Showing 39001 words to 42000 words out of 65935 words

Chapter 14 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf

03 Aug 2025

1491

zahra tayi ta Jima tana addu'ar neman mafita daga wata sabuwar rigimar da take
hangowa.
Nan Kan sallayar ta Dan kwanta barci yayi awon gaba da ita.

****
Zaune suke Yana cin abinci ita Kuma tana duba sakonni whatApps har zata wuce salon Faisal
saita dawo saboda Basu fi minti goma da Gama ways dashi ba Yana Mata magiyar ta turo da
kudi suyi sarin Kaya, ta nuna masa ya jirata zasu shigo ganin jikin Abban nasu sai ayi abinda ya
kamata, sai Kuma wata zuciyar ta kwabeta akan ta duba ita me majiyyaci ai share sako ba nata
bane.
Ta maimaita karanta sakon ya Kai sau biyar tana ganin kamar ba gaskiya bane.
Dialing din number Faisal Aunty Surayya tayi, Yana dauka Bata jira komai ba ta jefa Masa
tambaya.
"Shin text din daka turo min gaskiya ne".
"Eh wallahi Aunty ko jiya ma yazo gurin Abba mantawa nayi na fada Miki bakiga yanda yake
kula da Abba ba kinsan har daki ya canza Mana mantawa nayi na fada Miki ayi Mana godiya
gurin Auncle Mustapha".
"Ok shi kenan ina zuwa".
Ta fada tana yanke Kiran.
Auncle Mustapha ta juya tana kallo Wanda Shima ita ya zubawa idanu, batace Masa komai ba
sakon ta bude ta Mika Masa.
Yana Gama karantawa ya dago da sauri yana neman Karin bayani.
"Nima shine na Kira Faisal din ya bani tabbacin haka ne, Wai ya Kai wani Babansa ne".
Spoon din ya aje ya mike ya zari hularsa da key din mota ya fice, Surayya na Masa magana
hannu kawai ya daga Mata yayi gaba.

Duk yanda Aishat taso mahmud ya Bata hadin Kai suyi magana ya Kiya yace ta Bari sai dare
zasu zauna suyi magana sosai.
Abincin ta shirya a table ta nufi dakin da zahra take, samu tayi barci ya dauketa a saman sallar
da tayi sallah, Bata tasheta ba dawowa tayi tana fada Masa tayi barci da alama ta gaji.
Shida Abulkhairi sukaci abincin, yayin da Aishat ta dauki Afnan Wadda tayi barci ta haya da ita
sama.
Kamar jira ake ta shiga bedroom dinta Kiran sweet heart ya shigo.
Tana dauka ya Fara fadin.
"Sweetie Ina Mahmud din yake Dan Allah?"
Saida taja fasali sannan tace Masa.
"Yana down stairs, wallahi sweet heart kamar Almara nake ganin abin duk na rude Dan Allah
kazo kada ya Kara tafiya... Yace matukar na fadawa Abbie ko Ammi Bazan Kara ganinsa ba".
Ta fada tana share hawaye.

"Cool down your temper my sweetie Babu inda zaya, ban tsoro ne kawai yake miki yasan idan
yayi Miki haka bazaki fadawa kowa ba, ki jirani zuwa gobe da safe in Sha Allah, ki daina yi min
asarar hawayenki a banza, a gurina suna da mahimmanci , ki kyaleni dashi yanzu basai an
Jima ba zanyi informing din Abbie gara ayita ta Kare tunda shi Abu baya wucewa a gurinsa".
"Gaskiya dai Kam ki shiga cikin Lamarin kuyi Masa taron dangi, kasan da wata yarinya yazo
Wai 'yar gidan uban gidansa ce ya kawota Asibiti, nifa I doubt much akan yarinyar Nan kasan
dai halinsa baya sabga da macen daba muharramarsa ba ya kake ganin ze dauko yarinya
mace kamar wanna ka ganta kuwa? Allah Ina Jin ta hada iri da Larabawa Dan she is very
young and beautiful".
"Just ka bishi a yanda yake so idan na shigo zamu Yara da yaren garinmu rabu dashi".
Basu wani Dade ba yayi Mata sallama Yana Kara kwantar Mata da hankali akan tunda ya kawo
kafarsa har gida in Sha Allah komai yazo karshe.

A mota uncle Mustaphan ta karaso gidan duk da babu nisa Amma sai yaga idan yace ze tako a
kafa kamar baze zo ba.
Directly part din Ammah ya nufa Don baya son maganar ta fita tun kafin su tabbatar da abunda
aka fada, very lucky ya samu yayan nasa general a part din.
Batool ya bude Masa kofa ya shigo tana gaishe shi.
Ya amsa Yana fadin.
"Ina Abbie Amminku take?".
"Tana part din Abbie na cikin nan".
Ok, Bari na kira shi"
Ringing Daya ya dauka Yana fadin.
"Ko Ina kake Mustapha maza kazo Ina son ganinka ina kokarin kiranka naka Kiran ya shigo".
I
"To ai gani a part din Ammi Nima neman ka nakeyi".
Ya fada yana nufar kofar baya yabi corridorn da ze sada shi da part din General din".
Yana shiga da sallama a bakinsa yayi turus ganin Ammi tana shafe hawaye, a sanyaye ya
karasa cikin parlourn.
"Lafiya! meya faru?".
"Zauna Mustapha yanzu ne Abbas ya kirani daga Jamaica inda yaje aikin da nake fada maka,
wai Aishat ta kiwo shi ga Dan uwansa yazo Yana tare da ita".
Neman guri uncle Mustaphan yayi Yana tabbatar da gaskiyar maganar Faisal.
"To ai Nima abinda ya tasoni kenan na taho, kasan Alhajin su Surayya Yana can Indian an sake
Masa gyaran kafa shine suka hadu da mahmud din yaketa dawainiya dasu shine ya fadawa
surayyar tayi min godiya kasan ba kowa ne yasan case din da ya faru ba kawai dai an wayi gari
ba'a ganinsa duk da zancen duniya baya buya nasar Surayya Bata fada musu komai ba
gaskiya, Ammin Yara ki daina kuka ko lokacin da ake cikin tashin hankali ba Wanda yaga
hawayenki sai yanzu da asking ya I gaban gashi".
Share hawayen tayi tana fadin "
dole nayi kuka ni kadai nasan dacin Dana ci a lokutan baya da dararen Dana Raya akan
ubangijina ya dubi Lamarin yaron nan ya juyo min da hankalinsa gida".

"To godiya ya kamata ki yiwa Allah Daya amshi addu'ar ki ba kuka ba".
Wani murmushi general yayi yana duban Mustapha.
"Ni bansan lokacin data aje karar 'ya'yan fari ba da ko me zakayi musu Bata daga Kai ta dubeka
amma yanzu dibi yanda take Kora bayani Kamar ba ita na".
"Kan barta tayi Yaya ai taking jarunta ma ba uwa duka ba, yanzu Yaya kenan za'ayi? Da nida
madam zamuje next week amma dole mu raba tafiyar a yau Zan shiga neman visa ko nawa
Zan bayar saina samu nan da jibi in Sha Allah Zan tafi Indian Zan kadi shi mu taho gida da
izinin Allah. Amma dan Allah kada a fadawa Hajiya Inna wallahi idan taji cewa zatayi kafarta
kafa ta".
"Kaje kayi shiri zanyi magana akan visar taka, ka Zama cikin shiri kawai".
Tashi Ammi tayi ta shiga ciki ta barsu suna tattaunawa akan Lamarin.

*****
Saida zahta tayi barci Mai isarta sannan ta tashi, wanka ta shiga tana fitowa lokacin magariba ta
kusa kawo jiki, tayi mamakin dogon barcin da tayi.
Lotion kawai ta shafa sai roll-on da tasa sure sai body midt da normal turaruka da take amfani
dasu designers na kamfanin Alharamaini, rigar atamfa ta saka simple style A shape ta yafa
Karamin gyale sai tayi wani sansanyan kyau, a hankali ta bude kofar ta fito tana takunta gentle
ta shigo parlourn Aishat ta gani a zaune da Abulkhairi a gefenta tana koya masa homework,
kafin tayi sallama har sansanyan kqmshinta ya jewa Aishat.
Dago Kai tayi tana amsa sallamar da Zahra tayi.
"Masha Allah!"
Abinda Aishat ta fada kenan Dan babu karya yarinyar ta hadu ta ko Ina macece ga asalin kyau
Dan gaske, murmushinta Mai kayatarwa zahra tayi Mata tana fadin.
"Sannu da hutawa Aunty".
Hannu Hanan ke dagowa Zahra tana zillo daga cinyar mamanta.
Daukarta tayi tana Zama daga dayan gefe Kan wata kujerar.
"Yauwa sannu, Zahra ko?"
Kaita gyada Mata alamar eh.
"Kinsha barcin gajiya, ga abincinki can Kan table muje kici kin kwanta da yunwa, bro yace na
fada Miki yaje Asibiti sai dare ze dawo".
"Ok, nagode kiyk zamanki Bari muje da 'yar gidana Aunty ki bani ita Dan Allah Ina sonta".
Dan murmushi tayi idan mijin da Zaki aura ya amince ki dauka Ni tawa Mai sauki ne na Baki".
Gaba tayi tana dariya kasa-kasa ta nufi dining din save da Afnan.


Sun Dade suna Hira da Aunty Aishat har barci ya Fara Kama Zahra sannan tayi Mata sallama
ta nufi inda akayi Mata masauki, bayan ta wuce Aishat da Dade tana auna Lamarin Zahra a
zahiri Sam batayi Kama da yarinya marar tarbiyya ba ko masu budedden idanu Amma tayiwa
tafiyarsu da Dan uwanta Question mark, idan ta tuna da irin warning din da yayi Mata kafin ya
bar gidan.
"Gata Nan amanace a gurinsa shi yasa na kawo ta Nan inda zata zauna safe, ki kula sosai
nasan halin sayyid a Kan mata duk da kince yayi tafiya to Koda za'a samu akasi yazo bana nan,

to ki fada masa yarinyar nan da mijinta Dan muna komawa za'ayi bikinta ya dauke idonsa daga
kanta idan Kuma ba haka ba za'a iya samun matsala.
"Maji ma ganj, an binne tsohuwa da Rai"
Ta fada a fili.
A Nan taci gaba da Zama tana jiran ta inda Dan uwanta ze bullo, wurin Sha Daya da minti goma
ya bude ya shigo gidan, ya yi mamakin ganin Aisha Ido biyu.
"Ashe dai Hali yana nan, yanzu Dan Allah bakiyi barci ba".
"Naka wasa ne kana tunanin Zan iya barci banji komai daga gareka ba Nima ban Amayar maka
da abinda ya faru bayan baka nan ba".
"To ai shikenan Bari nayi wanka na fito inaga kwanan zaune zamuyi yau".
Ya shige ainihin dakin da yake sauka idan yazo wani aiki kasar bata yarda ya sauka a hotel ko
Daya daga cikin gidajensa, inda Allah ya taimakesu Abbas Dan kanwar Abbie ne Kuma sa'anni
suke da yayunsa gashi tasu tazo Daya da mahmud sosai Dan kusan tare suke aiwatar da
ayyukan kamfanonin Abbie. Bai Dade ba ya fit Yana baza natural kamshinsa ya zauna yana fadin hada min coffee sai zance
yafi tafiya dai dai".
Ta tashi ta nufi kitchen tana fadin. "Bari na hada coffee maker yanzu na kawo maka".
Tashi yayi ya nufi dakin da Zahra take, a hankali ya tura kofar a kwance a tsakiyar bed din ya
hangota da wayar ta a yashe a gefe da gani batasan lokacin da barci yayi awon gaba da ita ba.
A hankali ya tako har gaban gadon Yana Kare Mata kallo a cikin dim light din dake dakin, Dan
sunkuyawa yayi daidai lips din ta ya Bata light kiss ya shafa gashin kanta a hankali, wayar ya
dauke ya Dora Kan bed side ya gyara Mata blanket din ya rage karfin A/Cn ya tofa Mata Addu'oi
ya ja Mata kofar ya fice yana Jin wata irin kewarta. A tsaye ya samu Aisha da kallon tuhama ta bishi, yana kallonta Sarai yayi Mata fuska.
"Bani idan ya Zama ready".
Ya fada yana Mika Mata hannu.
Kada hakuri tayi ta kalleshi idi cikin ido.
"Wai wacece wannan yarinyar a gurinka? Kuma meye dangantakarka da ita Naga ka shiga inda
take alhalin ba muharraminta bane Kai?".
Ta fada tana tsare shi da Ido amma zuciyarta sai dokawa take Bata fatan abinda take sak'a
Mata ya kasance gaskiya.
"Ple Aisha zauna ki nutsu ki tambayeni duk abinda ya shige Miki duhu".
Bataki tasa ba zaman tayi tana Kara jaddada Masa tambayarta akan dangantakarsa da Zahra.
"Wai meye damuwar ki da ita ne na fada Miki 'yar uban gidana ce, daga haka me kike son ji
Kuma?"
Lokacin da suke wannan maganganun ita Kuma Zahra kishirwa ta tasheta Karamin fridge din
cikin dakin ta duba Babu ruwa a ciki Wanda Kuma Auntyn ta shigo Mata dashi dazu ya huce
bazeyi Mata dadin Sha ba. Kofa ta bude ta fito da niyyar zuwa kitchen ta dauko ruwan ta saka
ma a fridge din dakin, maganganu ta rinka jiyowa kasa kasa da farko har tsoro ya kamata sai
daga baya ta ringa jiyo maganar Mahmud ne da 'yar uwarsa.
Abinda taji ya masifar daga hankalinta.
"Na fada miki babu komai a tsakanina da yarinyar nan kina ganin Zan iyayin gaban kaina nayi
Aure ba tare da sanin iyayena ba? ki rubuta ki aje duk abinda Ammi ta yanke a kaina na karba

ita zata nemar min matar aure da kanta, idan kin tuna ta taba fada tayi min Mata a
Niger,Wadda har aka kawota tayi sati biyu a lokacin Abbie ya Hana maganar to yanzu zanje
natsuguna a gabanta na nemi yafiyar abinda nayi Mata Kuma ta zabar min duk wadda tayi Mata
Zan karba da hannu biyu tunda ni dai babu Wadda na gani ta kwanta min da sunan Aure, Kinga
gara ita ta zabar min da kanta"..
Ai jikin Zahra karkarwa ya fara me yake nufi duk abinda yake Mata pretending ne ba gaskiya ba
kenan? Da kyar ta Kai kanta dakin Dan tana shiga ta zube a kasa tana fadin .
Naga ta kaina Ni Zahra Ashe ni kadai nake kidin girbina bani da wata kima da daraja a idanun
Dan tahalikin nan?.
[19/02, 11:46 pm] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI*


MAMAN FATEEMAH.


09061432330
Or
09055362975


Page 71
..…....
Sai da Zahra tayi kukanta ta bawa uku Lada sannan ta share hawayenta tana hakurkurtar da
kanta, lallai irin wannan cin fuskar da ciwo ita meta rasa da yake gudun nunata a matsayin
matarsa? Wai 'yar ubangidansa, To ita Kuma zata Kama Kanta in Sha Allah ba Kuma zata
nuna taji hirar nan tasu ba. "Ya ubangiji ka shiga cikin lamarinta ka Bani hakuri da dangana bisa jarabawar da kake
jarantata da it's Dan isar fiyayyan halitta Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w.".
Ta fada a fili tana tashi daga inda ta zauna tana kissima abubuwa da yawa a wannan karo.
Amma dole ta nemi tudun dafawa dole ta iya Kanta tunda abun yazo da cin fuska har ze ringa
gudun hada kansa da ita.
Ranar barci dai sai barawo, kwana tayi tana nafilfili da rokon ubangiji mafita.

Bayan tayi sallar Asuba ta koma ta kwanta lamo batajin zata iya fadawa kowa wannan maganar
zatayi hiding din kayanta taci gaba da addu'ar samun mafita a gurin lillahil wahidul Qahhar ya
shiga duk lamuranta.
Da safe kin fitowa tayi har Aunty Aishat ta biyota daki, Tana ganinta Zahra ta tashi zaune tana
fadin.
"Ina kwana Aunty, Ina Afnan da Abul?"
"Lafiya kalau, ya bakunta Kuma? Afnan Kuma Bata tashi ba sai takai twelve tana barci in dai ta
farka da Asuba, shi kuma Babana ya tafi school"
"Ok. Allah sarki".
Zahra ta fada tana Dan Jan blanket din zuwa jikinta saboda yanda rigar barcin take sai a

hankali.
Dan zama Aunty Aishat din tayi gefen gadon.
"Ki tashi ki shirya kiyi break yau zamu shiga Asibiti a duba ki,tun jiya nayi Mana booking na
ganin doctor din, kinsan Hussein sai a hankali idan yaso Abu to babu sauki bare Naga ya dauki
lamarinki ba Nan kusa ba".
"Nifa Aunty ki fada masa na warke tun a Nigeria fa,na biyoshi ne kawai saboda na duba jikin
Baba Malam,Kuma wallahi azumi nakeyi yau".
Tsare Zahra tayi da Ido sai taga yanayin yarinyar ya canza ba kamar jiya ba, Amma dai batace
komai ba ta tashi tana fadin.
"Bari na fada masa".
Ta fice duk zuciyarta babu Dadi da gaske yarinyar tayi wani irin collapse Wanda Bata San
dalilnsa ba.
Tunda Aishat ta wuce yace duba tsadedden agogo Rolex dake hannunsa, shifa jiya da kyar ta
iya barci ba tare da ita ba a jikinsa sau uku Yana zuwa kofar yana jinta bam da key a rufe.
Sai Zuba Ido yake yaga ta bullo, Maimakon ya gansu su biyu sai yaga Aishat ita kadai ta dawo.
Kasa hakurin ta karaso yayi ya tashi ya nufi inda take.
"Tana Ina Kuma? Lokaci fa Yana tafiya nifa tun seven thirty na shirya".
Wani kallo tayi masa ganin duk ya wani rude.
"Tace ita babu inda zata ita ta warke, kuma da azumi ta tashi bazatayi break ba".
"What!! Bata da hankali ne? wane irin ta warke duka last week fa tayi ta fama da bleeding duk
ta daga min hankali, shine yanzu zata fadi haka, salon mu koma Kuma wata matsalar ta taso,
tasan halin Dana shiga a wancan lokaci Bari naje na sameta".

Ikon Allah Aishat ta tsaya tana kallo, lokaci Daya ya daga hankalinsa ya wani birkice, Wai me
taji Yana fada ne? Me kalamansa suke nufi idan ba Rami me ya kawo zancen Rami.
Da sauri ta rufa Masa baya duk ya wani susuce lokaci Daya ita ba taga abin daga hankali ba
tace Bata so Amma lafazinsa sun sakata a kokonto ba Dan kadan ba.
Da zafinsa ya Kama handle din kofar sai dai tayi locking dinta, a zafafe ya Fara dukan kofar
Yana fadin.
"Precious me kike nufi da baza kije Asibitin ba? kina son ki tayar min da hankali ne ko? maza
bude ki fito mu tafi tun jiya aka Gama komai".
Tsayawa Aishat tayi turus Jin kalaman da yake fada Wai ko ya manta a Ina yake ne?.
"Previousss...."
Ta fada a hankali tana girgiza Kai komawa tayi tunda Allah baisa ya ganta ba.
Ita Kuma Zahra tana jinsa yanda ya ambaci precious sai taji wani irin bacin Rai ya lullibeta wata
harara ta zabgawa kofar tana gunguni a ciki.
"Saina shayar da Kai ruwan mamaki saika karyata kanka da kanka Wallahil Azim, Ni Zahra nafi
qarfin cin fuska gurin 'yan uwanka saina saiwa kaina kimar daka Zubar min sai ka nunawa
duniya ni wani bqngare ce ta rayuwarka".
Toilet ta shige taba iska ajiyarsa.
Kasa hakuri Aishat ta dawo, Bata karasa inda yake ba daga dan nesa dashi ta tsaya tamkar a
yanzu ne ta biyo shi. "
"Wai menene na tada jijiyar wuya, tace bataso ka qyaleta Mana ba lafiyar jikinta bace, ka wuce

kawai Nima Ina son na shiga kasuwa saboda wasu Abubuwan amfanin sunyi kasa".
Wani duban Baki da lissafi yayi mata.
"Wai kinsan wahalar da Tasha kuwa, Kinga yanda ta daga min hankali kuwa? Kin..."
Ai baisan lokacin Daya ci wani burki ba shaf ya manta Aishat fa Bata San komai dake
tsakaninsu ba.

Tahowa yayi ransa a hade ta rufo Masa baya, Zama yayi ya dafe Kansa.
Daga sama ya tsinkayo maganar Aishat.
"Wai meya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login