Showing 57001 words to 60000 words out of 65935 words

Chapter 20 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf

03 Aug 2025

1493

Saba ba jiya da
zummar suyi kwanan zaune ya shigo sai kuma aka samu akasi ya bige da allurar barci.

Ta kofar baya ya shigo part din Ammin har ya Haye sama Bai hadu da kowa ba dakin da
Zahra ta kwana ya bude ba kowa sai kamshinta Wanda har ya Fara kama dakin, komai tsab ba
tamkar ba'a kwanta gadon ba, kofar ya janyo ya nufi dakin Ammi yasan a irin wannan time din
Bata ciki turo kofar yayi da sallama shiru sai kamshi kawai ke tashi a dakin. Wani sanyin dadi ya ratsa shi jinsa yake kamar an sauke Masa wani katon dutse daga kansa, a
tsakiyar dakin ya tsaya Yana tuno wasu lokutan baya da shigo cikinsa tamkar mahaukaci Yana
magiya Amma ko gezau Ammi Batayi ba Saima tsallakewa da tayi ta wuce ta barahi a
durkushe, Amma yau gashi ya shigo cikinsa da walwala da Aminci ba bacin Rai ba tashin
hankali.
Kwanciyarsa yayi a Kan sofa Yana fashi "Alhamdulillahi Ala kulli halin".
Yayi zaman kusan minti talatin kafin yaji alamun bude kofar a Hankali ya cira Kansa daga
wayarsa da yake duba sakonnin whatapps, Ammi ce ta shigo tunda ta shigo master parlourn ta
tasan ya shigo gurin Bata Kara tabbatarwa ba Saida ta hauro saman Dan kamshinsa na daban
ne. Tsayawa tayi a gurin tana Kare Masa kallo, Masha Allah gani tayi ya Zama Babba ya cika Ido
kenan jiya ganin tsoro tayi masa gashi ya Kara yin wani fresh dashi da gani ya samu nutsuwa
ba kadan ba.
Aje wayar yayi ya taso ya nufota inda take tsaya murmushi yaki barin Bakinta ta Kuma kasa
dauke idanunta daga kansa.
Ba wata wata mahmud na zuwa ya shige jikinta Yana fadin.
"Ammina fushi kike Dani ko? Nasan zakiyi fishi dani, gani Nazo kiyi min duk hukuncin Daya
Dace Dani in dai Zaki yafe min, Dan Allah kiyi hakuri Nima bansan me yake faruwa Dani ba,
Sam bana kaunar ko sunan garin nan naji an fada bana Kuma son naji ko sunan Wanda na sani
in dai Yana Cikin family wallahi". Zamewa Yayi ya tsuguna ya rike kafafunta sai hawaye.
Dan duk'awa tayi ta kamo hannunsa ya taso jansa tayi kamar Karamin yaro har gefen katafaren
gadonta ta zaunar dashi itama ta zauna.
"Waya fada Mata Ina fushi da Kai? Ko alama dama ma banyi fushi da Kai ba sai yanzu da
Ubangiji ya amshi rokona ya share min hawayena, bakayi min komai ba ko kayi ma na yafe
maka duniya da lahira, Allah yayi maka albarka ya baka kariya daga sharrin dukkan wani
abunqi, yanzu Ashe kana Bauchi state kayi zamanka akayi ta nemanka a turai da kasashen
larabawa?".
"Ammi Nima fa wayar gari kawai nayi na ganni a garin bansan ta Yaya naje ba, Saida Habib
Wanda ya ganni a yashe a kasa karkashin bishiyar gamji ya fada min a halin daya ganni nayi
mamakin to ta Ina nabi naje can? da kafata naje ko kaini akayi? duk ban sani ba, Ammi Ina jinfa
na rasa hankalina na wasu kwanaki ko watanni, Ammi hatta magana fa daina yinta nayi sai dai
Ido Ina Jin abinda ake fada Amma bana iya bude bakina na mayar mutanen Nan ba Karamin
jihadi sukayi ba gurin ceto rayuwata, Idan malam dawo har Azare Zan kaiki ki yiwa Baba malam
godiyar abinda sukayi min kudi dai bazasu iya biyansu ba sai dai Allah mutane ne su masu
karamci". Nan ya zazzage mass
Mata duk irin rayuwar da yayi a Azaren har ya zauna a dakin waje na amajirai.
Baiyi zato ba yaji shashshekar Ammi.
"Subhanallahi ! Haba Ammi me yasa Zaki Bata hawayenki abin fa ya Riga ya wuce, Ina fada

Miki ne kawai saboda ki Kara yi min addu'a saboda bamu San me goben zatayi ba".
Knocking din kofa akeyi mahmud ya bada izinin shigowa.
Aishat ce da suhailat suka shigo itace Mai bin batool.
Da murnarta ta Karaso sai Kuma tayi turus tana kallon Ammi dake share hawaye Aishat ma
jikinta sanyi yayi.

"Meya sameta take share hawaye?
Aishat din ta jefawa mahmud din tambayar.
Ammin ce ta Bata amsa

"Ba komai Hussein ne yake fada min halin rayuwar Daya shiga tamkar marara gata harfa so
akayi a haukata min d'a a banza wallahi Ina istigifari ga Ubangiji kafin na fada, dama wani Allah
ya bawa dukiyar Nan bashi ba da yake da kananun shekaru irin haka, wallahi da nasan wannan
condense milk din itace sila Dana yiwa jama'a unguwa rabonta an wuce gurin,to ba haka zanen
kaddarar take ba sai hakuri".

Suhailat ce ta dan matso kusa da mahmud tana fadin.
"Sannu Ya Mahmud ya jikin naka?"
"Jiki da sauki suhailat ya karatun kin Gama ko?".
"A'a da saura sai next year in Sha Allah".
"Allah ya taimaka".
"Amin"
Suka fada gaba daya.
Aishat ce tacewa mahmud "kaje Abbie Yana nemanka a parlournsa na part din nan, Ammi
kema yace a Kai masu abin break fast can kamar na mutun bakwai".
Mikewa yayi yana fadin "Bari naje Ammi".
"Jeki ki fara hada abinda za'a shigar part din Abbie din keda sauda da Batool Kice iya Halima ta
Zuba pepper soup din kayan Cikin Nan a babban warmer sauran ta saka a fridge".
"To Ammi"
Waje suhailat din tayi da sauri.
Saida suhailat din ta fice shima ya nufi kofar Yana Daf da ficewa Aishat tace masa.
"Ka fada Mata wacece zahra a gurinka Naga alamar ba iya playing match din zakayi ba".
Tsaye yayi shi Bai fice ba shi kuma bai juyo ba, sai Kuma ya juyo ya dawo a Hankali ya zauna a
gabanta ya sadda Kai da gaske wani irin nauyinta yakeji Wanda Bai taba tunanin zeji
kwatankwacinsa ba a tare da ita, a Hankali kamar baya son yin magana ya furta.

"Ammi ga zahra Nan an bani aurenta a Azare, tun watannin baya nace saina kawo Miki ita idan
ta kwanta Miki a matasyin suruka ki saka Mata albaka ki kaita dakinta da kanki idan Bata yiiki
ba ki saka a mayarwa da iyayenta ita a Basu hakuri, duk hukuncin da Kika yanke na karba da
hannu bibiyu". Yana gama fada Bai jira yaji abinda zata fada ba ya tashi ya fice da sauri Dan ba Karamin
kokari yayi ba gurin kinar bakin waken fada Mata ba.

"Eh to da dai hakan yafi a mayar musu da yarnyarsu tunda akwai alkawarin da nayiwa fulani,
Ina ga sai dai suyi hakurin gaskiya"
Abinfa ya iya jiyowa kenan daga bakin Ammin tasa bai it's cewa komai ba ya fice.
Daga shi sai Wanda ya halicce shi suka San abinda yake ji a kasan Zuciyarsa.
Aishat zatayi magana Ammi ta daga Mata hannu dole ta kame bakinta daga abinda tayi niyyar
fada.
"Kuje kiyi serving din ku kafin na fito, idan kun Gama ki hadawa yarinyar Nan kayanta Wanda
kikece min tsaraba yasa akayi Mata nafi son tabar gidan Nan kafin wani tsegumin ya fito".
Sororo Aishat tayi tana duban Ammi wadda ta tashi ya shige toilet kirjinta na bugawa da sauri
da sauri.
"Allahumma Ajirniy fiymusibati, wannan wane irin tashin hankali ne Kuma? Allah ka kawo
sauki".
Fita itama Aishat din tayi jikinta a mugun sanyaye, bedroom dinta ta nufa ta yiwa Zahra magana
suka fito tare, da kyar Aishat tayi ta maza ta danne zuciyarta sukaci abincin tare da su suhailat
duk da basa cin abinci da wuri Amma dole tasa tunda Umarnin Ammi ne.

**

Ammi najin fitar Aishat ta fito daga toilet din ta dauki wayar ta Kira number data karba a gurin
zahra, Bata so Kira a irin wannan lokacin na safiya ba amma dole tasa hakan.
Lokacin Ammah na kitchen Musaddiq ya kawo Mata wayar yace kiranta akeyi, tana wanke
hannunta wani Kiran ya shigo Saida ta goge hannunta ta karbi wayar, bakuwar number ce.
Dauka tayi tana amsa sallamar tana ficewa daga kitchen din ta barwa Alawiyya aikin, gaisawa
sukayi da Ammi kafin Ammin tace.
"Ko Hajiya Asma'u ce maman Fateemah Zahra?".
Sai Ammah taji gabanta ya Fadi ana ambatar sunan zahra.
"Eh nice, Allah yasa lafiya?".
Dan murmushin da Bata shirya ba ya kwacewa Ammi.
"Lafiya kalau sai Alkhairi,sunan Hajiya zainab daga Nan sokoto mahaifiyarsa Mahmud mijin
Fateemah".
Cikin nuna jin Dadi da tsantsar fari ciki Ammah ta Fara fadin.
"Masha Allah! Hajiya ya gida ya akaji da jama'a ai jiya ta fada min suna Nan naso na karbi
number ki mu gaisa sai tace min wai bazata iya tambayar mi ba, to yau naso na karba a gurin
shi mijin nata mu gaisa".
"Kai haba babu komai muya Kamata mu tako muzo muyi godiya yanzu ma bamu fasa ba wata
dai Alfarma nake nema akan 'yata yau komai dare suna Nan bisa hanya zasuzo tare da 'yan
uwa na sai anzo daga Nan an daukar min ita an kaita dakinta kamar kowace Amarya ba Wai a
wayi gari a ganta a matsayin matarsa ba bana son ayi Mata wani duba na daban kinsan Yana
yin kowa ne family da irin nasu matsalolin,duban irin kalubalen da aka fuskanta a Nan din kafin
barinsa gida, naso ace wani nawa yayi Miki wannan bayanin to basa kusa kiyi hakuri nayi rashin
kunya akan Dan Fara".
Ta fada tana 'yar dariya irin gentle din Nan.
Itama Ammar yin tata tayi, tana fadin.

"Na fashimta kina dai son kankarowa diyar taki mutunci ne ko?"
"Gaskiya dai Kam Allah dai ya saka Miki da Alkhairi kinyi abinda duk uwa ta gari zata yiwa
yarinya mace Hussein ya fada min komai, mun gode da Karamancin ku garemu kin dauki
yarinya kamar wannan kin bashi ba tare da kunsan asalinsa ba, sai nazo har gida nayi godiya in
Sha Allah". Sukayi sallama kasake Ammah tayi tana lissafo maganganun su da mahaifiyarsa Mahmud daga
ji ba wata Babbar bace sosai sai dai tasan kanta da alamar Allah ya karbi Addu'oin ta Wanda
take ba dare ba Rana akan Zahra na neman dace da kwanciyar hankali a gidan Aure, sai Kuma
tayi murmushi wannan sirikar ta Zahra za'a da ita tasan ta Kan duniya wato sai ansan yayi aure
ba Wai yazo da Matar ba kamar Auren bariki.
Part din Abban ta nufa na bangaren ta, tana shiga Yana aje wayarsa da ya gama. Ganin
fuskarsa da wani irin annuri yasa ta fasa fada Masa abinda tazo dashi gara ta Fara Jin nasa
tukunna.
"Wane irin albishir akayi maka haka Mai Dadi Daya saka Zuciyarka a irin wannan Nishadin
haka?".
"Zoki zauna yanzu muka Gama waya da sirikin uwata Wai ashe yaron Nan mahmud Dan wajen
General Muhammad Dange ne, Saida ya kirani yanzu na gano inda nasan fuskarsa Kullum na
kalleshi sai Naga nasan fuskarsa ko a wani gurin ne daban Ashe fuskar mahaifiyarsa nake gani
a tasa fuskar, kinsan kuwa waye General Dange? To babu abinda zewa Ubangiji sai godiya ya
sakawa uwata da abinda hankali da tunanin mu Bai taba kawowa ba mijinta fa shine Dan
general din Wanda ake hasashen Yana Daya daga Cikin matasan masu kudin Africa sahun
farko duk fa yanda family dinsu sukayi popular a kasar nan ta fuskar arziki yaron yayi musu
wata irin tazara, Abu Daya yake bani mamaki yanda ya iya jure rayuwa irin ta Cikin Almajirai ba
kyamata ko kadan Abu Daya ne dai kawai ya ringa sani a tunani yanda tun bayan samun lafiyar
yaron komai na makarantar ya canza akace NGOs sun shigo suna wannan mahaukatan
ayyukan Wanda ba'a yinsu a sauran makarantu Dan ma daga baya sun canza salo sun shigo
da wasu makarantu harma Dana Karkara".
Jinnina Kai kawai Ammah takeyi tasan wannan ba tsuminta ba ba Kuma dabararta ba Rahamar
Allah ce ga bawa kawai da yake yinta ga wanda yaso a lokacin da yaso, lallai sun kunshi takaici
da yawa a baya Amma Cikin Rahamaniyya ta Ubangiji sai gashi abun ya zamo wani haske
daga karshe abinda babu Wanda ya zata Koda kuwa a Cikin mafarki ne. "Abban Yara Nima abinda ya shigo Dani kenan na fada maka munyi communicating da
mamansa yanzu".
Nan ta fede Masa daga biri har wutsiyar yanda Sukayi da Ammin mahmud.
Dariya Abban yayi yana fadin "Nima ya fada min har Yana bani hakuri da halin Mata na bidi'a
Wai ita uwar sai tayi bikin danta kowa yasan yayi aure"

Sun Dade sun tattaunawa na Suma dole su nuna Mata gata tunda inda Allah ya kaita ba gurin
Wasa bane na take Abban ya turawa Ammi makudan kudi ayi abinda ya Kamata Dan ma da
furnitures a aje Wanda Ummee suka turo ba'a sakaba saboda babu guri Kuma Kaya ne na
garari.

******** Tunda su zahra suka Gama Break fast suka koma parlour na uku suka zauna suhailat ta
kunna musu tv ana yin wani series na 'yan Lebanon, manyan jakunkuna taga masu aikin Ammi
suna fita dasu daga dakin da aka aje kayan da suka zo dasu ba dadewa Kuma taji maganar
mutane daga dayan parlourn, sai kuma taga suhailat ta tashi da sauri tana fadin. "Kai su mummy Badi'a ne yanzu da safen Nan haka kamar Wanda suke daga wata unguwar"
Ta wuce ta nufi inda suke.
Da gudu suhailat ta fada Kan mummy Badi'a tana fadin.
"Sannunku da zuwa mummy keda Hajji zuwaira, ina kwanan ku Ya hanya? Amma zuwan Cikin
dare kukayi ko? Naga duka yanzu Sha Daya fa".
Gaisuwar suka amsa sannan mummy Badi'ar tace "ko kadan dazu muka zo wurin karfe Tara da
rabi ta baya muka shigo muna sama ne gurin Ammi itama yanzu zata sakko".
Aishat ce ta shigo daga wata kofa wadda zahra Bata San ko Ina bane, ranta a hade ta cewa
Zahra ta taso suka nufi gurinsu su suhailat.
Suna shiga bakin suka fara fadin.
"Masha Allah, wannan ce Fateemar? Matso mu gaisa Hajja zuwaira na fadin "nice dai ta karfen
keta katako ce" mummy Badi'a na tare mata, cikin Jin nauyi zahra ta tsuguna ta gaisheni su
Cike kunya da girmamawa.
Aishat sai taji tana jin haushin maganar Hajja ita ana ga yaki tana ga k'ura, Ammi na maganar a
mayar da Zahra gurin iyayenta a Basu hakuri ita Kuma tana maganar wani itace ta karfe. Ammi
ce ta shigo rungume da wani Abu anyi rapping dinsa tazo ta zauna kusa da mummy Badi'ar
tana fadin gara ku tashi komai ya Zama ready kada kuyi dare tunda tafiyar mota ce". Tashi tayi tana fadin .
"Hasana kuje kofar baya gamu Nan zuwa".
"Taso sister muje"
Ta fada tana taba kafadar zahra.
Ita fa Bata gane ba an sakata a duhu Ina zata kuma taji ana fadin kada ayi dare to suwa zasuyi
Daren? Ita Kuma meya hadata da bakin Ammin da taji kamar da ita zasu tafi.
Ita dai bin Aunty Aishar takeyi wadda taji kicin kicin da rai kamar ta fasa kuka.
Wata lafceciyar GLK Mercedes-Benz 2024 model Parke a kofar baya sai daukar Ido takeyi
Baba Habu drivern Ammi na Amana Yana gefe Yana jiran Umarnin Ammi.
Da saurinsa ya matso Yana gaishe dasu zahra, fa sauri zahra ta Dan duqa ta fadin.
Lafiya kalau Baba"..
Su Ammi ne suka fito har inda su Zahra suke tsaye Ammi ta Karaso, ta Kamo hannun Zahra ta
dankata a hannun Hajja zuwaira tana fad'in.
Gata Nan Hajja na Baku Amana ku damkata hannun mahaifiyarta Dan Allah, Allah ya tsare
hanya".
Kunshin abinda ke hannunta da wani gidan sarka White gold Mai azabar kyau sarkar kudinta
sun tasarwa milion hamsin ta mikawa Zahra tana fadin "Allah ya tsare hanya ki gaishe min da
mamanki".
Ta bude motar ta sakata ta juya ta koma Bata Kara kallonsu ba saboda ji tayi kamar rabuawar
kenan.
Wasu hawaye Aishat taji sun cika Mata ido da gudu tabi bayan Ammi tana fadin .

"Why! Why! Why! Ammai kin kashe min farin Cikin bros wallahi".
Mahmud ne ya fito daga part din Abbie yaji wannan kalaman daga bakin twin sister dinsa.
Yayin da a waje itama Zahra data Gama fuskantar inda aka dosa ta kifa kanta a gefen kafadar
mummy Badi'a tana sakin wani marayan kuka tana ayyana shikenan ta faru ta Kare wata
sabuwar matsalar kuma.
A Hankali zahra ta bude idanunta sharaf da hawaye Jin motar ta harba da wani irin speed ta
nufi main gate, ta juya ta yiwa gidan kallon karshe gidan data kwana Daya Tak a cikinsa da
sunan matar dansu wadda a yau kuma bata San wane suna zata Zama ba, wata Kika sunanta
ya tashi ya koma bazawa kuma, Dan rashin 'yanci ko Jakarta ta hannu ba'a Bata dama ta shiga
ta dauko ba.
[27/02, 11:13 am] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI*


AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fateemah

99061432330

Or

08056362975

Page 78


.............
Cikin wani irin karsashi mahmud ya riko Aishat Yana fadin.
"Meye haka kikeyi? Kinfi Ammin sannin abinda ya Kamata tayi ne, Ni ne nace Mata idan zahra
Bata kwanta Mata ba tayi abinda ya Kamata, ina cewa a gabanki komai ya faru? to meye kuma
na daga hankali Allah yasa hakan yafi Alkhairin".
Ya juya ya fice daga part din gaba daya, mota ya shiga yabar gidan gaba daya, isolation yake
bukata a yanzu Dan Kansa babu abunda yake sai Sara Masa besan me yasa Ammi tayi hakan
ba amma jikinsa be bashi Wai an rabashi da precious bane har abada, akwai wata manufar yin
hakan duba da zuwan gaggawa da yaga su mummy Badi'a da Hajja zuwaira matar kawu yusufu
sunyi yasan da magana a kasa Kuma ga tafiarma a sirrance akayita ta kofar baya motarma Mai
duhun glass ce,
Duk abinda mahmud ya fada Ammi taji shi sarai Amma tayi gaba dole ta nemarwa matarsa
uwar 'ya'yansa Qima da mutumci bazata biyewa yarintarsu ba a haifi Dan da babu idanu.
Sama ta Haye tana lalubo number Aunty Surayya matar uncle Mustapha.
Daki Aishat ta koma ta dubo ko Afnan ta tashi tunda Abulkhairi Yana gurin Batool,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login