Showing 9001 words to 12000 words out of 68809 words

Chapter 4 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf

M Shakur   

07 Oct 2025

1799

da kuka kafin ta kwallama
mai aikinta kira dagudu tazo wani irin tsawa tamata tace "zoki gyaramin kumbana".

Saida suka shiga hanya sanan Yusuf ya kalleshi ganin yay shiru yana kallon motocin dake
tafiya akan titin yasa yace "kasan inda zamu kuwa" girgizamai kai yayi, murmushin jin dadi
Yusuf yayi at least yau yana amsamai yace "anguwar tsamiya, Abba yaturani nakai ma Malam
Isya wanan kudin" yanunamai wani katon envelope dake tsakakanin su sanan yace "Malam
Isya yanada kirki shike kulan ma Abba da gonakin shi saisa duk idan Abba yay zakka yake
bashi" shiru yayi yana sauraron shi hakan yasa Yusuf yace "gaskiya yau zakayi aski gashin nan
naka yataru dayawa ga sajenka yay bususu, idan zamu koma saimuyi branching barbing saloon
ko" shiru yayi baice komiba haka Yusuf yay ta janshi da hira sabida Ya Mustapha yace adena
barinshi alone adinga yawan mai hira, Kuma Alhamdulillah ga so much improvement yanzu yau
dakanshi yaje dakin Goggo at least yana amsa magana, jiyama shiya koyama Fa'iza
assignment dinta, gashi yau ya yarda yabiyoshi sunfita. Lumshe ido yasake yi ya maida
hankalin shi sosai Kan tukin dayake yi yana tunanin zuci yace "Ya Allah ka warkar da bawan
nan naka gabaki daya, ya Allah kadawomai da farin ciki rayuwar shi, ya Allah kasanya mai
danganar rashin Aisha kabashi wacce tafita, itakuma Allah ka jikan ta" haka yayta tunanin zuci
harsukakai kai kofar gidan Malam Isya. Parking yayi yafito yadawo ta bangarenshi ya budemai
kofan yace "zomu shiga ciki" yatsine fuska yayi "am not going" murmushin jin dadi Yusuf yakara

yi ganin yanda yay dogon magana yau yace "okay I will be right back bazan dadeba". Barin
wajen yayi shikuma yadan kwantar da kujeran yay relaxing bayan shi tareda lumshe ido.
Dadan sauri take tafiya wanda yay kama da ahankali, goyone abayan ta wanda yarinyar data
goya ke kuka sosai kaman ansatota adaburce Yarinyar tace "yakuri Miemie gawani shago chan
muje nasai miki ruwa" ahankali takara sauri harta wuce motarsu Yusuf, Dumm yaji kirjinshi
yawani irin mugun bugawa, hannu ya daura akan kirjin tareda kara lumshe idanunshi. Karasawa tayi shagon abirkice tacema mai shagon "Malam a bani ruwa guda daya" kwanto
Miemie tayi daga bayanta tariketa a hannu sanan ta ciro naira hamsin daga jakanta tabama mai
shagon takarbi pure water tasa abaki ta bude, sama yarinyar tayi abaki da sauri yarinyar tafara
zukan ruwan hakan yasa budurwan tasaki wani murmushin kwanciyan hankalin tace "dats my
gurl dama kishi kikeji shine kikemin ihu kaman nasa to kiko, ke wlh Miemie kin iya jarababben
ihu" ganin yarinyar na neman shanye ruwan yasa ta fizge daga bakinta tace "cikin ki zai fashe,
is okay Miemie" wani irin ihu yarinyar tayi da saida ya amsa ko ina a anguwan dan ihu tayi
kaman an yankata, ahankali ya bude ido yana waige waige jin ihu dan kokadan yanzu bayason
hayaniya, idanunshi ne suka kai kan yar karaman yarinya dake kan shoulder wata data bashi
baya tana jijjiga yarinyar.. "Miemie I promise bazan kara fita dakeba, saidai nabarki agida, sai
mutum zai fita kiyita binshi kina kuka kaman zaki mutu inmun fito kiyita min kuka" Mai shagon
ne yay dariya yace "hajiya ai haka yara suke ungo chanjin ki" ahankali ta juyo sabida batason ta
tada Miemie dataji tafara gyangyadi akafadanta chanjin takarba daga hanun mai shagon sanan
ta juyo... Goge idanunshi yayi dan yakara tabbatar da abinda yagani lips din shine suka fara
rawa "My.. My... My.. My Eee.. My Eesha".
[6/9, 3:34 PM] Maman Jedda: *JARABTA*


Maman Abd Shakur

11...
Bude marfin mota yayi yafita ko kulle kofan baiyiba yawuce wajen shagon da sauri kaman zai
fadi yakarasa wajen daidai tagama goya Miemie abayanta, dan jakanta ta dauka daga kan table
din wajen ta rataya akafada sanan ta juyo, mutum tagani agaban ta ya tsaya chak yay folding
hannu akirji yanawani irin kallonta, wani irin mugun tsoro yabata daga juyawa tadau jaka saiga
mutum abayanta kaman aljani ta ina yafito. Addu'a tafara azuciyar ta kafin tayi gefenshi sadaf
sadaf zata wuce yace "My Eesha" ta gefenshi take kokarin rabawa ta wuce kai tsaye yakara
tare ta yana sake kallon fuskar ta yace "My Eesha?" ahankali yarinyar ta kalli gefenta da
bayanta dan kara tantance dawa yake magana "Eesha yimin magana, talk to me mesa kika
gudu kikabarni eh" matsawa baya tafara yi dan yanzu tafara tabbatar da aljanine wanan dan jibi
uban gashin kanshi wanda yafi na Miemie yawa, gabaki daya jikintane yafara bari takoma baya
ganin kaman zai sata ajikin shine, hanunta ya kama ya rike gam adan rude, cike da murna, da
murmushi yace "My Eesha am soo happy" yakara kamo dayan hanun nata ya rike arude yace
"wlh is real, kece fa my Eesha maisa kika tafi kika barni for more than a year eh" da karfi ta fizge
hannayenta bakinta har rawa yake tace "stop touching me, kai waye kaganni kawai kafara
tabani" share kwallan daya gangaro mata tayi tace "niba Eesha bane" tajuya da sauri zata bar
wajen dan idan takara minti biyu da mutumin nan wlh zata iyayin fitsari ajiki, hanunta ya kama

ya fizgota saida ta bugu dashi yana mata wani irin kallo yace "is you, karya kike, kece, Aisha
nane ke" ya nuna fuskar ta, kokarin fizge kanta take ganin yaki sakinta yana kallon ta kaman zai
cinyeta yasa tafara waige waige, mai shagon nan takira da muryan kuka tace "Mallam dan Allah
zoka rabani da bawon Allahn nan, wlh, wlh niban sanshi ba, dan Allah kataimake ni" takarashe
maganan tana sheshekan kuka, fitowa mai shagon yayi ya kalli Khaleel da hankalinshi nakan
yarinyar daya rike gam yace "Yallabai lpy dan Allah maike faruwa ne" kaman zai hadiye ta da
kallo yasake rirrike shoulder dinta yana kallon fuskarta ko kyaftawa ba yayi batare dayama bi
takan mai shagon ba yace "My Eesha plz come with me, zomuje gida, su Ammi sunyi kewanki
sosai, please karki sake barina kinji" yakarashe maganan gwanin ban tausayi, ahankali taji
fitsari na gangara yanabin cinyarta tunda take bata taba tsorata da firgita irin nayau ba sosai
kuka keson ya subuce mata,, ahankali ta kalli fuskar mai shagon tace "wayyo Allah na, Mallam
na shiga uku wlh ni bansan Shiba, dan Allah karabani dashi, na shiga uku... " "stop saying
bakisanni ba it hurts" wani irin tsawa ya daka mata ya daura hanunshi daya akan kirjinshi jin
wani irin zafi, hakan yasa ta fashe da kuka tsabagen firgita yasa ta mika hannu tana kokarin
kamo rigar Mallam mai shago daya tsaya yana kallon ikon Allah, mutum daizai rirrikeka haka
tabbas yasankane to ita ya akayi take cewa bata sanshi ba. Bayason ya shiga case din dan
daga ganin motar Yaron yasan dan masu kudine shagon nan nashi dashi yake ciyar da Mata
yen shi da yayan shi, ganin anzo siyan abu yasa yakoma cikin shago, sosai tafashe da kuka
tace "Mallam dan Allah kadawo karka banni dashi" "My Eesha" yakira sunanta, ahankali yace
"muje gida" hanunta yakama yanaja ihu tafarayi da karfi ta tace "Wayyo Allah na shiga uku, dan
Allah ka sakeni, Wayyo Allah nabani" ganin yakai ta gaban wani mota yana shirin budewa yasa
tai dabara ta take kafarshi hakan yasa yasaki da sauri sabida hill din yamai zafi akafa sosai, da
gudu ta arce hakan yasa yabita da gudu shima yace "no my Eesha don't leave me again, dan
Allah come back" sosai take gudu ga Miemie abayanta tana kuka, yana binta.
[6/9, 8:14 PM] Maman Jedda: *JARABTA*


Maman Abd Shakur

12...
Da kyar ta tseremai ta labe awani lungu tana haki sosai da tari, tunda take batajin ta tabayin irin
gudun nan datayi yauba, dafe kirjinta tayi dan jitayi kaman zai fito sabida yanda yake bugawa,
jin kaman motsi yasa tafice daga lungun da sauri ta bullo wani anguwa dat is very quiet mai
kyau, da dan gudu gudu takara sa gaban wani katoton gida dakeda brown gate, bude gate din
tayi ta shiga ciki da sauri, katoton gidane dakeda flowers a tsakar gidan sai motoci kusan biyar
a compound din, ahankali take tafiya dan ta bala'in gaji kaman zata fadi sai zufa take kofa ta
bude ta shiga babban sitting room din da aka rabashi bangare biyu bangare daya ansanya
kujera Kiran royal brown sai dayan Kuma asha ga wani makeken tv bango daketa aiki shi kadai
danba kowa adakin, maida kofar tayi tarufe sanan tadaura kanta akan kofar tareda da lumshe
ido ta dafe kirjinta tana sauke ajiyar zuciya, wata matace mai aikin su da akalla zatai 30 tafito
daga kitchen dauke da katon food flask tazo dining ta ajiye zata juyane ta hango ta tsaye a jikin
kofa, dan murmushi tayi ta karaso cikin falon cike da fara'a tace "a'a su Anty Islam har an dawo
ne" ahankali ta bude ido murmushi ta kakalo ware ido Matar tayi tana kallonta ganin yanda

idanuwan ta sukai ja tace "Islam badai ahaka zaki koyi rainon bako yanzu Miemie ne tasa kika
galabaita haka harda kuka" hannu takai dan ta kwanto kyakyawar baby da tunda ta ganta take
tsalle a baya dan ta dauketa, kwanto ta Islam tayi ta mika mata murmushi matar tayi tace
"oyoyo an babyn mamanta, iyye andawo daga anguwa ne da Anty Islam" dariya yarinyar takeyi
sosai kaman ba ita ke shegen kukan nan ba, zanin goyon Islam ta mika mata sanan tawuce
wajen stairs hawa tayi ta tafi sama, dogon corridor ne da dakuna kusan shida a wurin, wani kofa
ta bude ta shiga dakine dake dauke da gadon yan boarding house saidai shi wanan na katako
ne da akamai fenti pink, bunk biyu ne kadai adakin sai center carpet shima pink, da study inda
uban littatafai kekai, gaban wardrobe taje ta tsaya tana kallon mirron dake jikin kofan wardrobe
din ahankali takai hannu ta warware rolling din gyalen dake kanta dogon gashinta ne ya
warware ya zubo har kirjinta dan tsaki tayi ta ciro ribon din daya hade da gyalen ta kama
gashin, doguwar rigan jikinta tacire tabar shimi da sket ajikinta kan gado taje ta kwanta tareda
sauke ajiyar zuciya dan har yanzu kirjinta bugawa yake.

Harwajen motansu Mallam isya ya rako Yusuf yana karamai godiya ganin marfin mota abude
yasa Yusuf ya bude bangaren shi da sauri ganin ba Khaleel aciki yasa ya fara waige waige
adan arude, Malam Isya ne yace "lpy Yusuf" arude yace "nabar Khaleel a mota bangan
shibane" ganin yanda ya rude yasa yace "karka damu bari mudan tambaya" samarin dake
gaban shagon Adamu yatambaya dan Allah kunga wani matashi bako nane" da sauri Yusuf
yace "yanada gashi sosai akai" da sauri mai shago yace "to kodai wanan wanda ya rike yar
mutanen ne yace yasanta? Dan naga gashi rututu akanshi" da sauri Yusuf yace "shine a ina ka
ganshi?" "anan gaban shago na ya rike wata yarinya datasai ma wata yar baby ruwa yanace
mata Eesha wai sutafi gida" ahankali Yusuf yace "Eesha kace?" "eh haka naji yanata kiranta
nidai" "to yanzu ina suke" "Naga tagudu yabita chan sukayi" Ya nunamai hanyar dasuka bi da
gudu Yusuf yabi hanyar da aka nunamai hankalinshi atashe.
Akarshen layin Yusuf yaganshi ya zauna akan wani dakali ya rike kanshi, karasawa wajen Yusuf
yayi ya daura hanunshi akan kafadar shi, dago kai yay ya kalli Yusuf da idanunshi dasukai jajir,
zama Yusuf yay kusa dashi ahankali yace "Khaleel wat is d matter?" murmushi yay mai ciwo
yace "yau naga wata da ta tunamin da Eesha, for a second I tot she was my Eesha, yanda
Eesha ke tafiya haka yarinyar ke tafiya" shiru yadanyi kafin yafuzar da iska yace "I think am
loosing my mind" hanunshi Yusuf yarike gam ya girgizamai kai Yace "Khaleel Eesha tariga ta
rasu bazata taba dawowa ba, and inhar son dakake mata is real kamata yayi kadawo normal
kai kaman yanda kake da, kazaci inda Aisha na nan she will be happy da yanda kadawo ne?
Bakama mutane magana, bakacin abinci kullum kana daki Ammin ka kullum saita kira Umma
kusan 5 times tana tambayan jikin ka, duk ka rikita gabaki dayan family mu is that fair do you
think Aisha zatai murna dajin labarin nan?" shiru yayi kawai yana kallon Yusuf, tashi Yusuf yayi
daga dakalin yace" mutafi "ahankali ya sauko daga dakalin waigawa yasake yi kafin yajuya
sutafi.

"Islam, Islam" ahankali ta bude ido, wata yar budurwa ce wacce suke kai daya da Islam tana
sanye da doguwar rigar atampa ja take tashin ta, yatsine fuska tayi cikin muryan bacci tace
"uhnnn wat Farida" yaye bargon data lulube dashi Farida tayi tace "kitashi" juyawa tayi ta kife
cikin muryan bacci tace "leave me aloneeee" tsaki Farida tayi tahau up bonk dinta ta kwanta

abinta, tsaki tasakeyi tace "Islam" shiru tamata bata amsaba, hakan yasa tai kwafa tace "okay o
dama Anty Hindu ne tazo kinsan ta very well" zabura tayi ta tashi ta zauna ware manyan
idanunta tayi, leko dakai Farida tayi daga sama ganin ta tashi ta zauna yasa tai dariya, juyo
dakai tayi ta kalli Farida hannu tasa ta dafe goshinta tace "Faree please da gaske tazo?" gyada
mata kai Farida tayi, da sauri ta tashi gaban wardrobe taje zaro wani abayan ta baki tadaura
akan dan singlet din dake jikinta ta wuce tafita daga dakin.
[6/11, 9:19 AM] Maman Jedda: *JARABTA*


Maman Abd Shakur

13...

Juyowa kakkyawar matar tayi tace "Islam yaushe kika tashi Farida tacemin kanki na ciwo sannu
ko, kinsha magani?" Gyada mata kai tayi sanan takara matsowa kusa da Mum tai wani kini kini
da fuska kaman zatai kuka da murya chan kasa dan tasan Allah yama Anty Hindu baiwar kunne
tace "Mum wai mesa tazone, yanzu dukzata damu mutane da masifa" murmushi kawai Mum
tayi ta girgiza kai tana arranging abincin a babban tray mai kyau tace "yayar mahaifin nakine
kike cewa haka akanta ko yaran zamani, matsamin kiga na wuce jekiyi salla" fita Mum tayi ta
barta a kitchen din, fitowa tayi takoma sama tana shiga daki Farida ta fashe da dariya tace "our
Baba sister don land again" tsaki Islam tayi tana balle boturan abayan datasa Farida tace "wlh
ko yau datazo jinayi kaman inyi kuka shikenan yanzu mun shiga uku" abayan Islam ta wurga
akan gado tai hanyar bathroom Farida tace "Islam wai dan Allah mesa Anty Hindu batason
muna kiranta dawani suna kaman irin su Mama, Inna ko Goggo tunda dai yayar daddyn muce
amma saidai muce Anty Hindu" hararan ta Islam tayi tace "go and ask her" tabude bathroom
tashiga batare data karabin takan taba, daga murya Farida tayi tace "okay nikikema iskanci ko
next time bazan rufamiki asiri ba wlh" daga bayi tadaga murya tace "eh karkiyi din" dariya
Farida tayi dan tasan abinda zatayi. wanka tayi tareda dauro alwala tazo tai sallan magrib
sanan ta kalli Farida dake daddana waya tace "Daddy is back zomuje muyi dinner" sakkowa
Farida tayi suka sauka kasa, afalo aka zazzauna yara mazane manya guda uku biyu manya sai
karami da bazai wuce 5 years ba akan cinyar Daddy duk ana zaune anacin abinci, gaishe da
Daddy sukayi ya amsa musu sanan suka zauna kusa da Mumy, rice ta zuba a plate da pepper
soup na goat meat, spoon tasa a abincin tanata wasa dashi takasaci tunanin abinda yafaru yau
kawai take, tunda ta sakko Daddy ke lura da ita, dan gyara murya yayi yace "Islam" da sauri ta
dago kai ta kalli Dad ahankali tace "Na'am Daddy" "meke damunki?" murmushi tayi da sauri ta
girgiza kai tace "bakomi Daddy kaina ke ciwo har yanzu" Yayan ta Abdallah dake gefenta mai
kimanin 25 years ne ya kalleta yace "kinsha magani?" gyadamai kai tayi, murmushi yamata
yace "eat to ko kadanne" rice din tadebo takai baki tafaraci.
A massallaci suka fara tsayawa sukai magrib sanan suka wuto gida. Part dinsu suka wuce,
direct bayi ya shiga yay wanka yafito sanye da bathrobe white ajikinshi ganin Yusuf baya dakin
hakan yasa ya zauna akan kujera lumshe ido yay nayan sakkanni da sauri ya bude tareda fuzar
da iska tashi yayi yaje gaban wardope ya canza zuwa milk color jallabiya, tsayawa yayi agaban
madubi yadau turare a fesa, wayar shi yagani dake jikin madubi hakanan yaji yanaso yakira

Ammin shi, daukar wayar yayi yakoma kan kujera ya zauna yay dailing number Ammi ba
karamin mamaki Ammi tayiba dataga kiranshi na shigowa ba, ringing biyu ta dauka cike da
murna tace "Son" har cikin ranshi yaji wani irin natsuwa, ahankali yace "Ammina I missed you"
share hawayen daya zuboma Ammi tayi da sauri azuciyar tako godiya takema Allah, Allah na
godema daka amsa addu'a ta, ya Allah kadawo mai da farin ciki da walwalan shi back, ka bashi
mace tagari wacce zata maye gurbin Aisha. "Ammina are you there" da sauri yace "yes Son, ya
kake hope kanacin abinci sosai ko" Ahankali yace "eh" murmushi sosai tayi tace "are you okay"
shiru yayi baice komiba cikin wani irin muryan lallashin yaro tace "how about tomorrow kayi your
two fevorite thing, read your Quran, and kaje ka buga kwallo ko kaje stadium ka kalli kallo
anyone dakayi is okay" murmushi mai kara yay tunawa da dafa Ammin ce ke masifa duk idan
yaje kwallo, murmushi yasake yi yace "okay Ammi bari naje nai salla" katse wayar yayi yatashi
yafita dan zuwa massallaci.
Washegari da safe yadade yana karatun AL qur'ani da muryar shi mai dadi, sai wajen 9 yarufe
ya ijiye haka nan yaji kaman ancire mai wani nauyi dake damunshi arai, yajuya ya kalli Yusuf
dake bacci abinshi, bathroom ya shiga yay wanka yafito ya shirya cikin brown shirt, short sleeve
ne hanun rigar ya kama muscle dinshi hakan yakara bayana girman muscles din, dogon black
jeans yasa dayamai kyau sosai ya dauko turaren shi ya fesa, ya zira takalmin shi Prada,
agogon da Eesha ta bashi ya dauka daga gaban mirror, shafa agogon yayi yay shiru yana
kallonshi, ahankali ya daura ahannun shi sanan yadau car key dinshi da waya yay hanyar fita
daga dakin, da Goggo yacikaro tana dauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login