Showing 51001 words to 54000 words out of 65935 words
Chapter 18 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf
hanya?".
Ta fada tana mika hannu zata dauki Afnan, makalewa tayi a jikin zahra alamar bazata zo ba.
Gaba Ammin tayi ta zauna tana fadin huta roro waken gizo yaqi 'ya'ya".
Aunty Aisha ce dubi Ammi tana fadin.
" Ammi ga zahra nan 'yar Amanar Hussein diyar mai gidansa ce bata da lafiya aka kaita India
ganin likita shine yace na taho da ita Nigeria kafin yazo su 'yan jihar bauchi ne katagum local
government sunanta Fateemah zahra".
Dan gyara zama Ammin tayi tana kara kallon zahrar from head to toe, haka nan taji wani Abu
yana mata kai kawo a kasan zuciyarta.
"Sannu fateemah ya jikin naki?".
Kanta na kasa bata yarda ta dago ba ta amsa.
" Da sauki Sosai".
"Masha Allah, Hasana rakata sama dakin fake opposite da bedroom din ki bude Mata tayi
wanka kafin a hada muku breakfast".
" To Ammi bari muje,ko kuma muje can gurina saita zauna tunda duk cikin part din nan ne".
Kaita girgiza "kaita sama inda sauran 'yan uwanta yara suka can gurinki ba zataji fadi ba nan
kuwa gasu Batool nan kuma ba kince bata jin dadi ba sai saida babba a kusa maza kuje lokaci
yana tafiya gara taci abinci ta kwanta ta huta tunda ba irin ujilarku ta iya ba".
A kunya ce zahra ta mike tana sabe da Afnan.
Saida suka bacewa ganin Ammi sannan ta dauke idonta daga kallon zahra.
" ya rabb kai kasan abinda ke boye da make nuna min yarinyar nan tare da Dana sauran sirrin
kuma bani da masaniyarsa, ubangiji ka tsareni jin abinda ze zamar min tashin hankali".
Ya fada a cikin murya mai rauni.
Suna shiga dakin Aunty Aishat din tace "wow! Lallai matarmu you are special ai bansan haka
Ammi ta hada wannan bedroom din ba, bari na sauka da wannan 'yar taki makale matar kawai"
Ta dauko ta tana kuka ta fice da ita, tana jin Zahra na magiyar ta dawo da ita tayi mata wanka
Amma ta wuce kawai.
Lokacin da Aishat din ta sauko bata samu Ammi da Abulkhairi ba itama wata hanya ta nufa tana
dan jijjiga Afnan.
Kafin minti arba'in an hadawa su Aishat breakfast mai rai da lafiya, zahra tana fitowa daga
wanka tayi tsaye a gaban mirror tana kallon kanta yanda tayi wani irin kyau na ban mamaki
wato Inda ake gyaran jiki anayi dan tamkar anyi mata wankan inji,lotion din data gani ta Shafa
tunda nata da take shafawa yana can cikin kayansu ba'a shigo dasu ba saida ta gama shafawa
tayi turus Ashe bata da kayan sakawa kuma gashi towel din jikinta ma karami ne kusan Rabin
cinyoyinta duk a waje suke, gefen gado ta koma ta zauna ita dai bazata iya mayar da kayan
data cire ba, dan kwanciya tayi a jikin pillow dan tunda tayi wanka wata irin kasala ta saukar
mata ba, tayi minti biyu ba barci yayi awon gaba da ita.
Jin shirun zahrar yayi yawa yasa Ammi tacewa Aishat ta bita ta kirata ko nauyin saukowa takeji
tunda taga yarinyar akwaita da kunya.
Sau biyu tana knocking Amma shiru, kamar ba mutum a dakin a hankali ta murda handle din ta
tura kofar ganinta tayi tana barci,komawa tayi a hankali dan bazata so ta gashi taga ta ganta a
haka ba, haba dole bros ya rikice musu Ashe shi yasan sirrin kayansa Ashe a fuska wasa ne,
tasan Allah ne yayi mass tukuicin kazafin da akayi masa ya bashi irin wannan yarinyar. Sai data fara gangarowa ta tuna Ashe bata da kayan sakawa a tare da ita.
"Ya salam! Wallahi shaf ta manta tunda su basa dauko kayan sakawa suna dasu a nan.
******
Saida Mahmud yayi barcinsa mai isarsa ya tashi, sau uku Hajiya Inna tana zuwa ta buga masa
daki tana jinsa a rufe, wanka yayi ya fito cikin yadin filtex mai laushi fari tas, a parlour ya samu
Hajiyar da Aminiyarta Innoni suna hira, kusa da Hajiya Innar ya zauna yana gaishe da innonin,
kama haba tayi.
" kai kuma yaushe ka dawo garin namu?".
Tabe baki Inna tayi "kin gashi nan saida malamai suka gama karbar nasu rabon ya mula ya Mile
ya dauko jiki sinkin fakiti ya dawo, yazo kuma ya zaune min yaki ko leka kofar gidan nan, kofa
gidan iyayen yaki zuwa ni naga ta kaina kasan da irin wannan ranar amma ka tsallake kayi naka
guri sai yanzu zaka zo kana daddofar na kaika gidan". Wata dariyar da bai shirya ba ta kubce masa.
" Amma wallahi matar nan kin gama dani ni zaki cewa ina kamun kafa fake ki kaini gida,ni kadai
na fito ni kadai zan koma kuma kinyi da dan halak idan na fice sai kin shekara baki sakani a
idanunki ba".
Ya mike ya nufi kofa, nan da nan Hajiya inna ta rude.
"Idan ka bawa Annabi daraja ka dawo wallahi wasa nake maka ga abincinka can kazo kaci".
Ya tsaya Amma bai juyo ba.
"A aje min idan na dawo zanci lokacin magariba ya karato masallaci zani".
Yana gama fada ya bude kofa ya fice.
" miskili kawai idan ba haka nayi masa ba ko gidan baze leka yau ba duk kuwa yanda yake da
kawa zucin uwa".
"Ai mutumin naki sai ke".
Saida ya gaisa da masu gadi sannan ya shiga motar da yazo a ciki ya nufi unguwarsu tunda
babu nisa daga unguwar su Hajiyar, yana shiga ana kokarin tayar da sallah da sauri ya shiga
cikin masallacin gidan nasu tunda da alwalarsa.
Sahun bayan su Abbie dinsa yayi sallah da aka idar masu fita suka fita shi daman a dabi'arsu
yawanci basa fita sai sunyi insha'i zirillahi yaci gaba dayi Abbie din bai juyo ba shima bai matsa
ba sai Babban yayansu Ibrahim da yake daga jikin ginin masallacin ta kudu yake mamakin
yaushe Mahmud din ya dawo kuma uncle saminu ya dawo dazu yace Mahmud ya gudu daga
India, uncle mustapha ya bazu nemansa to ga Mahmud kuma a sokoto ga uncle mustapha ya
sauka a abuja ze biyo jirgin karfe bakwai na dare zuwa sokoto to me kenan hakan ke nufi?
Shifa daman ya dade yana zargin uncle saminu da wasu abubuwa marasa kyau a tsakaninsu.
Ana idar da insha'i Mahmud ya tashi ya fice kafin Abbie din su ya tashi, hannu kawai ya dagawa
securities din ya wucesu suna faman murna dan sunsan kakarsu ta yanke saka mai yiwa dawa
ruwa bare gashi a karkara,koda bayanan sakonsa yana iskesu to bare gashi ya dawo.
Ya dan jima a parking lot na gurin Ammi yana Karewa harabar gidan kallo ko ina haske ne tar
ga wata iska mai dadi da take busowa cikin motar tare da kamshin furanni mabanbanta,
abubuwan da suka faru suka dunga dawo masa daki-daki lumshe idanu yayi baiyi aune ba yaji
ruwan hawaye suna bin kumatunsa abinda baiyi ba kenan duk badaqalar da aka sha a gidan
nan a lokacin, kansa ya kifa jikin sitiyarin motar baiji alamun tafiya ko wani Abu sai dai jin
hannun mutum yayi a bayansa bai dago ba, bubbuga kafadarsa yaji an fara kafin ya tsinkayi
muryar Abbie dinsa yana fadin.
"Haba! namiji baya kuka tunda ka iya jure kwaramniyar baya baka nuna rauni ba yanzu lokacin
fuskantar gaba ne taso mu shiga ciki kada kannanka suga kana kuka, su raina min kai".
Da Saudi ya dago jin furucin da bai zata ba daga bakin Abbie idan yayi la'akari da lokacin da
guguwar abun ta tashi tsine masa ne kawai baiyi ba Amma yayi masa wata irin tujara ta Ala
tsine uwar mai karya.
Jikinsa ya fada yana fadin.
" wallahi Abbie ban aikata ba! Ban taba zina ba, ka bani Qur'ani zan rantse da Wanda ya
halicceni idan na taba zina a rayuwata Allah yayi min abinda yaso na azaba, ka yarda dani ka
fadawa Ammi banyi ba sharri ne akayi min na fada Amma Baku yarda ba...kum..."
Sai jikinsa ya langabe ya saki.
Da sauri Ya Ibrahim dake tsaye a gefe Wanda shima hawayen yakeyi ya zaburo yana fadin .
"Suma yayi Abbie bari na samo ruwa"
Ya tafi da gudu ya haura steps din part din Ammi, suna zaune ya bude kofar afujajun baiko kalli
su Ammi ba da saura yaran yayi kitchen da gudu ya dauko ruwan sanyi da sauri Ammi da
Aishat da Batool suka rufa masa baya Ammi na tambayarsa menene? Bai ko juyo ba yayi
gaba,suma gurin daya nufa suka nufa turus sukayi ganin Abbie a tsaye rungume da mutum Ya
Ibrahim yana bulbula masa ruwan sanyi.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da shashsheka abinya yake fada yaci gaba da fada.
Ka fadawa Ammi ni ba nazinaci bane ban aikata ba".
"Pls kayi shiru mana ta sani ka kwantar da hankalinka bama zarginka kaga Amminka tana jinka
fa".
Da sauri ya juyo sai kuma jiri ya kwashe shi ze zubar Ya Ibrahim yayi saurin rike shi suna faman
jera masa sannu, juyawa Ammi tayi idanunta fal hawayen tausayin dan nata kenan duk tsawon
lokacin nan yana fama da wannan damuwar wadda sai yau ya fasata gashi zata janyo masa
matsala a lafiyarsa. " Allah ka biwa yaron nan haqqinsa".
"Allahumma Amin".
Taji su Batool sun fada sai lokacin tasan a fili tayi addu'ar.
Su zahra na tsaye tana dauke da Afnan tun shigowar Wanda ya dauki ruwa ya fita su Ammy
suka bishi taji gabanta yayi wata irin faduwa, ta mike tsaye ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai
kuma taga an shigo da Mahmud din a rirrike yana layi kamar Wanda ya bugu da kayan maye.
Ai bata San yanda akayi ba ta dira a gabansa jikinta yana wata irin tsuma cikin rufewar idanu da
manta a ina ma take ne ta fara fadar
" Na shiga uku meya sameka meu amor...? Me akayi maka fada min dan Allah..."
Hannu Aunty Aishat da Dora a bakinta data bude tana fadin.
" kai? Wonderful...! the game is over".
[23/02, 11:59 am] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI *
AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fateemah.
Page 76.
.............. Aunty Aishat ce tayi sauri tazo gurin zahrar saboda kowa a gurin wutarsa daukewa
tayi barema Abbie da Ya Ibrahim da Basu da masaniyar da wata bakuwar fuska a gidan, itama
zahrar sai data fada ta dawo Cikin hayyacinta, wata irin kunya ce ta rufeta taji kamar kasa ta
tsage ta shige Dan kunya, me tayi kenan shike Nan tayi abun kunyar da zata Dade Bata hada
Ido da Amm bai wallahi.
Kan kujerar dake kusa dasu su aje Mahmud Wanda tun dirowar Zahra gabansa yaji wata irin
Rahama ta saukar Masa a zuciyarsa badan a gaban iyayensa bane saiya Bata hot kisses na
nuna godiyar nauyin data sauke Masa Cikin kankanin lokaci ta isar da sakon Daya Dade Yana
tunanin ta Ina ze bullo musu Sai gashi in some minutes tayi musu aikin.
Aunty Aishat na rike da hannun zahra suka shige Cikin wani parlourn har lokacin jikinta Bai
dawo normal ba, Afnan Auntyn ta karbe daga hannunta suka zauna.
"Ki nutsu babu fa abinda ya same shi inaga farin ciki ne ya sakashi sumewa, kinsan mutumin
naki da kwakawar son iyaye kinsan kuwa haduwar ai Daman za'a iya samun irin haka".
Ita dai Zahra kasa daga Ido tayi ta kalli Aunty Aishar wannan abun kunya har Ina da farawa da
iyawa ranar data sauka a ranar ta baza abin fada to Wai ita meye ya shiga kanta ne ta kasa
controlling kanta a gaban mutane?.
Itama Aunty Aishat Bata dameta da yawan magana tasan tana Cikin Jimamin abunda tayi
Wanda ya bude wwani murfin da suka kasa budewa sai gashi wadda aketa kunbi kunbiyar
bayyana wacece ita tayi ta bude aiki da kanta ba tare da itama ta sani ba, ta Kara girmamawa
girman Allah buwayi gagara misali Dan wani connection din idan aka hada shi sai dai kayi kallo
kawai, tashi tayi fice ta koma can main parlour din.
Da Ido Ya Ibrahim yabi su Aishat har suka fice daga parlourn Yana kissima abubuwa masu
yawa a cikin Zuciyarsa "kafa fa a gudu ba'a tsira ba".
Yayin da Ammi da Abbie suka dubi juna da alamar tambaya a fuskarsu, Ammi nayi masa wani
duba na Mena fada maka?.
Aishat na shigowa Hajiya Inna na shigowa atfujajan uncle Mustapha na biye da Auncle Autan
Hajiya Inna.
" Muhammadu Rasulullahi! Ni Hadiza Naga abunda ya isheni Ashe haka ka dunga gararamba
yaron Nan a cikin kasar nan kamar marar gata? saida ubangiji ya tallafeka da mutanan kirki
bayin Allah masuyi Dan Allah yanzu Nan Mustapha yazo min da wannan labarin daya jiyo gurin
bawan Allahn Daya tsinceshi a yashe a kasa ko takalmi babu a kafarsa ko magana fa yace
baya iya yinta a lokacin, wannan Dan taliki Ubangiji yayi Masa sakayya da gidan Aljanna, duk
Kuma Wanda yake da hannu gurin neman tagayyara min rayuwar jika Allah ya wulakantashi tun
anan duniya Kuma wannan yaron KAINUWA ne dashen Allah ba dashen mutane ne ba, ita
Kuma sameera mun barta da Allah suje suji da abun kunyarsu munafukarkar banza da Ido
kamar an rutsa mazuru a dakin tantabaru na godewa Allah da 'ya'yan da take haihuwa basa
Zama da yanzu ta tafi tabar mana mugun irin".
Ammi CE ta matsa kusa da Hajiya Innar tana fadin.
"Ayi hakuri Hajiya ai komai ya wuce ki daina tada hankalinki saboda lalurarki Bata son yawan
bacin rai".
"Yo bacin rai na nawa Kuma zainab ai saidai kada a Kuma".
Shi dai Abbie ya yayi shiru Yana jujjuya Lamarin a zuci.
Gurin Zama Ammi ta raka Hajiya Inna ta zauna kusa da inda mahmud yake zaune idanunsa a
rufe.
"Kai Kuma menene haka ta wani kike Riga sharaf ka kuma Kama ido ka rufe sai qif-qif kake
dasu kamar wani sabon makaho".
"Trouble woman".
Ya fada a zuciyarsa.
Abbie ne ya matso Yana gaishe da Hajiyar Yana fadin. "Haba Mustapha saboda me zaka dauko
ta da Daren Nan ku taho basai a barwa safiya ba".
"A'a nice nace baze taho ya barni ba kada ku taru ku nakasa shi a banza yanzu ma zuwa nayi
mu tafi ko abinci baici ba, gashi ya laimin kuwa nazo na tarar kunyi ira-ira da gani wani Abu
kukayi masa. Kai bude idonka ka fada min waye yayi maka wannan dibar albarkar ya jikeka
sharaf haka?". Abbie ne ya zauna daga gefenta Yana fadin.
"Babu Wanda yayi Masa komai murnar yaga Amminsa ce tasa ya sume Saida aka Zuba Masa
ruwa sannnan ya dawo hayyacinsa".
Tabe Baki tayi tana kallon Ammi wadda ta zauna daura da kafafuwan Hajiyar tana saurarenta.
"To Daman zuwa nayi na jawa kowa layi akan rayuawar yaron nan kada naji kada Kuma na
gani, anyi Daya babu Kari, Kuma na nazo Kan maganar waccen matar Mai idanu Yana
gwarawa wallahi ko bayan raina ka mayar da aurenta ban yafe ba sai Allah yayi Mana hisabi
akan,haka me akeyi da wannan matar Mai bakar aniya aini har abada bazan taba yafe Mata
ba".
Ta fada tana kallon Abbie fuskarta a hade alamar ranta a bace yake.
Hakuri suka dunga Bata mahmud najinsu Kuma yayi mirsisi ya bude idanunsa.
"Saika tashi mu tafi ka Gama zaman gidan nan gara ma kayi aure inga ta karyar sharri Kuma
haka kawai an takura maka kowa neman lika maka 'yarsa yakeyi an mayar da Kai na mamajo,
kazo muje Ina da yaran dana zabar maka har hudu idan ma duka kake so saina shige maka
gaba a aura makasu Rana Daya inga ta tsiyar kawo maka rida Kuma". Su dai hakurin dai suke Bata, shi kuwa da goyan tana ambatar ya tashi su tafi yayi wani Dan
murmushi a cikin Zuciyarsa.
"Tab ba inda zani yanzu dai da precious ke cikin gigita Sai taji dumina na kwantar Mata da
hankali Nima bana son mu zauna guri Daya matsla za'a samu gara muna Dan nesa".
"Wai bazaka tashin bane kayi min kunnen uwar shegu kana wani farfar da Idanu?".
Uncle Mustapha ne yace mata.
"Kiyi hakuri idan ya warware zuwa safe sai ya shigo ai Daman mahmud naki ne, bakiga a
gurinki yayi masauki ba daze tafi ma kece ta katshen daya gani kafin yabar gidan, kefa Dan
gata har sakawa yake azo takanas a kirashi video call Yana ganinki kofa tsiren da kikace Na
Maru yana badawa a kawo Miki saboda Alkawari tunda a gurinsa Mahmud yake sawo Miki Bai
daina kawawa ba, da naje nasameshi ya bani bill da adadin kudin tsiren Daya kawo Miki cewa
yayi Wai an turo Masa kudin tsirenki na shekara ne, Yana fadin haka nasan aikinsa ne, Dan
haka tashi muje na mayar dake gida idan Allah ya kaimu gone saina kawo Miki shi har gida" .
Yunkurawa tayi ta tashi sai lokacin idonta ya Kai Kan Aishat.
"Ke Kuma saukar yaushe Hasana? Ko Kuma ke Kika kawo shi kasar ne?".
"A'a bani na kawo shi ba arashi kawai akayi nazo shima yazo".
Mahmud naji suka wuce ita da uncle Mustaphan da uncle Aliyu.
Abbie da Ammi da Ya Ibrahim suka bisu a baya.
Saida yaji fitarsu sannan ya bude idanu Aishat da Batool kawai ya gani a parlourn duk sauran
yaran sun wuce ciki.
"Sannu Ya mahmud".
Batool ta fada tana Dan matsowa kusa dashi.
"Yauwa Batool"
ya fada Yana kallonta, Aishat din ya kalla Yana Mata inkiyar tana Ina?.
'yar dariya tayi tana fadin.
"Saboda Allah ka saka yarinya ta gigice irin haka har ta saki layi irin haka nasan saina amsa
tuhuma a gurin Ammi Dan Naga wani irin kallo da tayi min".
Batool ce ta Kara motsowa sosai ta kwantar da murya.
"Ya mahmud Wai da Allah wacece wannan? tunda na ganta naji Ina sonta ina sonta wallahi
gata very wise da ita, tana da kirki gashi duk abinda zata fada a Dan zaman da mukayi dazu
zakiga da hikima a cikin maganarta, hikimarta ta girmi shekarunta gaskiya, gashi Bata da Jin
Kai Sam idan wata ce yanda