Showing 48001 words to 51000 words out of 65935 words
Chapter 17 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf
fadawa doctor kada a sallamar masa patient sai tafiyarsa ta nuna kukunna.
Yana fita ya Kira Mr salahuddeen yace su hadu a Airport ze dauko mota.
Karfe biyu da mintuna flights din su Mahmud ya dago Nigeria text kawai ya turawa Ya Abbas,
itama Aishar ya tura Mata nata da bayanin komai.
Sayyid ya Jima a tsaye a parlour ko zaga ta inda Zahra zata bullo Amma yaga Shiru dole ya
koma ya dauko coffee dinsa ya wuce dakinsa.
Bai Jima da barin parlourn ba Aunty Aishar ta sakko Cikin gayunta kitchen ta shiga ta Fara aiki
tana tunanin irin yanda Hussein ya gindaya Mata dokoki akan matarsa tana ganin soyayya
Amma sai take ganin Dan uwan nata yayi zurfi da yawa.
Tana Cikin aiki Sayyid ya shigo yayi Shirin fita school.
"Aunty Ina kwanq?" Ya fada Yana shigowa ciki.
"Lafiya kalau Sayyid har an fito yau da wuri haka? Gashi ko break ban Gama hadawa ba".
"No Aunty I am ok, Nasha coffee tun dazu, Wai Ni Aunty bakuwa kikayi a gidan Nan ne ko
Kuma gamo nayi da safiyar Allah wata"Ala?".
Dariya tambayar ta bawa Aunty Aishar,duk yanda akayi yaga Zahra kenan, Amma sai tace
masa.
"Meta faru Kuma kake wata magana irin haka?"
"Wallahi Aunty ba maganar jocking Naga yarinyar India ko larabawa a gidan Nan har fa Cikin
kitchen din nan ta shigo muna had a Ido ta fice kamar walkiya ko dana fita ko Mai kama da ita
bangani ba wallahi".
"Eh bakuwa ce nayi Baku San juna bane shi yasa ita ma Bata San da zamanka a gidan bane
shi yasa inaga itama tsorata tayi gaskiya".
"Wow! Amma daga Ina Kika samo irin wannan Mai zafin haka? Gaskiya za'a da ita Dan Allah
Ina kamu wallahi daga wannan Kuma kallo ya Kare ki Fara min campaign Dan Allah".
Ya fada Yana hade hannu irin ba 'yan kabilar Hindi na nan Indian din.
Anzo gurin tab Allah kiyaye da mijinta baya nan da a gabansa zeyi wannan kwabar da kuwa
sun kwashi 'yan kallo.
"Wai kana nufi sonta jakeyi kenan?"
"Kwarai kuwa".
Ya fada da tabbatarwa.
"To ai matar Aure ce".
Dafe Kai yayi Yana fadin.
"Oh my God! Waye wannan Mai sa'ar da yayi min shigar sauri Dan Allah?".
"Wanda ya fika sonta ne ya dauke abarsa".
Langabar da Kai yayi Yana fadin.
"Shikenan na wuce school, Amma fa I really loved her".
"Matar Auren?"
Baice komai ba ya saka Kai ya fice daga kitchen din ransa babu Dadi. "Allah ya kyauta, wato
mahmud ya yiwa Sayyid wani irin farin sani kenan, yasan matukar zeyi arba da ita sai an samu
matsala gashi kuwa ya kasa ba marad'a kunya".
Sai da ta Gama komai ta dauko abincin data Zuba musu ita da zahrar a wani guri ta aje basket
din ta koma ta dauko wani Abu kaman story mat da table mat ya shinfida sannan ta koma sama
lokacin sweet heart din ya fito daga wanka, taimaka Masa tayi ya shirya tunda shi azumin litinin
da alhamis yakeyi itama Aishar lalurar mu ta Mata ta hanata dauka, fita zeyi Yana da wasu
ayyuka da Mahmud ya turo Masa Wanda zeyi masa su, tare suka gangaro Aishar ke fadar .
"Bari na kirawo Zahra ki gaisa tunda ba lallai yau ku hadu ba naji kace sai dare sosai zaka dawo
aikin da yawa".
Dan janyota yayi jikinsa.
"Kyaleta ai Dan uwanki ya dasa Mana 'yar kunya a tsakaninmu tunda yayi mata irin wannan
wawar rungumar a gabana kamar ze bude aiki kinji yanda jikinsa yake tsuma kuwa a lokacin?"
"Kai sweet heart Banda fa... Dan kaga baya kusa, shida abarsa har zakace Wai jikinsa Yana
tsuma Kamar wani sabon shiga".
"Ni dai abinda naji nake fada Miki bawai Qage nayi masa ba, Kika sani ko farin shigar ne koma
Bai shigan ba".
Ya fada yana dage Mata girar idonsa Daya.
"Wallahi Kai dai Yaya Babba ne, Banda irin haka da gani kasan ai Yana shanawa dubi fa yanda
ya damu daga Dan turza shi da tayi yanzu ma kaji yanda yake jaddada min na kular masa da ita
kamar wata jaririya".
"Ke dai mubar maganar lokaci ne ze nuna".
Har gurin mota tayi masa Rakiya tana fada Masa zasu fita fa.
Sama ta koma ta dauko Afnan wadda ta koma barci tun da akayi Mata wanka Dan kada ta tashi
suna can bazajiyo kukanta ba.
Dakin Zahra ta Dan buga kadan tana fadin.
"Pls open the door" .
Jim muryar Aunty Aishar yasa Zahra tasowa da sauri ta bude kofar tana sakin murmushinta Mai
kayatarwa.
"Ina kwana Aunty?"
Ta fada tana karbar Afnan dake barci, can tsakiyar gado Zahra ta kaita ta kwantar.
" Ki fito muyi break fast tun dazu na kawo na koma na sallami sweet heart ne shi yasa".
Tare suka jera zuwa gurin da tayi musu shinfida, abincin gargajiyar ba bahaushe tayi musu
kunun tsamiya ne da kosai sai pepper soup din cow legs.
Suna gamawa Zahra ta kwashe kayan ta mayar kitchen ta wanke su ta aje komai a muhallinsa,
taso ta yiwa Aunty Aishar magamar guy dai data gani sai wata Zuciyar ta kwabeta, Bata sani ba
ko kaninta ne shaqiqi muharraminta.
A gurin ta dawo ta Sami Aunty Aishar tana amsa waya daga ganin yanda take amsawa kasan
ba wayar sawa bace Mai wayar Yana da girma da kima a idanunta.
Zahra Bata zauna ba ciki ta shige tana shiga taga Afnan tana daddaga kafa tana Wasa ta tashi,
daukarta tayi tana fadin.
"My Afee Babyyy.."
Yarinyar na ganinta ta Fara dariya shaidar ta ganeta kenan.
Saida Aunty Aishar ta Gama wayar ta shigo tana fadin.
"Au Kice mutuniyar ce ta tashi? Sai ki shirya fita zamuyi yanzu guri ya kure sosai kinsan
Hussein shi komai nasa baya fada sai guri ya kure, sosai jibi fa zamu wuce Nigeria shine yace
muje kasuwa kiyi tsaraba shi ya wuce Nigeria".
Da madaukakin mamaki Zahra ta dago ta kalli Aunty.
"Ya wuce Nigeria?"
Sai idonta yayi kwal-kwal ta tabbata abinda ya fada gaskiya ne, shikenan ita Kuma haka tata
kaddarar take.
Girgiza Mata Kai Aunty Aishar tayi.
"Haba Banda shagwaba Mana, keda kike fushi dashi, yasan ko yazo bazaki saurarasa ba shi
yasa ya tafi tunda baisan laifin da yayi Miki ba kike dafa shi da naki salon, Dan Allah a
rangwanta Masa shi bako ne a cikin soyayya Bai taba yinta ba ke Kuma Naga taki da zafi ta
kamashi batayi Masa da Wasa ba". Da kyar ta iya mayar da hawayen, da suka so zubowa ta rasa dalili itama tata zuciyar Bata da
wani karfi a Kan lamarinsa.
"Shike nan Aunty inda sabo na Saba yayi tafiyarsa Bai fada min ba".
Aunty Aishat ji tayi yarinyar ta Bata tausayi, kenan shima Yana gwada Mata halin miskilancin
nasa, nata ne baya iya jurewa.
"Ki rabu dashi tafiyar ce tazo masa ba zato kiyi hakuri dole zamu zauna ya daina Miki irin haka
tunda ke ba sanin halin yawonsa kikayi ba, inaga duk duniya Amminsa kadai yake bude Baki ya
fada Mata duk inda zaya a cikin duniyar nan kafin yayi fushi kenan".
A hanya ma sosai Aunty Aishar ta dinga bawa Zahra Baki harta Dan ware, sun shiaga manayan
shagununan kayan sakawa Ganin Zahra taki daukar komai yasa Aunty Aishar lodar kayan da
take ganin sun dace, sunje bangaren jewelry's ma ta dauka Kamar me shoes and bags ta
dauka kamar Gori ita Zahra Abu har tsoro ya Fara Bata kashe kudi ake kamar yayi daurin cargo
aka yiwa kayan Aunty Aishar ta cike komai sannan suka bar gurin, sun shiga kasuwa nan ma
ba kananun kudi ta kashe ba suma awon cargo din tayi musu daga karshe suka nufi gurin
gyaran gashi da jiki Aunty Aishat ta saki kudi ba kadan ba anyi Mata gyara iya gyara, suna Cikin
Yi Mata gyaran jiki matar Mai gurin tazo tana tambayar Aunty Aishar cikin yaren indianci, tunda
su dai basa Jin turanci duk da India suma suna English.
Zaru Aishat din tayi domin ta rasa yanda zata tunkari Zahra da tambayar domin wani Abu matar
ta sakawa Zahra a hannu taga yaki Zama kuma a ka'idarsa na matan aure ne kuma an fada
Mata matar Auren ce gyara kawai za'a Kara yi mata, magana matar tayi Mata akan taje ta
tambayar Mata ita saboda tasan wane iri abubuwan zata yi Mata. Aunty Aishar ji tayi abun yayi Mata nauyi gaskiya, ai da kunya taje tana titsiye yarinya da irin
wannan tambayar,cewa tayi suyi Mata na 'yan matan kawai mantawa tayi tace musu haka ashe
Bata tare ba.
Zahra har Saida ta gaji da Shan abubuwa, Miko Mata ake tana shanyewa Saida taji tana neman
yin amansu sannan aka saurara Mata aka dosa tureren jiki, kunshi ne tace bata son irin nasu
Mai yawan Nan sai akayi Mata Dan kadan Mai azabar kyau, lokacin da aka Gama Mata komai
ta fito Saida Aunty Aishar ta shiga wani shock Dan yes matar bros ta wanku iya wankuwa Ina
ma Yana Nan da yau dai saiya maida yawu kenan maganar sweet heart da kamshin gaskiya
kenan tunda idan ba Rami meya kawo zancen Rami ance an saka Mata abun matan aure yaqi
Zama kenan budurwa ce, ita kwamacalarsu nema take tafi karfin tunaninta.
Sun dauki hanya sosai Afnan na jikin Zahra duk tayi laushi da gani ta gaji, sai 'yar mita take
Auntyn ce da Dan kallo inda suka tana ci gaba da driving din ta, tamabaya ta jefowa Zahra Wai
dazu kun hadu da Sayyid ne da safe?".
Dan Jim Zahra tayi sai Kuma tace "ko wani Dana gani a kitchen daga shi sai boxer short da
singlet Yana tsaye a gurin coffee maker?"
"Eh shi nake nufi".
"Na ganshi lokacin Dana fito da zummar na Dora abin break sai na gashi ba yanda ya kamata
ba tunda baligi ne shi Kuma ba gidansa bane, Kinga ai Bai kamata Yana fitowa a haka ba,ko
Dan bansan ya kuke dashi ba ko mamanku daya".
Wata kwana ta shiga kafin ta danyi tsaki..
"Wallahi kanin sweet heart ne, ni kaina bana son zamansa a gidan tunda idan Yana nan bana
sakewa nayi duk irin shigar da nakeso tunda Allah yasa shi Mutum ne Mai shegen son Mata
dan haka yau a sama Zaki kwana bana son samun matsala Daman abunda yasa na baki daki a
kasa Ina muku wani zato ne ashae hasashena gaskiya ne, yanzu kuwa da baya kasar saina
shige dake ciki gudun samun matsalar da yaketa jamin kunne a kanta".
Nisawa Zahra tayi tana fadin Allah ya kyauta.
Koda suka shigo Basu huta ba abin bude Baki suka yiwa masa.
A tsakanin kwana biyun nan Zahra ta gaji iya gajiya
Kuma Basu Kara haduwa da Sayyid ba,dan duk wata kafa Aishat din ta toshe ta yayi nacin har
yayi zuciya Dan ko kasa Bata saukowa.
Ranar da zasu tafi Mr salahuddeen yazo ya daukesu da kayansu sai a ranar Abulkhairi ya dawo
gida, har dashi za'ayi tafiyar.
[23/02, 12:00 pm] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHIN*
. AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fateemah.
09061432330
Or
08055362975.
Page 75
......... Tunda jirgin su zahra ya sauka a filin jirgin sultan saddiq Abubakar dake Sokoto gabanta
ke faduwa,tasan a Nan ne komai fa ze iya tabbata ko ayi ko a fasa gata a Sokoto sai Kuma
abinda Rabbi Izzati ya hukunta shi ne ze tabbata, Afnan ce a sabe a kafadarta tana takawa a
hankali tamkar Bata son taka kasar Dan da gaske ta Gama yin giving up a cikin Lamarinsu da
mahmud.
Aunty Aishat ce tsaye a Kan kayan da sukazo dasu Saida komai ya kammala sannan ta nufo
inda Zahra suke ita da Afnan yayin da Abulkhairi yake biye da ita kafa ya kafa.
Kamar tare Aishat din suke da Sameer Dan tana karasowa shima Sameer Yana karasowa da
waya a kunne da alama doguwar waya yakeyi, saida ya Gama sannan su zahra suka gaishe
dashi har Aunty Aishat na fadin.
"Nayi fushi kaje har India amma ka kasa zuwa mu gaisa".
"Kiyi hakuri kinsan halin kayanki bashi da lokacina a lokacin Kuma infact ma dai bai barni na
zauna ba".
"Ai shikenan Daman ku Ina kuke Zama guri Daya tamkar marasa gaskiya Baku da standard
gurin Zama dole ku canza yanzu kun aje iyali suna da hakki a kanku baze yuwu ki ringa Abu
babu lisafi ba Daman kasan tun farko Ammi Bata son wannan dabi'ar taku ko misqalazarratin
Sai dai da yake Abbie ya tsaya muku ne yasa dole ta hakura". "Wannan gaskiya ne Auntyn mu za'a gyara in Sha Allah ko Baki fada ba zakiga canji ke dai kisa
Ido kawai zakice na fada Miki".
"Allah yasa hakan ta kasance".
"In Sha Allah".
Sameer ya fada yana Dan kallon zahra ta gefen Ido tana ta yiwa Afnan Wasa.
"Madam barka da sauka sokoto Allah yasa mun shigo kenan, yasa Albarka a cikin rayuwar da
zakiyi a cikinta".
Dan murmushi tayi, yayin da Aunty Aishat ta amsa da. "Allahumma Amin, ni jikina ya Gama
bani zahra Alkhairin mu ce".
Kayansu aka dunga jida ana kaiwa mota Sameer sai mita yake yiwa Aunty Aishat akan sun lodo
Kaya bayan Wanda suka turo jiya sukazo yauma ga wasu.
Kunnen uwar shegu tayi masa sufa sunfi son daga su sai kayan jikinsu, tunda suka dauko
hanya zahra ke kallon garin, yayi matukar burgeta ba kadan ba tayi santinsa duk da hankalinta
ba a kwance yake ba Amma ba karya sokoto tayi Mata % sai dai Bata San meze biyo bayan
zuwan nata ba, wata zuciyar ta fada Mata. "Khairan in Sha Allah"
Take ta Fara addu'ar sauka a sabon garin da kaje ba garinku ba, Dan harga Allah ta manta.
"RABBI ANZILNI MUNZILAN MUBARAKAN WA ANTA KHAIRUN MUNZILIN".
Ta fada a zuciyarta tana rokon ubangiji ya dafa Mata a cikin lamuranta gata ta shigo garin da
babu uwa ba uba ba dangin iya babu na Baba sai wannan bawan Allahn shi kadai ta sani,
kallon garin taci gaba dayi daga kasan Zuciyar ta Kuma abubuwa ne rututu gasu Nan.
Wani katafaren gida taga Sameer ya dosa tamkar fadar shugaban kasa, Zahra hankalinta ta
tattaro ta nutsu taga Nan kuma Ina ne Sameer ya kawo su Yana tsayawa a kofar katafaren gate
din Mai Kama Dana kofar gari saboda girmansa wasu masu uniform suka taso su uku suka
Karaso gurinsu Sameer kafin su Karaso sameer ya sauke glasses dan bada da baya,suna
sameer ne suka gaisa sannan suka gaisa da Aunty Aishat da suke zaune a baya.
Katafaren gata din aka bude musu suka shige, " masha Allah".
Abinda zahra ta fada kenan a zuciyarta, wasu gine-gine take ganowa kamar a cikin film, an
kawa gefen titin da flowes masu kyau da fitilu compound din ba mutane sosai sai 'yan tsiraru
masu banruwan flowers har kofar part din Ammi na baya sameer ya kaisu ita dai zahra ba baka
sai kunne Dan ba karya gidan gida ne tamkar dauko ginin akayi aka Dora a gurin a zuciyarta
take tunanin meya yi zafi da har Wanda yake rayuwa a nan ze tsallake ya bar shi yaje yana
rayuwar kwanan shago, ita dai saida Aunty Aishat ta Dan tabata ta dawo hayyacinta.
"Mu shiga ciki?"
Fitowa tayi dauke da Afnan a kafadarta tabi bayan Aunty Aishar wadda me rike da hannun
Abulkhairi, numbers Auntyn ta saka ta bude kofar Dan juyowa tayi kadan tana fadin "Bismillah".
A hankali zahra tabi bayan wasu parlours suka ringa ratsawa na garari sai da suka wuce parlour
biyar sannan Aunty Aishar ta cewa zahra ta Dan jirata tana zuwa ta nufi upstairs tana rike da
Abulkhairin.
A kan center carpet zahra ta zauna tana wasa da Afnan wadda duk tayi laushi ta gaji danma
yarinya ce mai hakuri, dogon tunani zahra ta shiga bata taba tunanin maganganun Hajiyar
makwarari gaskiya bane sai Yau wallahi duk a lokacin shirbtun tsufa ta dauki zancenta Ashe
batama fada mata gaskiyar zancen ba. A sama direct bedroom din Ammi Aunty Aisha ta nufa knocking tayi daga ciki taji Ammin na
fadin "shigo mana batool kinsan bana son yawan damu da safe"
A hankali tura kofar ta shiga da sallama, ai Abulkhairi na ganin Ammi ya Zane hannusa daga na
mamansa ya ruga ya rungume Ammi wadda tayi tsaye kawai tana duban Aishar Dan ba
karamin mamaki ta bata ba."surprise ko Ammina?"
Ta fada tana shgewa jikin Ammin tana dariya.
"Kin kyauta kenan ki dauko jiki daga uwa duniya Amma bazaki fada ba ko Addu'a ayi muku sai
dai ba ganku ba zato ba tsammani".
" Afuwan my Ammi nima bansan da tafiyar ba sai shekaran jiya waccan, kinsa dan gidanki baya
jira".
"Ina kika ganshi ko kuma daman yana tare dake kika ki fada? Ina kuma Afnan din take?".
" suna master parlour da bakuwa mukazo fa".
"Bakuwa kuma?".
" Eh shigowa nayi na fada miki, to sannunku da hanya muje kasan a Samar muku abun break
fast".
Suka nufo kasan takun takalmansu das das ya saka zahra dago kanta daga wasan da take
yiwa Afnan tana bulbula dariya, caraf suka hada ido da Ammi nan da nan taji gabanta ya fadi,
itama Ammi wani shock ta shiga babu ko tantama wannan fuskar take gani tare da Hussein
dinta a mafarki yau gata a zahiri, tayi mafarkin yarinyar nan yafi sau shurin masaki me hakan ke
nufi kenan.
Suna shigowa kamshin Ammin ya hade parlourn.
Zahra ba tayi tunanin haka zataga Ammin ba, babu Wanda zece ita ta haifi su Aunty Aisha sai
dai ace yayarsu ce, 'yar gayu ce ta ajin karshe ga jindadin daya hana shekarunta nuna Kansu,a
hankali take takowa idanunta na kan zahra wadda taji wata irin kunya ta rufeta, gurin da suke
zaune Ammin ta karasa tana fadin. "Sannunku da hanya, a kunya ce zahra ta bude bakinta tace.
" yauwa Ammy, ina kwana"..
"Lafiya kalau ya gajiyar