Showing 36001 words to 39000 words out of 65935 words
Chapter 13 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf
ba barina zatayi muyi hirar kirki ba idan Baku gaisa ba tunda
nazo take you min zancenki".
Wayar ta mayar Mata ta nemi guri ta zauna.
" 'yar Nan Daman kece ki kak'i yi min bayani dan Ashatta".
Gaishe da Hajiyar tayi tana fadin.
"Cewa nake Zaki ganeni fa, Daman kiranki nayi na gaisheki Kuma na fada Miki ciwon Nan na
cikina ya narke yanzu babu shi".
Wata zabura Hajiya tayi kamar yarinya tana fadin. "Kai Masha Allah kice nayo shiri na taho
Azare na kawo Mik wani maganin saboda bibiko da Kuma aasske- sassake saboda sanyin dake
Hana Yara haihuwa kinsan yanzu kuma sai a Fara shirye-shiyen haihuwa Kwana kadan ai sai
laulayi, Dan ma naji labari mijin naki ya Kara yin halin nasa ya fice daga kasar wallahi sai kin
jajirce kin zamar masa karfen kafa sannan zakiji dadin aure, Amma Kika zauna sanyin Nan sai
kinyi tsa-tsa a banza Naga shi matan ma basa gabansa ta Neman kudinsa kawai yake, Kullum
mutum na sama kamar tsuntsu to kinji dai na fada Miki".
Baki bude Rukayya ke kallon Hajiyar.
[2/7, 11:32 PM] +234 906 821 6318: * AUREN HUCE HAUSHI*
MAMAN FATEEMAH.
Page 65
---------- Wayar hannun Hajiyar makwararin Rukayya ta karbe tana fadin.
"Dan Allah ki daina fadin wata maganar ba girman ki bane".
"To uwata saiki hanani na saita yarinya, ai gobe in Sha Allah Mahfuz ze dangana Dani Azare, yo
duk abinda aka yiwa matar Mahmud ai bazamu iya biyansa abinda yayi Mana ba, Banda rashin
lissafi irin naki Rakiya ke kome nace zanyiwa iyalin yaron Nan ai naki idone,kina zaune ya
daukeni ya kaini wata uwa duniya aka gyara min ido da yanzu kina Nan kina min jagora ko
bakya so kuwa. Tashi ki kimtsa ni ki rakani kurmi na Sami abinda bani dashi, muje agadasawa a
Sami kilishi da dambun nama na tsaraba mu shiga madatai a samo gireba da su bakilawa to
kinji"
Ta yunkura ta tashi Tana daukar sauran kununta, ita dai Rukayya bakinta mutuwa yayi da
kalaman Hajiya, tunda ta furta tafiyar nan Allah ne kadai ze kawo abinda ze hanata zuwa Amma
badai Dan mutum ba, tun su Sameer na secondary tasu tazo Daya da mahmud tun Batasan
Allah ze daga shi haka ba.
A nutse Amatullah ke driving dinsu, taso ta wuce gida saboda ta gaji sosai Amma jin zahra na
garin Kuma babu nisa da gidan yayar mamanta da take zaune a hannunta sai kawai tayi waya
ta fada Mata zasuje unguwa.
Tunda suka shigo layin Amatu ke Kakabin gidan tana fadin.
"Kambala'i wannan Kuma waye yayi one in town din Nan? lallai Aunty Safiya unguwar taku ta
masu ido da kwalli ce".
Murmushi tayi mata tana kokarin Kiran waya.
"Mun shigo ki turo a shiga damu".
Dan saurare tayi kafin tace.
"Ok muna jira".
Ta sauke wayar daga kunnenta.
"Kika ce menene?".
"Cewa nayi unguwar taku ta Zama ta masu Ido da kwalli".
"Bakiji ranar nan muna maganar layin Dan America ba? To ai gidan ne ake cewa gidan dan
America".
Labarin yanda gidan ya Sami suna ta Bata.
Dai dai suna zuwa kofar katafaren gate din gidan.
"Dan tsaya a Nan mu jira muga ta Ina zata bullo Mai kaimu gidan".
Amma ita Safiyar ta hakikance matukar da gaske MAHMUD DANGEN ne da gaske mijin Zahra
to babu ko tantamar wannan gidansa ne.
Saka aya a tunaninta da bude Karamar kofar gate din ya Zama lokaci Daya.
Zilai Mai aikin gidansu zahra Amatu ta gani ta fito, zaro Ido tayi tana kallon Aunty Safiya.
Gyada Mata Kai tayi kawai, sannan ta bude kofar ta fito.
Gaisawa sukayi da Aunty zilan, sannan tace Mata.
"Ko kune Bakin Uwar dakina Zahra".
"Eh mune".
Aunty zilan juyawa tayi da sauri ta koma ta fadawa zayyan zahra tayi Baki.
Jim yayi Yana kallonta kafin ya samu zarafin fadin.
"Yallabai fa ya kafa dokar kada nabar kowa ya shigo gidan nan, Amma Bari na fada Masa duk
da nasan ba wadanda yake nufi bane.
Tana tsaye ya Kira Mahmud cikin sa'a ya sameshi, tun kafin ya fada masa wani Abu yace masa.
"I sw everything, just open the door".
Kawai ya katse Kiran Dan yana bibiyar gidan ne tun lokacin da yaga ta saka ayi wani girkin,
Dan har a kitchen Saida aka saka CCTV.
Gate din zayyan ya bude musu suka shigo, parking lot Amatu ta aje motar suka fito zilai tayi
musu jagaba.
Amatu sai raba Ido take Dan wallahi gidan ya tafi da imaninta ba kadan ba.
Suna shiga zahra tayo wani tsalle tana fadin
.
*Wayyo Allah oyoyo! oyoyo!! Sannu da zuwan ku Amatu, Aunty safiya nagode da Kika kawo
min Amah wallahi Daman Ina nemanta.
Dan ja Baya Amatun rayi tana fadin.
"Ni ba gurinki nazo ba Aunty safiya na rako".
Hannunta zahra ta riko tana fadin.
"Haba my bestie kiyi hakuri Dan Allah na tuba kowane laifi nayj kada a tona"..
. dariya sukayi su duka, Ammatu dai 'yar kauye ta zama Dan Saida ta tada Kai taga yanda
saman dakin yake kamar sararin samaniya Dan harda taurari da wata.
Dauko wancan kawo wannan zahra da Aunty suka shiga yi, sai murna zahra keyi na ganinsu,
sunci sun Sha sannan suka Dora da hira har aka Kira sallar magariba hirar yaushe gamo akeyi,
cikin hirar ne Zahra ke fadin "Wai da gaske kinsan Mahmud?"
Zama ta gyara tana fadin.
"Wallahi ba karya har gidansu na sani sai dai shi nasan be sanni ba". Daga Nan ta tsaya itama
Zahra Bata zafafa ba taja bakinta tayi shiru.
Dakin kusa dana Aunty zilai zahra ta kaisu sukayi alwala, har Amatu zata Fara sallah ta tsaya ta
dubi zahra.
"Ya Naga ke Baki tashi kinyo alwalar ba".
"To sa'i'dawa Ina ruwanki".
Gurin zahra Amatun dawo ta zauna a gefen gadon in da zahra ke zaune.
"Zahra Wai ya haka, ko dai planning kikeyi ne? Amma ace har yanzu babu wani labari, Ni da
naganki kinyi wani sirrin kyau nayi zaton ko an Mana ajiya ne? Kuma kice Wai bakya sallah".
Dariya zahra tayi tana Fadin.
"Cikin lafiya? Ai ni ban isa haihuwa ba".
Wata malalaciyar dariya Amatullah tayi.
"Kice min 'yar yaye aka kawo masa, Wai Ina yallaban? Ko yana ciki kin Hana shi fita Dan Naga
yanda Kika cika din Nan nasan baya Wasa gurin zagaya gonarsa tunda ga yabanya Nan tayi
kyau da gani ana samun ban Ruwa akai akai".
Ta fada tana Kara wata dariyar.
"Wallahi Amah ki daina wannan dabi'ar Baki da magana saita wannan sabgar Kinga fita ta, Ni
idona da sauran kunya a cikinsa Banda tsabar jaraba a gaban Aunty safiyar kike fadar irin
wanna magana, Dan tsabar gulma da kinibibi kinyi alwala Amma Kika zauna Zaki Fara zancen
da ze karya Miki ita, wallahi mijinki yaga ta Kansa irin ku ne maza suke guduwa daga gida
saboda halinku".
Tana Gama fada ta Mike ta fice, wayar ta aje a Kan gadon.
Daukan wayar Amatullah tayi tana juyawa, ba karamin mamaki tayi ba da ganin wayar dake
hannun Zahra.
"Wai ba zakiyi sallar ba kema Naga da alama ma kin Manta zakiyi sallar in dai lamarin gidan
Nan ne bakiga kamai ba, I'm telling you in dai 'yan wannan family din ne, kinsan Allah duk
wannan Wasa ne ko ita kanta Mai gayya Mai aikin Batasan wa take Aure ba, kin manta na fada
Miki indai shine baze iya rayuwa da matarsa a wancen gidan ba?". Kai Amatullah ta gyada alamar haka ne, Bata iya tofa wata maganar ba saboda shigowar zahra.
"Au bakiyi sallar ba kenan? Gaskiya kina Wasa da sallah".
"Kema dai Kya fada Mata, gashi na baro baby na Dan ma tana cin Abinci shi yasa Honey Bai
takura min da Kira ba, suna cikin gari duka gidan Baba Dan lawan".
Tashi Amatullah tayi ta tayar da sallah.
Basu suka bar gidan ba sai bayan insha'i Shima Saida mijin Aunty safiyar ya Kira Dan bayan
sunyi sallar babin karatu Aunty safiyar ta budewa zahrar Dan idan ta Fadi wani abun rufe Ido
zahrar takeyi Amah na Mata tsinyar Wai muna furcine idan suka shige other room wata Kila ita
ke Jan sitiyarin motar ai tasan ba'a banza ba tayi irin wannan cikowar tasan ta gane garin. Sai a Nan Zahrar ke fada musu mahmud din ma baya kasar Yana India an Kai malaminsu
Asibiti ya samu matsala a bayansa. Sun jajanta sosai, mayuka da turaruka Zahra ta basu, Aunty
safiyar tayi mata Alkawarin kawo Mata wasu kayan Mata dasu tureren mara Mai fitar da oga
daga hayyacinsa duk iya yanda ya Kai ga kame bakinsa, Amma Bata fada Mata hakan ba tasan
halin kayanta sai taki amfani dashi.
Har gurin mota zahra da Aunty zilai suka rakosu, bayqn sun tafi ciki Zahra ta wuce wanka
takeso Dan ki take kamar ya Bata Mata jiki.
Basu Dade suna Hira ba Zahra taga Aunty zilai tana hamma sai tace Mata taje ta kwanta kawai
tasan har yanzu da sauran ramuwar barcin a idonta.
*********
Tun karfe shida na safe Mahmud ya wuce asibitin shida Mr salahuddeen, Saida ya jira doctor
din yafi son ya Gama da doctor din kafin yaje gurin Baba malam misalin bakwai da rabi doctor
ya shigo office dinsa be Jima da shiga ba mahmud ya shiga suka gaisa da yarensu na indianci,
sannan yayi Masa bayanin yanzu takwas dai-dai zasu shiga dashi suna tunanin zasu dauki awa
goma Sha biyu suna aikin Dan ma lakkar Bata tsinke ba. sallama sukayi ya nufi dakin da Baba
malam din yake.
Lokacin da suka shiga har an shirya Baba malam cikin Kayan aiki.
Murmushi ya fara yi da yaga mahmud ya shigo.
Da sauri Shima ya nufe shi Bai taba jin karaya ba irin ta yau daya ganshi kwance sandam babu
inda yake motsawa daga kugunsa zuwa kafarsa.
"Sannunka jarimin namiji, ubangiji yayi Albarka Mahmud ko yanzu Allah ya bani abunda bani
dashi da namiji, kayi min komai Babu abinda zance maka sai godiya, idan Allah yasa na tashi
falillahil hamdu idan Kuma lokacin komawar yayi to muna rokon Allah yasa mu cika da imani, ga
Zainabu Nan Dan Allah a kula da ita, ga Kuma makaranta Nan Daman yanzu ni suna ne kawai
na me makaranta, Amma kune ke dawainiya da ita, to kada a kasa ko bayan Mana Nan bamu
San abinda ubangiji ke nufi da kawoka gurinmu ba shiya barwa Kansa sani, a kula da ibada da
Kuma riko da gaskiya, Mai gaskiya baya tab'ewa kayi duk Mai yuwuwa ka koma mahaifarka
Dan girman Allah a rage fushi kaji mahmud bashi da kyau ko alama ka Zama Mai yafiya kaima
Allah ya yqfe maka kaji, Nima ka yafe min Zaman da mukayi Kona saba maka, Kuma ka
rokarmin sauran jama'ar da muka zauna dasu Suma a fada musu na yafewa kowa Nima su yafe
min, Abu na karshen da Zan fada maka ga yarinyar nan kaji tsoron Allah a Cikin lamarin ta
nasha yin istikhara Ina ganinka a Cikin wata irin wadata Wadda na kan samu kaina da tunanin
abun to duk yanda rayuwa ta juya ka kula da Amana ta Fadima marainiyar Allah ce".
Tunda Baba malam ya Fara Masa wannan magqngaun masu Kama da wasiyya jikinsa ke
tsuma daga ciki Yana ta faman rokon Allah akan ya rufa Masa asiri kada bawan Allahn nan aikin
ya Zama sanadinsa.
"Idon jajur da gani kukan zuci yake ya Kara rike hannun Malam.
"Baba in Sha Allah lafiya za'ayi aikin nan a Gama Kuma ka warke in Sha Allah saika taka da
kafarka ka zagaya Asibitin Nan Alfarmar Manzon Allah s.a.w.w, Allah ya baka lafiya yasa kaffara
ne ya bada nasarar aikin da za'ayi, ai sunce babu wata matsala Mai yawa dama mun zauna a
Nigeria anyi aikin". Kafin Baba malam ya fadi abinda yayi niyya ma'aikatan da zasu tafi dashi sun shigo da gadon
da zasu tura shi zuwa theater room din, lokacin da zasu canza Masa gado ya ringa fadin.
"Wash!!! Allah kuyi a hankali bayana bana son ana motsani" .
Da sauri Mahmud ya karaso Yana musu magana da yarensu, da sauri suka mayar dashi suka
fita.
Sannu kawai mahmud ke jerawa Baba malam Nan da Nan jibi ya rufe shi.
Kusan mutum bakwai suka shigo suka hadu aka Dora shi a gadon sannan suka tura shi a
hankali suka fice daga dakin mahmud na biye dasu, har kofar karshe mahmud ya raka baba
Malam Bai tsaya ba saboda dauriya kawai yakeyi Amma Yana Daf da zubar da hawaye.
Guri ya nema ya zauna Yana kallon yanda manyan doctors manya da kananu suke Kai kawo
kafin time ya cika suka rufe kofar.
Yana Nan zaune har kusan one hour sannan Kiran Habib ya shigo Masa.
Cikin dari dari Habib ya Fara fadin.
"Yallabai ya maganar zuwa Asibitin ne munji shiru baka fito ba tun bayan da muka dawo daga
sallar Asuba".
Tsaki mahmud yayi dama duk ransa ba dadi ga wani sabon salon da Habib ta tarka Wai
yallabai.
"Wallahi ka Kara kirana da wani yallabai sai munyi uwar watsi a kasar nan da Kai,ba dai ba
barci kuzoyi ba sai kuyi tayi, yanzu Baba malam ya samu good one hour a dakin tiyata, zaka
wani ce min maganar Asibiti,kaima wallahi inaga saina kaika Inda zaka Kwana a tsaye kana aiki
ko Abinci sai dai kaci a tsaitsaye sannan zaka fashinci namiji Allah yayi ka, ka fadawa dayan ya
kawo ku yanzu Ni tun shida Ina nan".
Ya yanke Kiran ya dafe goshinsa da yake Sara Masa.
* *
Karfe bakwai da rabi dai dai Mai a dai daita ya sauke Salma a kofar katafaren gate din
gidansu,kudin dake hannunta ta Mika Masa ta wuce da sauri ta shige ciki, ba kowa a harabar
gidan ko Mai gadi ma ya shiga sallar insha'i.
Wuf tayi ta shige part din Mama cikin sa'a babu kowa a cikin parlourn directly master bedroom
dinta ta wuce, can ta hango Mama ta Zuba tagumi tana zaune duk tayi zumu ba wannan gayun
da kwalisa, tunda ta rasa tudun dafawa a Kan sakon da za'a kaiwa Zahra ta shiga halin ha'ula'i
tunda Saida aka gindaya mata sharadi ta amince gashi kuma kwabarta na neman yin Ruwa. Ganin shigowar Salma ko sallama babu yasa Mama ta wani zabura ta taso tana fadin.
" Ke!!! Salma lafiya? Daga Ina kike da wannan tsohon daren? Ina Hameeda Kuma?".
Zama tayi a gefen gado tana sadda Kai kasa tayi shiru.
"Wai ba magana nake Miki ba Dan ubanki kin mayar Dani banza".
Kuka ta fasa Mata Mai cin Rai, Wanda ya firgita 'yar sauran nutsuwar Mama.
[16/02, 8:31 pm] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI*
08055362975
09061432330
MAMAN FATEEMAH.
Page 70.
.........…..
Luggage din da Zahra ta aje matar ta dauka tana fadin "taso mu shiga,wallahi nayi loosing
control dina ne wallahj abun ne da mamaki ban taba tunanin Zan ganshi a irin wannan lokacin
dana hakura na sallama".
Jiki ba kwari Zahrar tabi bayanta suka shige ciki, a zaune suka same shi, yaron yana lik'e a
jikinsa ya lafe sai Karamar da yake yiwa wasa tana balbala dariya Kamar ba yanzu ta Gama
tsandara kuka ba.
Suna shiga matar ta karasa inda ya zauna tana fadin.
"Yanzu ina alkwarin mu? Haka mukayi alkawari da Kai, ka bace bat a cikin duniya ka manta da
kowa? Ba waya ba sakon Email? Wallahi ka dauki Alhakin Ammi ba kadan ba, kasan yanda
Hajiya Inna ta rude kuwa? Abbie ma ba karamin tashin hankalin ya shiga ba, da farko ya dauka
fushin 'yan kwanaki ne Saida yaga tafiyar ta mik"a yasan da gaske ne, har nan ko ya taso
takanas ta kano, Wai yasan ko baka fadawa kowa in da kake ba yasan ni dole nasan inda
kake".
Hannu ya daga Mata.
"Pls Aisha Dan Allah ki rage surutu, kin bar yarinya a tsaye ki kaita daki ta huta kinsan long
journey din da tayo? Ki tayata shiga da kayanta zata nuna Miki abinku na Mata da bakwa iya
tafiya Saida tsaraba".
Wata harara ta wurga masa.
"Ai duk Kai ka jawo na manta da ita, sorry sister kinsan abin ne da al'jabi wallahi twins dina ne
yayi batan dabo a duniyar nan, nayi kukan rashinsa har naba uku Lada, zo muje".
Wata ni'ima Zahra taji tana shiga jikinta, sai lokacin ta Kare Mata kallo kamarsu Daya Dan dai
shi namiji ita mace.
"I am coming".
Ta fada tana haura stairs da sauri.
Tana bacewa ganinsu ya juyo Yana kallon Zahra.
"Precious".
Bata amsa ba Amma ta dago tana kallonsa kafin tayi magana Aishat ta sauko da sauri da keys
a hannunta.
"Muje ko bakuwa ni ko introducing dinki Bros Bai yi min ba".
"Kije ki rakata Mana tunda na kawo Miki ita ai magana ta Kare, diyar uban gidana ce Bata da
lafiya ne zataga likita, sannan malamina ma Yana Nan anyi Masa aikin spinal cord ne da sauran
fractures Daya samu.
Ya fada Yana fuskewa.
Daki ne comfortable yaji komai, na bayan more rayuwa.
Aisha Bata fita ba Saida ta Taya Zahra saka komai a muhallinsa sannan ta fito.
Zama Zahra tayi a gefen gadon tana nazarin maganganunsa, me yake nufi da diyar uban
gidansa, Amma zata raka shi taga iya gudun ruwansa Shima namiji ya iya danne abunda ke
ransa bare ita mace.
Aishar ce ta Kara shigowa da tray an dora snacks da Ruwa da drinks.
Da murmushinta ta karaso tana fadin.
"Ashe Fateemah ce, sannu da hanya zahra, ya jikin naki nagi Bros yace Baki da lafiya, Ni
Sunana Aishat Muhammad Dange, twins din Al-husasain".
"Masha Allah, Aunty nagode kwarai sannu da kokari".
"Lah ba komai, ki Sha ruwan kiyi sallah saiki fito lokacin an shiya muku abinci"
Sallar