Showing 15001 words to 18000 words out of 65935 words

Chapter 6 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf

03 Aug 2025

1498

kenan? duk sanyi ya game min jiki har
attishawa na Fara nasan mura Kuma sai abinda hali yayi kawai".
Da sauri zahra ta karasa kusa da Hajiyar tana fadin "Ayya wallahi nayi tunanin ko zakiyi nafilfili
ne fa shi yasa na fita dauko wayata da kayana Dana Bari a wancen dakin, taso muje kici abinci
kinji Hajiyarmu insha Allah bazakiyi mura ba, Aunty zilai Naga da kaji a can bangaren inda
muka fito kiyi Mata irin pepper soup din da Naga kin yiwa Inna maimuna lokacin tana mura, ko a
soya Mata ta tafi gida dashi".
"To in Sha Allah Bari naje ai kayan dazu wani mutum ya debesu ya mayar kitchen din part din
da muka koma harma an karo wasu kayan masu yawa mun shafa'a mu nuna Miki su".
Ta fada tana mik'ewa ta nufi kofa ita Kuma zahra ta nufi dining ta daukowa Hajiyar abinci.

*** *** ***



Tunda garin Allah ya waye Mama ke faman Kai kawo a cikin Daki ta Kai gwaro ta Kai mari, tun
bayan wayar da sukayi da Aunty larai hankalinta Bai kwanta ba sai yarfe gumi takeyi baji ba
gani, ta Kira wayar Asabe yafi Shurin masaki amsar Daya ce switch off.
Wannan wane irin Abu ne Kullum tana tubkar gaba baya na warwarewa, Wai ita wannan Matar
meta taka ne, duk abinda takeyi ya tashi a banza Kenan?
Tun bayan kaiwa Mai gadi sakon Nan Basu Kara samun damar shiga gidan Nan ba ko kofar ma
tafi karfin zuwansu gashi yanzu Kuma aunty larai tazo Mata da wani Abun d'aga hankalin ga
sako Amma isar dashi shine aiki ga wayar Asabe Bata shiga da sai ta Kai ko ta bayan gidan ne
ta jefa abin bukatar dai ya shiga gidan ga sakon ya taho daga Jos din Kuma ance ba'a son ya
kwana ba'a aiwatar dashi ba, akwai matsala Dan ze iya warware duk ayyukan baya, kuma wani
aikin ze iya yin kome a Kanta ko 'ya'yan ta shine ta tada hankalin ta, tunda tasan idan tayi sake
kwabarta ce zatayi ruwa, tayi tunanin ko sahura zata aika Tasha ta karbo sakon idan yaso sai
tayi Mata bayanin yanda zatayi da sakon idan ta Kai can gidan zahrar, tayi tunanin ko zilai zata
Kira tace Mata ta fadawa Zahra sahura zata je tayi musu share-share kafin su dawo, Nan ma
taga abun ba lallai ya yuwu ba. Kara Kiran Asaben ta gwada still dai a rufe, dangwarar da wayar
tayi duk abin duniya ya taru yayi Mata yawa.
Duk iya tunanin ta ya Kare ta rasa Ina ne mafita dole ta tashi ta fice daga dakin tana tunanin
dole ta tura sahura taje ta Kirawo Mata Asaben in ba haka ba tasan watan Jin kunya ne yake
neman Kama Mata.
Wannan kenan.

Tunda Ammah ta fita daga bangaren Abban take kokarin neman zahra Amma Shiru har bayan
Azzahar inda taji Dadi da zilai tace Mata zahrar a gidan ta kwana Kuma Mai gidan ma yazo,
tasan kome ne ne zezo da sauki. Banda kada yaron Nan Sameer yaga Kamar ta raina abinda
yakeyi da yanzu ta tsufa a Kano, sakon text ta turawa zahrar ta tashi ya nufi bedroom dinta.



**** **** ****


Tun bayan fitar zilai zahra ta wuce bedroom tabar Hajiya nacin abincin ta, a gurguje ta sake
wanka ta gyara jikinta Bata wani Bata lokaci ba ta shirya cikin wata doguwar Rigar lace cotton
Mai kalar blue black, anyi touching dinsa da silver ash yayi Mata kyau sosai.Bata daura
dankwalin ba rolling tayi da ash din gyalen ta feshe jikinta da turenta ita abin har mamaki yake
bata, ta rasa yanda akayi duk inda take sai taga turaren da take amfani dashi a gurin. Dan
watsa hannu tayi irin baka gane Abu ba din nan.
Parlourn ta koma gurin Hajiya dai dai lokacin da su Sameer da Mahmud suka shigo.

"Bakin Hajiya ne yaki rufuwa data hango zahra ta nufo ta Fadi take "Masha Allah! Haka ake so
wwnnan 'ya naga alama bazakiyi saken da za'a karbe miki miji ba, ki Kama abinki ki rike wallahi
sonsa akeyi kamar goron hannun sarki ki matse kayanki tunda Allah kadai yasan
gwagwarmayar da yasha kafin ki shigo hannunsa..." Sameer ne ta katse Mata hanzarin zancen data dauko ya Fara fadin "ki tashi na mayar dake
gida garin Zan Bari yanzu Banda kina Nan da nayi nisa a Hanya".
Shi kuwa Mahmud Banda kallon zahra ba abinda yakeyi gani yayi ta Kare Masa wani sanyin
kyau a idanunsa, Kuma fir Taki yarda su hada Ido dasu duk kowa da kalar kunyar da takeji tasa.

"Hajiyarmu ya zaman guri Daya nasan kin gaji sosai ko".
"Mahmud din ta kalla Wanda ya nufo ta.
"A'a ban gaji ba ai wannan yarinyar da Abun gari take, jiya ma dai an Bata Mata Rai ne yasa na
ganta Kamar marar wayo Amma yau ai ka gani sai Ina taka saka Dani takeyi".
"Dan Allah ki taso bana son nayi dare a hanya ke Kuma kin tsaya sai maimaita zance kikeyi,
abinda ya wuce ai ya wuce".
Da sauri Zahra ta juya ta koma ciki ta barsu Sameer nata yiwa Hajiyar Dan zance, turarika da
sabulai ta daukowa Hajiyar ta fito, lokacin Hajiyar na gyara lullubin gyalenta tana fadin "ai Zan
dawo ne tunda ban karbo Mata dawa'in Dana saka ayi Mata ba a sanka, Kasan duk wannan
jidaliyar ta jiya Bata Hana da almuru Saida Tofeek ya kaini Sanka naje na fadawa Malam karami
ya taimawa jikata da maganin tsarin jiki Dana Baki, yo anyi sake Baki ya Kamata dubi fa yanda
take tubarkalla, yo tunda ya fito da ita Nan ai magana kuma ta gare haka ze dunga reto da ita,to
kasan wani idon da bakin ba masu kyau bane, shi yasa gara a dafata daga Nan" shi dai
mahmud ban kunshe dariya ba abinda yakeyi yasan kadan da aikin Hajjaju ne hakan, shi Kuwa
Sameer ya cika yayi fam shi yayi Dana sanin kawota gidan nan Dan Allah kadai yasan abinda
ta fada Mata tunda kanwa Bata jiqa a bakinta.
"Wallahi Zan tafi na barki a gidan nan haba saboda Allah kin kama zance kamar an saka Miki
batir".
Dakuwa tayi Masa ungo Nan. Dan nema kake wani zaro min Ido to tsoron ka zanji kome? wato
gaskiyar ce baza'a fada ba".
Juyawa yayi ya nufi kofa da hanzari Hajiyar tabi bayansa itama zahrar da sauri tabi bayan
Hajiyar, ji tayi an riko ledar da hannunta gaba daya ya dawo da ita jikinsa.
"Precious ba irin huge din Nan na welcome saiki wani shareni"
Ya fada Yana Dan goga Mata sajensa a gefen kumatunta cikin wani irin low voice.
Wani yar taji a jikinta.
Cikin shagwaba tace "Dan Allah ya Bari na rakata kada su tafi ban Bata komai ba, Kuma na
saka Aunty zilai ta dafa Mata nama".
Juyota yayi suna facing din juna. "Baze tafi ba kawai ya gaji da surutun Hajiya ne itafa Bata
gajiya da magana, kawo na gani dame-dame za'a bawa kakar tamu?"
Ya fada Yana duba cikin ledar.
"Inye ashe dai da wayonki irin wannan Abu haka? jazakumullahu khairan. Bari na Kara gyara
Miki kudi ya Ciro daga aljihun wandonsa ya saka a ledar Yana fadin sai kice ta sayi man
shafawa ko kice ta sayi goro, bari mu dawo ki bani abida ya samu, Kuma idan anjima Zaki
rakani gidan su Sameer na gaishe da mommy sannan muje muga Mai sunana"

.
Bai saki hannun nata ba, a haka suka nufi kofar fita.
Taso ta zame hannunsa daga cikin nata tasan ba Karamin aikinsa bane su fita harabar a haka,
kuma taga alama gidan da mutane da yawa ga kuma Hqjiya da Sameer.
Ganin kada ya Bata kunya yasa ya saki hannun ya rike ledar kawai kafin taje gurin motar ta
shiga gurin su Aunty zilai ta gani ko angama.
Cikin ikon Allah ta samu an Gama soya Mata cikin roba, Ashe Daman tun safe suka dafa aka
saka a fridge yanzu soyawa kawai sukayi, a ciki babban warmer aka zuba zilai ce ta dauko suka
fito suka nufi gurin da suke tsaye suna jiran zuwansu.
Saida Motar tabar harabar gidan sannan suka juya suka koma, Saida suka wuce idanun jama'a
ya janyota jikinsa Yana shagar kamshin jikinta, a haka suka shige ciki zame jikinta tayi tana Dan
dubansa. "ga abinci Nan na kawo maka nan ko can table Amuje".
Dan bakinta ya shafa kadan ka Yana kwaikwayon maganarta..
"Bari nayi wanka sai muzo muci abincin nasan kema bakici ba ko?".
"Kai ta gyada masa.
Gurin da Hajiyar taci abincin ta gyara sannan ta dauko wata table mat da shimfida a kasa ta jera
abincin, gurin kayan kallo taje da gani ko hadasu ba'ayi ba, ta tsuguna tana hadawa ya shigo,
yayi wanka ya saka Riga armless da wando three quarter blue black na kamfanin Adidas sai
fitar da wannan kanshin nashi yakeyi wanda har ya Zama constant a jikinsa, direct inda take ya
nufa dago ta yayi "oya taso kibar wannan ba aikin ki bane akwai Wanda zaya hadasu".
Kai ta gyada masa ta bishi suka koma, abincin ta zuba musu sukaci Saida suka koshi, sannan
ta tattara gurin ta dauke komai ta dawo ta zauna a gefensa.
Jikinta ya Dan kwanto Yana Dan matsa kafadar ta.
"Precious".
Ya Kira sunan sunanta.
"Na'am".
"Fada min me Haseenar ta fada Miki Kika yi yaji Zaki Kira min Ruwa? Banda Allah yasa Ammah
tana yina da kin tayar min da zaune tsaye, ni na taho Ina mararin ki ke kuma kina gudun Zama
dani ko?".
Sakin kafadar yayi ya kwantar da ita a cinyarsa suna facing na juna.
"Nifa na fada maka ba guduwa nayi ba to a cikinsu ai ba Wanda yayi min laifin da zanyi yaji?
Kuma Dan lalacewa na tsaya Ina yiwa wannan Mai saffar mazan yaji,kawai dai Naga bazan iya
tolerating na nonsense dinta ba,wato zatayi amfani da damarta tayi min illah tunda Nina hanata
cikar muradinta ki? Ai naji ance tare kukayi karatu ba a UK? Dan Allah ka fada min waye Kai
wallahi zuciyarta taki samun nutsuwa, abubuwan da nake gani a Nan sun girmewa tunanina, pls
tell me, Me amor".
Tsuru yayi da Ido Yana kallonta Dan kalmar ta bashi mamaki data fito daga bakinta.
"A ina Kika iya yaren Portuguese?".
Ai Yana fadar haka ta bude Baki alamar mamaki da sauri ta yunkura zata fece ya mayar da ita
jikinsa.
"Ya haka Zaki gudu daga tambaya".
"Nima bansan ko wane yare bane na fada sunan ne naji yayi min Dadi shi yasa na fada maka
Ni ko ma'anarsa ban sani ba".

Ta fada tana Kara sunne Kai a kirjinsa.
"A'a idan ba Rami meya kawo zancen Rami? Meye na Jin kunya tinda kince Baki San ma'nar
sunan ba duk da haka yau ranar Nan special ce a gurina badan da dutse tsakanin mu ba da
Saina bada special gift Nima".
























.
[2/1, 6:08 PM] ASHMAR: ✨✨✨

AUREN HUCE HAUSHI.

✨✨✨


MAMAN FATEEMAH.


Page. 47



________Duk yanda Mahmud yaso zahra ta bashi amsa abun yaci tura da gaske take
kunyarsa Bata taba zaton Yana Jin yaren ba, shima kyaleta yayi dan bashi da amsar
tambayarta a yanzu dai sai hakan yayi Masa dadi, wata hirar ya dauko Mata ta tafiyar da yayi
da ire-iren cigaban da yake ganin makarantun mu zasu samu, har aka Kira sallar la'asar suna
gurin tashi yayi suka shiga ciki yayi Shirin masallaci.
Misalin karfe takwas da kwata suka fito zuwa unguwar da zata raka shi, sunyi wata irin
dacewa dole idan ka kallesu ka Kara, Dan kallonsa tayi "Zan leka na yiwa su Aunty zilai
sallama".
Daka ya amsa Mata saboda Yana amsa waya.
A parlour ta iskesu suna Hira, a gurguje suka gaisa ta fada musu zasu fita, a dawo lafiya
sukayi Mata ta juya ta nufi kofa har ta kusa fita ta ji maganar Aunty zilai bayanta.
"Uwar dakina Ammah tace a fada Miki ki bude wayarki tana son magana dake, yanzu ba
dadewa ta kirani tace na Kai Miki tawa, na fada Mata Mai gidan Yana Nan shine tace to idan kin
fito na fada Miki lallai ki bude zakuyi magana".
Dan rausayar da Kai zahra tayi da alamun damuwa a fuskarta.
"Ni wallahi na kasa bude wayar ne laifi nayi Mata fa".
"Laifi Kuma kina Nan tana can akayi laifin?"
Kai ta gyada Mata alamar Eh.
"Dan Allah ki bude wayar kuyi magana ko hankalinta ya kwanta,Allah a cikin damuwa take".
"To shikenan sai mun dawo din".
Ta fice tana amsa a dawo lafiyar Aunty zilan.
Motarta daya kawo ta gani, Wanda ya Kira da safwan dazu ya fito daga ciki da alamar shiya
kawota nan seat din kusa da driver Mahmud ya budewa Zahra Yana fadin "Bismillah"
Saida ta zauna sannan ya nufo gurin safwan din yayi Masa magana sannan ya shigo ya tayar
da motar suka nufi gate din fita, a dawo lafiya masu gadin sakayi musu Dan ba mutum Daya
zahra ta gani ba.
Sunyi tafiya Mai Dan nisa kafin ya riko hannunta Bai kalleta ba gabansa yake kallo yace.
"Kina tambaya ta wannan gidan na wanene ko?"
Ya Dan juyo Yana kallonta.
"Eh" ta fada a takaice.

"Gidan a hannuna yake, kusan Kuma ni aka wakilta a Kan ma'aikatan cikinsa to Yana yin
rayuwa ne yasa nayi nesa dashi Amma yanzu bani da sabgogi da yawa Ina ga ma anan zamu
Dan Zauna na wani lokacin kafin muga yanda za'ayi akan matsalarki ta fibroid din nan dan
tunda aka fada min hankalina kasa kwanciya yayi Saida na Kira likitan dana fada Miki, shine
yace ya kamata muje suyi nasu binciken su tabbar da abinda Nan din suka fada".
Dan marairaice Masa tayi.
"Nifa wallahi na warke na fada maka ba wani ciwo fa yanzu Dan Allah ka hakura, kaga su
Ammah Basu San zamu Dade ba, kaga harda Mai aikinta ta bani aro fa Kuma kusan itace
ma'aminciyarta a fannin abincin bangaren ta".

"Kin warke kamar Yaya? Ai abinda ze Hana a duba min lafiyarki sai ikon Allah kinaji fa Yana
Hana Mata haihuwa Ni Kuma da nake son duk shekara ki aje Mana baby koma babies, idan

Allah yasa nafi ki karfin jini ki dinga bamu twins, kawai lokaci kadan ki ciki gidan da 'ya'yan mu".
Ya fada Yana Kai hannunsa akan cikinta Yana kashe Mata Ido daya.
"Oya talk Mana kinyi shiru".
"To me kakeso nace ai ka Gama Yanke hukunci".
Saita share maganarsa ta biyu.
Gidan Sameer suka Fara nufa Sam Sameer din besan da zuwansu ba Saida ya kusa da shiga
kuntau din sannan ya kirashi ya fada Masa gasu Nan zuwa.
"Masha Allah gida ne shima Babba Mai kyau sosai Amma baiko Kama kafar inda sukayi
masauki ba, da fara'a sosai Fateeha ta tarbi zahra wannan shine haduwarsu ta farko face to
face ba karamin mamaki Fateeha tayi ba, duk da Sameer ya nuna Mata wani hoton zahra
amma sai taga hoton Wasa ne akan zahirin gaskiya ba karya oga Mahmud yayi mace dai dai da
level dinsa Dole 'yan bani na iya su dauki na wuta Dana gashi da ita, me wannan mezeci da
irinsu Haseena.
Da sauri ta garasa gurin zahrar tana fadin "maraba da babbar bakuwa irin wannan zuwan
bazata?
Ta mika Mata yaron da yake hannunta tana murmushi, itama zahrar murmushin ta mayar Mata.
Cikin parlourn suka shiga gaba daya, gaishe da Muhmud din Fateeha tayi, yayi Mata barka,
sannan zahrar ma suka Kara gaisawa da oga Sameer, taje ta Mikawa Mahmud Babyn.
"Ki rikeshi a haka na ganshi, wallahi bana iya daukar Yara a haka tausayi suke bani, Sai naga
kamar Zan karya su ne idan na dauke su".Ya fada Yana jifanta da wani kallo.
Itama kallon nasa Zahra tayi da yi Masa alamar zakayi bayani da hausar garinku, tana Dan
kada Masa sexy eyes dinta. A haka yayi masa addu'a ya shafa kansa, cheque ya Dora Masa a
jikinsa abinda ta gani jikin cheque din ba Karamin mamaki ya Bata ba, shi Kuma Dan gogan
Saiya fuske yayi kamar baiga kallon tuhumar data bishi dashi ba. Godiya sosai Fateeha tayiwa Mahmud ta dauki cheque din ta kaiwa Sameer, ba karamin
mamaki yayi ba yana Kara duba cheque din Yana kallon Mahmud. Kai ya girgiza Masa "don't
say anything pls shi yasa ban baka ba na madam ne wadda tayi nakudar haifar min takwara"
Shiru yayi kawai Dan wata kyautar tafi gaban godiyar fatar Baki, a haka Fateeha ta wuce ta
barsu tana kakabin abun a zuciyarta Wai shi wane irin kudi wannan bawan Allah ya mallaka
Wanda baya Jin ciwon kashe da kyautar su irin haka?.
Abubuwa motsa Baki Fateehar ta kawowa Mahmud, sannan taja zahra suka shige bedroom
dinta.
Kan sofa zahra tayi masauki tana rike da Ayyan sunan da ake fadawa yaron kenan, Fateeha
na fadin " Masha Allah, Amarya kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login