Showing 54001 words to 57000 words out of 68809 words
Chapter 19 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf
idan kaga yanda ta rame kaman mai
wani ciwo, tai wani irin yaushi, wani irin tausayin tane ya shigi Abba amma hakan bai hanashi
daure fuska ba ya kalleta tareda gyara murya yace "ina jinki" dago kai tayi ta kalli Abban
ahankali tace "Abba dan girman Allah ka karamin lokaci wlh banda kowa har yanzu ne Abba,
dan Allah" takarashe maganan kaman zatai kuka hakan yasa Abba ya kasa dauke idonshi daga
kanta da hannu yamata alamun tazo hakan yasa taje gabanshi ta zauna duktai wani iri da ita ya
kafeta da ido, hanunta har rawa yake ta daura akan kafarshi tawani irin fashe da kuka tace
"Abba wlh na tuba na mugun yin nadaman abinda nama Islam, babu randa zanyi salla da bazan
nema mata addu'a samin lpy ba, Abba dan Allah kadena fushin nan dani dan Allah kayakuri
kayafemin ka kiramin Islam na rokesu suma" ta kife kanta akafarshi tana kuka hanun Abba
dataji akanta yasa ta dago fuskarta ta kalleshi, share mata hawayen yayi dadan murmushi akan
fuskarshi yace "nadade da yafe miki Farida komi yawuce" murmushi sosai tayi ta goge kwallar
tace "nagode Abba" kanta Abba yasake shafawa yace "inaso kifadi mini gaskiya meke damunki
maisa kika rame haka Farida, kar wani ciwon yazo ya kamaki, meke cinki araine" wani sabon
kukanne yazo mata dukda yanda taso ta danne kasawa tayi tafashe da kuka sosai da kyar tai
shiru Abba yace "inajin ki" wasu zafafan kwalla ta goge ahankali tace "Khaleel, Abba narasa ya
zanyi nakasa cire sonshi azuciyana, nina rasa wanan wani irin sone, narasa yanda zanyi da
raina, Abba please help me wlh zuciyata har wani zafi take kamar garwashi" sosai Abba yaji
tabashi tausayi ya gyara zama yace "inaso kiyi azumi koda uku ne sanan kullum zan dinga
tadaki da daddare kidinga kiyamul laili ki roki Allah yabaki ikon cin wanan jarabawan, haka Allah
yake abinshi yakan jarabce ka da komi yaga yaya zakayi, so kidage kici wanan jarabawan karki
biyema zuciyar ki ta kaiki ga halaka, kikoma ga Allah sai kiga Allah yassare miki matsala dake
damunki, bari nabaki labarin Khaleel dinan kiji sabida kingane cewa auren nan nashi da Islam
Allah ne kawai yahada, robone atsakanin su saisama har yazo garin nan suka hadu har sukai
aure" nan ya gyara zama yabama Farida labarin Khaleel tiryan tiryan yanda su Abba suka
bashi, ba karamin mamaki Farida taiba, bakin da Abba yay yasa tafito daga dakin jikinta duk
asake.
Da kyar ya iya controlling kanshi yabarta ganin yanda take numfashi kaman zata shide dama
bawani lafiyan kirki gareta ba yakoma gefenta ya kwanta yana kallon fuskarta da hawaye kebi
ta gefen ido tana wani irin saukar da ijiyan zuciya, da kyar ya iya daga hannu ya lalubo hanunta
yakama yarike gam yadan runtse ido danbai masan mezaice mataba, hanun yajawo yadaura
akan bakinshi yadan sakin mata light kiss akai sanan ya mayar ya ijiye, sakkowa daga kan
gadon yayi hakan yasa ta kara runtse idanunta, dan murmushi yayi yawuce bayi yahada mata
ruwa mai zafi sosai yafito hanunta yarike zai tado da ita yace "zomuje kiyi wanka Baby" fizge
hanun tayi cikin kuka tamake mai kafada batare data kallai ba tace "uhm 'uhh" dan rankwafo wa
yay yace "u will feel better" kara makemai kafadar tayi tana kuka abinta, hannu yakai zai tabata
ta tureshi tana turo baki ta tashi zaune da kyar tana rurrufe jikinta da bargon tana kukan banza
batare data kallai ba, ahankali ta saukar da kafafunta kasa tai jimm, jikin gadon ta dafa ta mike
tsaye da kyar tana faman kakkare jikinta da uban bargon dataja, dan murmushi yayi yay folding
hanunshi yana kallonta, wani irin kuka take rerawa mai kama da waka takara kamo bargon tana
tattarewa sabida yanda yabazu akasa sanan tafara kokarin daga kafanta dan tai tafiya wani
azaba dataji yasa tasake kara karfin kukan ta ta kankame bargon da hannu daya dayan hanun
kuma tana yarfewa, tashi yay yazo gabanta yanadan murmushi yakai hannu zai riketa ta
bugemai hannun tana kuka takuma ki yarda su hada ido, kara kai hanun yayi zai tabata takuma
bige hannun hakan yasa yay folding hanun akirjin yana mata wani irin kallo yace "okay
dannama kyaleki kikemin tsiwa angaya miki nakoshi ne" kaman daga sama yaji tafado jikinshi
tawani kamkame shi tana kukan da nidai nakira na banza í ½í¸‚ sakin hanun yayi ya rungumota da
kyau yana patting bayanta yakai kanshi saitin kunenta dawata irin murya yace "is okay am sorry
kinji, da zafi ko?" gyada mai kai tayi tana kara gyara kwanciyar kanta akan kirjinshi, dan
murmushi yayi yace "sorry to, muje kiyi wanka kici abinci u will be fine kinga sha biyu tayi" cirota
yayi daga kirjinshi tareda manna mata light kiss a lips sanan yawani dauketa kaman jaririya
sukai bayi.
[7/1, 2:02 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
69 & 70
Da taimakon shi tai wanka ta tsarkake kanta sanan yanado ta a bathrobe yafito da ita sai wani
murmushi yake ya zaunar da ita abakin gado, yar doguwar riga maidan kauri yaciro mata
sabida sanyi sanan yakawo mata mai ya shafa mata yadau rigar zaisa mata ta fizge tana turo
baki murmushi kawai yayi yajuya yafita daga dakin, kitchen ya shiga yadauko egg yasoya mata
dan abinda kadai ya iya kenan aduka girki sanan yahada mata tea yadau bread dukya jera akan
tray din yakoma dakin, shi yadinga bata tanaci harsaida ta sanye tea sanan ta kauda kai,
magungunan ta ya dauko mata da paracetamol yabata tasha sanan ya zauna gefenta ya rike
mata hannu gam yana kallonta dan dago kai tayi kadan ta kallai zata kawad dakai yasa hannu
yajuyota yana murmushi yace "thank you Islam" kunya sosai yabata hakan yasa ta boye kanta
ajikinshi kwantar da ita yayi yace "bari naje nai wanka nima" yawuce bayi hakan yasa ta gyara
kwanciya ta lumshe ido tana tunanin su Abba da Farida ahaka bacci yay gaba da ita. Ranan
gabaki daya haka yawuni yana kulla da ita duk idan zatai wanka saiyasa takara shiga ruwan
zafi.
Washegari bata wani tashi da zazzabi ba shiya taimaka mata ta shirya cikin doguwar riga baka
tai gayu kaman irin larabawan nan sai kallonta yake kaman zai hadiyeta hakan yasa ya jawota
jikinshi ya rungumeta sosai sanna ya rike mata hannu suka fita daga gidan bayan ya kulle gidan
hospital suka tafi inda Dr Om ya dubata he was so happy da yanda tai maganan yace musu ai
tariga da ta warke zama su iya tafiya basai sun kara dawowa ba unless akwai any complication.
Khaleel ya kasa daina murmushi nan yama Om godiya suka fito wani hadadden saloon ya kaita
yana rike da hanunta suka shiga da sauri turawan suka tarbesu suna musu sannu da zuwa
zama yayi akan wani kujera sanan yace "a kwance mata kitso a gyara mata gashin kar amata
wani kitso" zaunar da ita sukayi akan kujeran gaban madubi suna kwance kitson duk idan zata
dago kai ta kalli mirror sai sun hada ido hakan yasa ta murguda mai baki ya nuna kanshi ta
madubin irin ni? Takara murguda mai tareda gyada kai murmushi yayi ya mata kwafa tamai fari
da ido baki yadan bude yana kallonta kafin ya dauke kai ya jawo Jaridar dake nan tsakiyar
dakin kan center table ya bude zai karanta yakara dago kai ya kalli fuskarta ta madubi gwalo
tamai hakan yasa yay maza ya maida kanshi kan Jaridar yana murmushi kasa kasa.
Kusan 3 hours ya dauke su gama tsifan da wanke gashi da gyara shi danhar stretching gashin
saida akai mata gashin yakara tsawo saiwani kyalli yake sanan suka juyomai da ita sukace "sir
yamaka haka kokuma akara wani abu?" dagokai yayi tareda rufe jaridar hanun nashi yana
kallonta yanda gashin ya bazu a bayanta dan basuyi mata pakin ba, ba karamin kyau tamai ba
ya kalli baturiyar yace "is fine amma kimin parking gashin sanan kima bakin gashin coils,
nafison hakan" dariya baturiyar tayi sosai ta kalli Islam tace "wanan mijin naki yama fiki sanin
abinda zai miki kyau" yanda yafada hakan ko tayi aiko ba karamin kyau hakan yamataba sanan
Matar tasake juyo da ita tace "Ya yanzu?" dago kai yayi ya kalleta tawani turomai baki wayar
hanunshi ya maida aljihun gaban riga sanan yama Matar alamun perfect í ½í±Œ da hannu, tashi
Islam tayi daga kan kujeran ahankali dan duk ta gaji da zaman adan hankali tai tafiya jin zafi zafi
akasan har zuwa inda yake yana kokarin bude wallet dinshi ahankali yace "muje gida saiki
shiga ruwan zafi zai dena miki zafin gabaki daya" gyadamai kai tayi yaciro kudi dayawa yabama
Matar aiko ba karamin dadi tajiba tace "musu come back soon" suka fito mota suka shiga ta
daura kanta akan kafadar shi sabida yanda tagaji gyara mata kwanciyar yayi gabaki daya
ajikinshi nan nan da nan bacci yay gaba da ita, sai Wuraren 6:50 suka kai gida sabida yanda
dan holdup yakamasu ahanya.
Ahankali yay tapping fuskarta hakan yasa tabude ido ta kallai kofa yabude mata tafita sanan
shima yafito ya sallami mai motar yabude musu kofa suka shiga gidan, zata wuce daki ya kamo
hanunta ya matseta ajikin bango yana mata wani irin kallo "wakike ma gwalo and all sort of
things dazu?" dan turo baki tayi kafin tasaki bakin da sauri tace "sorry" girgiza kai yayi yace
"inaa naki saina.. " bakinta yakama ya shiga kissing dinta kaman zai cinye bakin jin tsayuwa na
neman gagararta tafara kokarin silalewa kasa ya rikota ya zaunar akan kujera batare daya saki
bakinba kiran sallan da aka kirane yasa ya saketa yana kallonta da idanunshi dasuka dan
chanza launi yace "jekiyi wanka kiyi salla bari natafi massallaci" tashi yayi yawuce yafita tadade
zaune daga baya ta tashi duk jikinta yay tsami ga zafi zafi datake ji, bayi ta shiga tahada ruwa
mai zafi sosai tashiga sanan tai wanka tafito tai salla.
Bayan sallan Isha ya shigo gidan da takeaway yatasa ta agaba taci abincin da kyar ya dauko
magani yabata tasha, wayarshi ce tai ringing ya dauka ya kalleta tareda nuna mata wayar yace
"Abba ne and is video call" da sauri ta dawo kusa dashi, ganin dan shimi ne ajikinta yasa ya
nuna mata hijabi tasaka sanan yay picking call din Abba ne da duka yayin ta Ya Abdallah
Ibrahim harda Sameer auta bakaramin dadi taji data gansu ba tanata murna suma sai murnan
fara maganan ta suke sunamata ya karfin jiki tace "Alhamdulillah taji sauki, Abba yamusu
addu'a sosai suka amsa da Ameen ahankali tace "Abba ina Faree?" janye fuskar shi Khaleel
yay daga wayar yana mata wani irin kallo, bama ta lura dashi ba sabida yanda take kallon
wayar Abba "yace gatanan itama dukta damu zatai magana dake" Bama Farida dake gefe
wayar yayi hakan ya bayyanar da fuskar Farida, hannu Islam tasa abaki jin kuka yazo mata
ganin yanda Farida ta chanza ahankali tace "Faree wat happen to you like this? Innalillahi
bakida lpy ne?" murmushi Farida tayi with so much regret yar uwarta data damu da ita hakane
ta cutar sabida namiji da kyar ta iya girgiza kai sabida kukan dayazo mata ahankali tace "Islam
dan girman Allah kiyafe mini na cutar dake sosai, wlh wlh dis time dagaske nake natuba Islam
natuba, dan Allah kiyafe min bazan sake abinda nayiba" takarashe maganan tana kuka sosai
itama Islam din kuka tafashe dashi ta sauko daga kan gadon ta zauna akasa tana kuka da kyar
tace "Faree nima am sorry, wlh bakimin komi ba, I understand your actions, nadade dayafe miki
u are my only sister ke kadai gareni I can do anything for you, tell me bakida lpy ne meya
sameki kika rame haka?" girgiza mata kai Farida tayi tareda goge kwallan dake zuba tace
"bakomi kawai zafi zuciyata kemin ne koda yaushe amma ko ciwon kai banayi" sosai Islam ta
fashe da kuka tace "sorry Faree" kasa daure yanda take kuka yayi hakan yasa ya sakko kasan
yazo kusa da ita ya zauna tareda daura hanunshi akan kanta ya kwanto dakan nata kirjinshi
yana bubbuga bayanta kokarin tureshi takeyi sabida yanda Farida ke kallonsu amma shiko
fuskar wayar baima kalla ba danko fuskarta bayason gani, tarin dasuka ji Farida nayi sosai yasa
tajuya ta kalli wayar sosai Farida ke wani irin tari Islam tace "sorry are you ok, kisha ruwa" dan
murmushi tayi tana kokarin hadiye tarin takai hannu bakinta jini tagani da sauri Islam da kaman
idanunta zasu shiga wayar tace "Faree blood, tarin jini kike?" hannu taga Farida ta daura akan
kirjinta tana wani irin tari tana kallon fuskar Khaleel dahar lokacin baima kalli screen dinba
hasalima lumshe ido yayi tareda jingina da gado yakai hanunshi cikin hijabinta yana wasa da
jelar gashin ta, sosai Farida ke tari jini nabin bakinta takama zuciyar ta da hannu daya tana
kallonshi har lokacin, Islam tace "Faridaa, Abba" ta kwalama su Abba datake jin hayaniyan su
kira, da sauri su Abba da Ya Abdallah suka zo wajen daidai ta lumshe ido ahankali tace "M.. K"
banbare wayar Abba yayi daga hanunta ya kalli Islam yace "bari mu kaita asibiti, Allah kara
sauki Islam" katse wayar yayi Islam tafashe da kuka sosai sai a lokacin yabude idonshi ya
kalleta bakaramin cin ranshi kukan nata yakeba yacire mata hijabi ya ijiye hanunshi yakai
saman kan idonta yana share hawayen datake yi yajawota zai rungume cikin kuka ta turemai
hannun tace "bakaji yar uwata bata da lafiya bane" dan bude ido yayi ya kalleta da kyau sanan
yace "to ai naji Abba yace zaikaita hospital ko" kara fashewa tayi da kuka ta tashi taje gaban
wardrobe tana ciro kayanta tace "ni wlh nigeria zamu koma yanzu nan Farida batada lpy I need
to be with her" "babu inda zamu" yafada cikin kakkausar murya yana kokarin cire rigar jikinshi
da sauri tadawo gabanshi ta kalleshi tace "sabida ba kanwar kabace ko?" wani irin kallo yamata
sanan yace "yes" kan gado yahau yaja bargo abinshi tareda lumshe ido bakaramin ciwo
maganan yamata ba tsugunnawa tayi ta dinga kuka akasan wajen takai kusan minti biyar sanan
ta tashi bargon daya rufa dashi ta yayemai ta jefar hakan yasa yabude ido ya kalleta, daure
fuska tayi ta tsayar da kukan datake tace "wlh bazakayi baccin ba bayan kaine sanadin ciwon
nan datakeyi, is all ur fault, Kaine kasamata wanan ciwon am sure ciwon zuciya ne yakamata,
tunda nahadu dakai matsaloli keta faruwa dani, tunda nahadu dakai farin cikina yaragu,
karabani da my only sister, is because of you yar uwata takusa kasheni, ta tsaneni, taso kashe
kanta sabida kai, ni bana sonka Farida ke sonka, ka sakeni dan Allah ka aureta karta mutu da
ciwon zuciya, are you dat wicked dabaza sota Koda sau daya bane? Karka kashemin yar uwa,
kasaken... " kasa karashe maganan tayi sabida wani irin mugun mari daya dauketa dashi.
[7/1, 2:02 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
71 & 72
Dafe kuncinta tayi tana shafawa, jikinta har wani irin barbar yake sabida yanda taga fuskar shi
bata taba ganinshi hakaba, nuna ta yay da yatsa cike da bacin rai, dawa ta irin kakausar murya
yace "ni kike gayama magana haka akan wacce ta kusan kaiki lahira? Ni kike ma rashin
kunya?" kasa magana tayi saima jada baya da tafara yi tana kuka sabida yanda taga idonshi ba
karamin tsoron shi taji ya shige ta ba, wani irin kallo yamata abubuwan data fadin mai yana
yawo akanshi juyawa yay yafita daga dakin tareda bugo kofar sabida tsabagen yanda ranshi
yabaci.
Zubewa tayi a wurin tafashe da kuka sosai tafi hour daya tana kuka daga baya bacci yay gaba
da ita anan kasan.
Dakin Ihsan ya shiga ya zauna tareda dafa kanshi yafi minti biyar ahaka dan rashin yay bala'in
baci da kyar ya mike tsaye tareda fuzar da iska yawuce ya shiga bayi ya dauro alwala yadawo
dakin yasaka jallabiyar shi daya dauko ya kabbarta salla.
Ahankali take bude idonta ganin gari yay haske yasa ta mike tsaye da dan sauri, cije baki
tadanyi sabida zafin dataji ta bude kofar bayi ta shiga brush tafara yi sanan ta gasa kanta tai
wanka ta dauro alwala tadan lumshe ido sabida yanda taji kanta namata ciwo, towel ta daura
tabude bayin tafito hada ido sukayi yana sanye da jersey ya zauna abakin gado yana daure
igiyan sport shoe din kafarshi, kallo daya yamata ya dauke kai tareda cigaba da abinda yakeyi
kasa karasowa cikin dakin tayi ta tsaya a wurin tana wasa da yatsun ta wani irin shakkar shi taji
tanayi karan fesa turare dataji yasa tadaga kai tadan kalleshi yana tsaye gaban mirror yana fesa
turare ahankali tace "ina kwana" ijiye turaren yayi bayan yagama fesawa yajuya zai fita daga
dakin batare daya kalleta ba yace "kintashi lpy" baijira mezata ceba yabude kofa yafita daga
dakin, kofan tabi da kallo yanda yabuga kofar har cikin ranta saida taji ta runtse ido, wani irin
kuka ne taji yazo mata tafara kukan da kyar ta shiru tawuce wardrobe taciro wata simple
doguwar riga ta saka tadau hijabi tasa tai salla, ta dade zaune tana azkar daga baya tamike ta
cire hijabi ta ijiye jin tanajin yunwa sosai. Dakin tafara gyarawa tass tafashe ko ina da turaren
daki sanan ta shiga dakin Ihsan din nanma ta gyreshi tass sanan tawuce falo ta gyara dudda
babu wani datti ta shiga kitchen din, shiru tayi tana kallon ko ina wani irin kuka ne taji yazo
mata, Indomie da tagani kawai ta iya dauka da kwai daya ta dafa ta juye adan karamin plate
tadau fork tawuce dakinsu tadan ci dan jitayi batada wani karfin cin abincin, magungunan ta
dake gaban mirror tagani wani kuka takara ji yazo mata inda yana nan dashi zai bata da kyar ta
mike tsaye ta dauko su tasha tahada da paracetamol duk tasha tafito da kwanon tazo ta ijiye ta
kwanta akan doguwar kujera tana kallon TV ahaka bacci yay gaba ita. Wuraren 2 ya shigo
gidan na rana ya dade tsaye afalo yana kallonta karfin yawuce ciki