Showing 6001 words to 9000 words out of 65935 words
Chapter 3 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf
Mai glass ta Shiga Daya part din da yake tasan wanancin lambobin kofofin
tunda duk sati suke zuwa da sauran yaran gidansu suna gyara bedrooms din kawai sauran
Kuma da masu aikin da sukeyi dakunan kwanan ne dai Batasan dalili ba masu aiki basa shiga.
Ko Ina tsit a gidan baka Jin komai sai kukan kananun kwari da dai daikun tsuntsaye ta gefen
inda zahrar ta kwana ta wuce da gaske ko ita data Saba da Shiga gidan wani lokacin tsoron
Yana kamata bare a irin Nan da sauri ta shige parlourn na uku ta wuce corridor da za sadata da
dakunan. Tana bude dakin zilai ta bude ta fito tana fadin "sannunku da dawowa, Dan Allah lafiya kuwa tun
rana sai Yanzu sha biyu ta wuce?'.
"Lah ba wani damuwa munje unguwa ne motar ta samu matsala sai dazu muka shigo garin
muka biya gidan mommy a can muka Shantake Sai Yanzu ya Sameer ya kawo mu".
Wani sanyi zilai taji a ranta, "to ai shikenan Allah huta gajiya da ko barci na kasayi ina ta tunani
barkatai".
"Kai haba ba komai Allah ya tashe mu lafiya ta bude kofar ta shige itama Zilan ta Koma ciki.
Tun bayan fitar Rukayya zahra ta dosana gefen ta zauna ta zabga uban tagumi, da sauri tashi
ta fito ta dauko handbag dinta ta biyo Hanyar da suka shigo kofar fitar ta murda tajita bam ko
motsi batayi, tayi tayi taji kamar tana taba dutse, hakuri tayi ta juya sai lokacin tsoron ya rufeta
da gudu ta shige dakin tana turo kofar, dube-duben makulli kofar ta Farayi ita dai bataga gurin
wani key ba har zata hakura taga wasu numbers a jikin wani Abu kamar switch din kunna wuta
numbers din ta Danna Yanda suke a jere taba taba ta karshe taji want Dan sound daga jikin
kofar handle din ta Kama zata bude taji ta rufe gam, sai lokacin ta Dan samu peace of mind, ta
nufi gadon ta aje jakar a gefe ta nufi toilet dole saita sake gyara jikinta. Tana Shiga ta cire rogar
material din sajida data sako ta taho da ita ruwan zafi ta hada tayi wanka ta fito da towel a
jikinta sanin ba wasu kayan sakawa a Nan yasa ta Haye gadon daga ita sai towel ta rage
hasken dakin ta janyo lallausan bargo ta rufe jikinta sai fuskar kawai ta Bari a hankali ta Fara
Addu'oin kwanciya barci, kafin ta Gama barcin yayi awon gaba da ita.
Karfe Daya da rabi daidai jirgin Max air ya sauka da duban jama'a daga kasahe daban daban
na duniya, cikinsu harda Muhmud Muhammad Dange, a hankali yake tako stairs din jirgin sanye
yake da kananun Kaya Ash T- shirt da black jeans a jikinsa sai jakar laptop dinsa a kafadarsa.
Yana karasa saukowa wani matashi fari marar jiki ya nufe shi Yana fadin "barka da sauka
yallabai, ga key din motar Nan a hannunta oga yace na kaika gida, sai Balarabe ya bimu da
wata motar sai mu dawo tare dashi".
Hannu ya mikawa Mai bayanin Yana fadin "bani key din kawai kace masa na gode kwarai da
kulawasa, zanyi driving da kaina".
Mika masa Yana fadin "Allah ya tashemu lafiya kayi min godiya sosai ya Ciro kudin America ya
mika Masa sannan ya bar gurin.
Lokacin Daya fito daga airport din Daya da minti ashirin da bakwai, tuki yake cikin nutsuwa sau
biyu kawai ma'aikata suka tsayar dashi, har yazo gate din gidan ba Wanda ya Kara tsayar
dashi, sau Daya yayi Horn Mai gadin ya falfalo da gudu yana leken waye a Nan baisan motar
ba Dan haka ya koma ya dauko abinda ze Bashi kariya. Kafin ya bude ya fito, Mahmud ya fito ya harde hannusa a kirjinsa ai Mai gadin Yana ganinsa
yayi sauri ya koma da gudu Yana Fadin "barka da sauka fari Mai farar Aniya Allah ya Kare
gabanka da bayanka baya Mai goya marayu"
Dan murmusawar Mahmud yayi Yana fadin "wani Abu sai Malam Musa shi Babu ruwansa da
dare". Ya fada Yana kunna Kai harabar gidan wadda take kamar rana, mutane hudu ne suka
bullo daga mabambantan gurare. Parking lot suka nufa sun San Mai gidan ne tunda suka jiyo
hargagin Malam Musa. Shima da gudu ya karaso gurinsa Yana cigaba da Yi Masa kirari. Sun gaisa sosai dasu har kusan minti biyar sannan yayi musu sallama Saida safe ya nufi
babban part din, Murtala ne yayi sauri ya sameshi "yallabai Ina ganin madam din kamar tana
can sabon gurin can Dan Nan Naga Sameer ya ajesu dazu ita da Rukayya kanwarsa, can ya
nufa Yana mamakin me yasa Sameer ya kaita can alhalin yace a barta a tsohon part din.
AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH.
Page 44
_________ kamshinta ya Faraji Yana shigowa parlourn, wani limshe idanu yayi Yana ayyana
abubuwa da yawa a ransa, direct ya wuce bangaren bedrooms din Yana jinsa cikin nishadi,
wato Sameer Yana expecting dinsa ne a kasar shi yasa ya bude Mata nan kenan, a hankali ya
taba handle din kofar farko ya jita a bude Shiga yayi komai tsab, iska ya huro daga Bakinsa ya
aje jakar laptop dinsa a Kan sofa da take dakin, ya zauna a gefe Yana cire takalman kafarsa,
wanka yake son ya Fara kafin ya Shiga gurin waccen danger girl din "yar yarinya ta Hana shi
sakat duk ta birkita Masa Lissafi" ya fada a fili Yana rage kayan jikinsa.
Wanka ya shiga bai wani dauki dogon lokaci ba ya fito saboda dare ya Fara nisa ga gajiyar
zaman guri daya, pyjamas ya saka masu kalar sky-blue ya fesa turarensa ya dauki wayoyinsa
ya fice daga dakin ya nufi dakin da zahrar take, wani Abu ya taba mai Kama da socket din
electric na kunna wuta sai kofar ta bude,a hankali ya shige Yana Jin kamshinta yanda ya cika
dakin, shi dai yawanci duk matan da suka zamar Masa dolensa suna bala'in son kamshi, yana
ida shigowa kofar ta rufe Kanta Wai Abu ya taba ba Wanda zahra ta taba ba, yayi gaba Yana
nufar gadon inda ya hangeta ta kudundune cikin bargo, da gani a tsorace tayi barcin, wayoyinsa
ya aje a Kan bed side ya zauna a gefen gadon Yana Kare Mata kallo, shifa duk hankalinsa ba a
kwance yake ba tunda aka fada masa matsalar dake damunta yaji ba shida sauran nutsuwa
idan ba zuwa yayi ya ganta ba, Kuma Dole ma yasan abinyi akan ciwon Nan ko ana Wasa da
wasu lamuran Banda lafiya baik'i tasan kowaye shiha a wannan lokacin dole ya dauketa ya
kaita inda za'a dubata Masa ita duba na gaske.
Remote din AC ya dauka ya rage gudunta dakin yayi sanyi da yawa duk da Yana son sanyi
amma wannan yayi yawa, a hankali ya saka hannu ya janye bargon daga fuskar ta barcinta
takeyi shower cap din dake Kanta ta cire sai gashi Baki sidik Yana ta walqiya a cikin Dan
hasken data Bari a dakin, Kara zame rufar yayi har zuwa kirjinta jikin sai wani glowing yakeyi Jin
sanyi Yana shigarta yasa ya juyo da fuskar ta inda yake zaune "ya Salam". Ya fad'a a hankali,
gani yayi ta Kara yi Masa wani kyau na musamman, Kare mata kallo yayi yaga daga ita sai
towel a jikinta, murmushi yayi da gani Batasan da Kaya a dakin ba.
Kayan jikinsa ya cire ya Zama daga shi sai boxer short ya shige jikinta ya janyo lallausan
bargon ya rufesu Yana sauke ajiyar zuciya, a cikin barci taji an rungumeta gaba dayanta jikinta
ne ya dauki rawa shikenan tasan tata ta Kare shi yasa suka nemota da tsohon dare suka
kawota Nan Yan ko wane irin ihu zatayi ba Mai jinta, cikin murya Mai rauni tana cracking ta Fara
farin "innalilllahi na Shiga uku wayyo Allah na....
Bata katasa fadin abinda tayi niyyar fada ba taji yace "shittt...Ni ne fa cool down precious ba
abinda ze sameki a cikin gidan Nan sai ikon Allah, akwai kyakykyawan tsaro".
sansanyan kamshin turarensa ne ya shiga hancinta, kokarin kwace jikinta takeyi Dan yayi
Mata kane-kane so take taga zahirinsa Amma ya Hana hakan, ita mamakinta Daya yaushe
yazo garin kuma ta Ina ya shigo Dan ita dai tasan ta rufe kofar nan. Dai dai kunnenta ya saka
Bakinsa "ki kwanta muyi barci na gaji da yawa kin hana duniyata kwanciyar hankali kina min
kisan mummuqe ko wayar ma kin haramta Mana yinta, tunda Naga alama Nima Mai laifi ne". Ya
fada yana shafa gashin kanta zuwa bayanta, hannu Daya yasa Yana zare towel din data daura
a jikinta da sauri ta rike tana girgiza Masa Kai.
"Dan Allah ka Bari bafa kyau muyi barcin to".
Wani guri ya taba a jikin gadon wasu irin fitilu suka Kama kamar star masu haske sosai, Bata
ankara ba ya fizge towel din gaba Daya daga jikinta Yana Mata wani mayen kallo hannu tasa ta
kare kirjinta cikin matsananciyar kunya tace Masa "Dan Allah ka kashe hasken Nan wallahi
kunyarka nakeji". "Ni kike Jin kunya?"
Kai ta gyada Masa, 'Well done Yanzu kuwa Zan cire kunyar nan daga idonki".
Wani bed sheet data gani a gefen gadon ta janyo da sauri ta lullube jikinta dashi tana Kara
sadda Kai kasa Dan da gaske ya saka taji kunya sosai.
Wutar ya kashe ya matso sai Jin mutum tayi ya shigo cikin Bedsheet din data rufa dashi ya
hanye shi ya maye gurbinsa da lallausan bargon.
"Ki hanani Zama a gurin neman abincina sannan na dawo ki Kama guduna, ai impossible
wallahi muyi barcin da safe mayi bayanin".
Ya Kara mannata a jikinsa suka samu body contact da kusancin zahiri.
Sun jima yana sarrafata.Tayi laushi iya laushi dan da gaske da kishirwarta ya shigo garin tamkar
mayunwacin Zaki badan tana cikin rashin tsarki ba da Babu abinda ze Hana labarin sauya salo,
dan tuni ya wani manta da Alkawarin da ya daukarwa Kansa, Saida tafiya tayi nisa ya ji abinda
yayi Masa cikas Dole ya saurara Mata, sun kai kusan karfe uku da rabi a haka shi Mai fad'ar
barci ya keji sai gashi ya bige da Hana Mai barcin yin Bata barcin.
Sai sauke ajiyar zuciya suke su duka har lokacin hannunsa Bai daina shafe shafe ba, wani irin
yanayi jikinta keyi har mararta ciwo ta Dan Fara Mata cikin dashashshiyar murya mai dauke da
salon shagwabar da Batasan iya ba,ta kankame Shi jikinta na wata irin tsuma muryarta ta dishe
tamkar me yin mura ta Fara magana. "Dan Allah ka bari wallahi marata ciwo takeyi...".
Baiyi magana ba sai kakkameta da yayi kamar ze shige jikinta shima ya hade bakinsu Yanda ba
Yanda za'ayi ta iya furta wata maganar ba, hannunsa ya tura Yana shafar marar ji yayi tadan
tasa kamar ta Dan kumboro, hannun ta rike tana girgiza Masa Kai.
Zare hannun yayi ya dawo dashi sama yaci gaba da sabgarsa ya Kuma ki sakin bakin da zatayi
korafin, suna haka har wayarsa ta Fara rera kiran sallah.
A hankali cikin muguwar kasala ya saki bakinta yana Maida numfashi da sauri da sauri gefe ya
margina Yana dafe da tasa marar idanunsa a rufe, Zahra naji ya raba jikinsu ta Kara takurewa a
cikin bargon wani irin tsoro ne ya lullube ta da gaske yazo Mata da wani lamari Mai girma, ita ai
ko idanu bazata yarda su hada ba ai da kunya wallahi duk yabi ya tsorata tas ya lalube ko Ina
na jikinta, Ashe can baya Wasa ne kawai yayi Mata yanzu ne ya nuna Mata true colour dinsa
tana ganinsa salihi Dan bawan Allah Ashe shima guda ne ba gyale ba, kirjinta sai zogi da ciwo
sukeyi mata yayi son ransa da jikinta.
Tana jinsa ya tashi ya shige toilet ya jima tana jiyo motsinsa, sannan taji ya fito alamun
tsayuwarsa taji a Kanta,a hankali ya saka hannu ya janye bargon kankame jikinta tayi Dan daga
ita sai pant Kare Mata kallo yakeyi take yaji alwalarsa na neman warwarewa, laimar hannunsa
ya Dan yarfa Mata a jikinta "wash...Allah na!". Mayar Mata bargon yayi ya shige clothset din dakin jallabiya ya sako Fara tas da hula
mahadinta raka'atanul fajri yayi, jikin gadon ya matso ya Dan zauna "zanje masallaci".
A dawo lafiya tayi Masa tana kudundune Yanda take, tanaji ya fice daga dakin.
Sai ta tabbata ya Kai masallacin sannan ta yunkura ta tashi ta nufi toilet, tsabtace jikinta tayi
sannan tayi wanka ta fito,lotion din data gani ta shafa sai body mist na itacen sandal wood Dana
oud ta hada ta fesa kayan da zata saka ne ya zama cikas Dan bazata iya mayar da Wanda ta
cire ba Kuma bazata Kuma Zama da towel ba tunda taga abinda hakan ya janyo Mata,
Shawarar duba clothset din tayi idan taga Kaya sabo Kona waye zata saka, tana mamakin ace
Mai gidan Nan bashi da Mata Kuma ya sakarwa abokai irin haka baya gudun a ring aikata
fasadi a cikinsa, were Dan wannan sai ka shekara a ciki ba'asan kana nan ba.
Ba karamin mamaki tayi ba ganin kayan Mata masu yawa har Sunfi na wancen apartment din
ba wani d'ar undies ta saka ta saka doguwar Rigar material Bata daura Dan kwalinba wasu
hulina na Mata ta gani da yawa ta duba kalar ash irin flowers din jikin material din ta saka a
Kanta, barci takeji sosai Dan tunda Allah yasa ya tasheta da aalonsa Bata Kara rintsawa ba
shiko gogan Allah besa an raba barcin jiya dashi ba.
Harta juyo zata bar gurin taji tana son ta bude dayan side din, kayan make up ne dasu turarika
shoe and bags turaren ta dauka tana dubawa duk yawanci irin nata ne sai wasu irin nasa ga
Kuma kayan maza nan Lodi Lodi dasu underwears tana tsayen tana dubawa taji kawai an
rungumota ta baya, ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe ido Sam bataji alamun bude kofa ba ko
takun tafiyarsa, Kansa ya Dora a kafadarta Yana Dan hura Mata iskar Bakinsa a kunne "Good
morning my previous".
"Morning Yayana".
Ta fada da wani salo, juyo da ita yayi suna facing din juna.
"Bude idonki ki kalleni ki fada min waye yayan naki? Wato har yanzu da sauran Rina a kaba
kenan ko? Nifa bazaki tauyeni ba Ni ba wani Yayanki bane a bani special name Dina, kodan
kinga mu 'yan gargajiya ne "ya'yan Alarammomi Malam soro, bamu da wayewa irin taku ko?"
Batasan lokacin data sauke ifanunta a Kan nasa ba, tana jinjina maganarsa.
"Wayewar saita kasheku".
Tayi subul da baka ta fada harga Allah a zuciyar ta tayi niyyar fada bakinta ya subuce ya fada.
"Kai! Nine wayewar saita kashemu to nida waye zata kashe din?"
Kauda Kai tayi tana Jin kunyar maganar.
*Ni ba haka nake son fada ba Bakina ne ya furta hakan".
*Ok, zomu kwanta barci nakeji tunda kin hanani barci da fitinarki".
Rigar ya zuge zif din ya cire mata ita ya barta daga ita sai undies kawai ya dauketa can ya nufi
bed din da ita tana mutsulmutsultun ya sauketa ya kiya Saida ya dangana ta da saman bed din,
shima jallabiyar ya zare ya janyota ya lullubesu da gaske barcin za'ayi Dan tunda ya sakata a
jikinsa Bai Kara yi Mata komai ba.
*** *** ***
Tunda Ammi tayi sallah Bata Koma barci lazimi ta zauna tana yi amma zuciyar ta Babu dadi
kwanan nan kusan Kullum sai tayi mafarkin Mahmud da wata yarinya budurwa Yana rike da ita
da hannu Daya dayan Kuma Yana ta faman fada da wasu irin halittu mara kyawun gani, to yau
ma shita Karayi Saida taga wasu mutane dattijai guda biyu sunzo sun Taya Shi kashe
wadannan halittun sun tasa su shida yarinyar har wani gida sai da suka shige sannan suka juyo
suka tafi.
A haka Mai gidan ya sameta Saida ya zauna ya Kare Mata kallo yasan da akwai damuwa a tare
da ita sai dai tana kokarin biyewa.
"Ammin Yara me yake damunki duk kwanakin Nan Baki da walwala Sam ko kula dani ma tayi
baya ko Baki huce bane har yanzu?".
Kai ta girgiza "A'a kawai dai lamari Hussain ne yake damuna kofa da Rana Daya Bai taba
kirana ba ko sako ta email Bai taba Yi min ba, gashi a kwanakin nan sai wasu irin mafarkai
nakeyi dashi marasa dadi abinda yafi tsaya min a Rai Kullum da wata yarinya budurwa kamar
'yar India nake ganinsa da ita Ina tsoron wani Abu wallahi na rasa yanda zanyi Dan Allah kayi
wani Abu akai".
Sai hawaye sharrrr.
"Subahaballahi! Haba zainab ya Zaki ringa yi Masa kuka kinsan masifar zubarwa da d'a hawaye
kuwa ko wani abun yake aikatawa ai saiya karu idan kina Masa kuka, addu'a zamuci gaba da Yi
Masa nifa jikina Yana bani Yana Dubai Dan last week na samu leakage akan Yana can din Dan
yayi wasu ziyarorin bazata a can harya dakatar da wasu ma'aikatansa sai dai duk kokarin a
gano min masaukinsa sabo hakan yaci tura Dan ba'a inda yake sauka ya sauka ba tunda gudun
hijira yayi".
Hawayen ta goge ta tashi tana ninke sallayar ta zauna kusa dashi. "Shikenan Allah ya shiga
cikin lamarin ya kureshi daga sharrin zinace zinacen zamani wallahi badan komai nufin Allah
bane Wanda yaso yake bawa kyautarsa danace dama bashi ya samu wannan budin ba da
kananun shekaru to yanda yaso haka yake tsara kayansa, Amma ga yayunsa Nan ba Wanda
ya takura musu Suma ai suna da wadatar,tunda Allah yayi muku karfin arziki waye talaka a cikin
family din nan?".
Dan murmushi general yayi Yana kallon yanda take fadin magana abinda ba halinta ba inda
akan twins ne sai dai wani yayi magana Amma ta zage tana fadin son ranta.
"To ya zamuyi da hukuncin Allah shi yaso ya daukaka a cikin zuri'ar da Wanda ya Isa yace a'a
Ina cewa