi ta ce "Kina da wanda zai aureki mana Majeederh" Majeederh ta ce "Wallahi babu, ko
zance ban taɓa yi ba" Latifa ta ce "C'mon ni na amince Mijina Aliyu ya aureki ko gobe ne...
Not edited
MIJIN MALAMA na kuɗi ne pay before you read..... More information via WhatsApp number
08119237616"Na auri mijinki? Do you want me to marry your husband?" Da wani Expression na
tashin hankali take faɗar maganar tana kallon idanun Latifa Omar. Latifa ta watsa hannunta
cikin rashin damuwa ta ce "To mene na tashin hankali a nan? Bayan iyayena dake, babu abinda
nake a cikin duniyar nan irin mijina, amma wallahi na amince miki hundred patient da ki auri
Aliyu, ki auri mijina mu zauna tare, ba zan taɓa yi miki kallon kishiyata ba, don Allah ki rufa mini
asiri ki auri Aliyu" Latifa ta faɗa muryarta na rawa. Miƙewa Majeederh ta yi tana ɗaukan
handbag ɗinta da wayarta ta nufi hanyar fita daga cikin parlourn. Da sauri Latifa Omar ta miƙe
tana shan gaban Majeederh ta ce "Ina zaki? Ki tsaya mu yi magana don Allah, this is the right
time da zamu kawo karshen matsalarki Majeederh" Murmushin takaici Majeederh ta yi hawaye
na sakko mata a a kumatu ta ce "Well-done Latifa Omar, sbd na tako ƙafa da ƙafa har cikin
gidan ki na faɗa miki matsalata shi ne zaki dubi idanuna kika ce i should come and marry ur
husband? Are you mad?" Magana take amma hawaye ne ke zuba daga cikin idanunta. Latifa ta
girgiza kai itama hawaye ya shiga sauka daga cikin idanunta ta riƙe hannun Majeederh sosai
cikin nata ta ce "Wallahi that's not what i mean, tun kafin yanzu ayi miki maganar fitar da miji
nake son faɗa miki ki auri mijina ina tsoran abinda zaki faɗa, Majeederh na san halinki nasan
how hard you're, You have a deep heart, even if the worry will kill you, you will never tell anyone,
na kasa jure yanayin na kasa fahimtar cewa jarrabawa ce, maganganun mutane akan ki ya fara
yawa, me ya sa ina da maganin damuwar ki a hannu zan zuba idanu kina cutuwa? Aliyu na da
kyau, ilimi both boko da Arabic, yana da kuɗi ko kuɗin mahaifinsa bai damu da shi ba, Hajia
Mahaifiyarsa na da kuɗi, Ubangiji ya hore masa arziƙin da zai zauna da mata har huɗu ba biyu
ba, Zan iya mallaka miki komai na rayuwa daga ciki har mijina If that makes you happy,if that
will make you look like any other woman in her husband's house,Please marry my husband,
Aliyu!" A hankali Majeederh ta zare hannunta daga cikin na Latifa Omar ta durƙoshe a wajan
tana sakin wani irin raunataccen kuka, mai cin rai da ciwo a zuciya. Wani irin kuka take Wanda
ta jima ba ta yi irinsa ba, ga ƙoshi ga kwanan yunwa,ga maganin matsalarta amma ko duniya da
abinda suke cikinta zasu haɗu ba zata taɓa auren mijin Latifa ba, bata taɓa kawo hakan ba ko
da, da wasa. Zubewa Latifa ta yi itama ta rushe da wani irin kuka kamar an musu mutuwa ta ce
"Ashe ba zan iya rufa miki asiri ba? Ashe zumuncin banza muke? Ashe ban zama ƙawar da
zata ɗauki damuwar ƙawarta matsayin tata ba? I have been friends since we were children, we
trust each other, we know each other's behavior,Even if you marry my husband, there will be no
worries between us, wlh ko Aliyu kika aura babu ɓarakar da zata gilma tsakaninmu, babu wani
yaƙunanne ko shegen kan lafiya da zai sako lalataccen bakinsa, zamu zama abu ɗaya, zuri'a
ɗaya one single family mu zama Matan Aliyu, ki haifa masa yara tunda har yanzu Allah bai bani
haihuwa ba" Majeederh kuka take sosai kamar ance Abbu ko Little ko Aaliyyah wani ya mutu, ta
kasa cewa komai sai jikinta dake mahaukacin ɓari da ƙyarma kamar an jona mata shocking.
Bar Aliyu Sufyan Alhassan da tunda ya yi parting da motarshi ya shigo gidan ya tsaya cak a
ƙofar da zata sada shi da main parlour na gidan nasa, tun daga farkon conversation ɗin su har
kawo yanzu ya ji komai, zufa ce kawai take yanko masa all over himself, jira yake ya ji me
Majeederh zata ce akan requesting ɗin Latifa?. "Majeederh say something, ki daina kukan hakan" Majeederh ta kalli Latifa Omar da rinannun
idanunta wanda ba lafiya ya cika ba, ta ce
"Dole na yi kuka Latifa, ban taɓa tunanin watarana da zata zo ace zan auri mijinki ba, me ya sa
kike tunanin zan iya auren mijinki, why should I do that? Me mutanen unguwa za su ce? Me
ƴan-uwan ki za su ce? Su ce na zama munafuka, maci amana mayaudariya, wacce ta aure
mijin aminiyyarta? That's what you want? Sbd ina kawo miki matsalata ashe ke tunaninki mijinki
zan aura? Sbd ƙaddara ta faɗa mini shi ne zaki manna mini hauka ki zautar dani da
gurɓataccen tunaninki mara amfani a gareni, zaki forcing mijinki ya aureni? Bayan kin san
mazan guduna suke, basa ƙaunata, balle muradin aurena, banda Imran daya taɓa furta kalmar
so a duniyata babu wani ɗa namiji da ya ce yana so na, ko da sunan iskanci ne....," Kukan da
ya ci ƙarfinta ne ya sanya ya kasa ci-gaba da maganar ta haɗe kanta da qiwwa kamar ƙaramar
yarinya. Latifa kukan take sosai ta ce "Ba zan taɓa forcing Aliyu ba, nasan ba zai gujewa
maganata ba, ku zauna da juna na 1week am sure zaku ƙaunaci juna, mutanen gari kuma ki
barni da su" Majeederh ta miƙe tare da goge hawayenta tas ta saki liƙab ɗinta. "Kin Amince?"
Aliyu dake tsaye cikin zuciyarsa ya ce "Say Yes, Hawwa'u"
Har bakin ƙofa Lafita ta biyota amma Majeederh bata kulata ba, lokaci ɗaya suka saka hannu
akan handle jin an murɗa ya sanya Majeederh saki tare da komawa baya, a hankali ya buɗe
Ƙofar ganinsu a har gitse ya sanya Aliyu dake cikin nevy suit hannunsa ɗaya riƙe da rigarsa ta
lauyoyi sai zabga ƙamshi yake, a hankali ya ce "What did i miss?" Latifa ta ce
"Ka tsayar da ita" Muryarta bata fita sosai ta ce "Bani hanya" Gefe ya koma ta raɓa ta shige
abinta, muryar Latifa na rawa ta ce "Me ya sa zaka bata hanya, ba zata taɓa dawowa ba fa,
kuma na ce ka tsayar da ita" Bai ce mata komai ba ya mayar da ƙofar ya rufe, hannu tasa zata
buɗe Ƙofar Aliyu ya yi sauri riƙo hannunta ya ce "Let her go, Wife" Kuka ta fashe masa da shi ya
jawota jikinsa "Sorry" kawai ya samu zarafin faɗa sbd zuciyarsa da tayi masa nauyi, ganin taƙi
yin shiru ya sa ya jata har zuwa bedroom ɗinsa dake tashin wani cool ƙamshi na air-freshener,
cikin dabara ya shiga bata saƙo albarkacin Majeederh Aliyu ya samu abinda ya daɗe bai samu
ba a wajan matarsa Latifa tsayin wata wajan goma. Yana zaune saman wata ƙatuwar kujera ya
harɗe ƙafafuwanshi saman sofar idanunsa lumshe breathing ɗinsa na sauka a hankali alamar
bashi da lafiya, ya ƙara yin wani farin idanunsa sun faɗa, cikar haiba da da zati da kamalar shi
na nan zaune daram a jikinsa. Wata Embroidery Islamic jallabiya ce a jikinsa fara tas, sai jiramin
daya ɗora akansa looking so good. Rohaan dake tsaye cikin damuwa ya ce "Allah ya ƙarawa
Mai martaba Ajlaal Sultaan lafiya, wannan tunanin da kake isn't good for ur health" Mai martaba
Ajlaal bai magana ba sai idanunsa ya buɗe yana kallon ɗan uwan nasa Rohaan, ganin kallon da
Mai martaba Ajlaal Sultaan yake masa ya sa ya ce "Ba tare da sanin abinda ke faruwa ba, a
karo na farko wani jininmu ya sako ƙafa zuwa Nigeria, ka matsa yanzu kuma gashi ka ce mu tafi
ba tare da yin abinda ya kawo mu ba" Nan ma Ajlaal bai ce komai ba, Rohaan ya numfasa ya
ce "Idan akwai abinda ke damunka yana da kyau ka faɗa, tunda kasan idan har a duniya yake
dole zaka same shi, ka tsallake Zaytoon, da Mimi wacce kai kaɗai kake controlling ciwonta idan
ya tashi, ka bar Fulani Ƙhulud da tagwayen yaranta, Palace ba kowa sai Hadiman, Meke faruwa
dakai Mai martaba? Yana da kyau ace....," “Rohaan” Ajlaal ya kira sunan Rohaan da ɗan ƙarfi a
kuma taushashe, Rohaan ya ce "Tuba nake Mai martaba" A nutse Ajlal ya duba agogon Rolex
dake hannunsa yana mai kikewa tsaye cikin izza har ya je bakin ƙofa sai ya tsaya ya juya kaɗan
ya kalli Rohaan, da sauri Rohaan ya durƙosa ya ce "Prvt jet ɗin na hanya, ban san ya akai aka
samu labarin zuwanka Nigeria ba, gabaɗaya zuwan naka shi ne latest new in the world" Da
wani irin Expression Mai martaba Ajlaal Sultaan yake kallon Rohaan jin abinda ya ce, zufar
dake tsastsafo masa a tsakiyar goshinsa ita ke nuna tashin hankalin jin mummunan labarin, ya
dunƙule hannu tare da kallon Rohaan alamar ƙarin bayani.
Rohaan ya ce "A karo na farko Sarki makka Mai martaba Ajlaal Sultaan magajin Ex Sarkin
Makka Sultaan ya sauka a Nigeria, har yanzu ba a san dalilin zuwansa ba, ana kyautata zaton
zuwan sirri ne ya zo ganawa da wani ɗaya daga cikin sarakunan Nigeria, zuwan nasa ya ja
hankalin dubban mutane ganin tun ƙarnin baya na kafuwar masarautar Saudiyya jininsu bai
taɓa zuwa ƙasa Nigeria ba, ko mene dalilin zuwan nasa?" Daga nan Rohaan ya kashe T.v da
remote ɗin hannunsa ya ce "Ire-iren wannan sune news ɗin da suke trending a duniya da Social
media tare da photonka, alamarin ya fi tsamari a Al Jazeera, BBC World News,CNN
International da kuma Arise News" Duk maganar da Rohaan yake a tsorace yake yinta, Ajlaal
ya zame idanunsa yana riƙe kansa da kyau, duk da tashin hankalin da yake ciki, a taushashe
cikin tarin ilhamarsa nutsuwa da kamalar dake zaune a jikinsa cikin kamilalliyar muryarsa yana
lumshe idanu ya ce
"A san yadda aka yi, aka dakatar da news ɗin" Ya shiru yana juyawa can ya ƙara fesar da iska
ya ce
"Kowa na Palace, ya zama lafiya, a san yadda akai aka ƙaryata zuwan namu Rohaan" Da
girmamawa Rohaan ya ce "An gama Mai martaba, Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana" Tuni ya
kai cikin bedroom ɗinsa yana hana kansa jin abubuwan da suke masa yawo a jiki... Majeederh
na zaune a ƙasa an haɗa family meeting kowa da kowa yana nan cikin babban parlourn na
gidan Abbu, Uncle Isma'il da Uncle Bello, Innati,Yaya Bilkisu, Maman Alpha, Anti Hajiya
Maryama, Sona, Du'a, Widad, Raihana, Ruma, Aaliyyah, Mami, Jawaad,Sahar. Kaf Familyn
Khan General Alpha ne kawai babu a ciki, Idanun Maman Alpha ya nuna tsananin kewar ɗanta
da take shekaru sun ja, babu ko labarinsa gashi abin mamaki fur Uncle Bello ya rufe ido akan
bai yarda ayi cigiyarsa ba, ko headquarters na sojoji ba a maganar shi har sun yi replacing nasa
da wani, kamar wanda aka rufe musu baki aka saka makulin a ruwan