Showing 54001 words to 57000 words out of 65935 words
Chapter 19 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf
Allah yayi halitta a gurin ai sai yanda Hali yayi kawai".
"Kice kin zurma dai batool irin wannan kodawa haka?"
"Gaskiyar kenan Aunty wallahi tayi, ji nake kamar jinin mu ce ita"
Lumshe ido dan gogan yayi jin yanda ake Koda Masa precious tun Bata kwana a garinba har ta
Fara shiga ran kannensa haka.
"Matarsa ce fa bakiga ta rude ba da aka shigo dashi a rirrke ba?"
"Yehhh... Yessss... Wallahi Ko yanzu Ya mahmud ka nuna kai jarimi ne ka dauko matar da babu
irinta a dukkan Family ai gara da akayi yunwa halin kowa ya fito".
Ta fada tana tsallen murna kamar Karamar yarinya.
A haka su Abbie suka shigo Amma ba Ya Ibrahim ya wuce parta dinsa da yake a Cikin estate
din suke shida saura yayunsa.
"Ke Kuma wane irin sakarci ne wannan da tshon dare kike yiwa mutane ihu haka?".
Jikin Ammi ta fada tana fadin.
"Wayyo Dadi Ammi Wai ashe Aunty Zahra matar ya Mahmud ce,".
Shi dai Abbie gurin mahmud ya nufa ya zauna kusa dashi ya Dan taba gefen wuyansa.
"Sannu me yake damunka yanzu?".
"Ba komai kawai kaina ne yake ciwon kadan".
"Ok.ai na yiwa doctor Hashim waya yace gashi Nan zuwa".
Jin abinda Abbie ya fada yasa Aunty Aishar da Batool suka nufi parlourn da Zahra ke zaune
Basu tarar da ita a gurin ba sama suka nufa Batool nata kakabin abin tana faman magiyar
Auntyn ta fada Mata ita ce ta hada Ya mahmud da Aunty Zahrar? Amsar Daya ce dai take fada
Mata yanda ta ganta itama haka ta ganta. Knocking biyu sukayi Zahra tace su shigo a kan sofa suka sameta ta Zuba tagumi tana aikin
tunani Afnan ta karba daga kafadar Auntyn wadda tayi barci kwantar da ita Zahra tayi.
"Kuma saiki gudo Baku gaisa da Abbie ba".
Sadda Kai tayi dan ji tayi Auntyn ma kunyar hada Ido takeyi da ita.
"Zamu gaisa ne ai yanzu bazan iya zuwa ba wallahi kunya nakeji, ji nake kamar nayi tsuntsuwa
na gudu".
"Kaji Aunty meye abun kunyar a ciki keda ba rungumarsa kiyayi ba "Dan kin nuna damuwa a
Kan halin da yake ciki ai Kara kankarowa kanki mutunci kikayi su iyayensa, ai Dadi sukaji ko
Basu fada ba irin wannan rudewa da antayo soyyaya a gabansu sun San idan aka shiga other
room Kuma sai yanda Hali yayi kenan,gaskiya a gurinki zanyi degree harda masters ma akan
soyyaya Naga alamar kina Dora Ya mahmud a network".
Riqe Baki Aunty Aishat tayi tana kallon Batool.
"Yaushe Kika lalace haka? Wallahi Zan sami Ammi ayi gaggawar saka Miki Rana kece Mai
fadar irin wannan maganganun a gaban idanuna gara a yiwa tubkar hanci kinyi service din a
gidan mijinki".
"Kai Aunty Mena fada Ina ce kece ya kamata ki zaunar dani kiyi min Karatun yanda Zan Kama
mijin nawa, Amma bakiyi ba sai kuma Kice Zaki hadani da Ammi Wai ayi bikin ko service banyi
ba salon laulayin ciki ya hanani yinsa cikin dadin rai".
"Allah ya shiryeki wannan yarinyar da Baki samu miji ba wallahi cewa zanyi Ammi ta fadawa
Abbie ya badaki sadaka Naga alamar idan Kika Kara watanni za'a iya samun matsala gaskiya".
Dr Hashim Bai Bata lokaci ba yazo bedroom din dake kasa wanda mahmud din ya mayar
dakinsa suka shiga Dr ya duba shi, ya auna B.p normal yace ya rage saka damuwa a zuciyarsa
saboda kada ta shafi lafiyarsa a irin wannan shekarun, tea yasa Ammi ta hado Masa ya Sha
yayi Masa Allura ya bashi magunguna Yasha sannan ya tafi. Ba'afi minti biyar dayi Masa allurar ba ya Fara hamma zuwa minti goma yayi barci.
Karfin A/C Abbie ya rage masa sannan suka fice daga dakin.
Suna fitowa Ammi taja ta tsaya tana duban General.
"Kaga abinda naketa fada maka ko? Game da mafarkin wannan yarinyar wallahi itace zahiri ake
nuna mini a Cikin mafarkina suna tare dashi".
Hannunta ya kamo suka zauna.
"Ki kwantar da hankalinki lallai Allah ya nuna Miki wani sirrine da yaso ki fara gani kafin zahiri
yazo Miki, tun ranar talata Mustapha ya turo min hirarsa da malamin Daya ya rike Miki yaro
lokacin da baya Cikin hayyacinsa da yanda Sukayi ta fadi tashi akan nemar Masa magani da
yanda ya fada anyi Masa asirin barin garin na har abada da yanda akayi auka bashi wannan
yarinyar yanzu haka dai in takaice Miki labari matatmrsa ce ta sunnan wadda marikinta yayi
Mata AUREN HUCE HAUSHI, saboda itama anata samun matsaloli ne a dukkan lokacin da
auernta ya tashi, shine markinta Kuma Aminin malamin ya yaba da hankalinsa ya bashi aurenta
ba tare da la'akari da irin matsayinsa na bako kuma Almajiri ya bashi ita, babu irin surutun da
ba'ayi Masa ba ya toshe kunnensa ana ta fadar Dan ba 'yarsa bace ya Bata marar gata. To shi
malamin ne ya gamu da jarabawar matsalar Spinal cord injury shi mahmud din ya fita dashi
India lokacin dashi malamin yake kokarin dawo dashi gida sai kuma ya gamu da wannan lalurar
yace a bamu hakuri sunyi kuskuren yi Masa Aure Amma mu dauka haka kaddarar take a
rubuce gurin Ubangiji shiya kawo aka samu matsalar da tasa mahmud ya tsallake yabar gida
har hakan ta faru da ba'a samu wannan matsalar ba da ta Ina zeje Azare ya zauna har a bashi
auren yarinyar? Kinga Koda matarsa ce sai dai su hadu ta wata fuskar badai wannan ba tunda
Allah ya hukunta matarsa ce".
Jinjina Kai kawai Ammi keyi Tana Kara girmamawa girman Allah s.w.a idan yayi wani abun sai
dai bawa ya kalla da Ido kawai.
"Na fashimta bazan ja da hukuncin Allah ba, duk yanda yayi da bawa shine daidai naji Dadi da
Allah yasa Dan uwanka yazo da maganar nan bashi Hussein ya fada ba da kuma abinda ita
yarinyar tayi yanzu a gaban Dan uwansa Dan haka saika tarasu kasa Mustaphan ya kunna
musu suji da kunnensu bazan dauki abinda na dauka a baya ba, Kuma sabon biki za'ayi kamar
yanda ake yiwa kowa a gidan Nan maganin tsegumi Dan haka da safe Zan Kira Ya I Ishaq ya
bani aron Aunty Badi'a zata rakata har Azare ta yiwa mamanta bayanin sabon biki za'ayi kosu
can Basu sake ba su hada jama'arsu za'a zo a dauketa kamar ko wace Amarya da dangin
mijinta suke zuwa su daukota, zatafi kima da daraja a Cikin family fiye da a wayi gari ace wai
yazo da Mata ai wani ma abin magana ze Zama ko Yaya kake gani? kasan tunanin mace da
namji ba Daya bane".
"A maganarki babu gyara hakan yayi Amma idan har hakan za'ayi no need a ce sai kowa ya
San gaskiyar maganar kawai Mustaphan yace an daura aure ne yanzu bikin za'ayi kawai
Daman suna Shirin dawo dashi gida ubangidan nasa ya samu matsala Yana asibiti a India inda
aka kawo labarin ganin mahmud din Ashe jiyya sukeyi a can". "Hakan yayi Allah ya Kara sutura"
"Allahumma Amin" Abbie ya fada, muje ki bani wani Abu marar nauyi naci tunda Naga Alamar
murna ta hanamu yin dinner a gidan nan, ki kawo min can part dina".
"Kaiiii Yallabai ayi min afuwa yau Daya dai Ina da bakuwa ai nayi entertaining dinta".
"Babu wannan kizo Ina jiranki ki bar musu Nan din kinsan dai zasu iya abinda zesa ki kusa
nutsewa a kasa Dan kunya kuma ma ke Ina ruwanki dasu ba tare Kika gansu ba kinsa auren
nasu ya dauki watannin da yinsa?".
Dan murmushi Ammin tayi.
"Ni fa Banga alamar yarinyar nan an mayar da ita mace ba gaskiya budurwa ce".
"Kamar yaya, yarinya da mijinta ki ringa fadar haka?"
Shiru tayi masa ita dai taga abinda ta gani tun ganinta da tayi dazu kafin ta sauki daga steps ta
kiduri duba abinda Hajjo ta fada Mata da yake nuna yarinya budurwa ce ko tana ma'amala da
maza, da niyya taje da niyyar daukar Afnan Saida ta gani sannan taji ta Samu nutsuwa.
Lokacin da Ammi ta haura saman shiru da alamar sun kwanta,Saida ta Gama duk abinda zatayi
ta rufo kofarta kamar zata shiga gurin zahrar saita juya ta nufi downstairs kawai tasan idan ta
shiga kinya zata Bata gara ta Bari abun ya Dan bi jiki tunnna, downstairs ta nufa tana ayyana
sai ta Dan yamutsa musu lissafi ko Yaya ya ne Dan su Kara sanin darajarta itafa tana kishin
mace ganin an bashi yarinyar Nan a sama saiy
Zahra ta Dade tana tunanin makomar aurenta baran barama dai tariga tayi sai Kuma yanda ta
yuwu Wai Dan daudu a lahira.
"Koyaya jikin nasa?"
Ta fada a zuciyarta, ta Jima tana sakawa da kwancewa, gashi duk yanda taso ta Kira Aunty
Hasana abun ya faskara haka Ammah duk network yaki bada hadin kai. Sai wurin Daya saura
tayi barci, can a Cikin barcinta taji Kamar ana tabata, kwanciyarta ta gyara ba tare data bude
Ido ba sai tajita a jikin mutum da wata irin zabura ta yunkura zata Mike taji an mayar da ita Baki
ta bude zata zabga ihu taji carab ya hade bakinsu sai lokaci taji kanshin turarensa a hancinta,
wata ajiyar zuciya ta sauke, tayi lif a jikinsa da gaske sunyi missing din juna Saida yayi Mai
isarsa sannan ya dan saurara Mata ya yanye bakinsa suna maida numfashi.
"Previous kin azabtar Dani whyyy... Me nayi Miki Kika haramta min ganinki kwata-kwata? Fada
min kinsan halin Dana shiga kuwa? Kikasa na kasa controlling kaina a gaban elder brother dina
kin kyauta min kenan?".
Ita dai mukus tayi to me zata fada masa tace labewa tayi taji shirarsu da Aunty Aishat ko tace
Masa me shirun shi yafi Alkhairi. Juyin duniyar Nan taki magana dole ya kyaleta ya koma wata
shirar da ban.
"Wai dazu da rungumeni zakiyi a gaban su Ammi?".
Saka kanta tayi a kirjinsa Cikin kunya tana gigiza Masa Kai.
"Kin dauka Zan tafi na barkine ko? To muna Nan sai kin haifo Mana fine babies masu Kama
dake".
Ya fada Yana Kai hannu akan cikinta Yana Dan shafawa.
"Ka Bari Dan Allah Ammi fa tana Nan ka tashi ka tafi Dan Allah kada wani ya ganka ka shigo
yayi zaton wani Abu fa".
"Kwantar da hankalinki ai kin Gama Mana aikin Dana kasa yinsa a Cikin kankanin lokaci meya
rage kuma? sai mu tattara mu tafi inda mukafi wayo Nima nasan nayi aure na huta da ragaita
mu fuskanci rayuwa kuma, badan nayi alkawarin kawowa Ammi ke a yarinyarki ba Aida yanzu
muna Shirin tarbar babyn mu ko ba haka ba?"
Wannan furucin nasa shi ya ankarar da ita akwai fa sauran Rina a kaba, Nan da Nan wani tsoro
ya kamata Nan ne fa karshen maganar, a Nan ne me afkuwa fa zata afku,tunda gata a sokoto
har dakin mahaifiyarsa saura da me ya rage kuma?.
Cikin shagwaba ta Fara fadar "Ni dai ka daina wannan maganar gaskiya wallahi ni Ina Nan
kusa da Ammina ai ba muyi haka da kaiba nifa tsoro nakejiiii..."
Wani special smile ya sakar Mata duk da dakin dimmer light ce Bata hanata ganin yanda dimple
dinsa ya lotsa ba.
"Wani abu nace zanyi Miki ne da zaki Fara tsorona? Ki zana feel free Dani har abada babu
cutarwa a tsakanin mu, kin manta Abba da Baba Malam Amanarki suka bani?".
Kai gyada Masa alamar eh.
Cikin jikinsa ya sakata Yana fadar muyi barci da sauran lokaci duka yanzu one thirty five am".
Kafada ta make tana kallonsa ta gefen ido ita fa da abinda yake figitata gaskiya.
"Dan Allah ka tafi kada kaja mini Ammi fa tana Nan kada ta ganka nidai babu ruwana wallahi".
"Nace Miki ki kwantar da hankalinki Amma Bata Nan fa tana gurin mijinta itama to Kinga Kota
ganni ai ba wata damuwa ko?".
Ita dai barci rabi da rabi tayi a kunnenta aka Kira sallar farko data biyu tana jinsa ta tashi ya
shiga toilet ya fito ya zura jallabiya Daya zo da ita Cikin ledarta ya Dan shafi gefen fuskarta
wadda tayi fayau a Cikin Dan hasken dake dakin.
"Tashi lokacin sallah yayi, Zan wuce masallacin daga can zanje gurin Hajiya inna, jiya Baki
ganta ba ko lokacin kin gudo tazo gidan Nan Wai zata tasani a gaba mu tafi Wai na daina
zaman nan. Kin amince nayi nesa dake?".
Jin za'a tada sallah yasa yayi sauri ya fice daga dakin, Karan rufe kofa yasa Ammi dawowa ta
bude kofarta wadda shigarta dakin kenan Dan yallabai na tafiya masallaci ta nufo part dinta,
bayansa kawai ta iya gani saboda saurin da yakeyi na kada ya rasa raka'ar farko, jinjina Kai tayi
tana fadar.
"Dole ayi yanda za'ayi ku tattara ku Kama gabanku badani za'ayi wannan dibar Albarkar ba,
wato abinda general ke nufi kenan Daya tilastani zuwa gurinsa"
Sallah ta tayar ta zauna zaman azkar da lazimi Ala ala take shida da rabi tayi ta Mira Niger,
Saida ya dai daici lokacin dawowa daga masallacin yayan nata sannan ta Kira shi.
Yana ganin Kiran yasan ba lafiya ba Dan Yana dagawa ya Bai saurari gaisuwar da take masa
ba ya Fara fadin.
"Zainab lafiya? Meya faru kuma?".
"Wallahi ba komai Yaya sai Alkhairi".
"To Alhamdulillahi, lfy kalau ya yaran da Mai gida"
"Kowa lafiya, daman Mira nayi na fada maka danka ya dawo harda tsarabar Mata aka Mata
aka bashi tana nan sunzo ita da 'yar uwarsa can ya Kai Mata ita"
Sai kuma ta dauko masa Asalin dalilin kiran nasa shima supporting dinta yayi harma ya Kara da
fadin dole a hada da babbar mace su tafi tare kamar zefi girma da daraja a gurin Iyayen nata,
sunyi sallama akan idan an samu tickets dinsu damagaram to sokoton zasuyi waya wata irin
nutswa taji ta saukar mata, gara ayi a wuce gurin. Da gari ya Fara haske zahra ta tashi daga Kan sallayar da tayi sallah ta ninke ta kintsa gurin
wanna tayi ta shirya Cikin rigar material Mai budedden dinki San rigar Bata Kama Mata jiki ba
tayi rolling da gyalen material din Nan da Nan ta gyara dakin ta fesa roomfreshner ta fito Cikin
so take ta gaishe da Ammi Amma Bata San takamaimai Ina ne dakinta ba sannan kuma
Batasan da wane Ido zata dubeta ba, tana kokarin juyawa ta koma kenan kofar dakin Ammi ta
bude ta fito Shar da ita tana baza kanshinta da mamaki a fuskaerta ta fito tana fadin.
"Masha Allah, harkin tashi kenan?"
Ta tambayi Zahra.
Da sauri Zahra ta tsuguna tana fadin.
"Ina kwana Ammy".
"Lafiya kalau ya bakunta?".
"Lfy kalau".
Ta fada tana Wasa da gefen gyalen da tayi rolling, ta kasa hada Ido da Ammi din.
Ciki Ammi ta koma tana fadin
"Shigo nan magana zamuyi dake"
Zahra ji tayi gabanta ta yanke ya fad'i, jiki ba kwari tabi bayan Ammi ta shiga gefen gado Ammin
ta nuna Mata ta zauna amma ta Kiya ta zauna a Kan carpet din dake gaban gadon tana jiran taji
abinda za'a fada Mata.
Zama Ammin tayi tana karewa zahra kallo yarinyar tana wani irin kyau Mai daukar hankali.
"Kina jina Fateemah number mamanki Zaki bani ina son nayi magana da ita".
"To Ammy gata"
Ta Fara karanto Mata harta cika.
"Tashi kije zuwa anjima Ina Jim zakuje unguwan insha Allah Amma Bari nazo muje ku gaisa da
Abbie dinku".
Ammi na gaba zahra na binta a baya suka nufi katafaren part din Abbie compound din ba kowa
silent da alamar gidan bashi da yawan hayani kowa Yana gurinsa a kame sai munafurci fall a
cikinsa a parlour suka sameshi tunda suka shigo zahra ta sadda Kai kasa har kusa da inda
yake zaune zahra ta karasa ta tsuguna har kasa ta gaishe shi, Cikin muryarta Mai nutsuwa,
albarka dai zahra Tasha ta gurin Abbie da godiyar abinda iyayenta suka yiwa gudan jininsa,
cewa yayi ta zauna sosai ta zauna ya ringa yi Mata tambayoyin tun tana dari dari dashi harta
dan sake dashi, lokacin da zasu dollars din America ya Bata raffer biyu ya Bata a Leda.
Ammi ta karbar Mata Tama godiya.
Har suka dawo Basu hadu da kowa ba ba Karamin Dadi Ammi taking da faruwar hakan ba,
suna shiga suka samu masu aikin girki da share -share.
Zahra Bata koma sama ba gurin Aunty Aishat ta wuce yayinda Ammi ta nufi kitchen.
Auntyn kawai ta Sami ta tashi yaran duk Basu tashi ba, waya takeyi saida taji tace gata Nan ma
Bari na Bata, wayar ta mikawa Zahra tana fadin
"Bari nayi wanka tunda Allah ya kawo min ke bana son na shiga wanka ba kowa a Musa dasu*
Wayar ta Kara a kunne tana sallama, amsawa yayi Yana fadin.
"Pls My preccious Kina jina, dan Allah anjima da yamma ki biyo Sister Aishat kuzo tare ki gaishe
da Hajiya inna Kuma na cika wani alkawarin Dana dauka tun ranar Dana bar gida nayi shi to
shine nakeson cika shi ai asan zaki tayani mu cika alkawarina ko?".
Ya fada da sigar rarrashi.
[25/02, 7:40 pm] Abu Saleh: I *AUREN HUCE HAUSHI*
09061432330
Or
08055362975
AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fateemah
Page 77
.............karfe bakwai dai dai mahmud ya baro gidan Hajiya Inna, bayan yayi wanka,dole tasa
yazo gidan tunda a gidan Ammi baya da kayan sakawa ya duba baiga komai ba be sani ba ko
canza musu guri akayi ko bayarwa tayi abinda be bi ba'asi ba kenan yaga gara ya taho Nan ya
shirya kawai, shigar kananun Kaya yayi ya fito Shar dashi, Bai koma gurin Hajiya Inna ba duk
da albishir din da tayi Masa na sinasir da tasa ayi Masa da pepper soup din kafafuwan shanu.
Yaso ya shiga gurin Abbie Amma gurin Amminsa zaya har yanzu bakinsu Bai