Showing 45001 words to 48000 words out of 65935 words
Chapter 16 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf
ta Fara gyarawa ta Dora a wuta ta debo fresh fruits ta
wanke ta Fara hada fruits salad ta saka a fridge tayi lemon kankana da Madara pepper chicken
tayi da chicken rice sai coslow data hada ta dafa ruwan tea Mai hadin spices masu Dadi na dafa
tea kafin magariba ta Gama komai, Babban tray ta hadawa zahra kayan bude Baki ta aje a gefe
sannan ta ringa fita da nasu zuwa dinning tana jerawa Saida ta Gama komai ta dauki na zahra
lokacin har duhun magariba yayi, knocking Daya tayi Zahra ta bude Mata ta matsa gefe tana
fad'in.
"Sannu Aunty da aiki Aunty".
Ta fada tana karbar kayan Amma taki yarda su hada Ido.
"Zanje nayi sallah idan na Gama zamu zauna dake Ina so mu tattauna wasu abubuwa".
Aishat ta fada tana juyawa.
"To Aunty zanzo basai kin dawo ba".
Dan dakatawa tayi da tafiya ta waiwayo.
"Kiyi zamanki ai Amare 'yan lalashi ne, ni zanzo on behalf of my beloved brother".
Ta fada tana dariya, itama zahra murmusawa tayi.
******Daga gida direct Asibiti su Mahmud suka nufa, sun samu Habib da Abubakar, Ya Abbas
yayi mamakin ganin Abubakar a gurin sosai Amma baice komai ba kenan da wadanda mahmud
yayi hijirar dasu.
Lokacin Baba malam Yana zaune suna Hira, har gabansa su mahmud suka karasa suka gaishe
shi da Kara suba shi, sannan su Habib suka gaishe dasu mahmud, Ya Abbas ne ya kalli
Abubakar Yana fadar.
"Wato har Kai gurin kufe Mana gaskiya ko? Kana ji ana ta Fadi tashin nemansa kayi fumfurus
kana kallon kowa daga karshe ma akace ka canza gurin aikine".
Sadda Kai yayi yana Dan sosa gefen wuyansa, gyaran murya Baba malam yayi Dan duk da
bayanin matsayin Ya Abbas da mahmud yake basa baisa ya dauke hankalinsa daga maganar
da Abbas din fada ba.
Jin gyaran muryar Malam yasa suka juyo gaba Daya suna kallonsa.
"Ayi Masa Afuwa shima Mai bin umarni ne,sai yanda akayi dashi kada aga laifinsa amanar
kenan da baya da Amana baze yarda dashi irin haka ba. Allah yayi albarka ya kiyaye gaba, ai
karfin addu'a ne yasa komai ya Zama tarihi naji dadin ganinka sosai Malam Abbas Dan Allah
kayi min aikin Dana kasa ka maida min Dana gida tare da iyalinsa ka bawa mahaifinku hakurin
karambanin da mukayi musu wallahi nagarta muka duba ba komai ba tunda Bamu San gaibu
ba, in Sha Allah idan lafiya ta Samu Ina Nan zuwa sokoton da kaina".
Waje su Habib suka fice, ya Zama daga Malam din sai su Ya Abbas.
"Babu komai Malam Allah ya baka lafiya, muke da godiya ya fada min duk dawainiya da kayi
dashi tunda kuka tsince shi har kawo yanzu ai kaima ubane ka Isa kayi yanda kaga dama dashi,
Allah ya Kara lafiya da sutura yasa kaffara akeyi in Sha Allah amanarka Zan idata, ai mu bamu
da Bakin godiya sai dai ubangiji ne ze biyaka". Sun Jima suna tattaunawa anan Malam yake farawa Abbas yanda kayiwa mahmud makaru
abinda Bai taba fada Masa ba sai yanzu yakeji, har wasu hawayen gefen Ido Mahmud yaji sun
taro Ashe haka akaso a kassara Masa rayuwa Allah yayi Masa gada da Rahama ya kawo
Habib ya gashi a gurin da yake a yashe a kasa. Anan sukayi magariba sukayi insha'i sannan sukayiwa Baba malam sallama, mahmud ne yace
suje su duba jikin Alhajin su Aunty surayyar uncle Mustaphan Shima Yana nan.
Shima sun samu 'ya'yansa maza biyu sunzo duba jikin nasa, sun gaisa tare da jajanta musu,
shima Alhajin jikin da sauki sosai Dan har Yana takawa shima da karfe.
Gida suka koma mahmud yayi dinner tare dasu, haka Nan yayi ta maza bai nemi zahra ba
Suma babu Wanda yayi maganar ta har suka gama, Mahmud Bai wani zauna ya shiga dakin
da ya mayar nasa tun ba yanzu ba ya dauko laptop din da wayoyinsa ya fito.
"Ka Bari na saukeka Nima Ina son fita ne".
Ya Abbas ya fada.
"No, ka barshi kawai nayi waya da Mr salahuddeen Yana kusa da isowa, kawai dai Alfarma
za'ayi min twins zasu shiga Nigeria a tsakanin kwanakin nan harna Fara musu processing na
visa harda yaran duka".
"Ba damuwa Nima Ina son suje Nigeria din to saboda makarantar Abulkhairi ne, Amma yanzu
dole suje tunda ta Kama amma naji kana fadar kana nemar musu visa Kai kana Nan kenan?".
Kai ya girgiza Yana fadar "A'a akwai dalilin raba tafiyar ne jikina Yana bani wani Abu da bansan
ko menene ba".
"To Allah ya rufa asiri, Zan fadawa sweetie ka wuce tana can gurin 'yar daru ita da dare take
tata rigimar amma da Rana lafiya kalau za'a wuni da ita".
Dan murmushi Mahmud yayi Yana ayyana Wai babyn su ce da zahra suna tarairayarta.
Yana fitowa harabar gidan motar sayyid tana shigowa, dai dai gurin Mahmud ya tsaya ya kashe
motar ya fito da sauri ya rungime Mahmud Yana fad'in .
"Ina ka shiga a duniyar nan ka barmu da tashin hankali? Munyi nema har mun godewa Allah
kasan Umma cewa tayi a saka nemanka a jaridu da mujallu da kafafen sada zumunta na
zamani,Su uncle Mustaphan ne suka Hana sukace abun ze zama tonon sillil Wanda Bai sani
bama ze sani". Dan zare shi daga jikinsa mahmud din yayi Yana fad'in .
"Ai gashi Nan dawo sayyid ya karatu ace ka koma PhD ko?"
"Wallahi kuwa".
"To Masha Allah. Allah ya taimaka, Nima Zan wuce ne matar abokina na kawowa Aishat su
zauna a Nan asibiti sukazo zataga likita".
Ya mika Masa hannu yayi gaba, sayyid Yana da kirki amma fa gurin lamarin Mata sai a hankali,
ko baya Zina ta zahiri akwai 'yan tabe -tabe.
Yana fita ya turawa Aishat text message a waya.
Amma fa karfin Hali kawai yakeyi Sam zuciyarsa Bata nutsu ya tafi yabar zahra da wannan
Karen farautar a gidan ba, amma dole ya kauda Kansa yayi kawaici da Kara kada Ya Abbas
yaga Bai dauki maganarsa ba.
Koda ya koma su Habib suna gida Suma sun baro asibitin, coffee ya bukac Mr Ajey ya kawo
Masa ta wuce ciki Saida yayi wanka ya bude laptop dinsa Yana aiki Yana sipping din coffeen, ya
Kai kusan biyun dare Yana Abu Daya Saida ya tabbatar da komai ya dai daita sannan ya
kwanta zuciyarsa da gangar jikinsa suna mararinta, filo ya rungime a haka barci yayi awon gaba
dashi.
Bayan sun sallar Asuba barci mahmud ya koma knocking din da ake a kofar bedroom dinsa ya
tashe shi daga barcin da yake Mai Dadi Wanda ya saka shi nishadi.
Umarnin budewa ya bada Yana daga Cikin blanket dinsa.
Mr sunny ne Mai yin share share da goge goge.
" Good morning Sir"
Ya fada Cikin ladabi daga Bakin kofa sannan ya Dora da fadin.
"Akwai Baki daga Nigeria".
Wani smile yayi Yana tashi zaune yasan za'a Rina sai yanzu ya gane hikimar ya Abbas na cewa
ya dawo nan shi kansa baze so zahra taga dabin da za'ayi ba".
"Kaje ayi musu duk abinda ya kamata, Mr Ajey ya Basu abinci kafin na fito".
Toilet ya shige yayi suk abinda zeyi sannan ya fito Yana tsane sumar kansa da Karamin towel a
nutse ya Gama shirinsa ya fito a Mahmud dinsa, ya riko wayoyinsa hannu ya nufo main parlour.
Da uncle Mustaphan ya Fara yin tozali kafin ya sauke idanunsa a Kan uncle saminu, nan da
nan ya hade girar sama data kasa tamkar yaki ya rigshi kofar gari.
A ciki ya gaishe su duk da shafi ce ta shafi uncle Mustapha sai yayi musu kudin goro, neman
guri yayi ya zauna Bai Kara cewa komai ba, uncle saminu ne yazo iya wuya Dan ba haka yayi
zaton zega Mahmud ba l,Dan an Bashi assurance na ya Gama lalacewa,dan a yanda a kayi
Masa aikin rigar sawa ma sai tafi karfinsa, bare wani arzikinsa sai dai komai ya lalace masa, sai
ya Zama abinda zeci ma saiya fi karfinsa, sai Kuma yaga sabanin haka Dan yanda yake da
kyawun gani a yanzu ko kafin faruwar matsalar da suka Zama asasin fatuwarta Bai Kai haka
kyaun gani ba.
A zuciye ya taso yana fad'in.
"Kai din banza har yaushe kayi arzikin da zamu tako har inda kake ka wulakantamu eyeh? Ka
maida mu 'yan iska Wanda Basu San ciwon Kansu ba ko a Nan ma halin akuyancin kake
tabawa shi yasa ka makale kana gyallin goshi?'
Uncle Mustapha ne ya taso da sauri yana fadin.
"Meye haka kakeyi saminu? Daman abinda ka shirya kayi kenan? Amma kaji kunya wallahi Dan
zumunka? ko abinda kuka kitsa kaida munafukarka kuka lankaya Masa sharrin da gaske Yana
yinsa ai ka rufa Masa asiri ba kazo kana wannan shirmen ba Wanda Allah ya daga ya daga shi
sai dai mahassada suyi kuka, dai dai gwargwado meka nema ka rasa da yawa ta taka suke
nema Basu samu ba wace irin sutura ce Ubangiji baiyi Mana ba Amma ka tsaya kana yiwa dan
Dan uwanka hassada saboda Allah ya daukaka shi a cikin family din kace ya auri 'yarka yace
baya so to nuna kin jini na me Kuma wani ya taba auren matar daba tasa ba ka ragewa kanka
wannan walahar Dan babu inda zata kaika sai fagen Dana sani, Ashe 'yar burumburum kayi min
ka nuna komai ya wuce muzo mu tafi dashi gida". Sadda Kai saminu yayi baiyi zatom Mustapha zeyi masa haka ba Dan Saida ya shirya ya taho
da zummar duk abinda yayi babu Mai iya tanka Masa.
Maganar Mahmud uncle Mustapha ya tsinkayo daga bayansa.
"Ka daina Bata Bakinka uncle Wanda yayi nisa baya Jin kira,ni Mahmud ta zamar Masa kadan
garen bakin tulu ya barni na Bata ruwa a karni a Kar tulu, babu abinda ya Isa yayi min tinda
bashi ne ya halicceni ba Kare ya canza min kaddarata kuma har abada Bazan taba auren
wannan karyar 'yar tasa ba, yaje yayi bincken wacece ita kafin ya samu bakin fadawa mutane
maganar suna Zina aje asibitin tugar barau ka nemi solomon kaji sau nawa ya zubarwa da 'yar
taka ciki? Ko an fada maka bamu San haka ba Dan anyi shiru an kyaleta ba' a fasa maganar a
family ba idan kace karya ne yanzu na nuna maka hujjata Mai karfi, kaci gaba da abinda kake
kada ka fasa Dan Allah mu Zuba sharri dai Dan aike ne kada ka rufe kofa ze dawo Komai
Daren dadewa, uncle Mustapha kayi hakuri wallahil azim Bazan bika ba yanda na fito ni kadai
haka Zan koma indai da wannan mutumin zamu tafi Saida na mutu ban koma ba, bani da wani
Hadi dashi Wanda ze shige min gaba a dukkan lamurana.
Uncle Mustapha baiyi yunkurin Hana shi ba saboda yasan irin bakin Cikin da yaron ya kunsa a
wancan lokacin.
Juyawa mahmud yayi ze fice daga parlourn, uncle Mustapha ya riko hannunsa.
"Ina zaka tafi?".
Idunu jajur ya kalli uncle din, yana girgiza masa Kai, wallahi bazan zauna dashi ba idan ka
matsa min za'ayi Dana sani, yanzu babu abinda ze hanani nayi abinda banyi a wancan lokacin
ba, uncle kana da daraja da qima a idanuna to ka fada masa ya fita faga sabgata idan Yana so
ya tsira da Dan sauran mutumcin Daya yage Mana to ya kiyaye shiga duk abinda ya shafeni,
mu hadu a Sokoto two thirty flight dina ze tashi duk abin bukata a kwai shi a nan, idan ka shiga
asibiti Faisal ze rakaka gurin malamina ka duba shi anyi Masa aikin spinal cord ne"..
Ya kada ya fice abinsa.
"Yanzu irin wannan Ina ranar ta ka zubarwa da kanka qima da girma saboda sakawa Rai
hassada a banza, shima ya juya ya fice daga gurin zuciyarsa babu Dadi Dan ko kadan baiga
laifin yaron ba an Bata Masa fiye da kima. ya bar uncle saminu ya kasa ko kwakwjwaran motsi.
[19/02, 11:46 pm] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI*
AISHAT ISAH MUSAH.
(Maman Fateemah)
Bismillahir Rahamanir Rahim.
P. 73
........... Tunda Zahra ta farka daga barci taji Sam Bata Jin Dadi jikinta ita ba Mai zazzabi ba duk
jijinta ciwo yake Mata, ta Kuma kasa fita Dan Bata son su hadu da Dan gidanta kada ya Kara
Bata kunya Dan taga alama tasa tayi kaura daga idanunsa sai ya iya yi Mata abinda yafi
hugging ma ga Kuma uwa uba tana Jin bala'in nauyi Ya Abbas tunda ko banza yayan mijinta ne
ya wani kwakumeta ko kunya babu, agogon waya ta duba karfe Tara saura kwata na agogon
kasar, tattaunawrsu da Aunty Aisha ta ringa dawo Mata tiryan-tiryan. Tasha mamakin halin da
aka saka mahmud Ciki yaga masifa da tashin hankali ace kowa yayi maka naqi, kuma dadin
dadawa kowa ya kasa fashimtarsa, ta yarda kamar yanda Aunty Aishat din ta fada abun an
Dade ana shirya shi Saida aka Sha Kan kowa sannan aka fasa maganar, kuma tayi wani irin
tasiri Banda taimakon Allah da wani labarin akeyi ba wannan ba.
Yunkurawa tayi ta tashi sai taji tana bukatar kasancewa kusa dashi ta lallashe shi, abin tausayi
be kuma abunda ya fada gaskiya ne, sai yanzu ta gane gundarin me maganarsa take nufi duk
da na gari dole yabi iyayensa, kawai shedan ne ya tunzura ta ta hau dokin zuciya Mai mmakon
ta Zuba Ido taga yanda abun ze kasance sai ta kasa ta hau fushin fari, ai dole ma hakan ce
zata kasance tunda Yana da magabatansa, idan sun amince da auren da akayi Masa laba'asa
idan Basu amince ba shikenan.
Tana zuwa wannan gab'ar taji wata irin faduwar gaba, kada fa iyayensa Suki yarda da ita a
matsayin mararsa.
"No!!!. In Sha Allah mutu ka raba takalmin kaza.".
Ta sauko daga gadon gara ta fita ko tayi arba dashi tayi yanda tayi ta Shawo Kan kayanta.
Wanka ta shiga shaf-shaf ta fito ta shirya ta saka rigar cotton lace marar nauyi tana baza
kamshinta, bata daura dankwalin lace din ba karamin gyale ta Dan rufe gashinta dashi ta sako
plat shoes ta fito zata shiga kitchen tayi musu abin break fast kada ta Zama cima zaune sai dai
ayi a Bata. Parlourn ba kowa shiru sai karar a/c kakeji kawai sai Kuma sansanyan kamshin turarukan daki
tunda gidansu akazo, kitchen ta nufa Kai tsaye saboda tana da yakinin masu gidan Basu tashi
ba, da sauri tayo baya ganin mutum tsaye Cikin kitchen din daga shi sai boxer short da singlet,
shima Jin motsi daga bayansa ga wani scent Mai shegen Dadi ya bakunci hancinsa yasa shi
juyowa babu shiri.
"Ya subhanallahi!".
Ya fada lokacin daya Dora idanunsa Kan fuskar Zahra, da wani mahaukacin sauri ta juya fit ta
fice daga Cikin kitchen din, shima sayyid da sauri ya aje cup din Daya dauko ze Zuba coffee din
daya dafa.
Ko duriyarta sayyid Bai gani ba sai dai kamshin da tabar Masa.
Zahra na shiga daki ta Danna Masa key tana maida numfashi.
"Waye wannan Kuma da yake da irin wannan freedom din a cikin gidan matar aure irin haka?
Gaskiya wannan rayuwar da sake, dole meu amor yazo su bar shi ai da matsala sosai gidan
musulmi Kuma matar gidan Matashiyar mace Mai jini a jika, shaidan ake gudu gaskiya.
Wayarta ta dauka tana neman Aunty Hassana su gaisa.
______
Mahmud yana fita kofar baya ya koma ya shiga bedroom dinsa ya dauko abokiyar tafiyarsa
jakar laptop ya shiga mota sai tashin motar uncle Mustapha yaji Dan ya fita har waje baiga
mahmud din ba Bai Kuma kawo Yana Cikin gidan ba.
Da sallama ya shiga dakina da aka kwantar da Baba Malam din Yana zaune shi kadai Yana
lazimi ga kayan break fast Nan an kawo Masa Bai Kai ga cinsa ba.
Sallamar Baba malam ya amsa Yana fadin.
"Sannu da zuwa mahmudu, Amma yau kayi sakko, ya Naga ran naka babu Dadi lafiya dai ko?"
Dan murmushi yayi duk da iyakarsa fuska.
"Babu komai kawai dai bana Jin dadin jikina ne".
Ya fada Yana karasawa kusa dashi ya gaishe shi ya Kara duba Jikin nasa, abinci ya dauko ya
hada Masa yaci sosai sannan ya fada masa Yana son yaje Nigeria a yau in Sha Allah, addu'a
yayi Masa sosai tare da Kara bashi Baki yayi hakuri ta koma ga iyayensa, sadda Kai kasa yayi
kafin yace. "A karayi Mana addu'a can na nufa idan Allah ya amince Mana".
"Kai! Masha Allah kazo min da abinda ya faranta min Raina mahmudu ubangiji yayi maka
albarka ya Kara Kare ka daga dukkan sharri abin halitta Dan isar Manzon Allah s a w.w, kaje
babu abinda ze faru da yardar ubangiji,Ina Kuma Fadimar ko ba tare zaku tafi ba?".
"Eh su sai jibi zasu taho da Hasanata wadda Dan uwana da mukazo dashi ya dawo ya kawota
ta duba ka".
"Ikon Allah ai Bai min bayani ba yace dai ga iyalinsa tazo ta gaisheni, yanzu mahmudu daman
takwayene Kai? Koda Wai ban taba sani ba, ko danma Kai ai saidai hamdala Amma me kake
fada".
Murmushi yayi Yana Dan shafa sumar Kansa wadda Tasha gyara.
"Ayi hakuri yanayin ne yazo a haka".
"Babu komai hakan shine dai dai Allah yayi yagora ya Kara arziki Mai dorewa".
"Allahumma Amin".
Nurses ne Wanda suke bada maganj suka shigo, suka gaisa da malam Cikin harshen turanci
sannan suka gaisa da mahmud da yarensu, magunguna suka bashi ya Sha sannan suka
fice,Hira sukaci gaba dayi inda Baba malam ya dinga bawa mahmud Addu'oi masu karfi na
tsarin jiki sanan ya Kara bashi wata yace ya dunga karantawa duk bayan sallar farilla in Sha
Allah badai sihirin Dan mutum ba.
BISMILLAHI WA BILLAHI BISMILLAHI MASHA ALLAHU BISMILLAHI WALA HAULA
WALAQUWWATA ILLABILLAH ÷ QALA MUSA MAJI'ITUM BIHISSIHIR INNALLAHA
SAYUBDULUHU INNALLAHA LAYUSLUHU AMALAL MUBSIDIN FAWAQA'QAL HAQQU WA
BADALA MA KANU YA'AMALUN FAGULIBU HUNALIKA WQNQALQBU AAGIRIN. Godiya sosai mahmud ya yiwa Malam yace masa ze tafi Amma baze wuce sati daya ba ko biyu
ze dawo tunda ya