Showing 1 words to 3000 words out of 65935 words

Chapter 1 - Auren Huce Haushi Book 2 By Maman Fatima .pdf

03 Aug 2025

1452

AUREN HUCE HAUSHI.

MAMAN FATEEMAH.


Page 41.



________Wani irin barci me nauyi yayi awon gaba da zahra, sai da Sameer ya shigo yace
Rukayya ta duba Masa Zahra oga ya Kira yace Masa da matsala.
Dakin Rukayya ta shiga ganin Zahrar tana barci ga wayar Ya Sameer a gefen ta, daukar wayar
tayi tana dubawa a airplane mode taga wayar 'yar dariya tayi tana fadin "good yarinya kinsan
kanki kenan ai Ina bayanki ki tsaya tsayin daka akan wannan mijin naki idanun Mata a kansa
suke kinyi dai-dai wallahi". Wayar ta cire daga flight mode din tayi waje da sauri tana fadin "gashi ya Sameer wallahi barci
takeyi" .
Wayar ya Karba Yana dubawa gashi Nan a kunne take haka datar itama ba wani matsala.
Tsaki yayi kadan Yana fadin "duk nema suke su dagulamin lissafi wallahi har na rasa Yanda
zanyi" .
Rukayya najinsa tayi Shiru haushinsa takeji tun buyagin da ya yi Mata dazu,waje ya juya ya fita
Yana kokarin Kiran waya.
Hajiyar makwarari ce ta fito daga daki da manyan tabarmin roba a hannu tana fadin "zo Nan
Rakiya ki shimfida su cikin baranda kafin mutane su Fara taruwa".
Zuburo Baki tayi "Allah ki daina fada min sunan nan ni sunana Rukayya haka a ringa batawa
mutum suna".
Ta taso tana karbar tabarmin.
"Gidanku, nace Rakiya ba sunan ki bane, Kizo ki shiga kurmin ki karbo min masoro gurin Alhajin
Baba nayi na hadawa yarinyar Nan magani na Bata tun yau ta Fara amfani dashi ba'a bori da
sanyin jiki".
Saida ta Gama shimfidar ta shiga gurin Hajiyar cikin falonta suna duba kayan da za'a bawa
masu kawo kefen robar da aka zuba chicken pepper ta bude tana fadin "bari na dauki Daya naji
kamshin yayi min Dadi".
"Ki rufe wannan gashi can a kitchen a waje ki diba harda snacks din duka, Amma ki Fara karbo
Mata sakon a kasuwar tukunna kuje da sadiya ta rakaki ku shiga a dai daita tunda ba nisa ga
cunkoson cikin kasuwa Kuma kinsan Sameer baze Baki motarsa ba, wadda mukazo da ita
Kuma Aliyu yayi nasa gurin da ita". Basu dauki minti talatin ba suka dawo da sakon har lokacin Zahra barci take sai da jama'a sun
Fara taruwa a gidan duk dangi need sai dai-daikun Yan uwan mahaifar mujahidar.
A blender hajiyar taba mommy ta nika Mata masoron ta juyo mata shi a cikin robar da Hajiyar ta
bada a zuba a ciki.
Lokacin da mommy ta kawo Mata Hajiyar da kanta ta nufi dakin mujahidar tana fadin "Ina matar
Mahmudun take?.

Barcinta take sadidan Dan tabata Hajiyar tayi tana fadin. "Tashi 'yar nan ga maganin lalurar ki
da izinin Allah".
Tashi zahrar tayi tana bin Hajiyar da kallo lokacin data aje robar kusa da ita.
"Bude ki gani sai nayi Miki bayanin yanda za'ayi dashi".
Batayi musu ba ta bude robar taga garin masoron.
"Kina jina? Abinda za'ayi dashi ki ringa diba Kashi Daya bisa hudu na karamin cokalin shayi
kina zubawa a ruwab zafi tafasashshe cikin kofin ok ki barshi yayi minti ashirin a ciki sai ki tace
ki Shanye ruwan,haka Zaki ringa yi har ya Kare in Sha Allah ze narke yabi jinin al'adarki ya fice,
ki rabu da wannan shirmen komai ace za'a yanka mutum kamar kabewa" 'yar dariya Zahra tayi tana fadin in Sha Allah zanyi na gode madallah Allah ya saka da Alkhairi".
"Allahumma Amin. Allah ya Baki lafiya,ayi ta hakuri irin mijinki Mata Ido rufe suke nemansu sai
kin kauda Kai zakiçi ribar zaman aurenki. Amma kada ki kuskura ki yarda a nuna Miki San
iyawa akan mijinki, ki kula da sukarki Bata da damuwa ko kalilan ki girmama Masa danginsa da
kakarsa jiya ya wannan suna gidan Nan sunzo ganin Mai sunan mijinki na wurin Sameeru, Ni
cewa nake can wurinku zasu sauka ma sai naji Sameeru na maganar su fito zasu koma a jiyan
kinsan sha'anin tafiyar iska, ba wani nisa ke gareta ba".
Ita dai Zahra Jin Hajiyar take Dan ba komai ta fashimta ba.
Rukayya ce ta shigo da Abinci dasu snacks a babban tray tana fadin " Ai tunda naji shiru Hajiya
Baki fito ba nasan kin hanata barci kawai wallahi ke idan Kika so Abu ba sauki saina Allah idan
kinyi hakuri zata tashi ki bata".
"Ke tafi can waya fada Miki ana bori da sanyin jiki Baki San hadarin wannan abun bane baya
barin haihuwa fa ba dole a tari abun ba tunda wuri, wannan yarinya tubarakallah haka ai ba'aso
a samu abinda ze kawo Mata cikas a zaman aurenta ba, ni tunda na ganta ta kwanta min har
maganin tsarin jiki Zan karbo mata a Sanka, nan babban gida". Baki Rukayya ta rike tana kakabin Abun "Ikon Allah to ke Hajiya fada Miki tayi tana son na tsarin
jikin? Da kike faman fadin Zaki karbo Mata".
Kafin Hajiyar ta Kara magana Zahra ta rigata.
"Haba Aunty Rukayya Ina laifin Hajiya kuwa tunda na sako Qafa gidan Nan Bata huta ba
hidimata takeyi".
"Eh haka ne kam tunda har kasuwar kurmi ta aikeni, da girnana da komai nace bazanj ba tace
nayi mata kiwa dan rabon da naje cikin kurmi tun Ina secondary Dan ma ban manta shogon ba"
Ficewa Hajiyar tana fadin kyaji dashi idan Kaya ne".
Tashi zahrar tayi tana fadin Bari na dawo, ta fice daga dakin.
Toilet ta shiga ta Kara gyara Kanta, lokacin data fito dai dai lokacin masu kawo lefen suka
karaso suma Nan da nan gudan ya dauki jama'a Dan makota ma Wanda suka makara suka
ringa shigowa.
Ganin gidan ya kacame da jama'a yasa Zahra tayi amfani da wannan damar ta nufi hanyar
soron gidan, a soron ta tsaya ta Ciro wani face mask da yake cikin jakar ta da eyeglasses dinta
ta saka ta fice daga gidan.
Ba Bata lokaci tana fita Dan sahu Yana kawo Kai, ta dafe shi ta shige, tana fadin "Janbulo zaka
Kaini".
"Hajiya sai dai drop gaskiya Dan hanyar ta baude ni rimi na nufa".
"Muje Zan baka kudin drop din".

Ta fada tana Dan leken gefenta kamar narar gaskiya, hankalinta be kwanta ba sai da taga sunyi
nisa da unguwar, ajiyar zuciya ta sauke tana "na barka da Dr Sai ku cinye kanku haka kawai
za'a sabautani saboda Kai,Wanda har yanzu bansan daga wace bahiyar ka bullo ba, ayi min
sakiyar da Babu ruwa a cuceni a cuci rayuwata shi yasa na taho da hirina idan tayi ruwa rijiya
idan batayi ba ta Zama Masai"
Kafin su karasa layin su Ssjida tacewa Mai adaidaita din ya taya gurin me P. O.S zata ciri kudi.
Har kiofar gate din gidan ya kaita 10k ta bashi, cikin mamaki ya dubeta "Hajiya kudin sunyi over
dari bakwai ne kudin, Hala ke bakuwa ce?"
Gaga tayi Tana fadin na sani kaje kawai nagode Allah ya tsare".
"Na gode Allah ya rufa asiri ya kara Miki daukaka".
Tana tafiya tana fadin. "Allahumma Amin".
Ta shige gidan shi Kuma ya juya Kan mashin dinsa ya wuce Yana Fadin "Bari na koma na
sallami gidan sai na Kara fitowa".


***********


Bayan tafiyar masu kawo lefen an baje anata kallon kayan arzikin da suka kawo Masha Allah
kayansu sunyi kyau sosai Dan akwatuna set hudu suka kawo da manyan jakunkuna uku har da
adudu biyu.
Saida komai ya lafa sannan hankalin Rukayya ya dawo jikinta ta shiga neman zahra, abin
mamaki ba zahra ba alamarta Abu kamar Wasa ya Zama gaske Nan da Nan tashin hankali ya
wanzu a gidan Dan mantawa akayi da murnar wani lefe Nan da Nan Rukayya ta Fara share
hawaye. Mommy ce ta Farayi Mata fada "Haba Rukayya menene haka Zahra Karamar yarinya ce ku
shiga makota Mana ko taron jama'a ne bataso ta shiga can ta zauna ba kince toilet tace Miki
zata shiga ba? Kafin ta fito Kuma bakin sun shigo?"
"Eh haka ne Amma Naga fitowarta harta tsaya a can daga Nan mutane sukayi yawa ban sake
ganinta ba".
"Ke Zubaida maza ku shiga gidajen kusa ku duba ko can ta shiga ku kirawota".
"To mommy". Ta fada sukayi waje su uku.
Hajiyar makwarari kuwa cewa take "Ina yarinyar nan ta shiga ko masu kawo kayan tabi suka
tafi".
Wani kallo Rukayya tayi Mata "kaji Hajiya da wani zance kamar wata 'yar baby ce zahrar da
zatabi wasu mutane".
"Ungo Nan".
Abu kamar Wasa karamar magana tana neman Zama babba, duk kukkuken babu it's Babu
dalilinta komai Kama da Zahra Babu.
Mommy da Kanta ta Kira Sameer tace duk inda yake yazo yanzu tana son ganinsa.
Daman ba nusa yayi ba Yana tare da abokansa na unguwar Dan a hannun Hajiyar ya girma
harya Gama secondary school dinsa.
A tsakar gida ya samu su mommy anyi cirko-cirko.

"Gani mommy lafiya na ganku haka?".
Hajiya ce ta Fara fadar "Ina fa lafiya ba'aga matar Mahmudu ba har makota anbi baku ko
alamarta".
Mommy ya kalla. "Kamar ya ba'a ganta ba? To Ina ta shiga?"
"Allahu A'alam, da farko abin ban dauke shi haka ba sai yanzu da naga da gaske ne yasa nace
Bari na Kira ka".
"Ok, Bari naje Nan Ina zuwa"
Ya juya ya fice da sauri, cikin tashin hankali me ze fadawa Mijinta Ina ta tafi?.
Tambayar mutanen kusa masu sana'a a kofar gidan ya rinka yi, har ya juya sai wani Mai sayar
da Mai yace yaga fitowarta da face mask da glass a Ido ta hau a dai- daita sahu sunyi hanyar
nan ya nuna hanyar gidan shatema.
Dafe Kai yayi cikin tashin hankali, "wannan wace irin masifa ce haka kawai an tadawa yarinya
hankali har ta yanke Shawarar tayi tafiyar ta, to tana Ina? Ina ta tafi? Ba wani ta sani a garin
Nan ba ga Babu waya a hannunta, Saida ya fada masa ya fito Mata a mutum sak a wuce
wannan wasan yaran ya kaita inda ya Dace a duba Masa ita amma ya gano ya yiwa Haseena
waya ta a duba Masa ita yasan karshen film din ba Mai kyau bane"
Jiki ba kwari ya koma ciki..



***** ***** *****

Hankalin Zahra be kwanta ba so sai Saida ta ganta a cikin falon gidan su Sajida, Mai aikinsu ta
bude Mata parlourn tana fadin "A'a marhabin maraba da Amarya sannu da zuwa".
Ta fada tana murmushi, tare suka shigo ciki.
"Yauwa Mama Hauwa sannu da gida, ya naji gidan naku Shiru ko su Mamar basa nan ne?"
"Wallahi sunje Rimin sumaila duba kanin Baffa bashi da lafiya,a nan ya kwanta a Asibitin
Murtala to shine sukaje su Kara duba shi da jikin".
"Allah sarki ko kawu Musa?"
"Shine Ashe kin sanshi".
Eh nasan shi Mana, har a gidansa mun kwana lokacin da mukaje da sajida. Allah ya bashi lafiya
yasa kaffara ne"..
"Allahumma Amin, Bari na bude Miki dakin mutuniyar ki shiga na kawo Miki abinci can, inaga
sai dare zasu dawo tunda suka Kai har wannan lokacin".
Wanka ta shiga ta Dade a toilet din kafin ta fito tana tsane jikinta da towel, lotion ta shafa ta
dauko Rigar material marar nauyi ta saka a cikin kayan sajida.
Jallop din kuskus aka kawo Mata wadda Tasha kayan lambu da pepper soup na kayan ciki da
kunun aya Mai sanyi da ruwa.
Abincin taci ta koshi ta dora da kayan sanyi tayi hamdala ga Allah ta kishingida jinta take fresh
idan Allah ya kaimu safiya ta karawa motarta Mai, ganinta a araha yasa ake garata kamar
kwallo.AUREN HUCE HAUSHI.

MAMAN FATEEMAH

Page 42.

_______Abu kamar Wasa har kusan karfe taran dare ba zahra ba labarinta, iya Rahane
mommy ta Kira tana tambayarta kosu Rukayya sun dawo? Dan bazata fada ba direct tace ana
neman zahrar hakan dabara ce ta tambaya a fakaice.
Amsar data Bata ita ta Kara tadawa kowa hankali cewa tayi "Basu dawo ba tun fitar safe da
sukayi ga zulai ma duk ta shiga damuwa tace tun yamma Ammarta ke Kiran wayar zilan tace
wayar zahara'un Bata shiga".
"Yanzu ya za'ayi kenan?"
Rukayya ta tambaya.
"Ni damuwa ta Daya kada ta fada mugun hannu Dan ma dai ba lallai ansan matar waye ba
Amma yau abin tsoro ce kiransa zanyi kawai na fada Masa halin da ake ciki ko yasan wasu 'yan
uwansu a nan kanon, tunda barin Kashi a ciki baya maganin yunwa gara ya fada kawai asan
Yanda za'ayi tun guri be kure ba. Number dinsa yayi ta try Amma amsar Daya ce a rufe take.
Da kyar ya mayar dasu mommy gida har Rukayya a gidansu ta sauka, to ta koma tacewa
baiwar Allah da sukazo tare zahrar ta Bata ko me?"
Duk wani lissafi ya gama suncewa Sameer, duk wannan Abu be tashi faruwa ba Saida sukazo
gidan kakarsa, ita kanta Hajiyar makwararin tashi Dan kukanta tana mitar yarinyar Nan Bata
kyauta Mata ba ta rasa a inda zatayi irin wannan shegantakar sai a gidanta.
Jiki ba kwari Sameer ya shiga gidansa, sau Daya Fateeha ta kalleshi ta dauke Kai ta cika fam
da fushi tun safe Daya fice Bata Kara sakashi a idanunta ba, ta kirawo shi ya Kai sau biyar sai
dai yace Mata gashi Nan Amma bezo ba sai yanzu wurin Sha dayan dare.
A kusa da ita ya zauna ta kauda Kai, hannu yasa ya dauki yaron a Kan cinyarta, yasa hannu
Daya ya tallabota ta hada da babyn ya rungumesu, Jin ajiyar zuciyar da yake saukewa a jajjere
yasa Fateeha ta gane da matsala.
"Wai menene?"
Ta fada cikin damuwa.
"Bari kawai wlh hankalina a tashe yake, tun bayan Azzahar Zahra ta fice daga gidan Hajiyar
makwarari bamu San inda ta nufa ba, duk inda muke tunanin zataje munje Bata nan".
Itama mantawa tayi da fushin da takeyi dashi ta Fara sallallami "Yanzu Ina ta tafi? Kadafa wani
Abu ya sameta kasan mutane yanzu gaskiyar su kadan ce".
Dafe kansa da yake Sara Masa yayi "Bana tunanin haka gaskiya da Kanta ta fita ta tafi kawai
dai an Bata Mata Rai ne ban Kuma yi tunanin abin yayi Mata zafi haka ba da bazan barta a
gidan Hajiyar ba, amfani tayi da masu kawo lefen mujahida ana can gurin karbar lefe ita Kuma
ta fice daga gidan Dan akwai Wanda ya fada min Yanda ta fito nasan da niyya ta fice abunta". Zuru Fateeha tayi tana sauraren mijinta.
"Ka Kira ka fada masa?"
Kai ya girgiza Yana fadin na kasa samunsa nafi one hour Ina nemansa ban same shi ba".


*** *** *** ***

Karfe Tara su Umman sajida suka shigo gidan lokacin Zahra na parlour suna hira da Mama
Hauwa, turus Maman tayi ganin zahra ko rantsuwa tayi Babu kaffara, wannan ba zuwan arziki
bane amma sai ta share tana fadin "wa nake gani haka?"
Dariya Zahra tayi tana fadin "Umman mu sannunku da hanya".
"Yauwa sannu,aike za'a yiwa sannu kin sha doguwar tafiya".
Shiru zahrar tayi batace komai ba, kannen Sajidar ne suka Fara gaisheta suna fadin "Aunty
kin rigamu zuwa munata cewa idan Ya Abba ze Kai Miki sakonki da Baffan Rimi ya bada a Kai
Miki zamu bishi sai gashi Kuma kinzo"
Karamar kanwarsu ta janyo tana fadin "ai zakuje ko mutuniyar tunda anyi min Alkawarin
zuwan".
"Eh zamuzo Aunty zahra".
Nusaiba ta fada suna Zama kusa da zahrar, yayin da Maman su ta wuce bedroom dinta tana
cike da tunani barkatai a zuciyar ta.
Tana shiga jakar hannunta ta zuge ta Ciro wayar ta, Ammah ta Kira Dan bazata Zama uwar
banza ba da alama gudowa yarinyar Nan tayi.
Lokacin da Kiran ya shigowa Ammah tana duba wasu kaya da Hajiya kaltume ta Aiko Mata
dasu ne.
Ganin Umman sajida ne yasa ta aje kayan ta dauki wayar tare da sallama.
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
"Hajiya ya gida ya wajen Amare? Ina ta son na Kira mu gaisa Allah Bai nufa ba sai yau, itama
zahrar mun kwana biyu bamu gaisa ba".
"Wallahi kowa lafiya, Amare Kuma suna nan kusa daku Bata jin dadi ne mijin ya matsa suzo
Nan Kano a dubata ni tun safe da muka gaisa da wayar zilai ban Kara samunta ba, na Kirawo
zilan ma tace min har yanzu Basu dawo ba duk ta tada hankalin ta, nace ita da ba ita kadai ta
fita ba tare suke da amininsa da kanwarsa, Kinga duk inda suke ai suna tare". Shiru Maman tayi kenan hasashenta ya kusa Zama gaskiya Kenan.
"Hajiya ga zahrar a gidan nan,yanzu muka dawo daga Rimi Sai na tarar da ita Ina ganinta
nasan ba lafiya ba Ashe garin sukazo ta kawo min ziyara".
Jim Ammah tayi tana jinjina lamarin.
"Anya kuwa ki dai saka Mata Ido zuwa safe kome ke nan sai ki fada min idan anzo daukarta to
da sanin mijin tazo idan Kuma tace zata tafi ki hanata ki fada min na gode kwarai Allah yayi
Mana jagora ya Raya Mana zuri'a".
"Allahumma Amin". Sukayi sallama.
Zuciyar Ammah sai bugawa takeyi a hankali ta furta "meke Nan Kuma? Ni Asma'u Allah ka
taimaki 'yar marainiyar Allah, matsaloli daga an toshe wannan sai waccen ta bulle Allah yayi
Mana maganin wannan matsaloli yanzu kuma ko menene damuwar datasa ta tsallake tabar
inda suke gashi ta Kama wayar ta rufe Dan ma kada a San inda take,ai kuwa zamu gauraya
bazan dauki shashanci ba".
Ta hada duk kayan ta zuba a ledar da aka kawosu ta fice daga dakin ta nufi dakin Abban Yara
tunda ita keda girki.

Saida Umman sajida tayi wanka tayi sallah sannan ta fito har lokacin suna falon da yaran direct
dining ta nufa taci abinci sannan ta dawo falon.

Gaisheta zahra ta Karayi tana tambayar ya Mai jikin,
Dasu Baffa.
Sun dauki lokaci suna hira kafin Ummar tace "Wai daga Ina kikazo ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login