Showing 9001 words to 12000 words out of 65935 words
Chapter 4 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf
Alhaji Ishaq ne ya bashi jarin Daya Fara sana'a dasu tun Yana hannun Hajja, Amma
yanzu zaki hada arzikinsu ko kusa ko alama Babu Hadi,.koni Dana haifeshi ya mallaki abinda
bani da kwatqnkwacinsa, Keda Kika haifeshi kin mallaki abinda yake dashi? To kiyi istigifari ga
Allah tunda shine yace Yana azurta Wanda yaso ba tare da hisabi ba,ai kin gane?".
"Na gane Allah ya Zama gatansa a duk inda yake,Amma fa yarinyar Nan ta tsaya min a rai idan
Yana kusa da wannan ai zai manta da kowa ne tunda cikin bacin rai yabar gida ga Kuma kudi a
tare dashi kaga sai Allah kadai ze kare shi".
Dariya ta bashi sai da yayi sosai kafin yace.
*In Sha Allah in dai Zina gado ce to Alfarmar Manzon Allah s.a.w.w zuri'ar mu bazasuyi ba Ni ba
mazunaci bane haka kema ba ita bace in Sha Allah.Allah baze jarabcemu da ita ba, Kika sani
ko bushara ake Miki ke uwa kin samu sirika".
"Haba dai har abun ya Kai haka yayi aure ba sanin iyayensa ai kuwa da lamarin ya lalace".
'yar dariya yayi.
"Kedai kije ki shirya min breakfast daurin Aure zamuje kabba na Dan gidan sanata Abdul Aziz"
"Ok.bari na shiga kitchen din"
Ta tashi ta fice tana baza kamshinta as usual.
******
Tun idar da sallar Rukayya ta taso ta nufo part din da zahra ta kwana,abin mamaki an canza
pin kofar dan ta kwada yafi sau goma Amma taki budewa. Nan da Nan taji hankalin ta ya tashi
me Kenan badai wani bane ya shigewa 'yar mutane ba gashi jiya Taki Kai Mata wayarta da ba
saita kirata ba, gudun kada tace sai sun kwana ya hata ta Kai mata. Number ya Sameer ta lalubo lokacin Yana barci,
Yana dauka ko gaishe shi bata tsaya yi ba ta Fara fadin "Ya Sameer ka taimakeni wallahi tun
sassafe bake kokarin shiga part din da zahra take Amma kofar kofar kamar an canza pin din na
saka yafi sau goma Amma yaki budewa".
Tsaki yayi "Waike Dan Allah Ruky yaushe Zaki girma ne? to oga ne ya shigo cikin dare Nima da
asuba naga text message dinsa Dan haka ki Zama ready idan na shigo saimu wuce tare Amma
yanzu kada kuyi komai za'a kawo abinci".
"To ai su Iya Rahane har sun kusa gamawa baka fada min ba tun dazu".
Ok, ba komai sai a hada tunda gidan da jama'a, yauwa zuwa an Jima ki bude musu part din
Nan na kusa da parking lot sai su zauna a nan tunda shima ogan Bai san ze shigo kanon ba
harsu Gama su koma to matsalar madam din ce inaga ta caza Masa Kai Wai cewa fa yayi daina
amsa Masa waya tayi". "Kamar ya Bata amsa masa waya? Batasan kowaye bane da zata ringa yi masa haka?"
"Eh kusan hakan ne gaskiya"
"Allah ya rufa asiri" ta fada.
Sukayi sallama ta kashe Kiran tana dariya "su oga anzo hannu ana walagigi da rayuwar 'yan
Mata gashi kaima kazo hannun yarinya tana juyaka son ranta, nasan bana raba Daya biyu
saboda shi ta rufe wayarta jiya, taki magana dashi a wayar Ya Sameer karshe ma ta sakata jirgi,
yes! Haka nake son irin matansu su kasance, idan suka samu wadda ta mace a kansu ta Zama
sorry Amma wannan ta shuka mulkinta yanda takeso tunda Batasan waye shi ba".
Ya juya ta koma kitchen inda tabar su zilai suna aiki, tana shiga zilan tace Wai ni lafiya yarinyar
Nan? naji shirun yayi yawa ko dai rakani zakiyi na gano lafiyarta kada na Zama babbar kwabo
an hadoni da yarinya nayi wasarere da lamarinta".
'yar dariya. Rukayya tayi "gaskiya kinaji da matar big bro irin wannan shiga damuwa jiya fa ko
barcin kirki bakiyi ba kina zaman jiranmu yau ma tun Asuba kike ta nemanta, ki kwantar da
hankalin ki Aunty sirikinki ne ya taho ba Shirin wannan 'yar taki tsaye ce taki saurarensa ko a
waya dole ya tsallake hidimominsa ya nufo Nigeria". Iya Rahane ce ta aje Wukar hannunta tana duban Rukayya "kikace uban gidan mu ya shigo
garin?"
"Kwarai kuwa iya jiya cikin dare ya shigo Kinga kuwa sai ki fadawa Aunty ta kauda Kai kawai
gurin son ganin 'yarta ba yanzu ba gaskiya, Dan haka da an gama aikin Nan zamu bar Nan
Bangaren mu koma wancan".
"Wannan gaskiya ne inba tayi dalili ba yaushe zamu shigo wannan guri harda kwana a cikinsa,
Amma dalilin uwar dakinmu mun dangwali arziki ai wannan ba komai bane akan gidan da aka
sauke mu a sokoto, Kai Naga inda arziki ya amsa sunansa wannan yaro uwarsa tayi farar
haihuwa wallahi Nan kusa Banga mutane masu karamcin su ba, uwarsa yarinya karama sai
halin girma".
Ita dai zilai sai ta rasa Wai wannan maganar dawa ake ne waye suke zance a kansa ne ita fa
maganar Zahra take musu su Kuma sun kamo wata tashar Ina hadin zahra ba Wanda suke
magana a kansa ko dai Mai gidan ne ya dawo Basu gane me take nufi ba, ita Zahra matar
Almajirin Malam Bukar Wanda gidan zaman ma na Baba Malam ne mutanen da yaje yiwa aiki
turawa suka gyara Masa shi, to Ina shi Ina wannan Aljqnnar duniyar suda aka kawosu zaman
'yan kwanaki na ganin likita.
Cikin nuna mamaki zilan tace "ikon Allah ai ban sani ba kice da anyi uwar banza gara da Kika
fada min kada naje nakai kaina girma ta Fadi".
"Ai Koda kin shiga basa Nan ba a nan suka kwana ba".
Wayar Rukayya ce tayi qara ta dauka ta fice daga kitchen din shine abinda ya Hana zilai fadar
abinda tayi niyyar tambayarki Rukayyar.
Hira iya rahane taci gaba da yiwa zilai a Kan Mahmud amma ko Daya zilan Bata gano ainishin
waye take magana a kansa ba.
.[2/1, 6:08 PM] ASHMAR: ✨✨
AUREN HUCE HAUSHI.
✨✨
MAMAN FATEEMAH.
Page 45.
________Sai kusa karfe Sha Daya da rabi Mahmud ya farka shima yunwa ce ta tashe shi,
ido ya tsura Mata barcinta take hankali kwance tayi pillow da gefen kafadarsa, hannu yasa ya
shafi gefen fuskarta da gashi ya kwanta lambam, hancinta ya dan ja kadan, dan yamutsa fuska
tayi tana bude idanunta a hankali, Ido cikin ido sukayi dashi da sauri ta Maida nata ta rufe. "Ki tashi muyi wanka ki bani abinci Naga alama ke barci baya isarki".
Zare jikinta tayi still dai idanun a rufe, tana Jan bargon zuwa kirjinta.
"Kaje ka Fara Yi sai nayi nima".
Ta fada tana juya Masa baya, Dan murmushi yayi ya Dan rankwafa dai dai fuskarta.
"Ok, ba damuwa jeki hada min ruwan saina Farayi kafin na fito, saiki hada min abinda zanci".
Yunkurawa tayi ta tashi zaune, tana mutsumutsun yanda zata tashi haka a gabansa.
"Ka Miko min Riga na saka saina shiga na hada maka".
Ba musu ya dauko Mata Rigar ta Karba ta saka ta Mike ta nufi toilet din.
Saida ya tabbatar da ta shagala gurin abinda takeyi ya tashi ya nufi toilet din, tana zuba
turaren wanka cikin ruwan data hada ya shigo ciki ba zato ba tsammani sai ganin mutum tayi
ya shigo daga shi sai boxer a jikinsa, gurin da take tsaye ya nufo, da sauri ta matsa gefe kanta
a kasa Bata yarda sun sake hada Ido ba tace Masa. "An Gama hadawa".
Tana aje robar dake hannunta ta juya da zummar barin gurin. Taku biyu tayi taji anyi sama da
ita cak sai cikin ruwan daga ita har kayan jikinta, wata ajiyar zuciya ta sauke tana fadin "Dan
Allah ka Bari wallahi nayi wanka fa".
"I know, tayani zakiyi Dan rashin kirki ai ni bakonki ne ya kamata ki tarairayeni har wankan
ma kiyi min tunda kin hanani sukuni Saida Kika gargadoni na dawo gurinki Kinga kuwa ai duk
lokacinki yanzu nawa ne".
Har ta bude Baki zatayi magana ya Dora Dan yatsansa a Kan lips dinta "kin manta ba'a
magana a cikinki toilet? Muyi wankan later munyi maganar".
Janyota yayi jikinsa ya Fara cire Mata jikakkun kayan jikinta, a tsorace da Kuma wata
azababbiyar kunyarsa da takeji ta Kara ninkuwa, dan wani Abu ne da be taba faruwa da ita ba
a tarihin rayuwarta irin wannan kebewar da namiji baligi da uwar tana irin wannan Bata taba
yiba shi yasa Daya hade jikinsu ta shiga tsuma kamar wadda Zazzabi ya rufe, wankan sukayi
tare duk da shi dai kadai yake sha'aninsa Dan ita dai kam sai hankali.
Saida ya Gama son ransa sannan ya karasa wankan ya fito ya barta a ciki,Saida ta kimtsa
kanta sannan ta fito, lokacin har ya shirya cikin wasu kananan Kaya Yana daura agogo, tsaye
tayi a kofar toilet din ita Bata koma ba ita Bata karaso inda yake ba, kallon kasa kasa take masa
gani tayi gaba Daya ya canza Mata kamar anyi musanyarsa da wani ya Kara zaman wani
handsome dashi jikinsa ya Kara Zama fresh dashi.
Inda take tsayen ya nufa "pls ki shirya Ina son fita ne wurin after zuhur".
Kofa ya nufa ita Kuma ta nufi gurin mirror tana goge jikinta, hand dryer data gani a gefen mirror
ta dauka ta jona ta busar da kanta, cikin kankanin lokaci ta shirya gurin kayan ta nufa tsaye tayi
tana kallonsu. To Wai ita Nan din Ina ne gidan waye taga ya shigo ya barrarraje Yana tsula
sha'aninsa ga kayan Mata birjik Kuma ance mamallakinsa ko aure beyi ba to Ina ba"asin kayan
nan na can part din Aunty Rukayya tace nata ne to wannan fa na waye su kuma? Qundunbala
tayi ta dauko wasu English wears, ta saka masu kalar brown dark sai veil milk colour tayi rolling
ta fesa turarenta dake cikin handbag dinta sai lokacin taga maganin da Hajiyar makwarari ta
bata, Dan murmushi tayi a zuciyarta ta ayyana "zanzo na Baki hakuri Hajiya nasan ban kyauta
Miki ba dole ce tasa na aikata hakan".
Dakin ta Fara gyarawa ta cire bedsheet din ta duba gurin da take tunanin zata iya ganinsu ta
duba.
Very luckily ta gansu ta Ciro Daya ta baza zata Fara shimfidawa ke Nan ya shigo dakin Yana
waya, da hannu ya nuna Mata ta taso, ba musu ta taso ya nufo inda yake hannunta ya kama ya
nufi kofa wani Abu kawai ya taba daga can kasa kofar ta bude, da kallo ta bishi tana mamakinsa
gaba Daya ya canza Mata Kuma yanda yake mu'amala da gidan Yana Bata mamaki, har suka
fito parlour na biyu Yana ta wayarsa wadda ta fuskanci kamar suna maganar kasuwanci ne
sabo da aka Riga aka fara, direct dining ya nufa da ita Saida ya zaunar da ita sannan ya zauna.
Wani Dan guri ya danna jikin table din, ba'a Jima ba saiga wani saurayi ya shigo ta wata kofa.
Baiyi magana ba tun bayan sallamar da yayi Zahra ta amsa masa, wayar ya kashe ya juyo Yana
duban Wanda ya shigo din.
" Safwan Kada naji labarin Ina garin nan a bakin kowa, kaje inda na turaka jiya?"
"Naje oga komai ya Zama normal, harma sun Fara aiki saidai Zayyan yace wannan Matar tana
yawan zuwa kusa da gidan amma dai Bata karasowa take komawa".
"Ok ba damuwa kaje kawai idan ka dawo ka taho da fresh milk da fruits a saka a kitchen din
nan".
"Ok sir, na gode ya juya ya nufi inda ya fito har ya danyi nisa yaji maganar Mahmud.
"Safwan banji ka gaishe da madam ba, bahaushiya ce ba wani yaren zatayi makaba, Naga
alama saina miqaka makarantar koyon turanci tunda Naga shi kadai ne kake da matsalarsa".
Dan Sosa Kai yayi yana dawowa baya.
"Afuwan Auntyn mu wallahi na dauka bakijin yaren mu, Ina kwana?"
"Lafiya kalau ya aiki?".
"Alhamdulillahi Auntyn mu, Allah ya Kara sutura ya bar Mana ke a gidan oga Dan isar Annabin
Rahama".
"Amin ya Hayyu Ya Qayyum".
Muhmud ya fada.
Hanya ya nuna Masa alamar ya wuce bai Kara tofa wata maganar ba ya juya yabar gurin.
Ita Zahra kallon ikon Allah takeyi wallahi wannan ba Wanda suka zauna a Azare bane da
banbanci nesa ba kusa ba.
Iskar Bakinsa ya hura Mata a fuska saitin idanunta, "kallon na menene Kona canza Miki ne?
Kika tsareni da wadannan eyes din naki masu hanani sakat idan Ina kallonsu Dan Allah ki barni
naci abinci kome kike bukata saina Baki badai kin hanani zaman can ba, to aini gaba ta Kaini
gobarar Titi a jos, haka ake fada ko?" Ya tambaya Yana bude abincin. Dan kwabe fuska tayi tana Dan turza kafa a kasa.
"Ni wallahi bani nace ka dawo ba kawai Kaine kayi niyya da kanka ka dawo Ni ba ruwana to na
kiraki nayi maka me?".
"Au haka Zaki ce shike Nan yanzu dai bani abinci daga baya sai kiyi min bayanin yanda aka
haihu a ragaya".
Bata gane hausar tasa ba tayi Shiru dai kawai.
Abinci ne kusan kala biyar Banda pepper soup na turkey.
Kasa hakuri zahra yayi Wai daga Ina wannan abincin irin haka?"
"Daga jama'ar Annabi, kinsan mu 'ya'yan malamai ko Ina muka sauka gida ne".
Shiru tayi ta zuba Masa abincin zata Zuba nata ya dauke plate din.
"Kin manta ai ba raba Abinci a tsakaninmu muci kawai".
Tare sukaci abincin suka Gama, tana Dan kallonsa lokaci-lokaci, da gaske yazo Mata da
abubuwan mamaki da yawa Amma azarbabi ba nata bane. Dole tabi kamai a hankali saida ya
tabbatar ta koshi sannan ya saurara mata, Nan cikin parlourn suka dawo suka zauna ya dorata
a cinyarsa yasa hannunsa ya zagayo cikinta yana ta faman amsa wayayoyi, sai ya amsa way kamar uku, sannan ya aje ya fuskance ta. Wasu irin
wayoyine guda uku Wanda ita dai sai a T.V take ganinsu amma sai gasu a hannunsa kuma ya
wani ci magani Dan kada ta Tama Fara masa wasu tambayoyi.
'
"Bani labari ya akayi ciwo Bai tashi kamaki ba Saida nayi Nissan Zango, naji doctor tace Wai
rashin samun biyan bukata ne yake kawo miki yawan ciwon marar saboda sha'awarki tana
motsawa Baki samun biyan bukata".
Waro Idanu tayi Baki bude tana Masa wani kallo.."Ni kuma? Wane irin magana ce wannan
bayan fibroid din Kuma harda bita da kullin sharri? ta Nan Kuma ta bullo? To ai sai tazo ta ta
cire min sha'awar tunda ita ta ganta, kawai ta Fadi gaskiya tanaso tayi amfani da aikinta ta
cuceni,tunda da hadin bakinka Ashe ni aka mayar sakarya aka tasoni tunda daga kauyen mu
aka kawoni gurin budurwaka ta dubani,ta ganeni ciki da bai kaga ko idan ta aureka bani da wata
fuffuka da zanyi Mata, wata Kila da Allah baisa ta fito da maitarta fili ba da Allah kadai yasan
illar da zatayi min.Da Jin saita cire min mahaifa gaba daya, ka fada Mata wallahi da gatana Ina
da gatan da wallahi ta cutar da lafiyata Saida ta kare rayuwarta a life in prison, kuma indai
Kaine nabar Mata taje ta hadiyeka kada wata ta Kara ganinka tace tana so, an fada Mata Ni Ina
da damuwa ne da zata ringa wulakantani in dai saina Kara zuwa ta dubani ciwon yayi min
abinda Zeyi min Kuma yau in Sha Allah gida Zan koma bazan iya Zama a Nan ba Ni duk kanon
ma ta fice min daga Rai, ka mayar Dani inda nafi wayo".
Ta karasa fada tana juyar da fuskar ta gefe.
Kwanto da kansa yayi gefen wuyanta. "Cewa fa nayi ki bani labari ba cewa nayi meye
damuwar ki ba, Ni meye laifina daga na turoki a duba min lafiyarki".
Ai fadar hakan saiya tunzurata nan da nan sai hawaye.
"Oh! My God!, Mena fada Kuma? pls tell me".
"Kwace Kanta ta shiga yi tana fadin.
Daman nasan ba Sona kakeyi ba tunda Ni matar shige ce Bata da daraja kuma wallahi duk
Wanda ya Zama sanadin da wannan gararin rayuwar ya sameni ban yafe Masa ba, da qimata
da mutuncina an mayar Dani wata shakatafi kowa saiya takani yanda yaso bani da wata qima".
Ta sunkuyar da kanta tana wani kuka Mai cin zuciya.
Iya dagula lissafi tayi Masa Dan kasa cewa komai yayi sai sakata da yayi a jikinsa ya kwantar
da ita shi kadai yasan abinda yakeji, suna haka yaji wayar Daya Bari a kunne wadda yake
amfanin yau da gobe ta dauki kida Mai Dadi.
A hankali ya Kai duba gurin wayar, Sameer ne.
Dauka yayi baice komai ba "Ina kofar part din Nan kana da bakuwa".
"Dude ka shigo sai muyi maganar".
Ya kashe ya aje wayar, Jin ya ambaci Sameer ya shigo yasa zahra yayi kokarin zare jikinta
amma Dan bawan Allah nan kememe yaki sakinta saiya gyara Mata Zama kawai.
Dago Kai tayi da niyyar yi Masa magiyar ta saketa ta tashi dai dai lokacin Sameer ya karaso
gurin, be taba tunanin tana jikinsa ba tunda shi kadai ake hangowa Saida ya kure musu yanda
ba yanda za'ayi ya koma, tsaye yayi shi Bai Kona ba shi Kuma be karasa gurinsu ba ita kuma
Zahra kunya kamar ta nutse wallahi Bata taba tunanin rashin ta idonsa ta Kai har haka ba. "Have a seat, kazo ka tsaya Wai kuka take min na kawota an Mata wulakanci na Maida ta gida
ita ko sunan Kano Bata sonji".
Sameer 'yar dariya yayi "Ni ba ruwana a ciki Dan aikene