Showing 24001 words to 27000 words out of 68809 words

Chapter 9 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf

M Shakur   

07 Oct 2025

1811

dauro alwala see
dadduma kazo kai sallan asri da magrib mutafi gida dan an riga an sallamemu" rigar ya saka
sanan ya shiga bayin dakin ya dauro alwala yazo yay salla.
Bayan ya idar yana kan dadduma wayar Islam dake kan gadon tai kara hannu ya mika ya
dauko "My Heart beat" wani irin bugawa kirjinshi yayi dayaga sunan, duk yanda yaso ya hakura
yakasa saida yay picking call yasa a kunne daga dayan bangaren Fahad yace "princess inata
miki text baki replying, I miss you yau ba muyi wayaba" wani abune yaji ya tokare mai zuciya,
"Hello my princess are u there luv?" "mallam karka kara kiran layin nan, an riga an mata miji am
her husband to be, so be very careful" yafada cikin fushi ya katse wayar, tashi yay ya linke
daddumar yabama Yusuf dake kallonshi baki bude yadau wayar shi batare daya kalli Yusuf ba
yace "muje" fita sukayi sanan ya juyo ya Kalli Yusuf ahankali yace "am coming" zama Yusuf yay
akan kujerun dake reception din shikuma yay hanyar dakin da Islam take, ahankali ya bude
kofar, dayar gajeren sallama dan bama tajishi ba tana zaune kan gado da doguwar riga ajikinta
na atampa kanta da bakar hula da aka dan matsar dashi baya sabida bandejin goshin, ta mikar
da kafafunta taja doguwar rigar zuwa saman gwuiwowinta tana hura ciwon dataji dake mata
zafi.
Ahankali yake daga kafa haryakai bakin gadon ya tsaya yay folding hanunshi a kirji cikin sanyin
murya yace "is it paining you?" gyada kai tayi tana yarfe hannu tana hurawa batare data dago
kaiba dan gabaki dayan hankalin ta nakan ciwon, dago kai tayi da sauri ta kalleshi da katon
bandejin dake goshinta da sauri ta saukar da rigarta ta rufe kafafun ta, dan murmushi yayi
sanan ya zauna abakin gadon yana fuskan ta hararan shi tayi tace "waikai duk inda nake
sekazo, tracker kake amfani dashi ne? Wlh ko kafita daga dakin nan kona kirama Abbana
nahadaka dashi komame zai faru ya faru" murmushi yasake yi sanan yace "how are you feeling
now?" dauke kai tayi ta turo baki, sosai yake kallonta sake juyo dakai tayi ta kalleshi tace "wai
bazaka fitaba sai su Abbana sunzo, okay bari na kirasu" bude baki tayi zatai ihu yadaura hannu
akan lips dinshi alamun tai shiru, kasa magana tayi kaman wacce yama magic saima dauke kai
datayi daga kallon dayake mata jitake kaman ta makeshi, hanunshi yasa a aljihun wandon shi
yaciro wayarta ya mika mata juyowa tayi tana ganin wayarta ta karba da sauri akuma dan rude
tace "a ina kasamo wayata?" baice komiba yatashi tsaye yana kallonta yace "waye My
heartbeat" da sauri ta kallai sanan ta harareshi tareda murguda mai baki tace "meruwan ka and
kafita daga nan" kallon cikin idonta yayi yace "well I told him karya sake kiranki because am ur
husband to be" kwalalo ido tai ta kalleshi da so much pain a idanunta tace "Fahad din nawa ka
fadanma haka?" gyada mata kai yayi yace "yes" azuciye ta juya tana waige waige pillow dake
bayanta ta raruma ta jefamai da duka karfin ta ya chafe yana murmushi har saida hakoranshi
suka bayyana daidai lokacin Anty Hindu da Abba suka shigo, Abba yace "Ummi Khaleel din kike
bugama pillo mutumin daya taimakeki dabadan shiba da Allah kadai yasan mezai sameki" da
sauri ta kalli fuskarshi, dan murmushi yamata sanan ya tako yadan duka ya ijiye filon abayanta
ahankali yace "I will come and check you tomorrow, I love you" yay maganar ta yanda ita kadai
zata iyaji ya juyo ya Kalli Abba da Anty Hindu yace "Abba saida safen ku" addu'a sosai da
godiya Abba da Anty Hindu sukamai sanan ya juya zai fita daga dakin dan waigowa yay ya
kalleta daidai lokacin itama tadan dago kai suka hada ido hannu yadaga mata alamun bye,

kawad dakai tai da sauri murmushi kwance kan fuskarta.
[6/17, 6:38 PM] Maman Jedda: Novels
*JARABTA*
Maman Abd Shakur
32 & 33
Kaman mai rada yace "I love you so much, zuciya ta bazata iya jure rashin kiba, nasan baki
sanni ba but please give me a chance, ina sonki sosai" dan hawaye taji ya gangaro mata,
girgiza mata kai yayi ahankali yace "will u marry me please" dan lumshe ido tayi tareda dagamai
kai maganar Anty Hindu dataji tawaje ya mai do da ita hankalin ta da sauri ta tashi ta zauna ta
kawad dakai kirjinta na bugawa sosai tashi tsaye yayi shima yana kallon fuskarta, bude kofa
Anty Hindu tayi ta shigo ita da Dr, dubata Dr yayi sanan yace "Hajiya babu wata matsala, nan
da yan kwana biyu yan ciwukan nan zasu warke zaku iya tafiya" Anty Hindu tace "to nagode Dr,
bari nakira Bala yazo ya dauke mu" da sauri Khaleel yace "basaikin kirashi ba nina kaiku
Hajiya" yay maganar yana kallon fuskar Islam da har yanzu taki kallonshi, "to shikenan, ke tashi
mutafi" ahankali ta mike tsaye tadau Hijabin ta tasaka shiya fara fita sai ita da Anty Hindu
dasuka fito suna biye dashi abaya kofar baya ya bude musu suka shiga sanan yarufe sanan
yakoma gaba yabude motar ya shiga ya kunna yafara driving har suka fita daga hospital din, ta
mirror gaban mota yaketa kallonta amma taki dago kai saima wasa da yatsun ta da taketayi, har
cikin compound ya shiga dasu suka fiffito da sauri tai cikin gida dan bataso su sake hada ido,
Anty Hindu ce tamai godiya cike da fara'a da addu'a sanan ya kunna mota yafita daga gidan.
Afalo taga Farida ta zauna taci uban tagumi tsakanin jiya da yau duk tai zuru zuru tana ganin ta
ta taso da gudu ta rungumeta tsam tsam sakinta tayi ta kalli fuskarta tace "sannu Islam ya
jikin?" dariya ma tabama Islam hakan yasa tai dan dariya tace "ke dalla am fine ciwo fa kawai
naji, Ina Mum?" jiki a sake tace "tana daki" tace "bari naje na gaishe ta" sama tayi saida ta
gaida Mum tamata ya jiki sanan ta wuce dakinsu bayi ta shiga tai wanka da ruwa mai dumi
sanan ta fito, light kaya tasa tazo ta kwanta akan gado dan bacci takeso tayi ta lumshe ido,
fuskar Khaleel tagani yana mata murmushi da sauri ta bude ido tajuya dayan gefen tasake
lumshe ido tuna sanda ta daura fuskar ta akan hanunshi tayi, bude ido tayi da sauri ta tashi ta
zauna tareda jan uban tsaki dan mugun haushin kanta takeji tayaya ma tai hakan wat was
wrong with her, waya ta dauka tasake dailing number Fahad bai dauka ba, message ne ya
shigo wayar ta bude bakuwar number ce hakan yasa ta bude "I love you so much. Khaleel" wirgi
tai da Wayan akan gado tareda yin tsaki "mutum sai shegen naci anaci"
Misalin 9 na dare Yusuf ya shigo part dinsu ya sameshi yana zaune yana daddana waya
gefenshi kuma tea ne daketa kamshin su citta, zama Yusuf yay kusa dashi yadau tea ya kurbe
hakan yasa ya kalleshi batare dayace komiba, murmushi Yusuf yayi yay gyatsa sanan yace
"idan ma masifa zakamin naji amma kafara zuwa Abba na kiranka" filon dake kan kujeran yadau
ka ya naka mishi akai sanan yabar dakin. Sallama yayi ya shiga dakin Abban, shi kadai ne
sanye da farar jallabiya idanunshi acikin medicated glass yana karanta littafin addu'oi samin
waje yay ya zauna akasa. Saida Abba yagama sanan yarufe ya ijiye gefe ya kalleshi yace "Son"
"Na'am Abba" Abba ya gyara murya yace "ahh dama magana nakeso nai dakai kan yar
abokina, nafison naji daga gareka ne dan mahaifinta yacemin yayarshi tace kun dan dade da
sanin juna dan har gidan su kajema" shiru yadanyi yana nazarin fuskar Khaleel din sanan yace
"kana sonta ne?" sosai yaji kunyar maganan Abba hakan yasa yadanyi murmushi yana sosa

keya, dan dariya Abba yayi yace "a'a to to to, wanan murmushi haka Khaleel ta eh ce ko" dan
gyada kai yayi kanshi akasa Abba yace "to masha Allah dama nariga nai magana da mahaifinka
ran sati zaizo sai muje nema maka auran ta, banason awani nisanta bikin sabida dazaran anyi
auren kukadan yimana kwana biyu anan saika koma bakin aikin ka ko" gyada ma Abba kai yayi
Abba yay murmushi yace "saura dan uwanka yanzun nan nagama dashi nabashi wata daya
idan Bai fito da mataba nizan nema mai" dariya Khaleel yayi wanan karan, Abba yace "tashi
katafi Allah muku albarka".
Sheshekan kuka datake ji yasa ta farka cikin tsakiyar daren nan, ahankali ta mika hannu ta
kunna wutar dakin hakan yasa baccin idonta ya washe sosai, wawwaigawa tayi bataga kowa
akasa ba hakan yasa ta sakko daga gadon, Farida tagani ke kuka a kwance da sauri tahau
matattakalan bonk din tahau kan gadon ta dago ta, ta zaunar da ita takai hannu arude ta taba
wuyan ta tace "baki da lafiya ne?" girgiza kai Farida tayi tana goggoge hawayen dake zubowa
kaman an bude famfo, komawa tayi zata kwanta Islam tariko hanunta tace "talk to me please,
problem shared is problem solved" fadawa tayi jikin Islam tafashe dawani irin kuka harda
shesheka hakan yakara ruda Islam ta kankameta tace "Faree konaje na taso Mum ne?" girgiza
kai Farida tayi ahankali tace "wlh Islam ina mugun sonshi, son da bazan iya kwatanta miki ba,
amma kwata kwata bama ya daukan wayana yanzu, baya kulani na rasa yanda zanyi da kaina"
kama fuskarta Islam tayi tace "listen listen kidena kuka kinata wahala shi baimasan kinayi ba, ki
manta dashi jor, kanme zakizo kina wahala, ki manta dashi" girgiza kai tayi tace "bazan iyaba, I
tried but nakasa I love my superman so much Islam bazaki gane bane" shiru Islam tayi cike da
tausayin ta ahankali tace "to kinfada mai kina sonshi?" girgiza kai tai alamun a'a, tace "to duk
randa kika sake ganinshi kinfada mai am sure zaisoki back" murmushi tadanyi ahankali tace
"thank you Islam" kwantar da ita Islam tayi sanan ta kwanta agefen ta sukaja bargo suka kashe
wutan dakin.
Gabaki dayan su suka hadu suna aiki a kitchen sabida Abba yace zaiyi baki sha daya zasuzo,
Farida ta rame har Abba saida ya tambaye ta meke damunta tace bakomi Wuraren goma suka
gama aka zuzzuba abincin a hadaddun kuloli, sanan kowa yawuce daki danyin wanka.
Suna shiga daki Farida ta kulle kofar su hadda sa sakata sanan ta kalli Islam dake kokarin cire
kaya tace "kinsan me mommy tacemin?" girgiza kai Islam tayi tace "cewa tayi wai aurenki fa
za'a zo nema yau" sosai taji kirjinta yabuga dum! Farida tace "kinsan dama baki bani labarin
yanda kuka karasa da Fahad ba dama kin yarda yaturo ne?" arude ta girgiza kai tace "cemai fa
nayi sainayi magana da Mummy, baifadamin zai turo ba and kona kirashi baya picking fa rabona
damagana dashi tun Ina hospital" dariya Farida tayi harda kama ciki tace "yamin daidai,
gwarama daya turo kinadai ji Abba yace mungama school dinan zai xhanza mana wanine, to
mezaki zauna kiyi har next year, wlh nima dazaran na sasanta da superman dina aure zamuyi
abunmu na cigaba da school din a dakina" tsaki Islam tayi ta ijiye wayar tace "kinga yaki picking
ko" gwalo Farida tayi tace "ke dalla chan ki kyaleshi idan aka samuku rana yau ai automatic
soyayya ce zata wani kara kulluwa" harara ta wurgamata tasake dariya tareda yin wurin kofa
tace "kinga bari naje na debo mana abincin mu a flask dan dazaran iyaye sunzo bamu sake
sauka kasa ina zasuga Amarya kafin aure" takalmi ta dauka ta jefamata da sauri tafita daga
dakin tana dariyan shakiyanci rabon datai dariya haka harta manta.
Wuraren sha daya da rabi suka iso Babban Khaleel da Baban Eesha sai Kuma Abba da wasu
abokana yen shi biyu duk sunci manyan kaya, da kanshi baban Islam yamusu iso nan suka

zazzauna afalo ana gaishe gaishe kafin Mum da Anty Hindu da Maman Miemie suka fito aka
gaggaisa sanan aka gabatar musu da abinci sukaci suka sha sanan aka fara magana. Basu
boyema Baban Islam komi akan Khaleel ba ba karamin tausayin shi yajiba, nan ya yarda ya
amince yabasu Islam yace ai tun randa Anty Hindu tafada mai yatura a kamai binciken halin shi
Alhamdulillah duk yan anguwa sunce mutumin kirki ne ga zuwa massallaci. Aka fara maganan
sa rana wata biyu yace amma Abba ya roki alfarma abarshi wata daya sabida suna son Yaron
yakoma bakin aiki ya dade rabonshi da aiki nan baban Islam ya yarda, Baban Eesha ne yafita
ya shigo ga jakunkunan gorori mai gadi ya tayashi dauka da su sweet nan aka ijiye dubu dari
kudin nagani Ina so Anty Hindu tawani saki guda. Bayan anyi finalizing everything aka rufe
taron da addu'a sanan suka wuce massallaci danyin sallan azahar dagangan suna dawowa
suka tafi murmushi akan fuskar kowa.
*JARABTA*
Maman Abd Shakur
34 & 35
Aika Mum yayi takirasu zama sukayi su biyun afalon Abba yay gyaran murya yace "burin
kowani uban ne yaga yarshi ta sami miji dan mutunci yaro mai hankali da addini da hikima, to
Alhamdulillahi Ummi nariga namiki miji wanda kika sanshi sosai Muhammad Khaleel" ba
karamin bugawa kirjinta yayi ba har saida ta dago kai ta kalleshi ya cigaba yace "mun riga mun
gama magana da iyayen shi, an saka rana sati hudu, bayan biki zankudan yi kwana biyu anan
yola sanan ku wuce Abuja sabida ya koma aiki, idan kinada any abu dakike so ki fadama
Mummy ku sai asiyo miki" Ya gyara zama ya kalli Farida akunyace ta labe abayan Islam tace
"Abba nima kwanan nan zan fito da nawa" murmushi kawai Abba yayi yace "Faridan Abba
kenan to Masha Allah, Allah nuna mana ku tashi kutafi" atare suka fito daga dakin Farida ta
kalleta tadan zaro ido tace "ke waye kuma Muhammad Khaleel nazaci Fahad ne ya turo?" kasa
magana tayi sabida wasu hawayen bakin ciki da suka zubomata da gudu ta bude kofar dakinsu
ta shiga ta zauna akan gado, Farida ta zauna akusa da ita tace "waye Muhammad Khaleel din?"
kwallan daya dan zubomata ta share tace "wani ne fa datunda muka hadu duk inda naje saiya
bini kaman maye, yace yana sona ni banason shifa Fahad dina nakeso" Farida tace "to mesa
baki fadama Abba baki sonshi ba?" turo baki tayi ahankali tace "kasawa nayi wlh kaman
antushe min baki" murmushi kawai Farida tayi tace "lemme not waste my saliver akanki dan ga
sonshi nan kuri aidonki, nidai duk randa yazo I will love to meet him o" tashi tayi fuuuu ta dau
wayarta ta shiga bayi ta rufe tai dailing number shi harya gama ringing bai dagaba saida ya
katse ya kirata back cikeda tsiwa tace "nace ina sonka ne dazaka tura gidanmu?" murmushi
yayi sanan yay magana ahankali yace "ai basai kince kina sonaba wife, gangar jikin ki, rohin ki,
murmushin ki, kwayar idanunki sun riga suncemin suna sona so mezan jira? Yau dayake fada
kikeji shine harda kirana bayan idan nakira ki u don't pick" rasa abinyi tayi hakan yasa ta fashe
mai da kuka dan dariya yayi kafin ya sassauta murya yace "please don't cry, how about gobe
nazo na lallasheki da kaina" tsayar da kukan tayi tace "Allah inkazo gidanmu saina cirema
kafafu" wanan Karan dariya yayi sosai, shiru tadanyi tana sauraron yanda sautin dariyar nashi
ke fita kaman Karya dena, dan shiru yayi kaman yasan meke zuciyar ta yace "you like how I
laugh, na cigaba?" da sauri ta kashe wayar tana dan murmushi bude kofar tayi tafito daga bayin
Farida ta harareta tace "kai Islam keko, kina so kina iskanci hegiya pretender" dauke kai Islam
tayi kaman bataji taba tazo zata zauna akan gado filo Farida ta naka mata hakan yasa ta fada

gado tana dariya ita kanta mamakin kanta take to Mesa tama kasa fushi.
Wuraren biyar na yamma yazo yana sanye da shadda mai ruwan toka sai kamshi yake, Anty
Hindu tasa aka shigo dashi saida suka gaisa sanan tabar falon sama taje tasami Farida da
Islam zaune tace "ke tashi ki xhanza kayan jikin nan naki Khaleel yazo" ganin Anty Hindu ta
tsaya masu akai yasa ta tashi shiryawa tayi cikin simple brown material da akai mata doguwar
riga ta daura milk color hijab din gida daya tsaya mata acinya tadan shafa hoda tasa lipgloss
tadan fesa turaren Posess sanan ta kalli Farida tace "zomuje ki ganshi fa" girgiza kai tayi tace
"ke haka akeyi jeku fara gaisawa tukun anjima zanzo" fita Islam tai daga dakin. Shigowa falon
tayi batare data kalleshi ba ta wuce kujeran 2 sitter dake kusa da kujeran daya zauna ta zauna
tana gyaggyara hijabin jikinta. Ahankali yataso yazo ya zauna akan kujeran datake ya
fuskanceta yana kallon fuskar ta batare dayace komiba, dan dago kai tayi ta kallai, hararan shi
tayi sanan ta turo baki tace "katashi kabarmana gidan mu" make mata kafada yayi hakan yasa
ta dauke kai da sauri dan wani iri taji, ahankali kaman mai rada yace "I miss you ummina" dan
dago kai tayi suka hada ido hakan yasa tasake dauke kai, tagumi yay ya cigaba da kallon ta
kaman yau yafara ganin ta, batare data juyoba tace "stop looking at me" girgiza kai yayi yace "I
can't" juyowa tayi tace "kabar mana gidanmu kuma" girgiza kai yasake yi yace "I can't" juyowa
tayi cike da masifa tace "ninace ina sonka ne dazaka tura aje wurin Abban mu" Ahankali yace
"but I love u" yay maganar murmushi kwance kan fuskarshi, ahankali yace "Are you angry with
me?" hararan shi tayi ganin yamaida ita wawiya, hannu yasa a aljihun rigar shi yaciro chocolate
bude chocolate din yayi yadan matso kusa da ita ya Kalli fuskar ta yace "kinsan ance chocolate
na mantar da mutum fushin dayake yi ko" yay maganar yana kallon kwayar idonta...
Ahankali Farida ke sakkowa daga stairs sanye da hijab harta shigo falon, numfashin ta taji yana
neman barin kirjinta ganin Superman dinta da Islam suna wani irin kallon juna...
Cikinsu babu wanda ya lura da Farida, kallonshi Islam tayi sanan ta kalli chocolate din daya
bude yana miko mata make kafada tayi tace "I don't want" dan matsowa yay

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login