Showing 27001 words to 30000 words out of 65935 words

Chapter 10 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf

03 Aug 2025

1497


tana da mafaka a can.
Dan murmushi tayi itama tana fadin "Yaya sunan bakon da babu sallama? Kawai na wayi gari
da ganin mutun ai dole na rasana".
Dariya yayi Yana fadin "Good morning Aunty".
"Morning".
Ta amsa masa a dan darare din nan ba wani sakewa, tana kallonsa.
"I am Faruq Dange".
Ya fada Yana juyawa zuwa inda yake aikinsa.
A hankali ta bude bakinta tace Masa.
"Sunana Fatima Zahra Muhammad Sani, Ina maka.barka da zuwa".
Tana Gama fada ta wuce can inda ta hango Kaya akan dining table.
Sakato yayi Yana kallonta Bai taba tunanin tana Jin yaren ba, Kai kawai ya girgiza Yana dan
murmushi Yana fadin "wato Ya Mahmud sai a barshi kawai sannin inda ya dosa sai Allah, shi
yasa kenan duk yayi d'iban Karan mahaukaciya da matan daketa rashin hankali a Kansa yayi
tafiyarsa ya kyale kowa da nata salon rashin hankalin".
Ledojin ta shiga dubawa taga Dame Dame Nene a ciki, Wanda su Fateeha da mommy ta Bata
ta cire ta aje a gefe sai Kuma Wanda ya sawo jiya ta cire na kitchen, kofar data gani a tufe taje

tadan tura ga mamakinta a bude ta ganta shiga tayi kitchen ne modern sosai babu abinda babu
a cikinsa tsayawa tayi tana nazarinsa kafin ta juya ta koma dauko Kayan.
Saida ta aje komai a muhallinsa sannan ta bude freezer data gani ta kwance, nama ne dasu
kifa da kayan miya a Nike cikin manyan bikitin roba, kaji biyu ta Ciro da Zuba a roba ta tarasu a
famfo saboda kankarar ta saki.
Filawa ta diba ta kwaba da yeast da barking powder ta rufe ta koma ta gyara Naman ta Dora a
wuta.
Wani ruwan ta Dora daban ta dauko Madara ta bude ta diba Mai yawa ta dama Zuba akan ruwa
data Dora ta Dan zame murfin sannan ta ciro hollandia custard ta fasa ta dibi yanda take ganin
zata ishesu ta dama ta aje a gefe. Plates da cups da duk abinda tasan za'a bukata ta dauko ta
wanke ta aje a muhallin Daya dace. Filawar data kwaba ta dauko taga ya tashi ta ringa murzawa round sai ta Gama ta shafa Mai a
frying pan ta rage wuta ta shiga gasawa tanayi tana juyawa.
Biyu ta raba Naman ta dattaka rabi tayi source Rabin Kuma tayi pepper soup dashi ta dama
custard din ta dafa coffee Kuma.
Tun daga sama Mahmud ke jiyo wani irin kanshi girki yayi tunanin ko da wani sabon restaurant
a Nan kusa dasu, Saida ya fito yana saukowa yaji kamshin ya cika gidan.
Shigar kananun Kaya yayi yayi masifar kyau, yau shigar da yayi ta fito da ainihin ko waye shi
Dan ba karya kana kallonsa kasan matashi ne Mai cike da Jin Dadi da wadatar arziki Dan
agogon dake hannunsa kadai na millions of naira ne, shigar da ya Jima da daina yinta Nan gida
Nigeria rabon da ya fito haka tun kafin ya shiga rubibi. Hannu Faruq ya shiga tafawa Yana fadin "perfect match, wallahi kun Dace Ashe haka Auntyn
tawa take? Haba shi yasa baka sauraren masu yi maka rawar Kai, ya Mahmud Ashe da abinda
ka taka shiyasa kayi shuru ka kyale kowa, Mai irin wannan matar mezeci da tarkace irinsu
Safna, wallahi na Dade Banga ma'auratan da suka tafi da imanina kamar kai da Aunty na ba,
Dan Allah ka tsaya min na auri kanwarta pls".
Ikon Allah Mahmud ya tsaya yana kallo lokaci Daya faruq ya gigice masa wato yaga zahrar
kenan tunda ya sauko yaji gidan ya hade da kamshin girki yasa itace a kitchen, ko ba komai
yasan Allah yayi Mata baiwar iya abinci a Dan zaman da sukayi ya fashimci hakan.
Shi rasa abin cewa ma yayi a Kan kalaman Faruq, Dan uwansa ne na jini, amma ya gigice da
ganin matarsa, tab lallai da matsala Babba.
Bai nuna Masa komai ba sai Dan murmushi da yayi Yana fadin. "Ai mata ta ita kadai ce Bata da
Kani ko kanwa, nine wanta nine komai nata Sai dai ka duba ko a Ina ne Zan shige maka gaba
in Sha Allah".
"Dan Allah nidai ka taimaka ko cikin family dinta ne ayi min wanna alfarmar ka shige min gaba".
Kyale shi yayi ya nufi kitchen din lokacin ta Gama hada komai ta juyawa kofar baya tana cire jan
bayan kwakwa zatayi amfani da ita in anjima.
Kamshinsa ya Fara fada Mata ya shigo gurin a hankali ta juyo, Yana tsaye ya harde
hannuwansa a kirjinsa ya zubawa bayanta Ido,yanda ta juyo din nan shi Kansa da take
halalinasa Saida yaji wani yarrr a jikinsa Dan gani yayi gaba Daya ta canza Masa ga wani irin
cikowa da kirjinta yayi sosai. Lumshe Ido yayi Yana tunanin lallai dole addinin musuluci da yayi Hani ga mutum baligi ya
shiga gurin macen daba muharramarsa gaskiya. Yana can Yana tunani ya tsinkayi muryarta

tana fadin "Ina kwana" batare data Kara kallon inda yake ba.
Bai amsa ba ya danyi gyaran murya.
"Meye Kuma Ina kwana? Na fada Miki ki iya tarairaya ta wallahi, kada garin kallon ruwa kwado
yayi Miki Qafa, kina da kishiya fa kinsan idan ta fiki iya lafazi da tarairayata can Zan tare a
gurinta".
Warrr tayi masa da sexy eyes dinta tana Masa wani kallo.
"Yes ko Baki yarda ba? yanzu na Kira Miki ita ku gaisa".
Kai ta girgiza Masa alamar A'a.
"Come on, zo Nan ki fada min bakya son kishiyar?"
Ya bude Mata hannuwansa alamar ta shigo, kafada ta make ta aje kwakwar ta nufi famfon cikin
sink ta Fara wanke hannunta.
Cikin takunsa na nazantaka ya shigo ciki directly gurinta ya nufa Yana fadin "Ni gani na shigo
sai nazo ki bani hot one tunda ni ba'a son nawa".
Bai jira tace komai ba ya saka hannunsa ya rungumeta ta baya Yana shafa cikinta.
Shiru tayi Masa kamar ruwa ya cinyeta, Jin hannun nasa ya nufi wata jihar yasa tayi saurin rike
Masa hannu tasan idan ya karasa akwai damuwa sosai.
"Pls Dan Allah ka Bari kaga da bako a gidan kada ya jiyo mu fa".
Ta fada tana kokarin kwace kanta.
"Ok saboda shi Zaki hanani na sake kenan? To Bari na sender shi inda yafi wayo".
Dayan hannun ya saka ya ciro wayarsa yayi dialing din number Faruq, Sam batayi zaton
kiransa zeyi ba, Saida taji Yana fadar "Faruq kaje wancen part din ka qarasa aikin gani Nan
zuwa".
Bai jira yaji abinda yake kokarin fada ba ya kashe wayar ya Dora a gefen cabinet din kitchen
yana fadin "to saiki sake ki bani hakkina tunda sirikinki yabar gurin".
Juyota yayi ya hade bakinsu ya cire rolling din, yana shafar gashin da yaji gyara ga qamshin
hair spray sai tashi yakeyi ya jima Yana yamutsata kafin ya janye Dan Kansa yana Maida
numfashi.
Tsugunnawa yayi ya dauko Mata veil din ya rufa Mata a Kanta Yana fadin "dauko wasu flask din
ki zubawa Faruq nasa ki saka a basket na Kai Masa can idan ya gama ya tattara ya tafi gurin
bikin da yazo".
"Me yasa? ba yace min shi qaninka bane".
"Ok. Dan Yana qanena saina zauna dashi gida Daya Yana kalle min Mata ko? Ai ya tafi shine
mafita Dan akanki zamu iya batawa da kowa to maganin Kar ayi kada a fara, Dan Allah ki ringa
saka hijab idan munyi Bak'i ba kowa ne ze iya kawar da Kai a kanki ba Kinga kuwa yanda Faruq
ya gigice min na Nemo masa sister dinki, na fada masa babu Amma ya kasa fahimta sai rokona
yake na samo Masa mace ko cikin family dinku ne"
Ya fada a Dan zafafe.
Shiru tayi ta nufi abinda ya sakatayi Saida ta Zuba Masa komai ta saka basket din ta aje a gefe
ta dauko Wanda ta zubawa Mai gadi ta aje a kusa Dana Faruq din.
Malam Musa ya Kira yace yazo kofar parlourn su hadu, dauka yayi ya fice daga kitchen din
yabar zahra da dogon tunanin akan abinda yace Faruq din yayi.

___

Tunda garin Allah ya waye Ammah ke faman neman number zahra abin yaci tura, a yau dai
hakurinta ya Gaza Dan tun Daren jiya da zilai ta Kira Ammah tana fada Mata yanda fasalin
gidan da suke yake da kuma kudin da tace an Basu dubu ashirin da safe da yamma ma an
kawo musu wasu kudin dubu dari-dari ita da iya Rahane ga turamen atamfofi guda hudu hudu
da lace bibiyu, Kuma ta fada Mata tunda su zahrar suka fice Bata Kara ganin giccinsu ba ga
wayar ta ma a rufe.
Akalar Kiran Ammah ta canza ta shiga lalubo Number Abdul Hakeem.
Ringing din farko ya dauka yana Fadi "barka da Asuba Ammah, an tashi lfy?.
"Alhamdulillahi, idan ka tashi ka shigo Ina son ganinka" ta fada cikin damuwa.
"To in Sha Allah, gani nan shigowa"..
Ta kashe wayar, ta ajiye a gefe tana fadin "kazo ka nemomin wannan yaron ya fada min waye
shi Ina Kuma ya Kai min 'yata ko waya ya Hana muyi da ita inji meye dalilni Daya hana ta
amfani da wayar, tunda Naga Abban ba wani Abu zeyi ba, ga wannan kinibabbiyar matar tasa
da koma sai taji Masa kwakwaf". Tsaki tayi tana Jin duk Zuciyar ta ba dadi ko kadan, tana Nan zaune Abdul Hakeem din ya shigo
sanye da jallabiya coffee colour a jikinsa ya gaishe da Ammah ya nemi guri ya zauna Yana fadin
"lafiya kuwa Ammah?".
"Da sauki, Nemo min mijin Zahra a wayarka naji dalilinsa na yanke ma'amalarta Dani tunda
suka bar garin Nan ban Kara Jin duriyarta ba".
Shiru Abdul Hakeem din yayi kafin yace "ba haka za'ayi ba, Zan kirasa na saka handsfree sai
kiji yanda zamuyi dashi idan munji da alamun rashin gaskiya sai a San abunda ya Kamata
tunda ba'asan dalilinsa. Ba na hanata amfani da wayar, ke uwace kiyi hakuri babu abinda ze
Samar Miki 'ya da izinin Allah, in Sha Allah sai kinyi alfahari da Auren Nan Muhmud mutumin
kirki ne bashi da wata alama ta rashin gaskiya, kinsan ya fada min shi Dan Sokoto ne,.har
unguwar su da iyayensa duk ya fada min lokacin da zeyi tafiyar nan, yace saboda halin Rai
Koda be dawo ba na nemi Sameer ko sabon mai gadin Daya kawo a can gidansu na hayin
banki, ko Binya na gidan Baba malam duk mutanensa ne. Bari na kirasa Dan hankalinki ya
kwanta".
Ya Fara dialing din number sa.
Sun Gama break fast din kenan wayarsa ta dauki slow music daga kitchen inda ya barota tsam
ya tashi ya nufi kitchen din kafin yaje Kiran ya yanke, sunan Abdul Hakeem ya gani, kafin ya
Kira wani Kiran ya shigo.
Saida ya zauna daf da ita ya daga kiran.
"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu babban yayan mu, barka da Asuba".
Ya fada Yana murmushi.
"Wa'alaika Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu barkamu kadai, ya iyalin?" Dariya abin
ya bashi "Gasu Nan muna ta basu hakuri kasan Mata sai a hankali".
Ya fada Yana Dan Jan tsunin hancinta, Batasan dawa yake wayar ba.
"Wai meya samu wayarta ne Bata shiga kwata-kwata duk hankakii Ammah fa ya tashi, Jin
kwana biyu shiru ba suyi magana ba idan tana kusa ka Bata suyi magana Dan hankalinta ya
kwanta".

"Ya salam Dan Allah ka bawa Amman mu hakuri laifi tayi min na karbe wayar, amma Zan Bata
ita yau in Sha Allah, ai Zan shigo garin gobe ko jibi".
Tunda ta fashinci da Ya Abdul Hakeem yake wayar taji hankalinta gaba Daya yayi gida Jin cewa
zeje Azaren bada ita ba sai taji duk ta shiga tashin hankali da gaske gida take son komawa, ta
dauka da Wasa yake Mata lokacin da yace ze dauko Mata Rukayya idan zasuje Azare.
Wayar ya Mika Mata ya Mike ya fice daga parlourn gaba Daya.
Sallama tayiwa ya Abdul Hakeem din sannan ta gaishe shi.
Sannan ya dora da fadin "ga Ammah nason magana dake".
"Dan Allah Ya Abdul Hakeem ka Bata hakuri wallahi saboda bansan abinda Zan fada Mata ba
na kashe wayar Allah ba yaji nayi ba, kaina ne yayi zafi gurin fa buduwarsa ta turoni Asibiti ita
Kuma ta shiga wulakantani, Dan Allah ka rokarmin shi ya maidoni gida wallahi na gaji Ni tsoro
nakeji bakaga irin gidajen da yake kawoni ba kamar baza'a mutu ba fa". Ta ida fada tana kuka. Duk abunda ke wakana Ammah na zaune tayi tagumi tana Jin wani sanyi da tausayinta a
Zuciyar ta, amman koba komai ta samu nutsuwa taji lafiyar ta sauran Kuma tasan shegantake
ce kawai.
Wayar Abdul Hakeem ya mikawa Ammah ya tashi ya fice shima gara ya Basu guri su tattauna.
"Wai kukan Kuma na menene haka? ai kowa ya gyara ya sani kowa ya Bata ya sani, kiji tsoron
Allah ki rike sirrin mijinki kinsan baqi kinsan fari keba karamar yarinya bace,saboda me Zaki tafi
wani guri har ki nemi kwana bada izinin mijinki ba, haka kawai kin tashi hankakin jama'ar da
suka daukeki da mutumci kin kyauta kenan? To wallahi kada na sake Jin wani Abu makamancin
haka daga gareki ki nutsu ki rike aurenki kada na Kara Jin kin ambaci ya dawo dake nan, kinsan
dai ba'a nan zaku dawwama ba ina cewa ya fada Miki garinsu wata Rana dole ze koma gida sai
kice bazaki bishi ba? Akul na karajin magana makamanciyar wannan daga bakinki".
Tunda Ammah ta Fara magana Zahra ke shashsheka a hankali.
"Kiyi hakuri wallahi na daina bazan Kara ba, wallahi bansan laifin da nayi Masa ba ya dauke min
wayar da passport dina har da kudi da ATM duka".
Salati Ammah ta dauka tana fadin "Ni Asma'u yanzu harda passport dinki Kika dauka dole ya
kwashe wato guduwa kuka shirya zakiyi kibar kasar ko?"
Cikin gigita Zahra ta fashe Mata da kuka sosai tana Fadi "wallahi ba guduwa zanyi ba Daman
suna cikin jakar fa".
Ji tayi an zare wayar daga hannunta Batasan lokacin daya taso ta shige jikinsa ba tana fadin
"Dan Allah ka fadawa Ammah abinda take zargina dashi ba haka bane".
Ai Jin wannan furucin na Zahra yasa Ammah yanke Kiran cikin gaggawa.
Jin alamun yanke Kiran yasa shi Kara sakata a jikinsa baya son kukanta ko misqalazarratin.
[2/7, 11:32 PM] +234 906 821 6318:
* AUREN HUCE HAUSHI *



Maman Fateemah

Page 63.



............ cikin sa'a zahra ta Sami magajin a wayar, tsokanar ta ya fara.
"Dan Allah ka tsaya ka isheni da magana, kanaji Wai sahura ce zata tambaye ka Ina na koma
kada ka fada Mata kace Mata bana garin kawai".

"An Gama yallabiya, kinsan bazata Fara ma tunkarata da wannan maganar ba, ba sakar Mata
fuska nakeyi ba tunda na gane ita munafuka ce"
Tsaki zahra tayi.
"Can ta matse musu duk munafurcin mutum sai dai ya koma Kansa babu abinda ze sameni sai
abinda Allah ya hukunta min, Wai sako to sakon me? har wani abun arziki Mama zata taso
mutum ya kawo min wadda ko kallon arziki baya hadani da ita saboda tsabar kin jinina da tayi".
"Share kawai bakin ciki ne taga Allah yayi halitta a Nan take hasaada saboda nata 'ya'yan
Kamar ka yanka ka boye wukar, Ni bansan wace kaddara ta Kai Abba Aurenta ba, duk matan
jihar Nan Saida ya tsallake ya dauko ta Dan ma Allah yasa Basu da yawa da ansha kwantai".
Ya fada Yana wata dariyar rainin wayo.
Zahra ce ta katse shi tana fadin.
"Amma wallahi baka da kirki magaji 'yan uwanka nefa kake fada musu haka".
"Kema dai ai kinsan gaskiya na fada duba fa ki gani, kawai dai abar kaza cikin gashinta".
"Allah ya shiryeka wataran sai ka fada a gabanta, ta sauke maka ajja".
Tana Gama fada Masa ta yanke Kiran tasan sai su Kai minti goma shi ba gajiya zeyi ba.

Zahra Bata koma gurin Aunty zilan ba a Nan daki ta zauna, karatun Qur'an tayi sosai Dan
Saida tayi surori da yawa, sannan ta shafa Addu'a ta tashi.

*
Sahura ce ta shiga dakin Mama Jiki ba kwari, ganin ta shigo yasa Mama tashi zaune tana fadin.
"Meya faru Kika dawo? na dauka yanzu kinje can din?"

"Eh naje Amma gidan babu alamun da mutane a cikinsa gaskiya. Dan idan ba idona ne bega
dai dai ba babu wata alama data nuna giccin mutane ma a nan kusa a cikinsa, sai na Kirawo
zilai nace ta fada min suna Ina ne, sai cewa tayi Wai ita Bata San sunan unguwar da suke ba
tunda ba fitowa tayi ba tunda ta shiga gidan, Dan tsabar munafurci". Ta fada tana aje kunshin kayan da za'a Kaiwa zahra.
Wata shariya Mama ta lafta tana fadin.
"Har yaushe raini irin wannan ya shiga tsakanina da zilai? Har ta Isa ta nuna min wuyanta ya
Isa yanka, wallahi idan tayi Wasa saina yi mata sanadin barin aikin kwata-kwata, ai dama
matsiyaci be iya cin arziki ba".
Hakuri sahurar ta ringa ringa bawa Mama ganin Nan da Nan ta ture sai masifa takeyi bakinta
har kumfa yake fitarwa saboda bala'in da take kwasa .
Ita dai sahura sai abin ya daure Mata Kai, to menene najin zafi haka, dan zanyi maka Alkhairi

anje ba'a sameka ba, ba sai nabar abuna ba ko na bawa wani tunda Inda nayi niyya ba
rabonsu bane.

Cikin bacin Rai tace kije ko magaji ne ya rakaki Mana Zaki zo kiyi tsaye Kamar baki da wayo da
dabara Dan Allah wuce a gurin".
Kayan ta dauka ta nufi kofa tana fadin.
"Bari naje na gani ko Yana nan din".
Ta wuce ta fita.
Zugum Mama tayi tana nazarin yanda abubuwa suketa lalace Mata, Wai yarinyar Nan me take
takama da shine? duk abinda za'ayi da sunanta sai ya lalace,ko da tsiya-tsiya yau sai sakon
Nan ya shiga gidanta duk Inda ta koma ma saina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login