Showing 12001 words to 15000 words out of 65935 words
Chapter 5 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf
ni kasan Mata Dan Abu kadan saiya
tada musu hankali, Daman bakuwar tata ce Hajiyar makwarari ce ta kirani bayan nabar Nan Ina
gidan mommy na mayar da Rukayya saiga kiranta Wai lallai saina daukota tazo taga madam
shine mommy tace na kawo ta indan ba haka ba zata iya rikita lissafin kasan halinta dai". "Ok ba damuwa ku shigo tare ai Hajiyarmu ce ba inda bazata shiga ba".
"Ok sir".
Ya juya ya fice daga parlourn da sauri,mamakin Mahmud ne ya kamashi sosai ya rasa wane irin
so yake yiwa yarinyar Nan ne haka? Yana tare da wannan mezeyci da wata Haseena ai saidai
tayi hakuri da can Bata you tasiri ba gurinsa ba bare yanzu daya Sami abinda ya kwallafa rain a
kansa. Zahra Jin Sameer ya fice yasa ta dago da kanta daga kijinsa tana ajiyar zuciya, Dan just tayi
kukan ta Kama nasa guri sai mamakin furucin oga Sameer daya cika Mata zuciya wai sir to me
hakan ke nufi itafa kada su manna Mata Dan karamin hauka gaskiya.
Dan Allah ka barni na tashi kaji fa Hajiya ce yace fa
Zata shigo, Kuma Dan Allah bakaji kunya ba ka wani sakani a jikinta salon yace bani da
tarbiyya".
Wani kallo ya watsa Mata "ai yau ko waye ze shigo gurin Nan a haka ze samemu gara asan Ina
sonki tunda kina ganin ba sonki nake ba har kina kallona kina fadin Wai matar shige ce ke idan
aka sameni rungume da kayana Ina lallashi kuwa koya saiya sheda ina son abuna, nine dai ba
Sona ake ba anfi son wannan Mai jan kamar karas tunda saboda shi aka yarfeni da bakaken
maganganu".
Har ta bude Baki zata bashi amasa taji rangada sallamar Hajiyar makwarari, ai ita kanta Bata
San yanda akayi ba ta tsinci kanta a tsaye ballentana shi da ake zaune a jikinsa, shi dai Sameer
Bai San lokacin da dariya ta kubce Masa ba ganin yanda Zahra tayi wani wuk'i-wuk'i da ita
shima gogan dariyar yake Amma a ciki.
Da sauri ta nufi Hajiyar tana fadin. Oyoyo -oyoyo ga Hajiyata ga Hajiyata".
"Ke tafi can Ashe duk abinda na fada Miki ta bayan kunnenki ya wuce Saida Kika fice Kika
barmu da tashin hankali, jiya kukan da nayi rabona da yin irinsa tun rasuwar mijina. Amma Kika
sakani maimaitwa Dan Allah ke kuwa 'yar Nan Ina Kika tafi jiya".
"Haba Hajiya Dan Allah haka mukayi da ke a gida kafin mu taho wato kin karya Alkawarin
kenan? To a kazarki ta juma'a wallahi"
Ita dai Zahra borin kunya ta Fara "Allah ya Baki hakuri nifa na fada Miki kawai dai yawan
mutane ya Hana ki gane waye yake Miki magana, Amma yaushe zanyi Miki haka Allah naji
maganar ki kinga yanzu ma Zan Sha maganin fa".
Mahmud ne ya taso Yana fadin "Hajiyar mu ki shigo ciki ki fada min abinda ba'a so na sani Zan
Baki abinda yafi kazar ma".
"Yauwa nasan kafi da haka, kanaji jiya ne wata daukakkiya ta tadawa yarinyar Nan hankali Wai
kome gareta a mahaifa bansan dai sunansa ba da yaren Nasara Amma dai da hausa muna ce
Masa tsiron mahaifa Wai sai tayi Mata tiyata,haka kawai ta ragewa zukekiyar 'yar Nan kwaliti yo
an yanka mutum tun baiyi haihuwar fari ba Ina labari, shine nace baza'a yanka ta ba ga magani
Nan Tasha na wata Daya in Sha Allah ze narke, ai sai daga baya Rakiya ke fada min ita waccan
din ta Dade tana sonka tun Kuna turai koba haka bane? Ja'ira taga yarinya danya Sharab zata
zauce tayi Mata illah to Banda abunka yaushe zaka ce buduwarka ta duba matarka ai wauta ce
babba, wallahi kada a Kara kwatantawa, shine fa yarinyar nan tayi Mana batan dabo tun
azzahar muka nemi 'yar Nan muka rasa nayi kuka kamar Zan yada idona to me zamu fada
maka daga kawo yarinya ace ta Bata a gidana wallahi in takaice maka labari sai goma Sha
biyun dare aka ganota ta Janbulo gidansu kawarta, itama uwar da yake ta kirki ce sai tayi tunani
ta Nemo uwarta a waya take tambayarta duk da tana gurinta ta haka akasan guduwa tayi daga
gurina cikin dare suka daukota to kaji yanda magana dai take".
Wani kallo ya yiwa Zahra Mai ma'anoni da yawa, sannan ya juya Yana kallon Sameer Wanda
tunda Hajiyar makwarari ta Fara zuba ya sadda kansa kasa yayi Dana sanin kawota tafi cikin
cikin masaki.
"To shike Nan in Sha Allah za'a kiyaye yanzu kiyi hakuri bata kyauta ba za'a duba korafin, nima
ita ta tasoni na dawo ba Shiri wallahi hajiya yarinyar nan rikicinta yayi yawa".
"To ai tayi mini dai-dai ashe jikar tawa tasan kanta zo Nan Yar albarka".
Gurinta tazo ta zauna a kasa kusa da kafarata tana fadin "Hajiya Ina kwana?".
"Lafiya kalau ya jikin naki?"
"Nifa yanzu lafiya ta kalau ba damuwar komai".
Shima Muhmud Zama yayi kusa da ita da gani da shakuwa Mai yawa a tsakaninsu.
"Hajiyarmu kwana biyu Shiru ko nemana bakyayi ko?".
"Kaji kinibibi ta Ina Zan nemeka bayan kayi gudun hijira".
Dariya ya kamayi har ya bawa Zahra mamaki Daman Yana dariya haka.
Tashi tayi duk da Batasan Kan gurin ba Amma tana tunanin kitchen ne a cikin corridor din dake
jikin dining area.
Babban tray ta dauko ta sako ruwa da lemo da Madara da plates ta dauko warmer din da aka
zuba pepper soup din turkey din ta nufo parlourn ta dire cener table dake gaban Hajiyar tana
fadin gashi Hajiyata ki Sha ruwa kafin nayi Miki girki yau fa a Nan Zaki wuni tunda oga ya dauke
min Aunty Rukayya ko sallama bamuyi ba". Inda Sameer din yake Hajiyar ta kalla "baka kyauta ba ai sai suyi sallama Mana kaga bataji
Dadi ba".
"Ai zata dawo tunda zamuje Azare Nan da jibi".
Zahra na son taji ba'asin za'a tafi a barta Amma ba hali Dan tunda suka shigo ta kasa had'a Ido
da Sameer da gaske ba karamar kunyarsa takeji ba.
Fita sukayi dare suka bar hajiya da zahrar.
Hira Hajiya ke Mata sosai tamkar sun shekara da sanin juna, taci Naman sosai Tasha madarar
tana fadin "irinta muke Sha a makka laban kuke cewa ko tunda Sameer yace min mamarki
balarabiyar Jordan ce ko?"
"Eh 'yar can ce".
"Ikon Allah ke Kuma Allah ya kaddaro naki mahaifin a wannan nashiya tamu, ai Sameer ya bani
labarinki batun yanzu ba tun lokacin da mijinki ya kaini jidda akayi min aikin Ido da yaga wata
yarinya diyar larabawa yake bani labarin ya ganki a jirgi keda wani mutum ko mahaifin ne ko
Kuma dai mariki ne basu ba, Saida za'a daura Aurenki yazo yake dauko min tsohon zancen
harna gane nace nasa a Ina suka laluboki yace min ikon Allah ne ya hada ku, daga Nan ban
Kara ce masa komai ba, Fadima ki rik'e mijinki da kyau Yana sonki yanda Baki zato tun Baki
San meye so ba yake Miki shi, kingan shi nan tun suna makarantar sakandire suke tare da
Sameer Bai yadda shi ba, da Allah ya daukaka shi saiya Kara janyo shi jikin shi duk inda ya
saka kafa Sameer yake aje tashi, duk abinda Sameer ya mallaka mijinki ne sila komu iyayensa
da kakanni muna cikin cin arzikin".
Zahra abin jinsa take wani bai-bai me hakan yake nufi ne wai? Ana nufin Mahmud ne
ubangidan Sameer ko me ake nufi? Lallai biri yayi kama da mutum duba da yanda suke rayuwa
a Nan daga lokacin da sukazo garin zuwa yanzu kusan umarni ne oga Sameer yake karba
kawai kasa hakuri tayi Saida ta tofa tata tambayar.
"Wai ni Hajiya waye Mai gidan nan ne? na Ya Sameer ne? ko kuma na wani abokin nasu ne?
Naga ya sakar musu ragamar ko Ina na gidan Baya tsoron abinda zeje yazo,nifa tsoro ma yake
bani kamar baza'a mutu ba gaskiya ya mayar Dani gida inda nafi wayo, anan mutum saiya
shagala da duniya wallahi". Baki Hajiyar ta rike tana yiwa zahra wani kallo.
"Amma yarinyar nan lamarin ki da sauran gyara, gidanwa ze daukoki ya kawo idan ba gidansa
ba, yo wannan ai Bai kama kafar gidajensa na sokoto da Abuja ba, ni duk naje Kinga na
Abujan,? ganin likita naje lokacin Ina ciwon kafa, na sokoton Kuma bikin kanwarsa wadda take
a can Germany mukaje, wannan mutane da karamci suke, gashi kinyi sa'ar suruka Hajiya
zainab Bata da damuwa ko kankani" .
Tsai Zahra tayi da ranta Kenan da gaske shi Dan Sokoto ne kamar yanda ya fada Mata sannan
da gaske sunan Babar tasa zainab din Kennan lokacin da take fadar iya Abu yace ta daina
fada gatsal sunan surukarta ne ta dauka Wasa yake Mata wallahi kenan duk abinda ya fada ba
joking a ciki. "To ai shike nan nayi zaton ko gidan na wani ne muka Mike kafa a cikinsa"..
'Ko alama ranar dasu Hajiya Inna sukazo ai nayi zaton fa a Nan zasu kwana gurinki sai Kuma
suka juya surukar Taki ce Bata samu zuwa ba sai ita kakarsa da matar kanin mahaifinsa, ki yiwa
Allah ki taushi zuciyarsa yayi hakuri ya koma gida tunda Naga alamar kece Zaki iya wannan
jahadin, wani irin fushi yayi da kowa har Amminsa abin ya shafa ranar da nace Miki su Hajiya
innar sunzo Saida Tasha kukanta a dakina, wallahi Banda idan na Fadi ga inda yake abin ze iya
shafar tarensu da Sameer da saina fada musu kodan samun kwanciyar hankalin Ammin tasa
tafi kwanan watanni Bata gidan ubansa saboda rikicin da akayi a gidan yanda mijinki ya fice
yabar gidan itama ta fice ta bar musu gidan, abunfa Babu dadi kiyi wannan aikin ladan Dan
Allah ko an samu kwanciyar hankali a zuri'ar su.
Ita dai zahra Banda gyada Kai babu abinda takeyi, Dan ji tayi abin yafi karfin dan karamin
tunaninta.
[2/1, 6:08 PM] ASHMAR: ✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH
Page 46.
_______Sun Jima a gurin suna hira da Hajiyar tana Kara Bata labarin taren Sameer da
Mahmud, anan tasan mamansa 'yar Niger ce Kuma cewa shi din da gaske twins ne su kamar
na Ammah mace da namiji.
Suna nan suna hira har aka Kira sallah, da sauri Zahra ta tashi tana fadar "Hajiya Kinga guri
Yana neman kurewa ban Dora miki abinci ba ko".
"Kinga dawo ki kaini inda zanyi alwala nayi sallah Banda kinibibi ki wani ce Zaki dafa min abinci,
to Wanda Rahane da wannan yarinyar Dana gani akace tare kuka taho da ita Wanda suke
faman aikinsa kuma ayi iri dashi? Ina fada Miki ki nutsu mijinki yawa ke garesu Kuma duk
cikinsu mijinki daban ne sai kin koyi kamewa da gaske sannan Zaki fuskanci yanayin kowa Ina
ke Ina wani dorawa Baki abinci banqiba dai in mijinki Zaki ringa yiwa wannan ba laifi,amma ba
kowanne karabiti ba kice Zaki wani kama rawar jikin yi Masa, mujeni ki nuna min nayi dahara
kafin a shiga sallah".
'yar Jakarta ta hannu ta daukar Mata suka nufi bedroom din da suka kwana.
Saida ta rakata har cikin toilet din ta nuna Mata duk abinda ya kamata sannan ta fito, sallaya ta
shimfida Mata sannan ta karasa gyaran gadon da Bata Ida ba dazu ta saka freshner ta Daki ta
rage karfin A/C din dakin. Hajiyar ce ta fito tana fadin "Ina dalili komai ya Zama na tab'e tab'e sai
mutum yasha wahala kafin ya tantance yanda za'ayi"
Dan murmushi Zahra tayi "Haba Hajiya me yake da wahala saboda Allah?"
"Babu Miko min gyalena nayi sallah naji kamar an tada sallar"
Hijabin ta Mika Mata tana fadin "Bari naje na dawo ta nufi kofa ta fice.
Gaba Daya ta fice daga part din, ta cikin barandar Nan tabi ta shiga babban part din, ko Ina
tadal sai sanyi da sansanyan kamshi ke tashi Nan ma wani bangaren ne daban da gyar ta gano
inda ta kwana saboda duk gurin shine parlourn da yafi kankanta Amma yafi sauran tsaruwa, a
hankali ta bude dakin ta shiga yana nan yanda tabar Shi direct bedside din ta janyo wayar na
Nan yanda ta ajeta Saida kudin America dollars data gani a ciki shiya Bata mamaki Daman
dasu a ciki ta saka ko Kuma daga baya aka aje Dan tab'e Baki tayi tunda ba matsalarta bace,
gurin mirror taje ta dauko kayan da Aunty Rukayya ta saya Mata ta dauko luggage dinta ta zuba
kayan ta duka ta fito daga ciki, a nan parlourn ta aje luggage din ta wuce ta ratsa duk parlours
din Shiru ba motsin kowa, ta nufi inda su Aunty zilai suke Nan ma shiru, ta dawo kitchen Nan
ma shiru abin ya Bata mamaki to suna Ina ne? Hanyar fita ta nufa sai Kara jinjina maganganun
da sukayi da Hajiya takeyi abin yayi matukar daure Mata Kai shin abinda Hajiyar makwarari ta
fada haka yake ko Kuma rudun tsufa ne kawai.
Cikin sa'a tana fitowa ta hango iya Rahane ta bullo ta bayan wani gini da wani babban basket a
hannunta, ganin zahra yasa ya tsaya tana fadin "ai Daga can nake nayi zaton ko tare kuka fita
Maida Hajiyar makwarari da shiga naji Shiru a gurin naku".
"A'a Iya Ina nan Hajiyar ma tana nan sallah takeyi Ina wuni? Wallahi tun dazu naso fitowa to
saiga Hajiya ita ta zaunar dani sai data shiga sallah na fito".
'yar dariya Iya Rahanen tayi "Lafiya kalau ya jikin naki? Sai Kuma ga Uban gidan mu yayi Mana
zuwan bazata ko? Masha Allah, ai Hajiyar sai ku kai almuru Bata gaji ba kin Sha labari dai
Kam".
"Lallai kam nasha hira, Wai Kuna Ina ne? Na duba banganku ba a can".
Rike Baki tayi kamar yarinya " ke! 'yar Nan ki rufa Mana asiri, Banda dalilin wadalilatan Ina mu
Ina kwana a bangaren yallabai, tun sassafe muka dawo nan kafin Rukayya ta tafi, Bari na yiwa
zilan magana ko?".
"A'a mu shiga kawai".
Tare suka karasa shiga cikin bangaren. Masha Allah guri ne Mai kyau tamkar gidansu na Azare
abinda ya banbanta su kalilan ne tunda wancan Renovation ne,wannan Kuma haka aka tsara
shi sai banbancin furnitures kawai, nan ma question mark tayiwa abun.
Jin sallamar zahra yasa zilai fitowa daga kitchen din tana fadin "Masha Allah, wallahi jiya ban
samu kwanciyar hankali ba Saida Rukayya ta shigo tace min kin wuce Daki kin kwanta har
Ammah na Kira na fada Mata Baku dawo ba, tace min na kwantar da hankalina ba komai tunda
bake kadai Kika fita ba, Kuma sai muka wayi gari da zuwan yallabai? Ai ya shigo shida oga
Sameer mun gaisa".
"Eh wallahi muna cikin gari gidan Hajiyar makwarari kakar oga har dare, kunyi waya da Ammah
kuwa yau?"
Saita share zancen Mahmud din.
"Eh mun gaisa tun wurin karfe shida na safe har take tambayar ya jikin naki tunda wayarki Bata
shiga, nace mata da sauki amma dai kun wuni a Asibiti Dan sai wurin Sha biyun dare kuka
dawo".
"Ok.ba damuwa Bari na bude wayar na kirata sai yanzu na dauko wayar, Bari na koma na baro
Hajiya tana sallah inaga yanzu ta Gama kada ta jini Shiru amma dai Zaki zo can din ko?".
Ta fada tana mik'ewa tsaye.
Zaro Ido tayi Kamar wadda taga abin tsoro.
"A'a wannan fa Daya ai jiya ba yau ba, sai dai In da abinda za'ayi Miki ki fada min ta waya sai
nazo nayi Miki".
Sallama ta yiwa Iya Rahane suka fito tare da Zilan, Saida sukayi nisa sannan zahra ta tsaya
itama Zilan tsayawa tayi.
"Aunty zilai me Kika fashimta daga lokacin da mukazo zuwa yanzu?"
Zahra ta jefa Mata tambaya.
"To abin ne da yawa gaskiya, Dan ni lissafina ya kwance gaba daya wallahi na rasa tudun
dafawa Amma dai komai rintsin mijinki shine ke Jan ragamar gidan nan Dan dazu lokacin da
oga Sameer ya kawo Hajiya naji suna magana da wasu ma'aikatan gidan Nan akan oga yayi
zuwan bazata, sai Kuma lokacin Daya fito a can gurin Naga ya Tara su yana magana dasu oga
Sameer Yana gefe harya gama oga Sameer ya rarraba musu kudi muma har ya aiki wani
Wanda Naga ya shigo da waccen babbar motar ya kawo Mana dubu ashirin ashirin nida iya
Rahane".
Ajiyar zuciya zahra tayi tana duban bangaren motocin hango motarta tayi a cikin parking lot din,
kenan a Nan ya ajeta ko kuma jiyan yazo da ita Nan Dan kamar Bata ganta ba jiya, rausayar da
Kai tayi tana wani tunani kafin tace.
"Muje kawai Aunty zilai mu zuba idanu a hankali gaskiya zatayi halinta, nifa duk hankalina ya
koma gida Amma naji yana fadin zasuje Azare jibi za'a dawo min da Aunty Rukayya, Kinga ba
zancen komawar mu kenan, ni Kuma abinda bazan yarda ba kenan ya ajeni a wannan gjdan da
bansan asalinsa ba gashi Nan Kashi-kashi kamar gidan marasa gaskiya". "A'a kada kiyi haka ki Bari kiga iya gudun ruwansa Mana nasan dai baze cutar dake ba, to kiyi
Masa biyayya a duk abina ze umarceki matukar Bai sabawa shari'a ba,kiyi hakuri wata rana ma
garinsu ze koma sai kice bazaki bishi ba? ai shi aure ba inda baya Kai mace, ki duba Maman
Akwanga kin taba cewa tayi rayuwar Azare". Haka zilai ta dunga tausar zahra har suka shiga part din da suka zauna Zahra ta dauki luggage
dinta Zilan ta karba suka shiga ta ciki suka fito barandar nan zilai sai mamakin abin take Bata
taba tunanin da wani ginin a bayan wannan ba, Bata Gama sarewa da lamarin ba Saida suka
shiga ciki, a parlourn farko suka tarar da Hajiya ta rabsa uban tagumi ta zubawa kofa idon suna
shigowa ta sauke ajiyar zuciya tana fadin "Haba 'yar Nan daga Bari na dawo Kika nemi gurin
Zama Kika manta Dani saboda Allah kin kyauta min