Showing 30001 words to 33000 words out of 126765 words
Chapter 11 - MIJIN MALAMA COMPLETE by Nimcy Suleiman Sarauta.pdf
ce
"Firstly duk abinda ya halatta mace taiwa mijinta to ke zero ki ke a nan, ba sani ba ko baki da
lafiya ne ko sha'awa ce babu da bakya buƙatar mijinki, baki iya girki ba kullum ina yawon zuwa
restaurant sbd kunyar zuwa nake wajan Hajia na ce zanci abinci bayan ina da mata, irin
kwalliyya ta mata baki iya ba, ba kitso ba wannan zanen abun ƙunshi, sai tara ƙawayen banza
da iska da masifar kishin da bashi da amfani, wallahi wallahi ko zina na fara kece sila Latifa
Allah ba zai barki ba, Allah kana kallo duk nauyin daka ɗora mini a matsayina na miji na sauke,
kuma in sha Allah sai na auri Majeederh ita ce zata bani abinda nake buƙata ina son mace mai
ƙarfin addini da iya soyayya amma ke text message wannan baki sani ba, Mrs zero!"
Yana faɗin hakan ya zari key tare da ficewa daga cikin gidan ya nufi Chikenza Park and
Restaurant.
Misalin Tara na dare motocin His Excellency Abu-turab suka sauka gidan Uncle Isma'il, cikin
sauri P.a ya fito tare da buɗe masa ƙofar mota a hankali ya fito yana zabga ƙamshi Dolce and
Gabbana wanda sanyin ƙamshin ke fita a hankali cike da gamsar da mai shaƙar shi. Yana
sanye da wata dakakkiyar shadda sky blue ɗinkin jamper da babbar riga ta zauna a jikinsa
sosai a wannan lokaci babu ko hula a kansa sbd so yake yau Jiddo taga ainahin kyan da yake
da shi, cikin takun ƙasaita kamar wahainiya haka ya nufi cikin gidan Uncle dake sun da zuwan
na shi, Jawaad na parlour yana kallon ball ya yi saurin miƙewa ganin His Excellency Abu-turab
da kan shi ya durƙosa da girmamawa ya ce
"Wlcm sir" Murmushi Abu-turab ya yi yana jinjina kai "Kana lafiya?" Ya ce "Allahamdulillah,
sannu da zuwa" ya ƙara murmushi kawai. Jawaad ya yi masa rakiya zuwa parlour part ɗin da
Majeederh ke ciki kana ya shiga ciki ya sanar mata lokacin tana zaune har yanzu ko sauya kaya
ba tayi ba ta zubawa Ibrahimul-khalil Idanu. Ta jinjina kai kawai ya san ba zatai magana ba sai
kawai ya fi ce. Abu-turab ya kasa zama har tsayin mintuna kusan goma kafin ya ji motsi a bayan
shi. A hankali ya sauke wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya ƙarasa gabanta yana binta da kallo.
"Barka" ta furta can ƙasa ya ce "Can You remove the cover? Please i want see my wife ba
wannan hijabin" Ta ɗago kai ta kalle shi tana son ce masa ya jiki tunda taga harda carnoner a
hannunsa. "Please Jiddo, My wife aure ya halatta mini ganinki" ta runtse idanu sosai lokacin
daya zare hijabin jikinta a hankali ya jata jikinsa ya rungume sosai yana sauke numfashi da
ajjiyar zuciya ya ce "Allahamdulillah, Allahamdulillah, Allhamdulillah! Ina son ki Jiddertul-khair"
Rayuwa Kenan bayan tarin ƙalubalan rayuwa data sha ta tsallake ƙaddarori da surutu da
zunɗen jama'a yau ita ce matar babban mutum, ita ce first lady? Ita ce jikin Governor Abu-turab
Alƙasim rungume da ita yana faɗa mata yana son ta? Sai a lokacin wasu hawaye Masu zafi
suka shige fitowa daga cikin idanunta har bata san lokacin data ɗan ƙanƙame jikin Abu-turab
ba. Sannu a hankali kamar gilmar fitila cikin duhu rayuwarta ta baya ta fara dawowa cikin
Idanunta da tunaninta.... THE BEGIN OF THE BEGINING. Shekaru talatin da biyar da suka
shige a baya al'amarin ya fara......
MIJIN MALAMA
Littafin kuɗi ne book 1 and 2 1k ne.... If you read for free♀️♀️♀️
0811923761614
*Duk wata mace yana da kyau, ta nutsu ta bi labarin nan, ko bai zo daidai da rayuwarki babu
shakka zai iya zuwa daidai dana wan bak... MATA MA SU JINKIRIN AURE.*
Al'amarin ya fara a garin kano cikin unguwar Ƴan-kaba. Yamma sakaliyya lis unguwar ta yi shiru
saboda gabatuwar almuru. Yanayin ginin wajan zai baka tabbacin akwai ƙarancin wadata a cikin
mazauna unguwar musamman yadda aka samu kwatoci a gaban ko wanne gida da kuma kan
hanya akwai tarin gidaje wanda suke dab da juna kamar tsarin ginin cikin gari. Da sauri
magidancin mutumin ke tafiya hannunsa riƙe da wata jakar ƙaramar kai tsaye gidan da ya fi ko
wanne muni ya shiga lokacin daya shiga ya samu wata mata tsaye tana goge zufa ya dubeta
cikin damuwa ya ce "Ya ya ta sauka ne?" Bilkisu ta girgiza ta ce "Ayya ai sai abin da hali ya yi
naƙuda tun jiya ana abu ɗaya sai fama ake, gashi Malam ka ƙi a ta fi asibiti" Malam Abdul'aziz
ya haɗe fuska ya ce "Yanzu nan zata sauka lafiya, ni ban fiya yarda da aikin nasara ba yadda nayi wannan tofin
babu shakka zata rabo da cikin salin alin" "Allah ya sa, amma Fulani na shan wahala" cewar
Bilkisu.
Ta amshi maganin tare da ɗaga labule ta shiga, rawar dai har yanzu bata sauya zani ba. Domin
Nishi ake son ta yi amma abu ya gagara. Bilkisu ta ce "Sannu kin ji Fulani" ta bawa wata mata
dake zaune gefen Fulanin ta ce "Yanzu Malam ya kawo wannan tofin, taimaka ki ɗagata ki bata
kin ji Asabe" Asabe ta amsa cikin alhini ta tallo kan Fulani ta shiga mata maganin jikinta duk ya
riga ya saki.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, na shiga uku me zan gani ni Asabe Yaya Bilkisu ƙafa ce ta fito,
haihuwar dire za ta yi"
"Wanne irin dire ni ƴar nan matsa muga Asabe" Asabe ta matsa Yaya Bilkisu na dubawa ta ga
da gaske ƙafa ce guda ɗaya ta fito harta fara bushewa. Suka rasa yadda za su yi hakan alama
ce dake nuna musu ruwa ya ƙarewa ɗan-kada. Suka yi rufdugu akan Fulani wacce take jin
mawuyacin hali salati kawai take yi gefe guda kuma tana kiran sunan Hawwa'u. Da ga bakin ƙofa Malam Abdul'aziz ya ce "Ya ake ciki? Ta kusa sauka ko?" Yaya Bilkisu ta ce
"Wanne sauka za ta yi dire, Malam ka je ka kawo mota mu je asibiti ko na Murtala ko na
nasarawa" sai a lokacin Asabe ta ce "Ai bama za su amsheta ba, domin bata taɓa zuwa awo
ba, ko haihuwar Majeederh a haka ta zo mata" "Ikon Allah, Ubangiji ga mu gareka" da ƙyar suka taimaka mata ɗaya ƙafar ta fito suka dinga
yayyafa mata ruwa tare da bata shayi mai zafi cikin sa a nishi mai ƙarfi ya zo mata ta haifi ɗiya
mace a karo na biyu. Murna sosai sukai harda hamdala aka yanke cibiya tare da gyara
kyakkyawar yarinyar. Malam na waje Yaya Bilkisu ta fito tare da barin Asabe a ɗakin. "Ga kyautar da Ubangiji ya ƙara yi maka, uban ƴa ƴa mata" Malam ya yi murmushi ya ce
"Hakan ma suttura ce Yaya, kuma ina alfahari da ɗiyata Majeederh wacce zata bani abin dana
rasa a baya" Yaya Bilkisu ta yi murmushi tana faɗin
"A kan Soyayyar Majeederh baka da ɗauke ƙafa, tana ina ne?"
"Makaranta Yaya Bilkisu, ai tun tana shekaru biyu na sanyata a makaranta gashi yanzu dab
take da yin sauka" Yaya Bilkisu ta zare idanu sosai cike da mamaki da al'ajabi ta ce
"Yau na ga abin da ya isheni ni Mai gadon zinare ba bu tausayi shi ya sa gata nan duk a fige
saboda tsabar karatu" Wani Uban kira Asabe dage cikin ɗaki ta shiga ƙwalawa Yaya Bilkisu jiki
na ɓari har zaninta na faɗowa ta tsuguna zata ɗauka domin gyarawa ashe takalmi ta ɗauka
tana faɗin. "Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, Wanne irin ɗaukan alhaki ne haka
Asa....," Abin da idanun Yaya Bilkisu ya gane mata ya hanata ƙarasa duguwar maganar data
ɗakko. Fulani ce ke kwance kamar Matacciya sai jijjiga take harshenta ya fito waje ga jinin dake
fita a ƙasanta kamar an yanka rago. Yaya Bilkisu dake zuciyarta da rauni tuni ta fara sharɓar hawaye tana faɗin "Oh, mu mata muna
ganin jarrabawa a wajan haihuwa rabu ba a tsira ba" Fulani da numfashinta ke sama fuskarta
tayi fari sosai saboda jinin daya ƙare a jikinta ta ce "Ƴa ƴana, Ƴa ƴana Yaya a kira mini
Hawwa'u kafin na koma ga mahaliccina"
"Assha, Assha daina faɗa mai haƙuri albarkacin haƙurin ki Ubangiji ba zai amshi rayuwarki
yanzu ba, ke zaki raini yaranki da kan ki kamar yadda kika haifa" Fulani tayi shiru banda salati
babu abin da take ana haka Malam ya shigo jin shirun ya yi yawa. Wani bugawa ƙirjinsa ya yi
ganin halin da matarsa Fulani ke ciki, tsananin kyan da Ubangiji ya yi mata kasancewar ta
Fulanin Gombe Usul gaba-da-baya Fulanin kuma makiyaya masu kiwon shanu wanda nono ya
zamr musu jarin su wanda a yanzu shi ake sarrafawa zuwa madarar Rufaider yoghurt. Tun tana
shekara goma sha biyar da haihuwa aka ɗaura mata aure da Malam Abdul'aziz, a lokacin ya
ziyarci garin Yobe shi da abokinsa yin dillacin wata saniyya domin kiwo. At first sight soyayya
mai ƙarfi tayi dirar mikiyya a zuciyar matashin saurayin Abdul'aziz. Har Ubangiji ya tabbatar da
auren su, bata sami haihuwa ba sai da tayi shekaru ashirin da biyar a gidan shi, sannan ta haifi
ƴar ta Hawwa'u Majeederh Abdul'aziz Khan! Wacce kamar ka ki tayi ta zubar saboda zallar
kamannin da su ka yi. A nan ya samu wadata ya ƙara aure Majeederh na da shekara wacce ya
aura ta haihu ta samu ɗiya mace. Kasancewar kwanika take ta sake haihuwar wata ƴar lokacin
Majeederh nada shekara huɗu ana haka Fulani ta samu ciki. Har ya isa mizanin zuwa duniya a
daidai gaɓar da Malam ya bar gidan domin kawo tofi a lokacin naƙudar da ta ke tun jiya ta
tsanan.
Nishin da Fulani ta yi tare da salati ya dawo da Malam daga tunanin daya lula firgigit ya zube
gabanta yana faɗin "Fulani kada kiyi magana haka, ba mu shirya zuwan wannan ranar ba" ta
riƙe hannunsa sosai tana salati ta ce "Malam ka kira mini Hawwa'u ina son ganinta, ina son faɗa
mata wani abu mai muhimmanci a rayuwarta" Malam ya fara addu'a tare da cewa "Ki faɗa mini
ko ma mene, ni ne uban Hawwa'u kuma zan riƙe amana" ta girgiza kai ta ce "Al'amari ne daya
shafi uwa da ƴarta, da kuma dangina ka je ka dawo mini da Hawwa'u, dole zata ɓukaci sani a
lokacin da buƙatar hakan ta zo" Ta dinga rufe ido tana salati gabaɗaya wajan aka fara salati
Yaya Bilkisu ta zari mayafi ta ce "Wacce ƙaddararriyar makaranta ce har kusan almuru? Wallahi
yanzu zan je na dawo da ita, Allah ya baki lafiya Fulani"
Tana faɗin haka ta yi waje lokacin yaran duk suna makaranta banda guda ɗaya.
A hankali Yaran suke tafiya wajan su biyar, uku a gefe guda biyu a can gefe sai. Wacce ta fi ko
wacce nutsuwa ta ƙara ƙanƙame Alkur'aninta a ƙirji tana sauke numfashi, a hankali ta yi
kyakkyawan murmushi ta cikin liƙab ɗin dake maƙale a fuskarta. Murmushi daya haifar da
lomawar dimple ɗinta guda ɗaya. Farin ciki yau take ta ƙarasa bada haddar Alkur'aninta surar
ƙarshe kuma shafin ƙarshe na Suratul Bakrah. Latifa dake kusa da ita ta ce "Majeederh kina
dariya ko?" Ta jin jina kai ta ce "Uhm, Mimana na siyo mata alawa, kuma zan ga babyn da zata
haifa na samu ƙanwa" Latifa ta ce "Laa Mima haihuwa za ta yi?" Majeederh ta bata fiya
hayaniya da surutu ba sai ta ƙara jinjina kan ta cikin siririyar muryarta ta ce "E, ba kiga cikinta ya
yi ƙato ba? Zan je na ga baby kuma na ce mata na kammala hadda ta yi mini sadaƙa inji Ya
mu'alim" farin ciki ya kama Latifa sosai ta ce "Ai nima zani na ga baby kuma ni ma zan ce na
kusa gama haddata" Murmushi kawai Majeederh ta sake yi har ranta farin ciki take na ganin ta
riga kowa kammala haddar Alkur'ani ga Mima zata haifa mata ƙanwa. Tuna haka sai ya sa ta
lumshe idanu tare da rungume Alkur'an ta na ji tamkar ta yi tsuntsuwa zuwa gida. Amma kamar
wacce ake ƙara bayar da ita baya sbd yadda take tafiya a nutse da tarin kamala nutsuwarta ta fi
ta wata cikakkiyar budurwar. Tunda kuma ta fara girma Abu ya siya mata Liƙab kamar yadda Ya
mu'alim ya bashi shawara sbd kyan da Allah ya yi mata na musamman ne tamkar zara ce a
cikin sauran taurari ga sai dai ƴar firit take karatu ya sata gaba Islamiyya da boko ga tarin
hadisan da Abu yake ƙara mata idan ta dawo, bata barci sai wajan ƙarfe 1 asuba na yi take
tashi ta fara karatu.
Sun zo dai-dai wajan wa su matasa wani ya kalleta ya ce "Yarinyar nan daga gani munin ya yi
mata yawa, tunda nake ban taɓa ganin fuskarta ba" Wani ya ce "Kuma dai gata kamar fara ce"
"Ahhab, waya faɗa maka fari kyau ne?" Suka dinga surutu ɗaya ne ya ce "Ni kuma nutsuwarta
ke birgeni, idan ba makaranta ba ko aike bata fitowa mahaifinta ya gwammace ya je da kansa,
amma sauran ƴan uwanta ga su nan kullum suna fitowa" Latifa za ta yi magana Majeederh ta yi
saurin riƙe hannunta tana ƙarawa tafiyarta sauri. Burinta bai shige tayi tuzali da Mima ba tana
son jin labarin da a kullum take ce mata yana da muhimmanci a rayuwarta. Yau kuma ta yi
alƙawarin bata wannan labarin. Farin ciki ya danne yunwar da ta ke ji.
Tazarar gida ɗaya ne tsakanin gidansu Majeederh da na su Latifa, wannan dalilin ya sa
ƙawancan su ya ƙara ƙarfi duk da girmewa Latifa da Majeederh ta yi kuma suka samu nasarar
shiga makaranta ɗaya daga ta boko har Islamiyya akwai bambancin fahimta tsakanin su, wanda
ya sa Majeederh ta fi Latifa gane komai. Tun da ga nesa Majeederh ta hango Yaya Bilkisu tana
zuba uban sauri tare da share hawayen da ke bin idanunta. Cak! Ta tsaya sbd mummunar
faɗuwar gaban daya risketa Kur'anin hannunta ya nemi faɗuwa ta riƙe sosai fararen Idanunta
masu tsari kwance akan fuskar Yaya Bilkisu har zuwa lokacin data riski tsaiwar ta su.
"Allhamdu lillahi, maza zo muje ƴar albarka" Majeederh ta ƙurawa Yaya Bilkisu Idanu domin
Allah ya yi mata baiwar fahimtar abu dalilin da ya sa Abu ya ce psychologist zata karanta
bayan nan sai ta koma Islamic studies. "Haba Kulun Majade mu je mana" Kamar wacce take
karantar zuciyar Yaya Bilkisu ta ce "Mimana? Mene ya sameta? Ta ce zata bani labarin abu mai
muhimmanci, ta ce kafin na dawo zata kawo baby, ta haihu?" Tsoron ya kama Yaya Bilkisu
ganin tafarar ɗaya Majeederh ta kasance abin da ke shimfiɗe a fuskarta lallai tunani da kaifin
basirar Majeederh ya shige shekarunta. Ta ce "Eh, yanzu ma cewa tayi muje ta faɗa miki wani
abu" ta tsorawa mata Idanu sai kuma ta sauke ajjiyar zuciya mai nauyi tana jinjina kai. Sauran
ƙannenta Ruma da ɗayar kana ta kama hannun Yaya Bilkisu suka nufi cikin gidan domin suna
gab da ƙofar dama. Malam ya dinga girgiza Fulani yana faɗin "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un,
Fulani faɗa mini abinda ki ke son faɗawa ƴarki Majeederh" Ta ja numfashi da ƙyar tana karanta
kalmar shahada ta ce "Malam kayi mini wannan alfarmar kamar yadda aka baka ni ina shekara
15, to ka aurar da Hawwa'u a wannan shekarun domin akwai ɓoyayyiyen abu tare da ita don
Allah, don Allah..." Kalamanta suka tsaya sbd ajjiyar zuciya da tayi tana ɗaga idanu sama daidai
shigowar Majeederh ya yi daidai da wa'adinin rasuwar Fulani........ The destiny was just begun!
Duk wata mace yana da kyau ta nutsu ta bi labarin nan.
MIJIN MALAMA
Paid book
1 and 2 pay 1k to join us 0811923761615
She is too young a lokacin da Ubangiji ya amshi ran mahaifiyarta Fulani. Majeederh ba zata iya
cewa ta shiga maraici ba sbd Abbu ya ɗauke mata dukkan wani nauyin na uwa ya haɗa da na
shi na uba. Yarinyar da aka haifa lokacin mutuwar Fulani wacce take bin Majeederh ta amsa
sunan Aaliyah, motsin kaɗan Aaliyyah zata ce Anty Jeederh domin ita ta kewa kallon uwa
mahaifiya, Albarkaci kyauttukan da Majeederh ke samu tun lokacin ƙuruciya har zuwa matakin
girma ya taimakawa Abbu wajan rushe gidan shi tare da gina wani sabo rayuwar ta fara sauya
musu, ba sauyi mai yawa ba.
After 20yrs
Shekaru sun ja a lokacin da ta kammala karatun secondary wanda ya yi daidai da ƙara yin
saukarta ta uku, lokacin tana da Shekaru Ashirin, Ruma kuma Sha Takwas, Raihana nada
shekaru Sha Bakwai. Sai Aaliyyah mai shekara Sha biyar. Filin taron cike yake tab, da manya
da ƙana nan mutane, sarakuna da ƴan siyasa, sai kuma masu kuɗin jiyar da suka ƙara sawa
taron ya yi armashi. Zazzafar Musabaƙa ake gabatarwa tsakanin makarantar su Majeederh
Ahlul Madar, sai Nurul huda, a lokacin ne duk wacce ta lashe zata amsa sunan Gwarzuwar Jiha
kuma babbar malama wacce zata dinga wakiltar Ƙasar jihar bakiɗaya.
A hankali ta ɗago kanta inda take tsaye tana bin tarin tarin jama'ar da suke wajan da kallo, ta na
jin idanunsu a kan ta. Ta samu kanta cikin wani irin faɗuwar gaba, wacce bata taɓa jin irinta ba.
"Malama Majeederh, ke muke saurare" aka ƙara maimaita sunanta a karo na babu adadi. Ta
rufe ido tare da mai da kanta ƙasa cikin nutsuwa da kamala ta shiga rera karatun Alkur'ani mai
tsarki wajan ya ɗauki shiru sai sautin muryarta dake ta shi. Wannan shi ne karo na uku da
Malama Majeederh ke jan ragamar musabaƙar makarantar su, wacce ta zame abin alfahari
wannan gaɓar ne kuma idan ta samu nasarar lashe wa zata samu zarafin zama gwarzuwa a
garin su, kuma ta zama cikakkiyar Malama.
Kammala karatun na ta mai cike da Tajwid da makarujil-huruf ba tare da gyara ko tini ba ya
sanya wajan ya ɗaukar kabbara. Ta lumshe idanunta hawaye ma su zafi tun bayan rasuwar
Fulani ya samu damar fitowa daga cikin kyakkyawan Idanunta. Gabaɗaya ta cika burikan
mahaifiyarta