Showing 60001 words to 63000 words out of 65935 words
Chapter 21 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf
Amma fa
hankalinta yaki kwanciya so take taji daga bakin Ammi din dole su zauna.
Kwanciya tayi tana lalubo number sweet heart dinta dole su ta fada Masa halin da ake ciki
saboda a gabanshi Komai ya faru akan yanda ya gigice daga yi masa fushin d'an lokaci to Ina
ga anyi Mai dungurungun kuma, ai sai yanda Hali yayi tasan abinda ya fada kawai dauriya ce
bawai har Zuciyarsa haka abin yake ba.
*******Tunda su zahra suka dauki hanya tayi shiru mummy Badi'a ke yiwa Zahra Hira da
hannunka Mai sanda akan abubuwan da suka danganci zamantakewar aure da irin 'yan
dabarun rike miji yaji ba wata sai Kai, ita dai zahra daga eh sai a'a take fada ko hanyar Bata lura
da inda suke nufa,ita dai Hajja zuwaira barcinta take Sharawa tunda suka dauki hanyar dodar,
tafiya Malam Habu yakeyi iya tafiya ga kuma lafiyayar mota, a Kano sukayi sallar azzuhur da
la'asar suka dauki hanya zahra tayi mamakin yanda wannan bawan Allah yasan hanya haka
gashi dai ya fara manyanta.
Karfe shida da rabi suka shigo Cikin garin Azaren katagum, dan rage tafiya Malam Habu yayi ya
Dan juyo Yana fadin 'ranki shi dade Ina muka nufa gamu Allah ya kawo mu Azare".
Hanya ta ringa nuna Masa Yana bi har kofar gidan Abba.
"Masha Allah".
Mummy Badi'a ta fada a ranta ganin gidan da suka zo da gani Suma ba kashin yadawa bane da
nasu rufin asirin daidai gwargwado dan ko makaho ya Shafa yasan da abun.
Horn biyu malam Habu yayi Baba sani ya leko ganin Bai sheda motar ba ya fito ya nufo su dai
dai gurin window din driver ya leko gaisawa sukayi kafin Zahra tace Masa.
"Baba sani nice zahra ka bude Mana".
Da sauri ya juya Yana fadin "sannunku da zuwa ai bangane ba sai yanzu".
Suna sako Kai Cikin harabar gidan magaji na fitowa da sauri da alama wani uzirin ne ya taso
masa ganin bakuwar mota Mata na fitowa yaja ya tsaya yaga su waye ganin Bai sheda su ya
nufi hanyar ficewa yayi taku kadan yaji maganar Zahra daga bayansa tana fadin.
"Sulaimanu".
Da sauri ya juyo yana dariya.
"Kai Kice cere Bina ce ta shigo garin".
Mummy Badi'a bata san lokacin da dariya ta kubce Mata ba, tana kallon magaji Daya nufosu da
sauri.
Gaishe dasu mummy Badi'ar yayi Yana fad'in.
"Sannunku da hanya Bismillah ku shigo, yayi gaba da sauri don ya isarwa da Ammah sako,
haba Ashe da dalili shi dai yaga anata faman dafe-dafe Daya tambaya ba Wanda ya bashi
amsa, Zahra na gaba su mummy Badi'a suna bayanta cikin gidan shiru ba kowa sai su zilai da
sahura suna gyaran kitchen din waje daga nesa sahura ta hango su zahra zasu shige part din
Ammah.
"Kai zilai Kinga kamar uwar dakinki sa wasu mata sun shiga part din Ammah".
Banza zilan tayi Mata tana ganin tsabar gulmace kawai irinta sahura wace zahrar kuma wadda
bata kasar ma gaba daya, jin tayi banza da ita yasa ta hakura taci gaba da abinda takeyi.
Su zahra na shigowa Ammah da magaji suna fitowa daga kofar baya wadda aka Samar da ita
saboda part din Abba.
Cikin farin ciki Wanda har ya bawa zahra mamaki, Ammah ta taresu tamkar tasan da zuwansu,
Fadi take "sannunku da hanya kunsha doguwar tafiya nayi ta neman zahra dazu network ba
kyau sai hakuri nayi".
Zahra taso ta shige jikin Ammah kamar yanda ta Saba Amman sai taji nauyin yin hakan a
gaban bakin Ido sai dai dan kwantar da kanta tayi a jikin Ammah nan da nan taji wata karaya da
tausayin Ammah ya kamata tunda ta Zama budurwa Ammah Bata huta da kwaramniyarta ba
yanzu ma gashi ana murna anyi auren ga Kuma wata sabuwa ta bullo In "yan caca. "Bismillah ku zauna Hajiya sannu sannunku fa"
Alawiyya ce ta shigo da katon tray dauke da abubuwan sanyi ta aje tana gaishe da bakin nasu.
Mummy Badi'a ce tacewa Ammah.
"Yauwa sannu Hajiya ya muka sameku".
"Lafiya kalau Alhamdulillahi"
Ammah ta gaishe da Hajja zuwaira.
Ruwa kawai suka Sha kafin a rakasu dakin da akayi musu masauki a Nan part din Ammah din
Amma Yana daga can gefe daban ba'a fiye amfani dashi ba tunda da wadatar dakuna.
Magaji ma fita yayi da ruwa da kwalin exotic da Coke na gwangwani yaje ya budewa Baba
Habu dakin Baki na waje lokacin Yana gurin Mai gadi suna Hira.
Kayan dake Cikin motar malam Habu ya Fara fitowa da magaji yana fadin.
"Dan Allah shigar musu da kayan nan".
Zahra dakin da take Zama ta shige tana mamakin yanda Ammah Bata nuna tsahin hankalinta
ba duk da Batasan dalilin zuwansu ba ita da 'yan uwan Ammi.
Cikin Kan kanin lokaci magaji ya Gama shigo da kayan ya zube su a parlour ya shiga ya fadawa
Ammah.
***
Su zahra basu fi minti ashirin da tafiya ba Part din Ammi ya fara karbar Baki matar Aliyu
Halimatu ita ta fara zuwa Ammi batayi mamaki ba tasan karshen maganar kenan duk wanda ya
samu labarin mahmud ya dawo zaiyi kokarin zuwa ya gani da idonsa ballantana tasan maganar
zahra zata karade dangi shi yasa tayi wannan Kandagarkin ta turata gida duk masifar mutum da
iya gulmarsa Saida ya koma da gwiwa a sage Dan Mai Kama da itama baze gani ba, kafin
azzuhur part din ya dinke da jama'a 'yan taya murna, na gida Wanda suka Isa sai yan leke-leke
sukeyi basa sama basa kasa, irinsu Habiba matar uncle saminu har gidan Hajiya Inna sukaje ita
da Matar Ya Abdallah first born din Abbie, tasu tazo Daya da Habiba itama 'yar adawar mahmud
ce ta gaske sai dai ita ta iya takunta ba lallai ne lokaci Daya ka ganeta ba,haka suka dawo ba
wani labari sai Kuma suka shiga kokonton gaskiyar maganar yarinyar da aka fada yazo da ita.
Aishat na kwance Kiran Aunty Surayya ya shigo.
"Wai kina Ina ne tun Dan hantsi nake gidan Nan sai yaran nake gani Amma ke ko duriyarki
Babu".
Yunkurawa tayi ta tashi zaune tana fadin.
"Ina masaukina a kasa bana Jin Dadi ne shi yasa, Aunty Ina wuni".
Dariya Ammi tayi saboda wayar a speaker take, tana ayyana kina min dacin Rai dai na tura
muku Mata gida,Baku San nemar muku daraja nake yi ba duk wannan taruruwar murnar da ake
zuwa ba domin Allah ake yinta ba saboda aga yarinyar da aka Kai musu labarin ta.
" Lafiya kalau, kizo sama yanzu Ina bedroom din Ammi".
Ta kashe wayar, saukowa Aishar tayi ta zura takalma ta fice tana hawan strains taji Kira ya
shigo Mata tana dubawa Sameer ne.
Ta daga da sallama suka gaisa sannna ya Dora da fadin.
"Dake da waye zakuzo gidan oga na arkilla zaku duba wani Abu kuga Koda abinda za'a gyara".
"Ok Bari na fadawa Aunty Surayya sai muzo tare".
Ta fada tana tura handle din kofar bedroom din Ammin.
A zaune ta samesu su Aunty Surayya nata faman rubutu a Cikin wata jotter.
Da sallama a bakinta ta shiga ta gaishe dasu Ammin ta nemi guri ta zauna, Saida Aunty
Surayya ta Gama rubutun ta dago tana kallon Aishat din.
"Ungo duba kin gani Koda gyaran da za'ayi".
Jotter ta karba ai Bata San lokacin da tayi super ta Haye jikin Ammin su ba.
"Allah ya Kara sutura Ammi, ya jikan mahaifi yanda Kika faranta Mana Allah ya haskaka qabarin
Alhaji Haroona ya yalwata Masa, mun gode Amminmu sai yanzu na samu kwanciyar hankali
wallahi".
Murmushi Ammin tayi.
"Allahumma Amin, da kin dauki fushi Dani Dan Ina nemar muku daraja da kima kinsa yau har
sama Hajiya Babba ta hauro saboda taga kwakwaf tunda nasan yayan ki Ibrahim ya fada Mata
komai har dakun Nan ta shiga Wai sau Daya ta taba shigarsu Ina jinta dasu Batool Suma da
Taya bera Bari har kciki suke shiga Kuma jikin ba kwari ta sauka da kyar fa take taka kafar
Amma gulma ta hauro da ita saman Ina jiyo wash wash dinta tana sauka".
"Allah ya kyauta ai ba Karamin Basu kafa mikayi ba Ammi sai yanzu na gane plan dinki na
gaggawar ficewa da zahrar daga gidan Kinga kin kashe bakin tsanya babu batun mutum ya
bugi kirji yace ya ganta da idanunsa, yanzu Sameer ya kirawo ni yace muje gidan bros na
Arkilla muga wani Abu ko da abunda za'a gyara". "To Kuma da boutique dina zakuje a hado lefen da za'a Kai musu can nasan ba wani abun azo
a gani akayi Mata ba duba da yanda abun ya faru kinsan halin kayanki Kuma".
"To Bari mu Fara zuwa Arkillar in yaso sai mu wuce can din ko Aunty Surayya?".
A gidan suka Sami mahmud da wasu abokansa biyu sai sameer.
Suka gaishe da Aunty Surayya har tana zolayar mahmud.
Sameer ne ya shiga ya bude musu inda kayan da suka zo dasu daga Dubai da Kuma
akwatunan.
"Auntyn mu gasu Nan ku duba idan da abinda babu ko za'a canza ko karawa sai a fada"..
Ya ja musu kofar, kayan suka Fara dubawa ba karya komai yayi harda abinda ma ba'a sakawa
an saka sunyi santin kayan kamar me Dan naira da taci gidansu a gurin ba Bata lokaci suka
shiga zubawa a Cikin akwatunan abinda ya daukesu kusan awa hudu suna Abu Daya.
Saida suka Gama komai sannan Aunty Surayya ta Kira Ammi video call lokacin Ammin tana
gurin Hajiya Inna Dan ana shiga magariba ta fice ita da suhailat wadda ke driving dinsu suka
nufi mabera gidan Hajiya Inna taje ta fada Mata komai ake ciki ta Kuma Bata hakurin yanke
hukuncin da tayi ba tare da ta nemi Shawarar ta ba,nuna Mata Hajiyar tayi ba komai idan akace
sai an tsaya ciccira maganar abin baze Zama sirrin ba hakan da tayi shine dai dai.
To Kuma saiga Kiran WhatsApp tunda duk gidajensu da wifi suke amfani.
Akwatunan Ammi ta Fara gani gasu Nan birjik sai da suka Kai karshe sannan Aunty Surayyar ta
dago da wayar tana fadin .
"Ammi kin gani? To Dana ya Gama aikinsa Kaiwa kadai ya rage ba'a bukatar komai Ina za'a
kawo Kayan? Can ko kuma a barsu a nan kawai?".
"Masha Allah, Kice kun hutar dani? Ki fada musu su kawosu gidan Hajiya kawai sai a fadawa
Wanda ya kamata suzo su gani a Nan kawai".
Sukayi sallama Hajiyar ke tambayar.
"Me za'a kawo Mini Nan kuma?".
A kunyace Ammi ta fada mata".
"A'a kirawo su azo a kaini Arkillar na gani yaushe za'a wani kawo min Kaya da wani kiran jama'a
su ringa dodon gani Abu guri yana neman kurewa ga Azumi Yana karatowa gara ayi a Mika
Masa matarsa ai yayi rawar gani ma wallahi a 'ya 'yan zamani ba kowa ne zeyi abinda dan
Albarkar Nan yayi ba, shi yasa yaki zuwa gidan kenan yayi min zaune a Nan yake min wasu
maganganun a bai-bai".
Ita dai Ammi Dan murmushi kawai takeyi.
Daga Arkilla gidan Ammi su Sameer da Tajuddeen suka nufa da lefen har lokacin Su Habiba
suna nan Wai suna neman Ammi suyi Mata sallama da momin kano Maman su Faruq wadda ta
dawo da gefin magariba daga Dubai inda takeyo oder din Kaya, tana zuwa yaran ta suka fada
Mata dawowar Ya mahmud din shine bayan tayi sallah ta shigo sai Kuma Bata Sami Ammin ba
sun dauka ko tana part din Abbie ne.
Suna zaune aka Fara shigowa da akwatuna ana ajewa Saida aka shigo dasu gaba daya Nan
kallo ya koma sama suna mamakin daga Ina kuma wannan su Aunty surayya ne suk shigo
daga karshe Nan suke fada musu lefen mahmud ne, Akayi caaaa kowa na fadar Albarkacin
bakinssa aka Fara daddagawa, ana wannan rarumar Ammi ta wuce ciki. ****
Saida su Aunty Badi'a sukayi salllolinsu Alawiyya da zilai wadda tayi suf ta baro sahura ta shigo,
dazu Sarai ta gane zahra ta gwasale sahurar ne Dan kada tayi halin nata na kinibibi tunda Bata
San menene dalilin zuwan ba ga Kuma Bakin fuska suna tare tana gani zata shiga gurin Mama
ta Kai tsegumu Dan ma kwanan nan ta rasa me yake damun Mamar duk ta fada sai idanu gashi
ta rage wannan izzar da wulakancin nan na ganin kowa a banza.
Sai da suka Gama suka kimtsa wannan Ammah ta shiga suka gaisa sosai tayi musu sannu da
zuwa.
Aunty Badi'a ce ta Fara Kora bayanin dangantakarsu da Ammi sannan ta Dora da fadin dalilin
zuwansu duk da Ammi ta yiwa Ammah a takaice.
"Hajiya ga yarinyar mu Nan mun kawo ta badon mun Raina iyawarku ba a'a bisa wasu dalilai na
abinda ya faru da yaron muke son azo a daukar Masa matarsa a Cikin mutuncinta da kimarta
kamar ko wace yarinya budurwa da ake aurarwa a gaban iyayenta,kinsan ko wane family akwai
tasu matsalar da fatan bamu Bata muku ba". "Kai haba wannan ai gyara kayanka ne kuma kun nuna Mana yanda kuke kaunar zahra da
gaskiya mun gode sosai, ku huta kafin Abban nasu ya shigo ku gaisa".
Har Ammah taje baking kofa ta dawo tana fadin.
"Na shafa'a ga waya Hajiya zainab zata Kira tace min layinku baya shiga a nan kasar".
"Wallahi kuwa haka ake fama idan Suma suka shiga sai dai su sayi sabon sim na can wallahi".
Tunda zahra ta shige Bata ko leko waje ba, kwanciya tayi duk abun duniya ya taru yayi Mata
yawa, ga Ammah ma bata ko leko ta ba tana ta bakinta shima meu amor shiru Bai nemeta ba
haka Aunty Aishar itama shiru Sai taji Zuciyarta ta tsinke tasan shikenan sai yanda Hali yayi
tunda har zuwa lokacin Bai kirata ba tasan Amminsa Bata sonta gashi harda mutane ta hadota
a bawa iyayenta hakuri.
Aunty zilai ce ta shigo taga zahra ta rabsa uban tagumi ko daga inda take Bata tashi ba, ga
abincin da aka kawo mata ko taba shi batayi ba.
Matsowa tayi tana fadin.
"Haba uwar dakina tagumi ai ba naki bane, wane gata ne Ubangiji baiyi Miki ba ai ke sai
hamdala ta kamace ki".
Dago aexy eyes dinta tayi ta watsasu akan Aunty zilan tana fadin.
"Kayya Aunty zilai idan ana cin baure ba'a tona cikinsa Kuma daudar gora ciki ka shata, gida fa
Ammimsa tace a rakoni a bawa Ammah hakuri Kinga abinda ma ta bani da zamu taho tace min
sai wata rana".
Sai kukan da take rikewa ya kubce Mata.
Hakuri Aunty zilan ta Riga bata, tana Cikin kukan ne wayarta ta dauki Kira harta tsinke Bata
daga ba da gaske abin yayi Mata ciwo da tasan karshen abun haka ze Zama da Bata yarda tayi
irin wannan sabon dashi ba.
Wani Kiran ne ya shigo Aunty zilai ce ta dauka da sallama muryar yallaban taji duk sai ta
daburce ta rasa abun fada, Cikin in Ina ta furta."yal..labai Ina wuni".
"Lafiya". Ya amsa mata in short.
"Ina zahrar take ne?".
Da sauri tace "gata Nan yallabai bansan meye ya sameta ba sai kuka takeyi"
"What! Kuka kuma?".
"Wallahi kuwa yallabai nayi lallashin nayi lallashin taki ta saurareni".
"Pls Bata wayar".
Duk abinda suke zahra na jinsu ita fa wani Haushinsa takeji su baro wannan garin nasu Mai
shegen nisa tun Dan hantsi Amma ya kasa kiranta sai da ya mula ya mule da tsohon Daren
Nan ze wani kama kiranta tayi masa me.
Kin karbar wayar tayi ai ba bakuwa bace Aunty zilan da zataji nauyi ta dauka ko Dan kunyarta.
"Ta tashi ta fita yallabai Sai hakuri kasan da yarinta a Cikin Lamarin ta".
"Ok shikenan"
Wayar ya dangwarar a Kan bed side yana lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya.
"Haba uwar dakina yallabai baici irin wannan hukuncin ba, kiyi hakuri kome yayi Miki ki daga
wayar kiji meye ze fada miki".
Autane ya leko Yana fad'in.
Aunty zilai kizo inji Ammah tana bedroom dinta".
Ya juya ya fice daga dakin.
**
S.K.T
Saida kowa ya Gama iya nasa iya yin gurin ganin lefen Amma dai mutum ko shine hasidin Iza
hasada Bai Isa ya mushe kayan Nan ba, Saima korafin sunyi yawa yarinya Kamar wata diyar
sarki, ba dai Wanda ya tanka tsakanin Aishat da Aunty Surayya, ba'a daukesu daga parlourn ba
sai da Abbie ya shigo shida uncle Mustapha sukaga kayan Aishat taso ta bude musu uncle ya
Hana Yana fadin.
"Haba Hasana sai kace Mata zamu zauna muna bude kayan sakawa muna kallo, Allah ya
Sanya Albarka ya hada kawunansu ya kare fitina".
"Allahumma Amin"
Suka fada gaba daya, Aunty Surayya bata bar gidan ba Saida suka Gama duk abinda ya
kamata suyi na shirye-shiyen Baki Dan Ammi taci alwashin sai ansan danta yayi Aure.
Saida Aunty Surayya ta taya su Aishat shiga da kayan wani daki kusa da Wanda Mahmud ya
kwana a ciki, Amma Dan Karamin kit din da sarkokin gold ke ciki dakin Ammi aka kaisu.
Washe gari aka tashi da rabon IV na dinner da yini abinda ya girgiza duk wata yarinya data
kwana ta wuni a family din dake kokarin cusa kansu gurin mahmud Kota halin Yaya ne.
****
Su Aunty Badi'a basu samu gaisawa da Abbansu Zahra ba sai da safe, yaji dadin abinda
Ammin tayi sosai yayi godiya.
Bayan sun dawo sunyi break fast ne Ammah tazo musu da bayanin Abba ya sallami drivern tun
dare sukayi sallama ana yin sallar Asuba ya dauki hanya yace Bauchi za'a kaiku kubi flight
zuwa sokoton.
Godiya suka yiwa Ammah kamar wasu kayan duniya aka Basu, sai da zasu tafi Mama ta shigo
shima Abba ne ya turota su gaisa da bakin Ammah, Amma batayi niyya ba duk da sahura ta
kaimata tsegumin bakin ita abinda ya dameta shine a gabanta Lamarin salma wadda da kyar
aka Zubar da Cikin tamkar bazata rayu ba Dan ta Suma yafi sau goma da kyar aka samu ta
farfado, jini kuwa an Kara Mata shi yafi Leda bakwai Dan Zuba yake tamkar lalataccen