Showing 33001 words to 36000 words out of 65935 words

Chapter 12 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf

03 Aug 2025

1494

ko macen da bata haihuwa shima idan
tana amfani dashi In Sha Allah zata Samu haihuwa, abinda ta fada min kenan".
Zahra ta fada tana kallon Dr din.
"Masha Allah, batayi karya ba Babu komai a cikin mahaifarki yayi dissolving ya wuce a cikin
jinin da Kika zubar, Naga sun rubuta miscarriage irin haka ne yake kawo a batawa yarinya suna
alhalin ba haka bane".
Ta fada tana kallon Aunty zilai.
"Kinga sister dina budurwa ce dal babu wata alaka data taba hadata da wani namiji na gani Dan
haka ku bani number din Mama nayi Mata bayani nasan ba Karamin tashin hankali ta shiga ba
a jiya nasan har yanzu Bata da nutsuwa da wata ce ma tana Nan tare damu ayi komai a
gabanta". Kallan kallo ake tsakanin Aunty zilai da zahra.
Me maganar likitan ke nufi da tace zahra budurwa ce? Tsatstsare Aunty zilai zahra tayi da Ido
kafin ta juya ta kalli doctor Hajara kamar yanda ta gani a jikin Dan siririn freme a Kan table
dinta.
"Nagode doctor Amma ba sai kin Kira Ammatah ba Bata kasar taje ganin likita tana da hawan
jini ne Batasan ma bani da lafiya ba, ya pcv din Naga 48% ya Isa kenan?.
Murmushi tayi doctor din.
"Sister zahra ai yanzu haka sai ki bada jini,me 27% ma is ok basai an Kara masa jini ba sai dai
a bashi maganin Karin jini".
"Ok tom shike Nan nagode kwarai sai an Jima" zahra ta fada tana tashi tsaye, har sun Kai Bakin
kofar fita taji doctor din na fadin.
"Sister zahra bazaki bani number wayarki ba idan an tashi bikinki nazo Miki, bansan kowa ba a
garin Nan daga Jigawa mukayi transfer nida mijina shima doctor ne pediatric banu Dade da
Aure ba Ina son nayi kawa a nan".
Dawowa zahra tayi tana fadin.
"Ai kuwa na gode kwarai da gaske kawo na saka Miki number dina sai ki kirani Naga taki".
Ita dai Aunty zilai mamakin duniyar Nan ya cikata, har gurin mota doctor Hajara ta raka zahra

saboda Bata da patient a ranar zata shiga ante-natal zasuyi awo.
Address din gidan Ammah ta bawa doctor din, sukayi sallama suka wuce, suna hanya mahmud
ya Kara Kira yanda yaji muryar ta cikin nutsuwa yasan lamarin yayi kyau.
"I will call you later, we are on the way".
Ta fada Masa a hankali.
"Ok"
Kawai yace ya yanke Kiran.
Tunda suka shigo motar zahra ta hade gabas da yamma yanda Aunty zilai ma ba zatayi Mata
wata magana ba, don taga yanda ta zaro Ido lokacin da doctor ke bayani.
Har kofar parlour zayyan ya kawo su ya sauke Yana fadin.
"Ranki shi dade Allah ya Kara lafiya".
"Allahumma Amin"
Zilai ta fada.
Ita ta bude kofar Zahra ta shiga, suna shiga ciki zahra ta juyo tana fuskantar zilan.
"Aunty zilai wannan maganar ta Zama sirri yarda da Aminci yasa nake yin abubuwana a
gabanki tunda bamu taba samunki da wani abun ashsha ba, ko Ammah bana son taji labarin
wannan abun Daya sameni Kinga dai ance babu ya wuce to zancen ya tsaya ya junan mu".
"In Sha Allah babu Mai ji uwar dakina, Amma wani hanzarin ba gudu ba, ko kuma dai a fadawa
Ammah mijin naki bashi da lafiya sai a nemar Masa magani ai irin wannan ba'ayin shiru kada
karamar matsala ta Zama Babba, yaro har yaro Amma babu lafiya".
Ta fada tana Jimamin abun.
Dariya maganganun ta suka bata ita bilhaqqi da gaske take maganar ta.
"Ki daina dariya wallahi ba abun dariya bane, yanzu saboda Allah kuja Baki kuyi shiru Dan
yarinta, ai wannan ba Karamar matsala bace ba fa".
"Wai Aunty zilai waye yace Miki bashi da lafiya? Lafiyarsa kalau wallahi".
"Eh Daman lafiyar kalau Mana azahiri Amma a badini kuma ai Mai tsananin ciwo ne".
"Allah Ina fada Miki ba abinda ya sameshi fa".
Wani kallon Amma Baki da lissafi zilan tayi mata.
"Eh Naga lafiya a tare dashi tinda akace har yanzu kina nan a buduwarki Kinga kuwa ai lafiya ta
tabbata a gare shi, yo ko waliyi ne aka aje Masa danyar yarinya kamar ki ya aje walittakar ya
Raya sunna Amma shi yaro sharaf dashi ace ya Zuba Miki Ido tsawon watanni ai kinsan da
matsala". Ganin ba zata fahimce ta ba yasa Zahra fadin.
"Kinga Aunty zilai babu ruwan ki da shiga sangarsa ki Zuba Masa ido idan ma bashi da lafiyar ai
ya sani ze nemarwa Kansa magani".
"Gaskiyarki Kuma fa babu ruwanw kada na dauko ruwan dafa kaina da kaina".
"Da dai yafi".
Bedroom Zahra ta wuce barci takeji sosai.

Tana shiga ta cire rigar jikinta wani wankan ta sake, fitowa tayi daure da towel sky blue a jikinta,
jinta take wani iri Bata taba samun irin wannan bleeding din ba shi yasa duk ta takura.
Zama tayi tana shafa lotion na razac tana sonsa sosai, tana cikin shafawa taji ringing din
wayarta a Kan bedside tashi tayi tsam ta nufi gurin sunansa ta gani Yana yawo Kan screen din,

wallahi tausayi yake Bata ya kasa samun nutsuwa Kota sisin kwabo.
Video call ne, dauka tayi tana Masa sallama.
Tsura Mata Ido yayi yana tasbihi ga ubangijin da yayi wannan surar, wani yawu ya hadiye ba
shiri, kashe mata Ido Daya yayi Yana dage girarsa ta hagu.
"Precious..,"
Ya kirawo sunanta in a deep voice, lumshe Ido tayi Dan sai taji yau sunan ya zamar Mata wani
so special.
Gefen bed ta zauna ta Dan jingina da pillow a jikin gadon, sexy eyes dinta ta Zuba Masu kamar
Zaiba a ciki kafin ta amsa Masa gently.
"Na'am.. meu Amor....".
Saida ya lashe lips dinsa saboda wani abu ya tsirga Masa cikin mararsa har Saida ya rufe
Idanunsa, a hankali ya sauke su a kanta fal fitina Yana Mata wani kallon kasa-kasa.
"Kin tashi hankalina fa ba kadan ba, na rasa nutsuwa ta, hakurin zamanki nesa Dani ya Kare
gaskiya bazan iya wannan jarumtar ba, gangar jina ke Nan Amma zuciyar tana Nan Kinga kuwa
mutum ba zuciya ai babu mutum, ya jikin naki? Me suka fada da sukayi scanning din? naji
zayyan na fada min wai sun ce miscarriage kikayi, nace a'a sai dai wani abun badai shi ba". Gyara kwaciyarta tayi.
"Nima da farko haka suka fada Aunty zilai ma haka tace data gani, na fada musu bashi bane
Amma Basu yarda ba, sai doctor din data dubani da safen Nan tace fibroid din ne yayi
dissolving ya biyo period shine ya kawo heavy bleeding din, Kuma fa da har number din Ammah
ta nemi na Bata Wai zatayi Mata bayanin abinda ya faru Dani tasan hankalinta ba a kwance
yake ba ance 'yarta budurwa tana dauke da ciki tayi bari, gara ta fada Mata Babu wani Daya
taba sanin yarta a matsayin mace lalura ce kawai, kasan muna dawowa Aunty zilai ta tsareni da
maganar bamu da wayo Ashe baka da lafiya muke zaune bamu fadawa kowa ba ita zata
fadawa Ammah a nemar maka magani tunda Amana ta turota gurina, da kyar fa na fashimtar da
ita nace babu ruwanta ta barka ka nemi maganinka".
Dan cute pink lips din ta yake bi da kallo harta Gama bashi statement din.
Kankance Idanunsa yayi Yana Mata wani kallo.
"Gaskiya Kam maganar doctor gaskiya ce, Ni nasan har yanzu rainon a Bata nake yi koba haka
bane? Kice da Auntyn ki ta Kira Mana Ruwa? da bazan Kara yarda mu hada ido da Ammah ba
ai tonon sillil ne wannan shikenan na Zama ragon maza a idanunta".

Ai zahra Bata gane ta saki layi ba Sai daga baya, kunya taji ta rufeta.
"Nifa labari na baka ba Wai wani Abu ba".
"A'a gara na saka shimma kada a zaci da gaske ne, yanzu ita ta yarda bani da kuzari fa sai dai
tayi ta kallona a haka koba haka bane?.

"Pls dan Allah mubar zancen Nan yafi karfina".

Murmushin nan nasa yayi mata yana fadin.
"Bayani zakiyi da yaren garinku yarinya gashi nan kin jamin ana min kallon wani lusari ko?".

Kira ne ya shigo Masa daga Asibiti, da sauri ya yanke Kiran Yana fadin.

"Bari na daga kirane daga Asibiti.

Yana sauka daga online tayi ajiyar zuciya Allah ya taimaketa, da Allah kadai yasan meze baro
Mata taga alamar kamar hakurinsa Yana neman karewa, Dan wannan idanun nasa abinda suke
fitarwa Yana Bata tsoro.

______

Maganar canza lokacin aiki sukayi masa saboda wasu dalilai da suka saka za'ayi Masa aikin
gobe Dan haka suna iya shigowa sun fito da Baba Malam din daga investigation room din. Yana
aje wayar Abubakar da Habib suka shigo, tashi yayi Yana fada musu su shirya zasu wuce
Asibiti gurin baba Malam Wai sun canza ranar aikin gobe zasuyi Masa Ina ganin sun gano wani
Abu daya zama dole aikin ya Zama emergency.

Cikin abinda Bai wuce minti talatin ba suka shiga Asibitin office din doctor suka nufa tunda ya
bukaci ganin mahmud saboda ze cike wasu forms ze Kuma yi signing a takardun da za'ayi
aikin.
Basu Dade ba suka Gama da office din doctor suka nufi dakin da Baba Malam din yake.
Suna tafiya kawai Habib kallon mahmud yake ya rikide ya juye daga mahmud din Baba Malam
ya koma wani na daban Mai wani irin kwarjini da cikar Kamala ko Zama sukayi Hira irin ta da
yanzu sai Habib yaji baze iyaba sai fa mahmud ya matsa Masa sannan yake Dan sakewa, ga
Abubakar wanda shine babban guard dinsa Amma sukayi basaja ba Wanda ya gane, ga wani
Karin abin mamakin Wai Bilyaminu ma yaran mahmud ne.
Har suka karasa dakin yana ta faman tunanin abun.
Masha Allah ba karamin Dadi sukaji ba da ganin yanda jikin Baban yake.
Sallamar su ya amsa Yana sakin murmushi tamkar ba Mai lalura ba, gani ma sukayi har wani
haske ya Karayi duk da Daman farin mutum ne Shi, Yana kwance sandam da sauri mahmud ya
Karasa kusa dashi Yana fadin.
"Masha Allah! Baba jiki ya Fara kyau Alhamdulillahi, ya kaje jin jikin naka?".
"Alhamdulillahi Mahmud jiki ya Fara kyau ko yanda nakeji da banbanci akan kwana ukun baya,
sannunku da kokari Allah yayi Albarka yasa afi haka".
"Allahumma Amin".
Suka amsa su duka, Abubakar da Habib ne suka matso suna gaishe da shi da tambayar ya jikin
nasa.
Ya amsa musu da sauki suma yayi musu godiyar dawainiyar da suketa faman yi dashi.
A Nan suka zauna har dare suna dauke Masa kewa mahmud ya cika Alkawari ya kirawo
Bilyaminu video call yace ya Kaiwa iya Abu zasuyi magana da Malam, taji dadin yanda taga
jikin nasa Dan sun Jima suna Hira har su mahmud sukaje suka Kara dubo Alhajin su Faisal.
Sai wurin goman dare na agogon kasar suka wuce daga asibitin, ba gida suka nufa ba,
Abubakar ke driving sai Habib dake zaune a gefensa sai Kuma oga kwata-kwata dake baya
yana ta cinkunar wayarsa.
"Sir ina zamu Fara zuwa?"
Abubakar ya tambaya cikin ladabi.

Saida ya Gama duba results din club dinsa real Madrid, sunyi Wasa lokacin suna Asibiti shine
yanzu yake duba results din wasan.
"Wuce Africa Avenue kawai na gama ganawa dasu sai mu shiga Taj idan lokacin be Qure ba".
"Ok sir Leela palace kenan?".
"Eh a can nace musu zamu zauna"

"Ok."
Akalar motar ya canza daga hanyar da yake bi, shi dai Habib nasa ido ne Dan fadan da yafi
karfinka sai ka mayar dashi Wasa.
Ganawa ce mahmud din zeyi da managers na different companies dinsa ya Dade Basu hadu ba
sai dai ta Internet kawai, shine yayi amfani da wannan damar ya tarasu duk da yaso sai Nan
gaba to wata kura ce ke neman tasowa shine yayi musu Kiran gaggawa.


Habib yaso fita mahmud ya Hana shi, ba karamin abin al'jabi Habib ya gani ba yanda yaga
manyan mutane daga different countries suna Masa aiki a Nan Indian shifa har tsoro ya Fara
kamashi waye Mahmud ne Wai? Yanda yaji managers da Accountant suna bada lissafi saida
jikinsa ya dauki tsuma, basu suka baro Leela palace ba sai kusan Daya da rabi na dare. Suna shiga gidan Mahmud ya wuce bedroom, requesting coffee kawai daga gurin Mr Ajey.
Su Habib dai sunci Abinci sannan suka wuce, kowa ya shige nasa, tun jiya aka hada dayan
dakin Habib ya koma ya barwa Abubakar wanda suka Fara sauka.

A gajiye mahmud ya shiga bedroom dinsa wayar da eyeglass din ya aje a Kan bedside ya wuce
toilet.
Lokacin Daya fito Mr Ajey ya kawo masa coffee dinsa.
Saida ya saka pyjamas dinsa milk colour mai haske sannan ya zauna Yana sipping din coffee a
hankali yana Jin dadin yanda yake ratsa Masa makogwaro Yana gangarawa.
Kira ne ya shigo wayarsa yasan ba previous bace har ze share sai ya dauka ya duba Sameer
ya gani.
"Sameer" ya ambaci sunan a fili sannan ya daga Kiran.
Daga can Sameer din ya Fara magana.
"Sir Naga sakonka, wallahi da kyar na samu visar madam yau Amma sai Monday zata taho in
Sha Allah gara nima dai na huta".
Ya fada Yana dariya.
"Au dariya ma kakeyi ko? wallahi idan tace na mayar dakai China da Zama Allah saika koma
can,Kuma Banda madam zaka tafi, sai bayan wata shida zaka ringa zuwa Kuna gaisawa shima
sai ta amince, idan Bata amince ba sai dai once in year".
"Tuba nakeyi gani nayi ka kasa hakurin rashinta a kusa da Kai tun yanzu to Yaya idan labarin
yasha banban"?".
Ya fada Yana dariya irin ta shakakikan friends.
"Allah ya shiryeka badai abinda zakaji Dan saka Ido kawai, ka aje komai jibi ka wuce Nigeria Kai
da kanka zaka kawota min ita Kano".
"Ok. In Sha Allah".

Sukayi sallama,wayar ya aje yana tunanin ko ya kirata ko Kuma ya kwanta ya huta.


** *** **

Barci sosai Zahra tayi Bata tashi ba sai kusan la'asar toilet ta shiga ta sake gyara jikinta.
Alhamdulillahi Abun ya Fara sauki sosai, amma dai ha lrokacin Yana Zuba over, Saida ta shirya
ta nufo parlour tana rike da wayarta, ba kowa a ciki sai kamshin turaren daki da tureren wuta.
A hankali ta ratsa ta nufi dining Abinci ta gani kala biyu coconut rice ce sai danbun shinkafa da
yaji vegetable a ciki, dambun ta Zuba kadan taci kadan ta tashi ta dawo parlour ta zauna. Aunty
Hasana ta kiya har sau biyu ba'a dauka ba saita tura mata text, Aunty Safiya ta Kirawo lokacin
suna makaranta dalibai na Exams, dauka tayi tana amsa sallamar zahra tana fadin. "Kaga Mrs Dange, ya kanon?".
'yar dariya zahra tayi.
"Kaji dai Aunty Safiya, to Ina Azare Kuma kusa dake ma".
"Ahhh haba Dan Allah....!"
"Wallahi Ina layi na biyu bayan layinku".
Dan Jim Aunty Safiyar tayi tana tuna wani gida data gani lokacin da taje barka layin Wanda "yan
layin suke ce masa gidan Dan America, masu aikin ginin ne da wani ya tqmbayesu gidan waye
sukace Mai gidan Yana America shikenan suka sakawa Masa gidan Dan America.
"Kamar nasan gidan naje barkar haihuwa kwanaki baya Naga wani sabon gida akace mai shi
baya kasar Ina shine gamu Nan zamu shigo da Amatu in Sha Allah".
"A'a kice na tashi na shirya abin tarba, Ina jira, Dan Allah kuzo da wuri".

Aunty zilai ce ta shigo fadin.
"Wallahi daga na Dan kwanta na huta barci ya daukeni".
"Ai Rai dangin goro ne hutu yakeso, Ina laifinki sannu kema ai jiyan yanke Miki barci akayi shi
Kuma ba'a cin bashinsa sai an biya"
"Haka ne Kam ai anyi ta barka dai tunda na rabu da wannan kaddararren ciwon cikin gaskiya
duniya da magani waye ze taba kawo masoro zeyi irin wanna aikin?".
"Gaskiya dai Kam".
Zahra ta fada.
"Amma dai uwar dakina kin Kira Hajiyar makwarari kiyi Mata albishir ko?".
Kai zahra ta girgiza alamar bazata kirata ba.
"A'a ba'a haka,ki kirata ki gaisheta ki fada Mata magani yayi aiki kiyi Mata godiya ai zataji dadi'.
"To shikenan na kirata anjima saina fada mata, yanzu me za'a Karayi Mai sauri zanyi Baki ne
abokan aikina da muka zauna a Inda nayi service".

"Akwai samosa da nayi dazu na saka a fridge sai a soya Musa tunda da abinci da drinks ina ga
ai ya Isa ko?".
"Eh hakan yayi".
Kitchen Aunty zilan ta koma ita Kuma zahra tabi lafiyar kujerar.
Aunty Rukayya ta kirawo.

Bata kusa sai mommy ta dauka cikin ladabi zahra ta gaisheta mommyn ce tace Mata. "Ai kuwa
Rukayya na gidan Hajiyar makwarari dazu ta tafi ta manta wayar a gida garin sauri".
"To mommy Baki na Kira da layin Hajiyar na gode".
"To nagode Allah yayi Albarka, ya wajen Mai jikin Kuma Sameer yace sun wuce indai ko".
"Eh suna can da sauki".
"Allah ya bashi lafiya yasa ayi aikin a sa'a".
"Allahumma Amin nagode".
Sukayi sallama.
Akalar Kiran ta juya ga Hajiyar makwarari cikin sa'a wayar na hannunta ta Gama amsa wani
Dan uwanta Malam na Dala Kiran zahra ya shigo.
Dauka tayi tana fadin,
"Salamu Alaikum, waye yake Kira?".
"W/slm, Hajiya nice zahra".
Dan Jim tayi tana tuna Ina tasan muryar Nan.
"Zahra wace ce kenan? Ko Zahara,un Hajiya Fateen lalloki?".
"A'a ba ita bace".
Sai zahra ta rasa me zata ce Mata ne, tace zahrar mahmud abokon Sameer, sai taji da nauyi ta
fada Mata haka.
Rukayya ce ta shigo da cup din kunun tsamiya data damawa Hajiyar a hannunta.
"Wa Kika Sami haka naji kina ambatar zahrar lalloki".
"Ungo kiji ko wacece tayi shiru batayi min bayani ba ke kiji ko zata fada Miki".
Wayar Rukayya ta karba tana mikawa Hajiyar kunun a cup.
"Aunty Rukayya".
Zahra ta Kira sunanta.
Take ta dauki muryar zahrar.
"Au kice min amaryar big bro ce ai bayani Zaki yiwa Hajjaju, kince zahra Ina zata gane".
"Hajiya matar Ya Mahmud ce mutuniyar ki da Kika Gama maganarta dazu to gata 'yar halak ta
kiraki".
"Ga Hajiyar ku Gama gaisawa Dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login