Showing 42001 words to 45000 words out of 65935 words
Chapter 15 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf
jawo dacin rai haka daga fadin Bata zuwa Asibiti,Kuma sai sakin magana kake
kamar da wani Abu a tsakaninka da wannan yarinyar ni ka fada min kamanta bama rufewa juna
damuwa ko farin ciki tare fa muke sharing".
Bai dago ba Bai Kuma tanka Mata ba.
"Miskili kawai".
Ta fada a zuciyarta.
Itama Bata Kara tofa tata ba tayi wucewar ta sama.
Da Ido ya rakata Yana ayyana subul da bakan da yayi.
Lokacin da Zahra ta fito daga wanka Bataji motsinsa ba, ta kuduri aniyar sai dai wani tsautsayin
idan ya gotta ya ganta Amma ta haramtawa kanta haduwa dashi.
Yafi zaman awa Daya da rabi ko motsinta Bai Kara jiba ya koma kusan sau uku, amma babu
canji dakin dai a rufe.
Dole da yaga Babu sarki sai Allah ya hakura ya wuce Asibitin gurin Baba malam.
Yana ficewa Aishat ta sauko kasa ta nufi dakin da Zahra take knocking tayi Tana Kiran sunanta.
Lokacin tana chart da sajida tana fada Mata next week zasuyi graduation, taji kiran da Aunty
Aishat din ke Mata, tsam ta taso ta bude kofar arba tayi da Afnan wadda akayi Mata gayu sosai
sai kamshin Bom-bon tajeyi zallo ta Fara tana dariya, hannu Zahra ta Mika ta amsheta tana
matsawa daga hanya. "Sannu Aunty,ko fita zakiyi ne?"
Zahra ta fada tana Zama a gefen gado ita Kuma Auntyn ta zauna a Kan sofar dake dakin, kallon
Zahra tayi Ido Cikin Ido.
"Me yasa Kika rufe daki kina Jin bro Yana Miki magana kikayi kunnen uwar shegu dashi ko da
wani Abu a tsakaninku dashi?".
Girgiza Kai tayi.
"Ba komai Aunty Ina wankane Kuma na rufe jacuzzi din shi yasa ban jiba, Kuma maganar asibiti
mijina ne yace na Bari ba sai naje ba tunda an tabbatar da narkewar ciwon kada a jogalo min
wani Abu daban, lokacin da muka taho Baya nan sai Abbana ya hadoni da Ya Mahmud tunda
Shima zezo India din, sai a dubani sosai to jiya bayan na shigo ya kirani yace sunyi magana da
doctor Hajara tace babu komai kawai dai nazo yawo ne, shine yace to kada naje wani asibiti
zeyi magana da Ya mahmud din Ina ganin ya manta ne ko sai yau ze fada Masa".
Ta karasa maganar kamar Dade duniya haka akayi ta.
Kallonta Aishat keyi tunda ta ambaci mijinta ita fa nema suke su caza Mata Kai kowa da nasa
salon, shi yana wani furuci dake nuni da ita din kamar suna da wata alaka da daf da daf Dan
yanda ya ture dazu ita ya saka Mata shakku a cikn furucin nasa, itama kuma gashi tayi wata
magana wadda tayi karo da zarginta kuma.
Nisawa tayi tana fadin "Allah ya rufa asiri".
"To Zaki zauna a gida ne keda Afnan ko kuma Zaki bini muje kasuwa? To ai Kuma kina azumi
kada ki kwaso kishirwa".
Zubut Zahra ta Mike da Afnan a hannu tana fadin.
"Muje Aunty Nima Ina son nayi sayyaya Naga gari Kuma".
"To kin fadawa mijinki zakiyi yawo ko?"
Dan murmushi tayi tana wasa hannun Afnan.
"Ai ban tare ba, Kuma yace duk inda ya Kama naje yasan bazanyi rashin gaskiya ba".
"A'a Kice aikin gyaran amare ya sameni kinzo inda ake bidi'ar gyaran aure".
Dariya tayi tana fadin.
"kaji Aunty Ni wane gyara za'ayi min kawai ki Bari".
Ta fice daga dakin bayanta Aunty Aishar ta biyo.
Ita ke driving din motar Zahra na gefenta rike da Afnan.
Basu Dade a kasuwar ba suka dawo Zahra laffaya ta dauko tsaraddu masu kyau da tsada a
gurin biya Aunty Aishar ta hanata ta biya ta biya Mata.
Ba zato suka tarar da mahmud a parlour Yana ibadar kallon ball ana Asian cup, Zahra you tayi
kamar Bata San Allah yayi ruwan tsirarsa a gurin ba ta wuce da Afnan a kafadarta Wanda tayi
barci, har ta kule ganinsa Yana kallonta a zuciyarsa ya Fara tunanin Wai to meya shiga Kan
yarinyar Nan ne haka totally ta canza Masa yanda ta nuna tamkar Bata taba saninsa ba ko
gaisuwar Daya Raina ta Hausawan baici arzikinta ba.
Remote ya dauka ya kashe kallon Yana fuskantar Aishat.
"Shatu Wai me yake damun yarinyar Nan ne ko magana fa batayi min ba ta wuce, kota fada
Miki wani Abu da nayi Mata, wato Naga alamar raini ya Fara shiga tsaninmu.
Zama tayi daura dashi tana fad'in.
"Toni Ina Zan sani ne dazu dai ta fada min mijinta ne ya hanata zuwa Asibitin Wai yace kada a
jankwalo Mata wani Abu tunda a Nigeria sun Basu tabbacin babu sauran ciwon".
A zabure ya gyara Zama Yana wani kankance idanu.
"Kikace menene ? Mijinta kome?"
Gyada Kai tayi tana bashi assurance na abinda ta fada.
"Mijinta fa kikace? Haka ta fada Miki?".
"Eh haka ta fada min dazu kafin mu fita kasuwa, harma tace min Bata tare ba sai ta komai gida,
gaskiya mijin yarinyar Nan yayi Dace da mace ta gari Naga alama tana jida mijin nata...."
Bai jira yaji abinda zata fada ba ya nufi dakin data ke.
Yanzu ma ta b'ame dakin Yana zuwa yaji shi a rufe, baiyi knocking ba dawowa yayi ya zauna
Yana huci, Nan da Nan Yana yinsa ya canza har abun yaso yaba Aishat tsoro.
Ita ta rasa wane irin lamari ne haka idan ma da wani Abu a tsakaninsu to a Cikin gidan Nan ya
faru Dan jiya harta kwanta lafiya kalau suka rabu da ita, Amma wayewar garin yau aka tashi da
wannan sabon canjin daga gareta.
Har tausayi ya Bata da gani Yana Cikin damuwa..
"Dan Allah Dan sonka da Manzon Allah ka fada min meke tsakaninku da wannan yarinyar dazu
naji kana fadar maganganun da suke nuna kamar Kaine ke Jan ragamar rayuwarta wacece ita?
Wace irin alaka ce a tsakaninku? Yarinyar Kace? Ko matarka ce? Ka fada min Kona samu
nutsuwar zuciyarta,wallahi duk duniya babu Mai Jin wannan maganar".
Bai dago ba harta Gama fadar abinda ke bakinta, yasan Dole ya fuskanci tuhuma daga Aisha
dan ya kasa controlling Kansa tun lokacin Daya fuskanci tana fushin da baisan Kona menene
ba da Kuma ma'assasar yinsa ba.
Motsin bude kofa yasa mahmud dagowa yaga waye, yasan dole ya kasance ahalin gidan ne.
Abbas ne ya shigo rataye da jakar laptop dinsa, kallon kallo aka shiga yi tsakanin su Mahmud
yasan ko rantsuwa yayi babu kaffara Aishat ce ta gargado shi tunda jiya tace masa aikin wata
biyu zeyi a Jamaica kafin ya dawo duka jiya kuma satinsa uku a can, inda yake ya tsaya Yana
warewa Aishat hannu idan da sabo mahmud ya Saba ganin wannan sabgar tasu. Hannunta ya riko suka shigo ciki Yana kallon mahmud Wanda ya yi fuska.
"A'a sweetie wa nake gani kamar 'yan gudun hijira?"
"To gashi Nan dau".
"Ammah bansan lokacin da kika Zama Mai fuska biyu ba, shine kika zagaye Mika gayyato min
mijinki ko?"
Hannun Aishat Abbas ya saki Yana nifar gurin mahmud, dariyar farin ciki Yana Dan doka
kafadarsa.
"My man kace mun ciri tuta tunda mune masaukin bakin, dan duniya wallahi Mahmud baka da
dama,kayi masifar bamu kafa Wai ashe kana Bauchi state, Bari na watsa Ruwa na fito nayi
welcoming dinka sosai".
Harara mahmud ya Kara zubawa Aishat ita Kuma ta wani dauke Kai ai dai ta samu mataimaki
tunda ita ya rainata Yana it's shata Mata layin da bazata iya tsallakewa ba gara maza su shiga.
Suf ta wuce tana fad'in Bari Fara maka preparing na kayan wanka".
Saida ta wuce Mahmud yace.
"Ya Abbas yaushe matarka ta koyi 'yar kasa ta iya fuska biyu, nace Mata fa kada naji kada nagi
shine ita Mai mijin ta tattago ka babu shiri kuzo koyi mini taron dangi, dama kayi zamanka daga
Nan Sokoto nayi ayita ta Kare".
Ya fada Yana huci, Abbas na ganin haka yasan da abunda ya tunzura shi.
"Koma dai menene Abbie yace mu kaika sokoto dead or alive".
Ya wuce shi yayi strais da sauri.
Har Abbas suka sauko Yana inda suka barshi,.bayan Abbas yaci abinci ya dawo kusa da
mahmud ya zauna.
"Wai me yake damunka ne ko baka da lafiya mu wuce asibiti? Ko Kuma malantar ce tasa ka
zama haka? Kasan ku alarammomin nan da izza kuke".
Ya fada Yana dariya, shima mahmud din dariyar yayi.
"Kai Amma Aishat kin kware gurin kinibibi yanzu har kin fada masa wannan maganar gaskiya
min Dena sirri dake tinda yanzu babu Aminci a tsakaninmu kina da naki ma'amincin".
Itama dariyar tayi tana nufar corridor din dakin Zahra, tana tunanin wayon yarinyar da gani
akwai abinda suke boyewa su duka Dan da alama horo ne take Masa a Cikin ruwan sanyi Dan
ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba da wata a kasa.
Cikin ikon Allah tana kokarin knocking taga Zahra ta bude kofar tana sabe da Yar gidanta
Wanda ta tashi daga barci.
"Sannu Aunty, gata ta tashi tun dazu batayi dai kuka ba na Bata fresh milk dai sai Naga gara
Tasha natural nata dai".
Ta fada tana Mika Mata Afnan din, abun mamaki sai yarinyar taki zuwa gurin uwar.
"Huta roro Nima na huta da tsotsa, amma kuzo muje ki gaisa da sweet heart ya dawo shine ma
yake tambayar Afnan din tunda yau Abulkhairi baya Nan yaje week end gidan Dr Suraj abokin
Daddynsa".
"Allah sarki shi yasa banganshi ba Ashe baya gidan".
Bata bukatar komai Dan ta yafa wani veil Amma karamine ta saka abaya Dubai maroon Mai
adon stones kanana saita haskata sosai yarintarta ta Kara fitowa da wani sirrin kyau Dan asali
ga kanshin turarenta da Kuma irin Wanda Hajiya Amina ta hada Mata masu janyo Hankalin oga
duk irin kamewarsa kuwa. Tare suka Jero suna magana wadda tasa Zahra yin wani tsadedden murmushi sai akayi dace
duk su biyun suna facing din hanyar.
"Tabarakallahu ahasanil kaliqin".
Abbas ya fada.
Shi Kuma Dan gogan ya kasa dauke idanunsa daga kanta sai yaga murmushin kamar da gayya
take yinsa.
Cikin takunsu na matan da suka San takan gayu suka karaso parlourn, sallama Zahra tayi.
Abbas ne ya samu zarafin amsawa shi kuwa mahmud tamkar an rufe Masa Baki, ai shi Abbas
Bai zaci haka zahrar take ba yanda sweetie ke bashi labarin ta Sai yaga ai Sam Bata iya fasalta
mutum ba.
Afnan na ganin Daddy ta shiga irin rawar murnar kaga abinda kake so din nan da Yara sukeyi
tana zillo gurinsa zahrar ta nufa da nufin ta kaita.
Ita da duk saura ba Wanda yaga lokacin da mahmud ya diro gabanta Dan ja da baya tayi da
sauri tana fad'in.
"Subhanallahi! Lafiya meye faru?".
Baiyi wata wata ba ya rungumosu ita da Afnan din dake hannunta.
Kici kicin kwacewa take Dan Bata taba tunanin zeyi irin wannan danyan aikin ba.
"Na shiga uku! Aunty ku taimaka min Dan Allah ku janye shi inaga bashi da lafiya kada yayi
Mana illah Ni da yarinyar nan".
Ta fada tana kuka.
"Wallahi bazaki sakamin ciwon zuciya ba kin hanani sakat tun safe kin Hana ko fuskarki na
gani,kinki yarda muje asibiti, me nayi Miki Mai zafi haka har kike ikirarin Wai mijinki ya Hana kije
Asibiti, waye mijin naki bayan ni? Fada mini!!!..????"
Ya fada Yana hargagi abinda Bata taba gani ba kenan a iya zamanta dashi,kuka Afnan ta
kwallah saboda yanda ya matsesu ga Kuma hayaniya da yake musu.
Da sauri Abbas ya taso yaga mahmud din kamar baya cikin nutsuwarsa.
Hannunsa Daya ya kamo sai yaji jikin nasa na tsuma.
Daidai kunnensa Abbas yayi magana.
"Pls sakarta kaga ka saka yarinya kuka, ka nutsu ta fada maka me yasa tayi hakan kowa ai
yasan taka ce Ina ga da abinda kayi Mata Mai ciwo".
Da kyar ya yarda ya saketa ita da yarinyar. Zaunar dashi Abbas yayi ai Zahra na Dora yarinyar
a cinyar uwarta lokacin Abbas na can Yana bashi Baki ta fice.
Tana shiga tayi locking din door tana sauke numfashi tare da goge 'yan hawayenta na karya
data kakarosu.
"Wallahi saina rama zakayi bayani da bakinka guy ni zaka yiwa cin fuskar da ze Zubar min da
daraja da kimata sai zuciyarta da Bakinka sun Fadi gaskiyar da kake boyewa, Kuma Wallahil
Azim addu'ar tsamiya yanzu na Fara har FAHAZAMUHUM BI'IZIMILLAHI YA WADUDU YA
JAMI'U MALIKIN NASI MALIKI YAUMIDDIN zanta zabga maka sai ka Raina kanka kasan Dan
an baka kyautar zahra ba Yana nufi Zan Zama matar shige ba, sai duniya ta shaida zahrar
Zahra ce, tayi kwafa ko yanzu na rage tension ko ya yake tunda kaima kaji a jikina ka Kuma
karyata maganar daka fadawa 'yar uwarka jiya, Wai bakaga wadda tayi maka ba, sai kasan
bayanin da zakayi musu Kuma tunda magana zarar bunu ce bata komawa.
Lokacin da Abbas ya juyo da zummar yiwa Zahra magana yaga sai filin gurin kallon Ina take ya
yiwa Aishat..
"Ta gudu Ina zata tsaya ya nakasa ta yayiwa mijinta asara,kuma saboda Allah sai ka kakume
Matar mutane da yammacin gari yaushe ka Zama haka yarinya da aurenta da komai wannan
kasan haramun ne basai an fada maka ba, Ina cewa gida Daya kuka zauna ba diyar malaminka
bace me yasa kasan kana sonta kayi shiru har wani ya aura ni Naga kokarinsa Daya amince ka
taho Masa da irin wannan diamond baby din wata uwa duniya baya tsoron sharri shaidan ya
gitta tunda gashi a gaban mutane ka iya rungumeta yaya idan daga Kai sai ita ne ai labarin ba
irin wannan bane ki.."
"Stop!!!..... Aisha, ni kike fadawa abunda yazo bakinki? to Zahra halaliyata ce matata ce ta
sunna".
Ya fada a zafafe tashi yayi ze fice da sauri Abbas ya riko shi.
" Dawo magana zamuyi ta fashimta".
Baiyi gardama ba ya dawo ya zauna, ita dai Aisha rasa ta cewa tayi wai barawo a hannun Mata.
Very close dashi Abbas ya zauna ya riko hannun mahmud Yana fadin.
"Munji matarka ce amma yanda sweetie ta fada min kace matar ubangidanka ce me yasa ka
boye mata Bata cancanci haka ba, kasan irin wahalar Dana Sha da ita lokacin da case din Nan
ya taso? yanda kasan zata zautu wallahi Amma sai ka dawo Mata da wata fuskar daba taka ba
duk rintsi bakwa rufewa junanku komai, kasan ta fada min cewar wallahi matarka ce Dan ta
shaida bazaka taba yarda kayi tafiya da mace irin wannan da mace kamar wannan babu alaka
Mai karfi a tsakaninku".
Mahmud ji yayi duk ruwa ya cinye shi yarinya karama ta dagula masa lissafin da tasa ya saki
layi duk yanda yake shirya nasa planning din ta rusa a lokaci daya yayi amansa ya lashe.
"To tayi hakuri ni kaina bansan me yasa na kasa fada Mata ba Ina Jin nauyin yanda Zan tunkari
Ammi da Abbie da wannan maganar ba wallahi, sai Naga nayi wani Abu Daya sabawa al'adar
mu ta Malam bahaushe, Kuma ita na rasa abinda nayi mata lafiya kalau mukazo gidan Nan
Amma ta sauya min na rasa abinda yake min dadi wallahi Ya Abbas yarinyar nan itace
weakness dina a rayuwa ni kaina nasan hakan, itace fa wadda nake fada maka na gani da
dadewa a jirgi ita da Abbanta ka tuna?". "Off cause anyi haka,Amma how comes hakan ta faru?".
Furzar da iska yayi daga bakinsa.
"It's long story, idan ka huta zamu tattauna akai, yanzu dai ki tashi like kiyi min Biko tunda Naga
alamar kina da masaniyar laifina".
Baki Aishat ta dafe da hannu Wallahil Azim ban sani ba, nifa duk abin Nan hasashe nake yi ban
tabbatar ba sai yanzu, ni wannan aikin ba nawa bane Kai zaka gyaro kayanka da abinda kayi
Mata tunda Naga Bata da kwaramniya Sam, Kuma ya zakayi da ita kenan? Zakaje kace ga
matata nan tsaraba fushin da nayi ko Yaya za'a kayi?". "Ki Bari kawai alkawarin da nakeso kuyi min mu rufe maganar nan a nan duk da Faruq ma ya
sani amma nasan tunda na kada Masa warning bazeyi karambanin fadawa kowa ba, nina taro
match dina Ni zanyi playing din kayana kawai kuyi min addu'ar samun nasara kada Ammah tayi
min nak'i". Ya fada Cikin raunin murya.
[19/02, 11:46 pm] Abu Saleh: *AUREN HUCE HAUSHI*
MAMAN FATEEMAH
09062432330
Or
O8055362975.
Page 72
........... Cikin kankanin lokaci mahmud yaji ya Dan samu nutsuwar Daya rasa, yarinya karama ta
saka shi sakin layi a gaban mutane, ita dai Aishat sai jijjiga Afnan takeyi wadda har lokacin take
'yar mita, tashi Mahmud yayi da nufin barin gurin, Ya Abbas ne ya riko Masa hannu Yana girgiza
masa Kai. "Dawo magana zamuyi ta fashimta, baiyi gaddama ba.
"Kana ji yanzu ka Bata sarari ta huta ta Kuma Huce daga fushin da tayi da kai, idan so Samu ne
ka koma gidanka ka kame kanka, kada ka Bari ta Kara ganinka Nan kusa har sai an Kai wani
limit da zata nemeka ruwa a jallo ta rasa yanda ko kun hadu babu saura fishi sai dokin ganinka
dole ba Zama very strong a fannin soyayya Kaine namiji kada ka yarda ta gane itace rauninka,
sannan dole ka koyi takatsantsan kasan inda na dosa idan ba haka ba za"ayi amfani da wannan
damar a cutar maka da ita Koda ta furucin Baki ne".
Shiru mahmud yayi Yana saurarensa wato shi kansa zaman takewar auren sai an shirya mata,
Dan rausayar da Kai yayai yana fad'in.
"Anyway shike nan,Amma da so nake ta yarda muje asibiti su dubata tukunna sai na wuce din".
Wani kallon me yake damunka Ya Abbas yayi Masa.
"For God sake! Ashe bazaka Zama Mai karfin ba kenan? Tunda nace ka kame kanka ai sai kayi
yanda nace ko, tashi mu fita ja rakani na dubo patient din namu ma ida discussion din a hanya
tunda Naga alama ka rifta da yawa".
Ya fada Yana Masa dariya, sumar kansa ya shafa shima Yana murmushi.
Bayan fitarsu Aishar Goya Afnan tayi so take tayi barci, Bata Kara bi takan Zahra ba ta shige
kitchen ta Dora ruwa ta dauko kaza