Showing 36001 words to 39000 words out of 68809 words
Chapter 13 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf
baya kallonta yasa ta koma bayi da
gudu ta shirya tass, rashin sabulu wanki yahanata wanke doguwar rigan, folding tayi tafito daga
bayin sanye da hijabi ta tsugunna tasa rigan acikin akwatin sanan ta rufe ta daga akwatin tsaye,
ahankali take tafiya tazo zata wuceshi ta fita da sauri dan wani irin tsoro taji tanaji yanda daga
ita sai shi agidan nan, hanunta ya riko ya janyota ya daurata akan kafarshi da sauri ta mike
tsaye jikinta har rawa yake, tashi shima yay tsaye yasa hannu ya yaye hijabin ta yacire ya
wurga kan gadon da sauri tasa hannu tana kakkare gaban rigan kanta akasa duk jikinta na
rawa, ahankali taji yakamo hanun yasaka hanunshi cikin nata ya zaunar da ita abakin gadon ya
dauko tray din abincin ya zauna kusa da ita dan har jikin su na gogan juna, lafiyayyen fried rice
ne da kaji sai cold exotic drink da bottle water ga magani data gani agefe, baice mata komiba ya
debo rice din a spoon yakai bakinta girgiza kai tayi jikinta har baribari yakeyi tace "zan zanci
dakaina" hannunta ta mika zata karbi spoon din ganin yanda hanunta ke rawa yasa ya ijiye
spoon din ahankali ya daura hanun nashi akan nata yakai dayan hanun kumatunta yakira
sunanta ahankali "Islaam, Hey relax is me" bata kalleshi ba, spoon din yasake dauka yadebo
rice din yakai bakinta very calm yace "please" Ahankali ta bude bakinta kadan yasa mata taci da
kyar ta iya tai 5 spoon sanan tace "am okay" bayason yatakura ta hakan yasa yadau maganin
dake tray ya ballo kwara biyu yabata yana murmushi yace "for d stomach" Ya nuna cikin ta
kawad dakai tayi ta karba yadau ruwa ya bata tasha tana yatsine fuska, tashi tayi tai hanyar
kofa zata fita batare daya kalleta ba yace "kizo ki kwanta anan idan nagama cin abinci nixan
kwana a falon" dan kallon fuskarshi tayi ganin baya kallonta kokarin debo rice yake hakan yasa
ta dawo ciki ahankali tahau gadon nesa dashi sosai ta kwanta tareda jan bargo ta rufe jikinta
duka kanta kawai tabari awaje.
Yaci iya cinshi shima yaji ya koshi yatashi tsaye rike da plate din kallonta yayi yanda ta takure
waje daya ta juyamai baya murmushi yayi ya bude kofa yafita kitchen ya wuce ya ijiye tray din
yafito falo yay locking kofa sanan ya kashe TV ya kashe wuta sanan yay hanyar bedroom din,
bude kofa yay ya shigo hakan yasa takara kudundunewa, kashe wutar dakin yay sanan yawuce
bayi yay kusan 10min sanan ya bude kofa yafito duk tana jinshi, agaban wardrobe ya tsaya ya
cire jallabiyar jikinshi yamaida a hanger sanan ya ijiye, zagayowa yay ta inda take kwance ta
bakibakin gadon ya tsugunna batare dayace komiba, azabure ta tashi zaune tana kokkomawa
baya tana sheshekan kuka, hayowa yay kan gadon ya zauna agabanta tareda kunna hasken
wayarshi ya haskata, kare fuskar tayi da hannu tana kara matasawa baya tana kuka ahankali,
kafafun ta yakama yaza yana murmushi hakan yasa tai zuit ta kwanto flat, hayowa kanta yay
batare daya hade jikinsu ba kulle idanunta tayi gam tana kuka sosai, ahankali yace "shiiiii" gum
tayi ko tari bata karaba, hanunshi yakai tabayan wuyarta yadan dagota kadan yasa hanun ya
zare ribbon din data kama gashin ta dashi ya yar akan gadon hakan yasa gashin ya barbazu
akan filo ya tsaya yana kallon yanda ta kamkame idonta kirjinta na bugawa fat fat, wayarshi ya
dauka ya kashe flash light din sanan ya kwanta a gefenta, hanunshi yakai yadaura akan cikinta
hakan yasa takara zabura zata mike ya riketa tareda janyota tafado kan jikinshi.
[6/23, 1:42 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
45 & 46
Yunkurawa tayi ta tashi yasa hannu ya kwato da kanta kan kirjinshi yana shafa bayanta
ahankali yace "sleep" gabaki daya atakure take sabida yanda yawani riketa hakan yasa ta
lumshe ido kirjinta na bugawa fat fat fat tafi hour daya takasa bacci sabida yanda yake shafa
bayannata sai mutsu mutsu take daga bayane baccin dole yasace ta, hakan yasa tai relaxing
gabaki daya ajikinshi tana ajiyar zuciya ahankali. Jinyanda jikinta yasaki yasa yagane tai bacci,
ahankali gudun kada ta tashi yamika hanunshi ya kunna bedside lamp yana kallon fuskarta
yaune rana ta farko daya tabamata kallon kurinla haka, gani yake kaman Eeshan shi yake kallo,
dan lumshe ido yay ahankali yace "Allah ya gafarta miki my Eesha" ahankali ya bude ido tareda
sa hannu asaman gashin ta yana shafawa jin gashin taushi gashi warawara, d'ayar hanunshi ya
mika ya kashe bedside lamp din sanan ya mayar da hanun yanata shafa kanta ahaka wani
bacci mai mugun dadi da natsuwa yay gaba dashi.
Wuraren 3 nadare ta farka sabida fitsarin datake ji, jinta datayi akan mutum yasa ta tuna inda
take, kokarin cire hanunshi daga bayanta take takasa gashi dakin duhu batagani ko kadan
ahankali taji yace "mekike so" bata ganin idonshi da kyar cikin muryan bacci tace "hanunka"
hannu ya mika ya kunna bedside lamp din da sauri ta dauke kai ganin yanda idanunshi suka
kara kyau sundan kankance sabida baccin dasukayi, ahankali yasaketa hakan yasa ta sauka
daga jikinshi da sauri sanan ta zauna daga bakin gadon tana waige waige neman hijabin ta dan
bataso ta tashi agabanshi ahaka ganin bataga hijabin ba gashi fitsari takeji sosai yasa tadan
juyo ta kalli fuskarshi a lumshe taga idanunshi hakan yasa ta mike tsaye harda dan gudun ta
tashiga bathroom din jin kaman fitsarin zai zubo, bata wani dade ba tafito tsayawa tayi tadan
kallai ganin har lokacin idanunshi a lumshe yasa tafara tafiya ahankali tadan kwanta ta baki
bakin gadon taja bargo ta rufa murmushi yay ahankali. Hartadan fara gyangyadi taji yamata
peck a kumatu ya tashi ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito, jallabiya yasaka ya shimfida
dadduma yafara salla tun tana kallonshi har bacci yay gaba da ita.
Kamshin turaren dataji yacika mata hanci ne yatada ita daga baccin datake, ahankali take bude
ido harta gama budesu Khaleel tazani zaune kusa da ita yaci uban shadda dark brown har kyalli
take, ya gyara gashin kanshi da sajen shi sunata shining ya zauna yana kallon fuskar ta, tashi
zaune tayi tadan dauke kai ahankali tace "ina kwana" murmushi yamata tareda kamo hanunta
ya mikar da ita tsaye jitayi ya rungumeta hakan yasa ta tsorata batare daya saketa ba yace
"morning Baby ya darenki" yay maganan tareda sakinta, kauda kai tayi, murmushi yasakeyi
mata da sauri tabar wajen wajen akwatin daya bata jiya taje budewa tayi ta ciro wata atampa
vilisco dataga an dinka yanama cikin leda da duk wani abu dazata bukata sanan tadan juyo
kaman mara gaskiya ta kallai hada ido sukayi hakan yasa ta dauke kai ta tashi ta shiga bayi da
sauri ta rufo kofar harda saka key dan bata yarda dashiba wanan kallo kaman wanda yaci
maita.
Saida tagama wankan sanan ta shirya ta shafa mai tasaka kayan da aka mata dinkin riga da
sket, ba karamin haushi rigan yabata ba dan V neck akama dinkin saidai kayan sun mugun
amsanta, black da pink ne kalar atampar hakan yakara fito da hasken fatar ta, rashin comb
yasa ta tattare gashin nata tai pakin dinshi ahaka sanan ta daura dan kwalin dan simple daurin
tayi, gaban mirror bayin taje ta tsaya tana kallon kanta wani haushi ne yazomata ganin yanda
gaban rigan yasa kana hango saman kirjinta dan rigan yakamata chas ajiki, tsaki tayi ta tuge
daurin dan kwalin kanta ta warware sanan tadan yafa aka yarufe mata har wuya sanan tafito,
ganin baya dakin yasa ta bude box din ta maida kayan data cire ta feshe jikinta da turaren data
gani sanan tarufe akwatin tana kokarin daga akwatin taji yay sallama ya shigo, ciki ciki ta amsa
batare data kallai ba ta daga akwatin ta juyo fadawa jikinshi tayi dan kwata kwata batasan yana
bayanta ba, kokarin fita daga jikinshi tayi da sauri, yadaura hannayen shi a waist dinta yana
kallon idonta mayar da kanta kasa tayi takai hanunta ta daura akan nashi tana kokarin cirewa
daga waist dinta, kama hanunnata yay yarike hakan yasa ta fizge hanun da karfi ta tureshi ta
juya zata tafi, fizgota yay ya zauna akan gado ya daurata akan cinyar shi kokarin mikewa take
amma yariketa gam, dayan hanunshi yasa ya yaye lullubin datayi da dan kwalin ya ijiye agefe
yana kallonta kawad dakai tayi gefe ta daure fuska, ahankali taji yakai hannu yana shafa
wuyanta wani irin yarr taji tanaji ga heart dinta na racing, ture hanunshi tayi hakan yasa ya rike
hanunta gam sanan ya mayar da danyan hanun nashi yana shafa wuyan nata wani iri taji tanaji
hakan yasa tafara jujjuyar da kanta kaman wata kadangare, da kyar ta iya ta fizge hanunta ta
tashi dagudu zatabar dakin ajikin kofa ya ritsata hakan yasa ya daura hannayen shi biyu a jikin
kofar yasata a tsakiya yana mata wani irin kallo, hannu tasa tafara kakkare kirjinta tai crossing
hannayen ta daurasu akafada ta yanda bazaiga komiba idanunta suka cicciko da hawaye, cire
hanunshi daya yay daga jikin kofar ya daura akan hanunta yarike yacire hannun daga kafadan
yana kallon fuskarta, ahankali ta shiga reramai kuka tana mutsitsike ido, hannu shi yasa ta
bayanta jikinsu ya hadu tadan komar da kanta baya still tana mutsitsike idanun dake fitar da
kwalla, hanun nata yakamo yacire daga ido yadan hura mata iska a ido sanan yace "meke
damunki" kokarin cire hanunshi take daga bayanta ya girgizamata kai tareda hada forehead
dinshi da nata, hancin shi ya goga akan nata yadan kalli kwayar idonta sanan yace "talk"
kokarin kawad dakai take yaki bata daman yin hakan, da kyar tace "kama Farida alkawarin
aure, jiya ta shirya she was so happy she invited all her friends shine ka aureni bayan I already
told u bazan aureka ba, ashe wayau kamana, Allah kadai yasan wani hali Farida ke ciki yanzu,
why did you do dis?" takarashe maganan tareda da fashemai da kuka, tunda take maganan
yake kallonta baki ya bude zaiyi magana sukaji muryan wasu mata na buga kofa ta waje,
handky yaciro daga aljihu ya share mata hawayen sanan ya kamo hanunta ya zaunar da ita
akan gado yace "am coming". Falo yafita yabude kofa su Ihsan yagani da wasu manyan mata
guda uku, Ihsan tai murmushi tace "Umma tace nakawo su, za'a mata lalle ne da gyaran kai,
kuma wai kaje" cike da rashin jin dadi ya kalli matan yace "ku shigo" komawa yay ciki yasame ta
azaune hanunta ya kama ta tada ita tsaye yace "wurinki akazo, zomuje" make kafada tayi
hakan yasa yay folding hanunshi a kirji yana mata wani irin kallo da sauri tajuya zata fita daga
dakin yakamo hanunta.
[6/23, 2:07 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
47 & 48
Yakamo hanunta yarike gam yana yar dariya, turo baki tace "kasaken" make mata kafada yayi
yaja hanunta har gaban wardrobe, wani madaidaicin black hijab yaciro ya warware yasaka mata
sanan yarike mata hannu ya kalleta yace "banason ana kallon mu goody bag dina muje naraka
ki" akunyace ta dauke kai, tare suka fita daga dakin suna zuwa dining tafara kokarin kwace
hanunta sabida mutanen datagani su kusan five ga manyan kuloli kusan 5 dasuka ajiye a tsakar
falon, kin sakinta yay ahaka suka shigo falon, kasa daina kallonta su Ihsan sukayi, tana tsaye
agefenshi tadan kallesu tace "ina kwanan ku" manyan matan guda biyune suka amsa da lpy
lau, harara ya watsama su Ihsan yace "ku baku iya gaisuwa bane" atare suka taso sukazo inda
take tsaye Ihsan ta mika mata hannu tace "ni sunana Ihsan his sister, welcome to our family"
ahankali tai murmushi ta bata hannu, Ilham ma tace "sunana Ilham welcome to the family"
murmushi tamata tace "thank you" Fa'iza ma tace "nice Fa'iza welcome and u are very very
cute wlh" murmushi tai tace "thank you" hanunta Ihsan tarike tace "ga masu lalle nan mum tace
amiki idan angama za'a kaiki chan family house ne, muje afara yimiki sai muyi dishing abinci kiyi
breakfast ko" gyada musu kai tayi sukaja hanunta hakan yasa yasaketa, dan juyowa tai ta kallai
tai raurau da ido, girgiza mata kai yayi alamun no, ya kalli Ihsan yace "ku kullan min da ita
kuma, ko kuda karku bari ya tabata, bari naje" hanun yadaga mata alamun bye kunya taji
yakamata ta dauke kai da sauri su Ihsan sunata mata dariya. Harara ya balla musu sanan ya
juya yafita daga dakin yana kallon fuskar ta.
Lalle aka fara zizara mata, daya nayin na hannuwa dayar kuma na kafafu, Ihsan ta debo abinci
tana bata abaki, Ilham kuma da Fa'iza sun kwanta akasa suna bata labarin Khaleel suna tafawa
suna ihu, bakaramin tunamata da Farida sukayi ba, sosai taji tana kewan yar uwan nata da kyar
ta iya tahana kanta yin kukan. In less than awa daya lallen ya bushe da aka mata sabida
sanyin ac dakuma fanka dasuka kunna, wankewa akayi ba karamin kyau lallen amaryan
yamata ba, sanan aka wanke mata gashi akai using handryer aka busar dakan sanan aka fara
yaryada mata kitso yan mini mini. Sai Wuraren azahar suka gama sanan suka tafi yarage daga
ita saisu Ihsan sosai tasaki jiki dasu sabida yanda suketa janta jiki kaman sun santa, sata tai
wanka sukayi suka shiryata cikin wani ubansu lapaya, Fancy glamour suka dauko ta chanchara
mata makeup din amare idan kun ganta bazakuce itabane, sanan suka kira Umma cewa sun
gama, Umma tace "to, yanzu za'a zo ataho da ita". Anty Hindu ne dawasu mata duk sunci gayu
sukazo gidan, rungume Anty Hindu Islam tayi zatai kuka ta girgiza mata kai, sanan ta lullubeta
mata fuska aka dauketa suna wakoki aka tafi da ita gida fuskarta a rufe, ta lapayan ta take
hango yanda gidan ya cika da mutane sai taga gidan su kaman ba biki akeyi ba, wani babban
falo taga an shiga da ita an zaunar da ita akan kujera Anty Hindu ta zauna a gefenta tana
gaggaisawa da mutane anata guda, wata matace dataga suna kama da Khaleel taci gayu sosai
tazo gaban su, Anty Hindu tace "ga maman mijinki nan" yaye lullubin fuskarta Ammi tayi,
ahankali tasa hannu ta daga habarta kasa dago ido tayi sabida kunya hawaye taji ya gangaro,
murmushi Ammi tayi tace "masha Allah daughter" sababbin kudi taciro ajaka yan 500 tadinga
mata manni ana guda har saida kudin yakare sanan takoma ta zauna, haka ma Umma tazo ta
wanketa da liki, duk wanda yazo Anty Hindu tana fadamata waye, sosai aka dinga ihu ana guda
sanan aka tafi da ita bangaren Goggo, Goggo Kam harda rawa sabida murna tai manni tai
manni har saida duka kudinta ya kare, wata malama tagani ta tashi tai musu wa'azi da addu'a
sanan Goggo tace "to kowa yatafi abarmata amaryan ta tahuta" haka duk aka watse ya rage
Anty Hindu da Ammi da Umma, tashi sukayi suka shiga uwar daka Goggo sunata magana,
muryan Goggo taji tana cewa gaskiya anan zata zauna. Fitowa sukayi Ammi tazo ta dafata tace
"kinajin yunwa insa akawo miki abinci daughter?" akunyace ta girgiza kai, murmushi Ammi tai ta
kalli Anty Hindu tace "daughter na badai kunya ba" dariya Anty Hindu tayi daga nan duk suka
fita suka basu wuri, sosai Anty Hindu tamata wa'azi da fada akan tabi mijinta, sanan tacemata
Khaleel yamata sabon akwati set daban daban har 6, Abban ta duk yahada an wuce mata dasu
gidanta na Abuja. Sai bayan sallan Isha Anty Hindu ta tafi ba karamin kuka tasha ba hakanan ta
hakura tai shiru gyangyadi tafara yi akan kujeran Goggo sabida yanda tagaji gakuma kukan
datayi hakan yasa Goggo tace "tashi ki shiga ciki ki kwanta abinki ki huta kinji, sannu yarnan
yan iskan yaran nan duk sun wahalar dake" murmushi tai dan hakanan taji Goggo ta shiga ranta
gatadai tsohuwa amma akwaita da tsafta, "au bazaki tasoba" Goggo tai maganar tana kokarin
tashi daga kan tabarmar data shimfida a tsakar dakin, kamo hanunta tayi tace "muje ki kwanta
bakisan bacci nada amfani ga lafiyar dan Adam ba" kofar uwar dakanta ta bude da gadon ke
agyare tsaf tace "jeki kwanta abinki zanga dan kan uban dazaizo yafita dake, jekiyi baccin ki
saida safe kinji yar albarka" gyada kai tayi sanan tace "saida safe Goggo" kwanciya tayi akan
gadon da aka gyara tsaf dakin sai kamshin turaren wuta yake within 2 min bacci yay gaba da
ita, Goggo dake kishingide akan tabarma taji ana kokarin bude kofar ta tashi tayi ta zauna da
kyau tana wawware ido, Khaleel ne ya shigo sanye da doguwar jallabiya sai kamshi yake
yawani daure fuska yace "ina matata? Daga barinta tazo gidan naku shikenan kuma bakusan
ku komar da ita inda kuka daukotaba?" ko kallonshi Goggo bataiba taja filo abinta takara
kwanciya sanan tace "jeka tambayi uwarka, bata fadama daga yanzu anan gida zata zama ba,
to saikun koma Abuja ne zata tare a gidanka" karaso wa ciki yay yace "nida matar tawa lallai
nema" yazo zai wuce yay bedroom Goggo ta mike tsaye da sauri tasha gabanshi ta rike kugu
hakan yasa yaci birki yana kallonta cike da bacin rai, dariya tayi tarike haba tace "mara kunyar
banza, fitarmin daga daki tunda bakai ka ginamin ba wlh kona hadaka da ubanka" ganin Goggo
ta daure babu alamun wasa tawani rike kugu yasa yajuya yafita daga dakin rai abace, Goggo
tarakashi da dariya sanan ta maida kofa ta rufe harda saka Sakata tace "fitinannun yara"
kwanciya tayi abinta rai fes tace "dan kanuba to yarinya sai tasha gyara sanan za'abaka,
idanma nabari ka kara sata a ido ba sunana Lami ba" lumshe ido tayi tana sauke ajiyar zuciya.
Direct part din Ammi yawuce duk ranshi a dagule Yusuf yagani zaune afalo yana jiran Ihsan
tagama dafamai Indomie dayace tadafamai, yana ganinshi ya gimtse dariyar datazomai, ko
kallonshi baiyi ba ya shiga bedroom din Ammi wata kawarta ya tarar tana magana da ita hakan
yasa yaje kusa da ita ya zauna, sallamar matan tayi sanan ta juyo ta kalleshi tace "Ya akayi