Showing 63001 words to 65935 words out of 65935 words
Chapter 22 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf
famfo.
Ammah ce tayiwa su Aunty Badi'a bayanin wacece mama a gidan da kuma Matsayin su na
iyayen mijin zahra.
Har dakin da zahrar take Aunty Badi'ar taje ta samu zahrar tana karatun Alqur'ani mai girma.
Tana Kai aya zahra ta rufe Qur'an din.
Shigowa tayi tana kallon Zahra wadda ta saka rigar wani material da Aunty Fateeha ta bawa
tele ya dinka Mata sai tayi wani mahaukacin kyau, gefen gadon Mummy badai'a ta zauna ta
nuna mata kusa da ita, Bata zauna kusa da ita ba saita zauna a Kan carpet din dake kusa da
kafarta.
"Zamu tafi diyata me Zaki bamu mu kaiwa Dana kafin ki isko shi?".
Sadda Kai zahra tayi,duk kunya ta rufeta.
"Kina jina".
Kai zahrar ta gyada Mata alamar eh.
"Ki kwantar da hankalinki kada ki jewa yarona da rama, babu abinda ze rabaku in Sha
Allah,mun kawo ki ne Dan Kara nema miki mutumci a idanun 'yan uwan mijinki idan aka wayi
gari kawai suka ganki bazakiyi daraja da kima ba a idanunsu sai ayi muku wata fassara ta
daban kinji, ki yiwa Amminku biyayya yana sonki sosai wallahi tun kafin ta ganki Allah ya nuna
Mata ke a Cikin mafarkanta sau babu adadi tare da mahmud Kuma a zahiri ma Kuma ke dince
dai ba wata ba, zata turo matanenta suzo har Cikin gidan Nan su daukeki su danka ki Amana a
hannunta gadan dangin mahaifinsa da nata dangin, kuma duk jarabawar da tayi Miki a zaman
kwana Daya daikayi da ita ba'a samu matsala ba haka muma a namu bangaren babu kuskuren
da aka samu Sai ma abinda babu shi da muka samu Karin haske a cikinsa,Dan haka ki fadawa
kawayenki na kusa zasu rakaki dakinki na dindidin duk sauran Wasa ne ai ya fada min yanda
kukayi ta gantali kamar mararsa mafadi,Dan Allah kiyi Masa biyayya ki kula dashi jariri ne a
gurin soyayya ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba kece mace ta farko Daya taba so a tarihin
rayuwarsa da bakinsa ya fada min wannan yace min ya fara sonki tun Yana dan shekarar farko
a university lokacin ya Dan Fara business Sameer Yana raka shi, Bai dai bude min maganar ba
to kinji dai da sonki ya rayu Dan haka ki Zama jaruma a dukkan al'amuransa kinji diyata".
Kai ta gyada Mata alamar to.
Bayan tafiyar bakin ne Ammah ta dawo Cikin a parlour Ammah ta Sami zahra tana fada Mata
yanda ta yaba da halin surukarta ba kadan ba.
Ba jimawa Hajiya Kaltum ta shigo suka kule da Ammah bed room din.
Zahra ma Bata koma ciki ba zamanta tayi a parlourn ita kadai tana kallon girkin larabawa.
Wurin Sha biyu da rabi Ya Abdul Hakeem ya shigo Yana fadin.
Ina Zahrar tazo tayi bako".
*AUREN HUCE HAUSHI*
AISHAT ISAH MUSAH
(Maman Fateemah)
09061432330
Or
08055362975
Page 79.
...........
Maganar data sauka a kunnen Ammah kenan, wani kallo Ammar ta yiwa Abdul Hakeem na ina
tunaninka yake da lissafinka yake.
"Me naji kana fada tayi bako Kuma kamar yaya?".
Dawo yayi daga fitar da yayi niyya.
"Ammah bafa wani bane da ban Sameer ne abokin mijinta Ina ganin sako ne ze Bata fa, ya
za'ayi nazo kiranta idan bansan waye ba tubda da aurenta shima ganin na hannun Daman
mijinta ne Kuma ga bayanin da Kika yi min nasan da abinda ya kawo shi girinta".
"Ah to yanzu naji magana, turo min magaji ya bude Masa falon baki.
"Haba basai na turosa ba bani kawai na bude masa".
Gurin dinning Ammah ta nufa ta dauko Masa keys din ta bashi ya fice, Alawiyya Ammah tasa ta
Zuba abinci da drinks ta Kai Masa.
Sai da Zahrar ta bashi a kalla minti talatin tasa dai zuwa lokacin ya Gama komai sannan ta leqa
ta fadawa Ammah zataje gurinsa.
Lokacin da tayi sallama ta shiga Sameer Yana tsaye da waya a kunne Yana fadin.
"Dan Allah ka koyi hakuri Mana haba kamar a kanka aka Fara Aure duk ka tashi hankalina nace
maka Ina Cikin gidan abincin tarba aka kawo min kafin ita madam din ta fito.....yauwa gata Nan
ta fito".
Ya fada Yana mikowa Zahra wayar wadda ke fadin.
"Barka da sauka oga Sameer".
"Yauwa sannu amarya, ungo mijinki ya hanani sakat Saida ya tasoni daga aikin daya sakani a
garin nan Wai nazo na gani da abinda yake damunki".
Dan murmusawa tayi.
"Ni lafiya ta kalau kawai dai baya son ka huta ne, Ina baby na?".
"Baby sun dauki hanyar sokoto acan zaku hadu, harda su Rukayya da mommy da mutuniyar ki
ai Rukayya na fada Mata tayi tsallen albarka tace tafiya ta tashi".
Ya fada yana nufar kofa.
Wayar ta duba Yana Kan layin Yana jinsu.
"Karawa tayi a kunne tana fadin.
"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
A zuciyarsa ya amsa sallamar Amma a zahiri sai yace Mata
"Haba precious kunyi min adalci kenan? me yasa Zaki yarda a maida Mana hannun agogo
baya, Wai Dan kada mutane suyi surutu sai a dauke min ke? Nifa nayi zaton koma menene a
iya sokoto Nan ze tsayaKema na kiraki Dan na samu relief sai kik'i daga wayar sai ace min wai
kuka kikeyi wato so kike na nuna musu raunina a kanki ko? Shiru tayi ita ta rasa mema zata ce Masa Umarnin mahaifiyarsa zata tsallake, da kunnanta fa
taji Yana fadar Ammi ze bawa zabi ta zabar Masa Mata, to Kuma tace ta tashi tabi yan uwanta
su tafi to musu zatayi Mata tace bazata ba ko Yaya?shi me yasa ya Bata zabin tayi abinda ya
dace, ita Bata kullace shi ba sai ita zega laifin ta taho wato shi yayi biyayya ita kuma ta nuna ba
haka ba ace kwadayin dukiyar su take yi kenan,duk da itama a Cikin wadatar ta tashi gaba da
baya Amma ai ba kowa ne ya san hakan ba.
"Kinyi shiru precious".
"Me kake son na fada bayan biyayya na yiwa Ammi cewa fa tayi na tashi mu tafi kawai lokacin
banma San inda zamu ba Saida mukazo Kano Naga mun dauki hanyar Azare na gane Ina
zamu,ai Ina ganin kawai mu hakura mu yiwa Iyayen mu biyayya kaga Nima biyayyar nayi
lokacin da aka bani Kai bansan Koda waye aka daura min aure ba,Amma na hakura nayi
biyyyar iyaye kaima kayi biyyyar idan Ammi bani bace zabinta muyi hakuri haka Allah ya nufa
zaman takaitaccene kabi abinda takeso bazaka tabe ba in Sha Allah". Cikin tashin hankali ya Fara magana.
"Me kike fada haka preciousss? Kina son heart attack ya sameni? Waya fada Miki Ammi Bata
Sonki? Soyayyar tasa ta raboki da gidanta badan Bata sonki ba Kinga yanda ta kasa zaune ta
kasa tsaye duk fa kunyar Dan fari Ammi ta aje a gefe hidimarta takeyi babu Kama hannun yaro,
Ina gama da sakon data bawa Sameer ya kawo Miki, na Ammah Ina Jin sai gobe za'a taho
dashi, ki shirya dake za'a taho min fa a Mika min kayana daga cikin daki Nima naji abinda 'yan
uwan sukeji na gaji da gararamba gara na tsuguna Nima na Fara hada nawa family din, in sha
Allah da biyu Zaki Fara min ko 'yar gidana".
Runtse idanu tayi ita fa idan yana ambatar irin wadannan kalaman na haihuwa tuno yanda
sabgar take kafin samun abun haihuwar shine damuwar ta da gasken gaske tana hasaso ranar
da alama Kuma an dauki hanyar zuwanta.
"Dan Allah ya mahmud ka Bari ba kyau fa irin wannan maganar"
"Kam bala'in waye yayan naki Allah ki iya bakinki babu hadin Zuma da guna,ki nemi yayanki tun
dare be Miki ba,Ni ki barni a your love dinki kawai ko kin manta meu amor dinki ne...? Pls Dan
fada min irin tanadin da aka yiwa meu amor a wannan special day din?".
"Wayyo.... Dan Allah ka rufa min asiri.. ni wallahi wannan zancen yafi karfina pls Kan bariiii..?
Ta fada da sigar data yamutsa Masa jam'iyya nan da nan ya nemi nutsuwarsa ya rasa.
"Ya salam! Previousss Anya Zan iya hakurin kwana uku nan gaskiya tahowa zanyi na daukeki
mu wuce Dubai inda a tanadar Miki Dan amarcinki alkawarin nayi azumi uku kawai bazan iya
ba"
Ya fada Yana Mata wani irin numfashi a kunne, da sauri ta cire wayar daga kunnenta tana fadin
"nashiga Tara me kuma nayi Masa?
Da sauri ta mayar da wayar tana Masa magiyar ya rufa Mata asiri kada ya jawowa mahaifiyarsa
abun fada Cikin kishiyoyi.
Ba Karamin Kai ruwa Rana akayi ba kafin ya hakura, da gaske tuburewa yayi shi baya son
bidi'a ansan tun yaushe suke tare da za'a wani tarki bikin babu gaira babu dalili, tana samu ya
Dan sauka tayi Masa sallama tace Ammah tana kiranta anyi Baki,yasan neman guduwa takeyi
kawai Bai barta ba saida ya jaddada Mata ze Kira da dare. Lokacin data fito Sameer baya kusa tasan suna tare da ya Abdul Hakeem part dinsu ta nufa Ya
imam ta gani ta tambaye shi ko su Ya Abdul Hakeem suna nan? Tabbacin hakan ya Bata Kira
shi a wayar ta tace tana jiran oga Sameer.
Ba jimawa suka fito ya Mika Masa wayarsa, tana fadin .
"Gashi nagode".
Karba yayi yana fadin..
"Bari na dauko Miki sakon Ammi Wanda ta bayar a kawo Miki"..
Wata Leda Yar madaidaiciya ya Miko Mata Yana fadin.
"Gashi Aunty Aishat tace zakuyi waya".
"Ok Nagode, bazaka shiga ku gaisa da Ammah ba?"
Yar dariya yayi.
"Na nawa kuma? Na shiga mun gaisa".
Dan murmushi tayi ta nufi Cikin gida.
Ba zato tayi arba da Aunty Hasana da gudu ta shige jikinta tana fadin.
"Aunty kin manta Dani wallahi, laifin me nayi Dan Allah".
"Kuji mun yarinya ! Sai Kuma nayi ta kiranki a waya har mijinki ya Raina ni ya daina Jin 'yar
kunyar tawa da yakeji ai yawan damun kani ko d'a da Kira a waya bini-bini Yana kawo raini da
rashin ganin kima a tsakani gara a ringa daukar lokaci yanda duk lokacin daka Kira ya Zama
ana marmarinka ku rabu ana kewarka da Jin ba'a gaji da Hira da Kai ba". "Wannan maganar taki bisa hanya take, haka ake son Babba yaja girmansa".
Hajiya kaltume ta fada.
"Ah to Mamma fada Mata dai so take girma ya Fadi a gurin kanin nawa yanzu kuwa Aunty sama
Aunty kasa duk bayan kwana biyu saiya kirani ya gaisheni".
"Aunty Ina zuwa".
Zahra ta fad'a tana nufar bedroom din data yiwa kanta masauki, Bata Jima ba ta fito da abinda
Ammi ta Bata ta mikawa Aunty Hasana tana fadin.
"Gasu Nan na manta dasu Ammi ce ta bani jiya da zamu taho".
Bata zauna ba daki ta jiya tana rike da hannun Autar Aunty.
Aunty Hasana ce ta cire rapping sheet din na madaidaicin, white gold din ne yayi musu maraba,
da sauri Hajiya kaltume ta matso tana fadin.
"Masha Allah girma sai Dan girma wani kayan sai amale wane jaki,lallai babban goro sai
magogin karfe, irin wannan kyautar girma haka, 'yan biting bude sauran muga abinda ke ciki".
Wata ubansun Alkyabba ce baka da ratsin zare golden sai turarika masu azabar kamshi a ciki.
Jim maganar Hajiya kaltume yasa Ammah fitowa daga daki taga menene ake dagawa murya
haka?
Sarkar Hajiyar ta mikawa Ammah.
"Duba kiga Karamar arziki irin wannan daga uwar mahmud, Ashe dasu tazo gidan ta aje ta
shiga tata sabgar, inga fa sarkar Nan ta tasamma wajen fifty millions wallahi Dan kwanaki mun
siyar da wata Bata Kai wannan ba wurin forty seven milion aka sayar".
Ammah rasa abin fada tayi saboda abin ya Bata mamaki to su wane irin dukiya garesu mutanen
nan?.
Nan suka zauna suna ta maida yanda akayi har kusan la'asar duk abinda ya kamata sunyi yi
an bada aikin kayan garar da za'a Kaiwa Zahra Dana Iyayen mijin duk wata al'ada da ake a
sokoton Ammah ta tambaya an fada mata, da yammaci suna zaune Abba ya shigo Yana fadin.
"Asma'u ku tanadi abun tarbar Baki gobe in sha Allah bakin sokoto na Nan tafe yanzu ba
dadewa Kanin Alhaji Muhammad ya kirani yake fada min zasuzo naso na hanasu duba da nisan
dake tsakanin Bauchi da sokoto Amma ya nuna min a'a idan ma yafi haka zasuzo godiya ce
zasu zo tunda ba aure za'a sake daurawa ba inaga ko maza ne ko kuma Mata da maza ne ban
sani ba dai sai ayi dai abinda ya kamata nace Abdul Hakeem suje da magaji a debo zabi sai a
Kara Dana gidan idan yaso sai a kawo sabo Naman na gida.
"To Allah ya kaimu, ya Kuma maganar furniture's din da za'a tafi dasu daga nan?".
Sai goben insha Allah za'a had a da kayan da kikace za'a kawo daga Bauchi Sai a tafi dasu
gaba daya ai inaga hakan yayi ko?"
"Eh hakan yayi Allah ya saka da Alkhairi ya jikan mahaifa".
Ameen su Hajiya da Aunty Hasana suka fada ciki ya shige Aunty Hasana ya tashi tabi bayansa.
Aiki su Ammah suka Fara babu kama hannun yaro auta Ammah ta turo makota tace ya fada
musu su shigo gobe za'a karbi Kaya Kuma ya fadawa mamansu mujiba idan Abbansu yana
gidan ta tambaye should ta shigo zasuyi aiki.
Hajiya kaltume Bata bar gidan ba sai kusan Tara na dare, taso a Kara yiwa Zahra gyara Amma
Aunty Hasana tace a karba a tafar Mata dashi tunda Hasanarsa ta kaita gurin masu gyaran
Amare a India a barta haka Nan tunda Abu ne a duhu ba'asan yanda abun yake ba".
"Eh to kema da gaskiyar ki Naga 'yar tawa har yanzu zubin 'yan Mata gareta babu kamar
cikakkiyar mace a tare da ita".
Da haka suka rabu haka Nan taji Bata son a Kara Bata komai idan ba fruits ba gaskiya Bata son
wannan tonon sililin duk da bata da tabbas na wani Abu be shiga tsakani ba duba da tun lokacin
da akayi bikin to sai dai a yanda zilai ta fada Mata bayanin da likitar Nan tayi Mata Lamarin
abun dubawa ne kwarai, ita fa tausayin Zahra takeji yanda taga anyi Mata wannan gyaran tasan
sai yanda Hali yayi kawai Amma da Qura a gaba.
Washe gari da sakkon aiki suka tashi Dan tun shida Maman mujiba ta shigo ita da Aina'u
makociyar itama suna gaisawa sosai da Ammah din, duk bidirin da akeyi Mama Bata fito ba ko
kuma tace me akeyi babu Daya,itama Ammah ta bawa banza ajiyarta.
Karfe Tara Mai kyau su Inna maimuna sun shigo gidan a Bauchi suka kwana saboda sunyi dare
bana Wasa ba dole suka hakura suka kwana a can.
Wasu dunkuna ne aka kawo wanda Aunty Hasana ta bayar aka dinkawa Zahra express laces
ne na manyan Mata Wanda suke ji da Kansu na manyan kudi ta saya saboda yau masu kawo
Kayan walau maza ne ko Mata ya Zama dai babu raini duk da babu inda makusa take ta ko ina
kawai dai idan kana da kyau ka Kara da wanka ne. Karfe sha biyu ta gota wasu lafta laftan motoci suka tsaya a kofar gidan Alhaji Jafar Mai yadi wa
Bata lokaci Mai gadi ya bude musu tunda Alhaji ya fada Masa za'ayi Baki a gidan to Yana
ganinsu yasan bakinne.
Gate baba sani ya bude musu suka Sanya Mai cikn harabar gidan.
A can Kuma Zahra ce tayi make up simple ta saka fitted gown na rigar lace sai ta fito da ainihin
structure din jikinta yake. Su dai su Hajiya kaltume dasu Inna mainuna suna zaune Basu yi
aune ba sukaga an Fara shigowa da Kaya, tun suna girgawa har suka zubawa sarautar Allah
Saida aka zube set goma Sha biyu, sai kuma mata suka shigo bisa jagorancin magaji su kuma
mazan suna gurin su Abba da jama'arsa.
Sannu da zuwa aka Fara jera musu mutanen Cikin parlour din tare da Basu girin zama, Aina'u
ce ta ware murya ta zankada guda uku a jere abinda ya fito da su zilai da sahura daga Ina suke
zaune a gidan, Mama ma fitowa tayi da Dan sauri tana fadin.
"Menene akeyi a gidan nan haka da uwar Rana ake ta rafsa guda.
Part din Ammah ta nufa da sauri su zilai duna biye da ita a baya, turus tayi ganin Iyayen
akwatuna a zube a parlourn,kasa daurewa tayi.
"Wannan kayan fa na waye haka?" Inna Maimuna ce ta Bata Amsa "na Amarya Zahra ne kin
san mijin nata ya koma gida shine iyayensa suma zasuyi nasu bikin".
Taku biyu tayi sai ganin ta akayi a kasa ta fadi jikinta na wata irin karkawa Nan da Nan aka yo
kanta da sauri Dan Bata taimakon gaggawa.
********************** **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
************************* **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko
kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI
HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** **************************
.
,
.