Showing 18001 words to 21000 words out of 65935 words

Chapter 7 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf

03 Aug 2025

1479

Sha kamshi sai yau Allah yayi haduwarmu?".
"Wallahi kuwa Aunty, barka Allah ya Raya Mana".
"Amin ya Rabbi, nifa na dauka da Rana zakizo mu yini muna hira Amma sai naji sweetheart
Yana fadar Wai gaku Nan a harya".
Da gyarawa Ayyan riko tayi tana zame rolling din kanta. "nima bansan da fitar ba sai dazu da
yamma yace zamuzo nifa naso ya barni nazo suna lokacin Amma yace a'a saiya dawo
zamuzo".
Har Fateeha ta bude Baki zatayi magana ta tuna gargadin Sameer akan sakin bakin magana
yace ta iya bakinta akan abida Zata fadawa zahrar.
"Kinsan komai nufin Allah ne sai yau ne ya kaddari mu hadu,munga sako Allah ya saka da

Alkhairi yabar zumunci, Kaya irin haka kamar za'a bude Masa Boutique dasu, wasu ai har ya
shekara biyar sannan yayi amfani dasu, Kinga wannan material din da Kika sako min me kalar
peach wata sister dina da za'a yiwa biki ta kwallafa rai a kansa tana son tasa ranar dinner da
taje kasuwa kasa sayensa tayi 350k 4yrd, saita gano na sayar Mata da nawa tunda suna gidan
safwan ya kawo kayan".
Ita dai Zahra Shiru tayi Dan ji tayi wani bambarakwai tunda ita dai bataga wasu Kaya ba, amma
saita wayance da fadar "lah ba komai ai dan "komai nayiwa d'ana ban fad'i ba, Allah dai ya
Raya Mana yayi musu Albarka".
"Allahumma Amin".
Knocking akayi daga waje, umarni Fateeha ta bayar wata yarinya 'yar matashiya ta shigo da
babban tray da kayayyakin motsa Baki a Kai ta aje ta gaishe da zahra ta juya ta fice.
Suna cikin hira Sameer ya Kira yace zahra ta fito zasu wuce.
Har gurin mota suka rakosu suna ta godiya, jikin window din da zahra take ta Dan leka tana
"Fadin zamu mu shigo in Sha Allah mu yini a gurinki tunda ni bakizo Mana da rana ba".

"To ai ba laifina bane Kinga niba sanin garin naku nayi sosai ba sai a yanda akayi Dani".
Dariya Fateeha tayi "to ai kin Zama 'yar kanon kema tunda gaki a cikinta Baki San ranar barinta
ba".
Sameer ne ya yiwa Fateeha magana ta yiwa zahra sallama, ta bude back seat ta saka ledar
dake hannunta.
Direct gandun Albasa suka nufa gidan mommy, zahra Bata tashi Jin abinda tayi da Bata kyauta
ba Saida suka shigo harabar gidan mommy din.
Dan marairaice Masa tayi da fuska a Karon farko ta riko hannunsa.
"Please me amor ka shiga Kai kadai wallahi kunyar mommy nakeji bazan iya shiga ba".
Ta fada a shagwabe kamar zatayi Masa kuka.
Saida ya gyara parking sannan ya maido hankalinsa gaba Daya gurinta.
Meya hadaki da mommy Kuma da kike Jin kunyar haduwa da ita?".
"Jiya fa harda ita a gidan Hajiyar oga Sameer".
Mai gadi ne ya karaso Yana gaishe da Mahmud tare da jera masa godiya wadda zahra Bata
Dan isalinta ba, fitowa Mahmud yayi suka gaisa da Mai gadin,abinda ya tilastawa Zahra fitowa,
gaishe da Mai gadin tayi ta Dan Fara tafiya duk da Batasan inda kofar shigar take ba.
Gurin wasu kujeru data gani ta nufa ta zauna da alamar Kamar Baki ne suka tashi daga gurin.
A Nan ya sameta ya Mika Mata hannunsa ta kama ya mikar da ita tsaye, "zo muje ciki dare
Yana karayi kin zaunar damu a gurin Fateeha kome kuje fada ma oho Allah yasa dai ba gulma
kujeyi ba".
Kafin tayi yunkurin bashi amsa daga bayansu sukaji maganar Rukayya "lah wa nake gani kamar
Ya Mahmud da Auntyn mu?"
Da sauri zahra ta zame hannunta ta juya baya tana Fadin "wallahi Aunty Rukayya nayi fushi
saboda Allah saiki taho bako sallama".
"Ayya sorry wallahi Nima karfina akafi dole tasa na taho kinsan Ya Sameer ba sauki shine ya
tattaroni ko wanka fa sai a gidan Nan nayi".
Ta juya ya Mahmud Ina yini an dawo lafiya?".

"Lafiya kalau Ruky ya kikaji da 'yar rigima Ashe Kuma yaji tayi muku ta gudu".
"Wallahi kuwa ya Mahmud ai jiya nayi kuka kamar ba gobe tashin hankalina Daya idan ta B'ata
me za'a fada maka idan ka dawo Ashe kana hanya".
Baki zahra ta zubura tana kiftawa Rukayya Ido.
Kafin yayi magana sukaji magana daga bayansu.
"Waye nake gani kamar DANGEN SHUNI!?"
Da sauri Mahmud ya juya itama zahra juyawar tayi Jin kamar muryar data sani ce take Fadin
hakan.
"Lah! Lah! Lah! Wa nake gani haka? Zakariyya Daman ana ganinku, rabon da mu hadu tun
zuwana na karshen kontagora".
Zahra ce ta Matso tana Fadin Lah Ya Abba, Kaine ina yini?"
"Lafiya kalau ya kukaje gida? ai da safe na Kira Rukayya take fada min bakwa tare ta dawo
gida".
"Eh wallahi, yasu Umma?"
"Suna lafiya daga Ina haka?"
Dan kallon Mahmud tayi kafin tace Masa "daga gida muke Mommy mukazo gaishewa".
Kusa da Mahmud ya matso Yana Fadin "DANGEN SHUNI! Allah ya taimaki manyan kasa.
Daman ana ganinku haka available? Gaskiya na zama lucky. Daman wallahi neman number ka
nakeyi nayi interview da kamfanin ku na Nan Kano last two weeks Amma har yau ban samu
number ba, kasan lamarin kasar Saida wakasani,to ya akaji da jama'a?" .
"Lafiya kalau Alhamdulillahi, Rukayya ki bashi number ta zamuyi maganar later, ko kana Shirin
Zama sirikina ne?".
'yar dariya yayi "Hakan nake fata ai zuwan zahra jiya Ni Alkhairi ya zamar min".
Dan Jim Mahmud yayi, me kenan zakariyya kenan brother din sajida ne?
"Anyway we'll talk later in Sha Allah, madam let's go".
Sukayi sallama da Ya Abba suka nufi ciki zuciyar zahra fal murna wato duk abinda Allah yayi
akwai hikima a cikinsa, wannan dalilin ne yasa ta tattara ta nufi Janbulo Ashe ita zata Zama
dalilin haduwarsu.

Saida suka gulewa ganinsu sannan Ya Abba ya kalli Rukayya, "Daman Kuna da relation da
DANGE?".
"Eh aminin Ya Sameer ne tun suna secondary School, yanzu haka shine P.A dinsa ai jiya zahra
da muka dauko daga can wife dinsa ce an samu wani incidence ne tayi tafiyar ta can Janbulo
din".
Baki sake yake kallon Rukayya abin jinsa yake kamar Almara badan ya gansu tare ba baze
taba gaskata zance Rukayya ba, gaskiya he's surprised to ai shi ba haka maganar tazo Masa
ba daga bakin sajida.

"Wai kina nufin DANGE ne mijin zahra?"

"Eh Mana shine, Wai Daman Kasan Ya Mahmud din ne?"

"So sai kuwa farin sani, muna haduwa da a kwantagora a unguwa Daya ma kuwa, ai kakarsa ta
wurin Babansa 'yar can ce Nima kakata 'yar can ce Ummar mu kadai ta Haifa a Rimin sumaila
Aurenta ya mutu ta koma gida, duk 'yan uwan Umma suna can kwantagoran na Niger state da
Abuja, kinsa meya daure min Kai kuwa?" Girgiza Masa Kai tayi alamar A'a.
"Cewa fa akayi ita zahrar an aura Mata Almajirin wani malami da yake a unguwarsu saboda duk
Wanda yazo ze aureta sai an fasa Auren"

"Nima naji kadan daga labarinta gurin ya Sameer to ga dai mijinta Nan sauran bayanin Kuma
ban San yanda akayi ya faru ba, tunda ya Sameer ba fada mana zeyi ba".

A parlour suka Sami mommy da kannan Rukayya Mata Bilkisu da Husna sai karamar yarinya
'yar Auntyn su Sameer Afra.

Tunda suka shigo zahra ke sadda Kai kasa da gaske nauyin mommy take ji, gaisuwar yaran
suka ringa amsawa da gudu Afta ta nufo zahra tana Fadin "welcome Aunty" ta shige jikinta tana
tattabata.
Hannunta zahra ta riqe suka karasa gurin da mommy ke zaune yayin da su Husna suka koma
dayan parlourn.
A kasa Kan carpet suka zauna, a tare suka gaishe da mommy din, ta yiwa Mahmud sannu da
dawowa sannan ta Dora da godiya, hidima da akeyi da Sameer. Zahra ta kalla ganin sai sadda
Kai tajeyi yasa tace.
" 'ya ta ko jikin ne Naga bakya walwala sosai?".
Yana ji yayi fuska Bai tankaba ba dai iya shegen da tayi ba kenan jiyan saita magantu da
bakinta.
Bata yarda sun hada Ido ba tace.
"A'a ba komai mommy lafiya ta kalau".
"To Masha Allah haka nake son ji, kina jina ki saki jikinki Dani ki daina Jin nauyi na kinji, ni
uwace idan kina da damuwa duk da bama fatan hakan ki sameni ki fada min ki daina yanke
hukunci da kanki".
"To in Sha Allah bazan qara ba na gode". Ta fada tana Wasa kitson Afra kanana Yar dasu.
Tashi mommy tayi tana fadin "Bari na fadawa Alhaji kunzo sai ku shuga ki gaisa yaga 'yar tasa
wadda bai sani ba".
Ta nufi nufi wani corridor dake hannun dama.
Bata dade ba ta dawo tana fad'in "Mahmud kuje Yana parlourn kasa". Saida aka yiwa Afra wayo
da chocolates sannan ta yards tabi mommy dakinta ita Kuma zahra suka nufi bangaren Abban
su Sameer din.
A Nan suka same shi a parlourn Wanda yaji kayan more rayuwa dai-dai da shekarunsa, babban
mutum mai cikar Kamala, fari sosai kamar irin buzayen nan, a Nan zahra ta gano inda Aunty
Rukayya ta samo farin ta dan mommy dai irin wankan tarwada din nan ce shi yasa tayi
mamakin Jin Rukayya kanwarsa ce uwa Daya uba Daya. Da madaukakiyar fara'a ta taresu Yana fadin "Masha Allah sannunku da zuwa, ka kyauta
Mahmud daka kawo min yarinyar nan kaga na Riga Alhaji Muhammad ganinta ko? masha Allah

ku zauna".
Ya fada Yana nuna musu seat din Zama, basu zauna ba a kasa suka zauna suna gaishe shi,
ya amsa cikin sakin fuska, da gani shi mutun ne Mai yawan fara'a.
"Allah yayi muku Albarka ya kade fitina a tsakaninku naji Dadi kwarai daka kawo min ita, yarinya
ayi hakuri da juna kinji, mijinki na jama'a ne Saida hakuri kiyi Masa biyayya gwargwadon
iyawarki, Kai Kuma ka kula da lamarin ta kada ka yarda wani ya wulakanta maka ita amana ce
suka baka, a yanda kaje musu ba kowa ne ze dauki yarinya kamar wannan ya baka ba, to ka
kula da ita sosai ka Bata dukkan farin ciki tayi rawar gani, daga karshe Ina rokonka abinda ban
taba saka Baki a cikin duk kwaramniyar da akayi a baya ba sai yau, kayi hakuri ka koma gida
ba girmanka da mutuncinka bane haka ai ba'a fushi da iyaye duk rintsi albarkarsu ake nema
kome ka Zama indai kana da iyaye yaro ne Kai, nasan an bata maka Amma idan ka duba ko
tukwicin wannan yarinyar da Allah yayi Maka ai sai ka huce ka nuna godiyarka ga Allah Daya
baka ita, Kai ba karamin mutum bane a kasar Nan Koda kuwa a shekaru kake da karancin
girma, kaje gida ka hada hankalin ka guri daya, Allah yayi Albarka ya Kara daukaka numa ganin
sakonni mun gode kwarai da gaske, idan Kuma naji Shiru baka koma ba da kaina zanyi abinda
baka so ayi din, Dan ko shekaranjiya Saida Hajiya Inna Tasha kukanta a dakin Nan Ina amfanin
irin haka ai musulmin kwarai da yafiya aka San Shi kaji Mahmud ayi hakuri ayi afuwa Allah yasa
son masu yafiya".
Tunda Alhajin ya Fara magana jikin Mahmud yayi sanyi da gaske duk badak'alar da akayi ko
uffan Bai tofa ba sai yanzu Kuma yasan baya raba Daya biyu damuwar da yaga hajiya Inna a
ciki ta Dame shi.
Cikin ladabi Mahmud ya Fara magana. "Nagode Abba in Sha Allah Zan koma, Nima nayi
wannan tunanin ba fushi nayi dasu ba sune dai sukayi fushi dani, Ina son su huce ne tukunna
kada na koma a maido hannun agogo baya".
"Kai haba wannan maganar ai babu ita to ai itama zahara'u ta zamar maka garkuwa, ki tashi ku
tafi dare ya Farayi ga yanayin sanyi Allah yayi Albarka ayi kokari ayi yanda nace".
"In Sha Allah Abba".
'yar karamar Leda Fara Alhajin ya mikowa Mahmud Yana fadin "ungo rikewa 'yata".
Godiya sukayi Masa Sosai suka nufi kofa Yana saka musu Albarka.
Lokacin da suka fito Rukayya ta shigo suna tare da mommy.
"Aunty Rukayya har Ya Abban ya tafi?". Zahrar ta fada tana nufar inda Rukayyar take.
"Eh ya wuce tun dazu".
"Ok shikenan da sako Zan bashi gurin Ummah Amma na Kirata a waya".
Sallama sukayiwa Mommy Rukayya ta rakosu har gurin mota da ledar da mommy ta bawa
zahra kyautar dangin turaren wuta dasu humra.
Da sukazo fita kudi masu yawa taga ya bawa Mai gadin gidan sannan suka wuce, tunda suka
fito daga parlourn Alhaji Abban su Sameer Mahmud yayi dif da alamar anyi Masa famin wani
Miki a zuciyarsa.
Ganin haka yasa zahra ta Kama kanta itama.
Titin gidan Bashir tofa suka fito gasu can sun fita gidan Buhari, sahad store taga ya shigo ya
nemi guri yayi parking sannan ya bude Yana Fadi ki jirani ina zuwa ya wuce ciki.
Bai Dade da shiga ba wata mota tayi parking kusa da tasu, gurin akwai wadatar hasken da yasa
kana iya ganin Wanda yake cikin mota.

Ba zato ba tsammani kawai idanun Zahra suka sarke Dana Musbahu Wanda ya fito daga gurin
driver suna tare da wani Guy da alamar dayan irin ya'yan hutun Nan ne, da gani Suma sayyayar
sukazo, da sauri ya nufo gurinta jikinsa har rawa yakeyi Yana fadin "Zahra!" dai-dai lokacin
Kuma Mahmud ya fito tare da ma'aikatan gurin sun dauko Masa Kaya sun nufo motar, shi Kuma
wannan gayen Yana ganin Mahmud yayi wata irin zabura ya nufeshi ya rungume shi jikinsa na
wata irin tsuma Yana fadin "Ya Mahmud Ina ka shiga ka barmu".
[2/1, 6:08 PM] ASHMAR: ✨✨✨

AUREN HUCE HAUSHI

MAMAN FATEEMAH.

Page 48.

___ Rungume juna sukayi sosai, kuka ya saka Masa kamar karamin yaro da gani ba
karamin missing dinsa yayi ba , Shima Mahmud Jin wani Abu yake yi a zuciyarsa badan
namijin duniya bane da Babu abinda ze hana shi zubda hawayen shima, yayi kewar Faruq
sosai saboda sunyi wata irin shaquwa dashi ta ban mamaki,duk da ba uwa daya ta haifesu ba
Kuma kusan sa'anni ne Dan baifi wata hudu Mahmud ya bashi ba, Amma Yana bashi girma
sosai,duk abinda yakeyi hankalinsa dari bisa dari Yana Kan musbahu Wanda yayi mutuwar
tsaye shi Bai karasa gurin zahrar ba, shi kima bai dawo baya ba, me yake Shirin faruwa ne?
wannan din meye dinta yasan dai tayi aure ance wani k'olo aka aura mata, to Ina auren kada
dai gudowa tayi ta shigo yawon duniya?.
Ita ma zahrar ji tayi komai ya tsaya mata, har wata zufa taji tana tsatstsafo Mata a jikinta abun
kamar a mafarki, gurin da su Mahmud suke ta kara kallo still suna yanda suke Saidai gaba
Daya hankalinsa Yana gurinsu fuskarsa ba annuri ko misqala zarratin kamar dade duniya be
taba dariya ba, sadda Kai zahra tayi dan ji tayi wani irin tsoronsa na shigarta tuna karonsu tayi
wanda ya kusan cinye mata lebe, kasa tayi da kanta jiran taji ya zata kaya.
Bayansa ya Mahmud ya ringa Dan bubbugawa da tafin hannunsa Yana fadin.
"Haba Faruq meye na kuka da girmanka da komai Kai ba mace ba, ka nutsu ka share wannan
hawayen, akwai mace fa a kusa damu tana kallonka, wallahi wata Rana sai tayi maka gorin
ragon maza"
Ya fada Yana sakinsa da sauri yama duban masu rike da kayan daya saya a hannu "sorry na
barku da Kaya kuyi hakuri Dan Allah mu karasa ku saka a mota"
Yayi gaba yana yiwa Mushahu wani shegen kallo, Faruq na rike dashi ram Kamar Yana gudun
ya bace Masa.
Back seat Faruq ya bude suka zuba kayan,Faruq din ne ya curo kudin da baisan yawansu ba
ya Mika musu sukayi godiya suka wuce bakin aikinsu.
Jikin motar Mahmud ya tsaya Yana facing din musbahu da fuskar shanu.
"Dan Allah Ya Mahmud kana Ina ne duk tsawon wannan lokacin? Kuma wacece wannan da
kuke tare?"
Fuska Babu annuri Kona sisin kwabo ya Maida dubansa Kan Faruq din "Idan ka Gama abinda
kazoyi ka sameni a Bawo road komai dare Ina jiranka". Ganin yanda mahmud ya daure fuska

yasa yaja bakinsa yayi shiru be kara tambayarsa komai ba.
"Ok. Zan shigo yanzu ma in Sha Allah, Nima yau na shigo around four thirty, yanzu ma uncle
mushahu na rako, dan yayar Mamee ne gashi nan,bari nayi masa magana ku gaisa be ganeka
bane".
Da hanzari Mahmud ya daga masa hannu "pls Faruq no need". Ya fada yana dhugewa motar,
abinda ya daurewa Faruq kai kenan, wai Ya Mahmud ne yake driving da kansa, sai yake ganin
kamar an canza masa Ya Mahmud dinsa da wani.
Saida ya fice daga harabar gurin sannan Faruq ya karaso gurin Uncle dinsa yana fadar "Yanzu
fa a hanya muke maganar Ya mahmud da kai ashe yana kusa damu wallahi ba wanda ya zaci
yana kasar nan, abinda ya bani mamaki wannan Babyn da suke tare a sanina da Ya Mahmud
baya harkar mata gaskiya, sai dai ban sani ba ko bacin rai ya saka shi yin hulda irin wannan
dasu".
Faruq be ankare da shi kadai yake zubarsa ba sai da ya kai aya yaji Musbahu be tofa masa ko
A ba sannan ya dan taba shi.
Firgigit yayi alamun yayi zurfi a cikin dogon tunani.
Dogon numfashi yaja yana yiwa Faruq duban tsanaki, kafin yace.
"Faruq waye wannan nake gani kamar Mahmud?".

"Shine mana baka ganeshi bane?".
Wani gumi yaji nan da nan ya rufe shi tabbas Shiya gani a cikin hotunan da Najib ya turo masa
na daurin Auren zahra, ya dade yana hasaso inda yasan face din amma ya kasa tantancewa ke
nan DANGE shine mijin da aka aurawa zahra a matsayin Almajirin Alaramma? take a nan yaji
wata irin karaya ta mamaye masa zuciya yasan ya rasa zahra har abada, shi dinwa da ze iya ja
da wannan dan tahaliki, ko manyan manajojinsa bai isa yayi takara dasu ba kafin ma a kai ga
P.A dinsa.
Cikin nuna tsantsar karaya ya cewa Faruq.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login