Showing 24001 words to 27000 words out of 65935 words

Chapter 9 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf

03 Aug 2025

1481

wancan satin ta dawo sokoto. Lamarin babu Dadi ko
kadan ga Hajiya Inna ma ta tashi hankalinta Wai itace tayi silar barinka gida tunda ita ta kara
tunzuraka da maganganunta, ga Abie ya Kori Aunty Samira da Safna har da masu aikin part
dinta Dan sai daga baya maganganu suka dunga fitowa har da asiri fa sukayi maka akan kabar
Sokoto har abada ko sunanta kada kara tunawa, Kuma Duk abinda kake dashi ya lalace,kasan
wani abun mamakin Wai a cikin masu tayata wannan shirkar harda uncle Saminu".
Sai lokacin Mahmud ya dago da Kansa ya kalli Faruq dan tunda ya Fara maganar yaji kamar a
lokacin abin yake faruwa.
Cikin cikakkiyar kamalarsa yayi wani murmushi kafin ya bude bakinsa cikin Jin Kai Dan

maganar ma kamar baya son yinta Dan har lokacin jikinsa ba daidai yake jinsa ba yace "Na
sani mana sosai ma kuwa, ai kome akace yayi ba zanyi mamakinsa ba, kasan ya tareni gaba
da gaba yace min ba dai Ina takama da nafi 'ya'yan su rufin asiri ba shi yasa nace bazan auri
'yarsa Asma'u ba, shima ai ba matsiyaci bane to sai yayi min sanadin da sai zaman sokoto
dama kasar Baki Daya yayi min wahala, Sam ban kawo komai ba akan furucinsa Dan nasan ba
abinda ya Isa yayi min Saida Izinin Allah, Kasan Abu mafi yi min ciwo a duk cikin jumurdar da
akayi tayi?" Kai Faruq ya girgiza Masa.
"sharrin zina da akayi min Wai harda Cikin shege, ko Ina Zina me zaci da Safna kazama kawai
yarinyar data Zama karya ko wane kare binta yakeyi har ayi kokarin hadani aure da ita, wallahi
Dana auri yarinyar nan gara na mutu a gwauro babu aure, sannan Abu mafi ciwo babu Wanda
ya ji view dina an dauki abin da zafi kowa bakinsa yana kaina har Ammi Taki yarda Dani, tana
ganin D'an yanzu babu abinda baze iya aikatawa ba, shi yasa na nufi gurin Hajiya Inna Nan ma
gurinta babu sauki shi yasa naji gara nayi nesa da gida tunda kowa ganin mutumin banza yake
mini. kasan kuwa duk abinda yake faruwa Ina da masaniyarsa? har barin Ammi sakoto, kawai
dai na Kai zuciyata nesa ne sau uku Ina zuwa Yamai amma sai naji bazan iya tunkararta ba
saboda tana ganina wannan badakalar zata sake dawo mata a zuciya duk da gaskiya tayi
halinta, so nake kowa ya ji yanda naji lokacin da akeyi min nak'i aka juya min baya! Kamar bani
da gata, wallahi nayi Dana sanin Fara business dina da kananun shekaru Dana San idan na
Fara haka Zan Zama yanda na Zama da ban yarda uncle Ishaq ya dorani akan kasuwanci ba,
Allah swa yayi gaskiya Daya ce dukiya da 'ya'ya fitina ne, da Ina level irin na kowa a family din
ba Wanda ze dameni tunda duk familyn wanda baya da rufin asiri da nasa wadatar? To ni abin
ne yayi min waya wallahi ga kananun shekaru, kasan uncle Saminun dai ya taba fada min ko
kungiyoyin matsafa dai na shiga, shi yasa na Zama abunda ba Zama cikin kankanin lokaci, a
gaban Hajiya Inna da uncle Mustapha akayi har Saida suka samu mugun sabani da uncle
Mustaphan Dan ma Hajiya Inna ta tsawatar kasan Bata da Wasa a gurin 'ya'yanta, sosai ta
ciwa Uncle Saminun mutunci tace ze Bata Mata zuri'ar ta, na rasa mena tsare masa haka da
zafi Sam baya kaunata ko alama, haka Sam baya ko shiga part din Ammina sai dai idan guri ya
kure su gaisa Dan dole".
Ya fada cikin bacin Rai sosai Dan idanunsa sun kada sunyi jajir, kwantar da Kansa yayi jikin
kujerar yana sauke ajiyar Zuciya, da ganinsa kasan yayi famun ciwon da yake Zuciyarsa.
Dan muskutawa Faruq din yayi shima abin saiya dawo Masa sabo.
"Kayi hakuri Dan Allah Ya Mahmud kasan idan Allah yayi maka daukaka zaka gamu da kalubale
kala-kala ba cikin family ba ba cikin jama'ar gari ba ba cikin abokai ba dole hakan ta faru yanzu
dai ka koma gida, ayi duk wacce za'ayi duk da gaskiya tayi halinta an banbance tsakanin aya da
tsakuwa, wallahi rayuwa lami ta zamar min da baka Nan, kofa a email na turo maka sako baka
bani amsa nayi magiyar har naba uku lada, amma baka kulani Nima fushin ya shafeni ko?
Wallahi yanzu ma nasan addu'ar da nakeyi ce ba dare ba Rana Allah ya amsa min ya kawo
dalilin zuwana kanon Nan dafa harna cewa mamee ba, Kuma wallahi Allah kenan harna kwanta
naji uncle musbahu ze fito sayan wasu abubuwan na amfani da mamee ta bashi ya list ya sawo
Mata shine fa nace Bari na rakashi na Jima ban shigo garin ba na Dan Zagaya tunda ba
dadewa zanyi ba, Ashe farin gani zanyi Dan Allah Ina ka shiga a kasar nan? Wallahi babu
Wanda ya taba kawo kana kasar Nan ko alama Dan anfi maida hankalin nemanka a European
countries da Asia wallahi ba Wanda ya kawo zaka zauna a 9ja".

Girarsa Daya ta gefen dama ya Dan dage Yana yiwa Faruq wani kallo.
"Au kunyi zaton Ina waje kenan ko? To Ina gida Bauchi state, cikin garin Azare katagum local
government, nasan ba sai nayi maka bayanin komai akan Zahra ba, an fada maka wacece ita
tunda Wanda na ganku yasan komai a Kanta watakila Abu Daya ze bashi mamaki ganin mu
tare a Nan tunda ya sanni ko ba sosai ba a can tunda time to time Yana shiga gurin malamina
suna gaisawa idan ya shiga garin, sai albishir Daya Zan maka itace yarinyar da nake fada maka
mun taba haduwa da ita a cikin jirgi ita da Babanta wadda na tura Sameer ya bisu Zuwa
Jordan,ai ka gane bayanin ko?"
Kai Faruq din ya jinjina Yana fadin "Yes". Ya fada yana mamakin abun sosai wato shi Mahmud
komai ya sake a gaba saiya cimma burinsa. "Sai yanzu ya gane ka har hotunan daurin auren
ya nuna min a phone dinsa, Shima ya Dade Yana tunanin a Ina yasan fuskar ka tunda ba farin
sani yayi maka ba sai dai a hoto, shi yasa Sam be ganeka ba tunda ta Ina za'ayi tunanin zakayi
irin wannan rayuwar, Dan Allah fada min ta Yaya hakan ya faru harda Auren irin wannan
yarinyar haka wato ribar kafa kenan ko?"
"To abubuwan da yawa Dan Ni dai nasan na baro gidan Hajiya Inna cikin fushi kofa takalmana
ban iya tsayawa na saka ba kawai dai nasan duk phones dina suna jikina na kamo hanya a
kafata Amma Abu Daya nayi noticing kamar jama'ar da nake wucewa basa ganina sam, nayi
tafiyar da bansan iyakarta ba daga Nan Kuma ban Kara sanin abubuwan da suka faru ba na dai
tsinceni ne a gadon Asbiti bana magana ko kadan amma Ina Jin abinda ake fada mayarwar ce
Bana iyawa, Wanda suka shinceni wani babban malami ne da marikin zahra da d'an Kanwar
Malam din, shifa Malam din ya dage min da Addu'oi a kaina Dan har Taraba Saida yaje akan
matsalata gurin wani tsoho malaminsa, a haka har Allah ya bani lafiya, sai Kuma nayi arba da
Zahra a garin duk da Daman a bincken Sameer ya gano mazauna Bauchi state ne, sai naji
Naga gurin Zama na dage da Addu'a da sadaka amma fa ban fadawa kowa ba ko Sameer
saboda a lokacin maganar aurenta akeyi na shiga wani Hali a lokacin sai dai nayi Alkawari sai
halarci daurin aurenta Kuma sai nayi Mata kyauta ta ban mamaki kafin nabar garin, sai kuma
ubangijin da yake amsa addu'ar bayinsa ya juya lamarin cikin kankanin lokaci, aka bani aurenta
lokacin Dana yanke kauna da samunta a matsayin matar aure uwar 'ya'yana".
Ba karamin mamaki Faruq yayi ba ya Kuma Kara jinjinawa girman Allah swa, wato duk
gwagwarmayar da aka Sha Rabon wannan yarinyar ne ya rantse Kuma ya kaddaro shine ze
taka da kafarsa ya karbi aurensa ba tare da wakilcin iyayensa ba sai iyayen Amana.
"Wato Ni duk lamarin ya juye min wallahi".
Dan murmushi Mahmud yayi Yana fadin.
"Kaima kenan da ba a kanka hakan ya faru ba, sometimes idan na zauna sai naga kamar
Almara wasu abubuwan da suka faru, kasan abinda zakayi min".
Kai Faruq ya girgiza alamar "A'a.
Fuska ya hade Sosai Yana kallonsa Ido cikin ido.
"Kada naji labarin ka hadu Dani a Sokoto Koda wasa, Nina fita da kafata Kuma ida kafata Zan
koma Amma ba yanzu ba, Kuma kada naji labarin nayi aure a gurin kowa koda nazo da Zahra
kada ka nuna kasanta ko a fuska, Nina taro match din ni zanji da kayana".
Kai kuwai Faruq ke gyadawa tunda ya Fara maganar yasan ba Wasa a cikinta.
"In sha Allah hakan bazata faru ba".
Sun Kai kusan karfe uku suna tattaunawa akan abubuwan da suka ringa faruwa bayan

bayanan, kafin kowa ya nufi NASA gurin kafin lokacin sallar asuba. Ba karamin mamaki Faruq
yakeyi ba idan yaji Mahmud Yana fada masa wani abun Dan shi sai gurinsa yaji wasu
abubuwan duk da Yana cikin gidan.

Itama zahra Bata kwanta ba sai kusan biyu da rabi bayan ta gama karatun Alqur'ani ta Fara
nafifili sannan ta kwanta, harta gama addu'ar kwanciyar barci sai Kuma ta canza Shawara ta
tashi ta dauko Jakarta tana fadin "Bari na kunna wayar nan ba turawa Ammah text na ban
hakuri tayi breakfast dashi sai Kuma da Dan hantsi na kirata nasan zata huce ta saurareni
lokacin, sannan na Kira bestie musha hurar yau she gamo".
Jakar ta dauko ta koma saman gadon Tana gyara Zama, duk iya binciken ta tayi Babu duk wani
Abu Mai mahimmanci data saka a ciki, zazzage jakar tayi wayam kamar ba'a taba ajewa a
cikinta ba.
Tagumi ta buga tana tunanin, to a Ina suka zube wadannan kayan? Kuma me yasa sauran
Basu zube ba? ko jiya lokacin da suka fito daga gidan mommy komai Yana ciki Kuma ai ko
daga motar Bata fito ba lokacin da sukaje sahad din.
Jiki ba kwari ta matsa tsakiyar gadon ta kwanta ita duk lamarin ya tsinke Mata wa zata tambaya
Ina kayanta na jaka suke da wannan tunanin barci yayi gaba da ita.
Hudu da rabi Mahmud ya tashi as usual, duk da Daren da suka raba da Faruq besa shi ya
makara ba, nafila yayi sannan yayi raka'atanul fajri ya fito Jin an Fara Kiran sallar na biyu, harya
nufi Hanyar fita daga corridorn sai ya dawo baya ya tura kofar dakin da take, a kwace ya ganta
tsakiyar gadon hular data saka ta cire gefe guda Ribom din shima yayi nasa gurin blanket din ya
sauka har saman cikinta ga rigar ita da Babu duk Daya, a hankali yake shigowa cikin dakin
kamar Mai tsoron kada ya tasheta, Yana Kare Mata kallo yanda tayi wani mahaukacin kyau a
cikin dinligh din dakin, har ze tasheta saiya tuna condition din da take ciki ya juya ta fice daga
dakin, yaso ya gyara Mata gashin Amma yasan matukar ya tabata sai ya sake alwalasa, a waya
ya Kira Faruq ya fito su wuce masallaci.

A cikin barci taji kamar an bude kofa dakin, fargigit ta tashi tana addu'ar tashi daga barci,
kamshin turarensa da taji ya hade dakin shiya tabbatar Mata daya shigo cikin dakin. A gurguje
ta nufi toilet jin har an Fara sallah a masallatai, fatan ta Allah yasa har ta Idar Bai dawo daga
masallacin ba Dan ita fa wallahi tsoronsa takeji Bata shuryawa abinda yake muradi ba... [2/1, 6:08 PM] ASHMAR: AUREN HUCE HAUSHI.


MAMAN FATEEMAH.


Page 50.



_______Tun idar da sallar Zahra ta shiga kakkabe gadon Tana dubawa ko Allah zesa tayi
arba da tarkacen ta na cikin jaka amma ko alamarsu Babu dole ta hakura ta linke sallayar da

hijabin Adana saboda tsaro.
Bata koma barci ba gyara dakin tayi duk da ba wani datti Dan da gani sabon guri ne da
alama ma kamar a jiyan aka Fara amfani dashi Dan ko toilet din shima haka ne, Bata dauki
dogon lokaci ba ta gama komai ta bazawa dakin kamshi Dan ga Room freshners Nan kamar
anyi gorinsu, wanka ta shige, ta Jima tana gasa jikinta da ruwan dumi sannan tayi wanka ta fito
haka nan taji tana son tayi kwalliya Sosai.
Zama tayi ta tsara light makeup tabi jikinta ta Sanya turaren gabobi Dana bayan kunne duk ta
saka tunda gasu nan kamar ba da kudi ake sayensu ba, ita dai ta zubawa sarautar Allah Ido
taga inda wasan ze Kare, clothset din ta nufa ta bude dayan bangaren, English wears ta saka
riga da siket blue black masu ratsin fari a jikin coat din,rolling tayi da farin veil ta fito Shar da ita
gefe gadon ta zauna tana karanta addu'ar Azkar din safe.
Su Mahmud Basu shigo gidan ba sai wurin bakwai tun bayan idar da sallar sukayi zaman
karatun alqur'ani da Azkar din Suma a masallacin. Faruq yaso ya wuce gida amma Mahmud ya
Hana shi yace yayi zamansa a Nan ze fiye Masa shi yau ze koma Nasarawa Daman akwai
abinda yazo yi Nan din zuwa anjima Idan ya gama zasu wuce Kuma ma Basu gaisa da madam
ba, part din Daya kwana ya wuce shi kumq Mahmud ya nufi sabon part din har ya Fara hawan
steps din ya dawo Yana Kiran Faruq.
Shima gangarowa yayi Yana nufo Mahmud din Saida ya Karaso yace masa.
"Ina key din waccen car din akwai Kaya a baya za'a fito dasu".
"Oh! Sorry, wallahi na manta Yana ciki trouser din Dana sake jiya, harna na fito dashi na
manta ban baka ba, daman ni ka barwa ita Naga tayi maka kadan motar five millions ai sai mu
Kuma ma motar Mata ce"
"Nima ba tawa bace ta madam ce idan kana so ka tafi da ita kawai".
Baki ya rike alamar mamaki Yana 'yar dariya.
"Haba dai yaushe za'ayi haka da Wasa nake gani nayi dai tayi kankanta a gurinka harma ita
din gaskiya".
"To Yaya kake son ayi kenan?kaga dai bani na Bata ita ba Babanta ya saya Mata Kuma
saina ce batayi ba, Ina laifi da ake bani aro da ita fa nazo airport lokacin da zanyi tafiya,Kuma
anan na aje ta harna dawo sannan na dauko Mata abarta, Kuma kawai saina ce Mata tayi
kadan to ina wadda tafitan da Zan bata?". Ya fada Yana kallonsa, shima kallon nasa yake yi, shi wani zance yake masa me Kama da
zaurance me yake nufi da hakan Yana nufin a baibai ya ninketa kenan kome?.
"Pls jeka dauko min we will discuss later". Da sauri ya nufi ciki ya dauko key din suka nufi
gurin da motar take.
Kayan ciki suka dauko, da gudu malam ya taho ya karbe kayan hannun Mahmud Yana fadin
"Haba yallabai meye amfanin na a gidan da har zaka dauki kaya". Ya karba yayi gaba da sauri
Faruq ba biye dashi suka nufi parlourn kowa da dauke da ledojin a hannau.
Har gurin dining table ya Kai kayan ya Dora kayan Faruq ma a Nan ya dora na hannunsa,
Malam musa ne ya koma ya dauko sauran da suka rage a cikin motar.
Maimakon Mahmud ya shigo saiya Koma dayan part din bai jima ba ya fito rike da laptop da
wayoyi tablet guda biyu.
A parlourn ya iske Faruq Yana tsaye kusa da wani freme Mai hoton wani tsibiri a tsakiyar teku
gurin yayi matukar kyau sosai.

Jin shigowar Mahmud yasa ya baro gurin Yana fadin "gaskiya tsarin gurin Nan yayi kyau sosai
banyi zaton ze kai haka ba kafin a gama".
Wani kallo Mahmud din yayi masa Yana aje abubuwan dake hannuwansa.
"Amma Faruq ka fiye gulma, Ina cewa Kaine ka zana ginin Nan da hannunka zakazo kana wani
zance daban a Kai Kuma, ni zonan ka shigar min da wasu sakonni cikin laptop din nan jiya naso
yin aikin ka hanani".
Ya fada Yana kokarin kunna wayoyin dake hannuwansa.
Saida ya nuna masa komai sannan ya nufi upstairs.

Tunda ya doso saman yaji wani kanshin Dadi Wanda ya kasa tantance Kona menene, direct
dakin Daya kwana ya shige Yana son ya sake wanka yana son ya fita wasu sabgogin nasa
wanda yaken son yayi da Kansa.
Ya shiga ciki ba dadewa Zahra ta fito ta nufi kasa tana ayyana bari ta duba Koda kayan amfanin
kitchen Dana abinci tasan abinda ya kamata tayi kada ta Zama sakarya wadda ta rako Mata.
Plat shoes ta saka fari tas dashi ta nufo down stairs din cikin takunta mai daukar hankali, Bata
ankara da mutum a zaune ba Saida ta ahigo tsakiyar falon taja ta tsaya tana rarraba idanu tana
son tantance ya fasalin ginin yake da inda ya Kamata ta dosa,.
Carab suka hada Ido dashi ya aje abinda yakeyi ya Zuba Mata idanu irin kallon Nan na wuce
shari'a Yana tsarkake ubangijin da ya yi wannan halittar da take gabansa.
Dan zabura zahrar tayi ganin mutum ba zato ba tsammani.
Aje abinda yakeyi yayi ya taso har lokacin Yana kallonta Dan ja baya tayi ganin ya nufo ta.
"Ina Zaki Kuma nida na taso na gaishe da Aunty na".
Ya fada Yana murmushi, saida ya matso ta Dan gane shi, shine jiya ya rungume Mahmud a
kofar store din da yayi sayayya.
Sai lokacin ta Dan nutsu amma da tana tunanin ta Ina zata fece ta Koma saman tasan ko banza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login