Showing 18001 words to 21000 words out of 68809 words
Chapter 7 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf
irin kallo yamata sanan yace "Alhamdulillah yaji sauki" shiru
sukadan yi tana wasa da yatsa shikuma yana kallon dogayen yatsun ga fararen dogayen
kumbunanta dake mugun birgeshi, jingina yay da kujera anatse ya kira sunan ta "Islam" dago
kai tayi ta kallai ganin ita yake kallo yasa ta mayar da nata idanun kasa ajiyar zuciya ya sauke
yace "mesa kika zabi azabtar da zuciyata sabida kinsan kece ke mulkata? Islam!" Yasake Kiran
sunan ta dawani irin yanayi yace "nagaji inaso nai aure, niba yaro bane, banyi kokari ba tun kina
secondary school fa muna tare, please my princess ki yarda naje nasami su Dad ayi finalizing
everything kinji" ahankali tace "school dina fa" gyara zama yay ya fuskanceta yace "kina tunanin
bazaki cigaba da school bane bayan kinsan yanda nakeson karatu eh princess" girgiza mai kai
tayi yace "muna komawa chan zan nema miki University mai kyau kifara yi kinji My Islam"
murmushi tamai sanan tace "tom amma please kabari nafara ma Mum maganar kaji" murmushi
yamata yace "to naji rabin raina" yawani daga mata Gira, ahankali tace "Ya jikin Abba yaji sauki
sosai?" "Alhamdulillah an sallamemu inama ajiye su agida nataho na ganki, I missed my
princess so much" rufe fuskarta tayi da hannu sabida yanda yabata kunya, kunna motar yayi
yana murmushi yafara tafiya fira sukeyi jefi jefi gwanin ban sha'awa yana shiga kwanar layinsu
yay parking dan dama anan yasaba fakin bata bari yakai ta har kofar gidan su, tafito, daga mai
hannu tayi shima haka yana wani murmushi jiyayi inama gidan su zasu haka saida yaga ta
bude gate ta shiga sanan yatada motar yabar anguwan su.
Maman Miemie da Anty Hindu tasamu a falo gaidasu tayi tawuce sama danyi wanka gashi ana
Kiran sallan la'asar hakan yasa ta shiga bayi, muryan Farida dataji itama ta dawo yasa tai sauri
tagama wankan ta dauro alwala tafito da saurin ta dan tabama Farida labarin yanda sukai da
Fahad akan gadonta taga Farida ta kwanta tana bacci ko kaya bata cireba, murmushi kawai tayi
ta girgiza kai tace "lazy gurl" gaban wardrobe taje dan pink rigar ta data kaimata har gwuiwa
tasaka sanan tadau zani ta daura tasaka hijab tahau kan dadduma tai sallan la'asar. Koda ta
idar sauka kasa tayi dan debo abinci, jellof rice ta debo da fried plantain tadawo sama ta zauna
tanaci, ture kwanon gefe tayi ta daura kanta akan gado tana duba watsapp messages dinta.
Sama da awa daya da rabi kenan yana bakin anguwan su dan ko la'asar ma anan masallacin
bakin titin yayi, yana sanye cikin wani farin yadi mai kyau ya daura hula akai, agogon dake
hanunshi wanda Eesha ta bashi ya kalla 5:25, kunna motar yayi yay kwana ya shigo anguwan
nasu yay parking a kofar gidan su shiru yayi yakasa fitowa, toshi yanzu wama zaice yazo nema
baima san sunan ta ba, yafi minti uku a zaune ganin zuciyarshi takasa hakura yasa ya fito ya
rufe motar. Mai gadi dake zaune kan benci a kofar gidanne yataso da sauri dan yagane shi
mutumin daya gani jiya da Islam ne lokacin daya fito daga kewaye, washe baki yayi yace
"yallabai barka dazuwa, wajen hajiya kazone?" shiru yadanyi dan baigane wace Hajiya yake
nufiba, zaiyi magana mai gadi yace "koba Kaine wanda nagani tareda hajiya jiya kasa kayan
kwallo?" murmushi yamai yace "eh nine" mai gadi yace "to biyoni dan Alhaji yacemin na dinga
kai baki cikin gida bayason yaran shi na tsayawa a waje" bai jira amsar Khaleel ba yabude gate
ya shiga Khaleel yabi bayanshi har suka kai wajen kofar shiga dakin mai gadin ya juyo yace
"bari nagaya musu" bude kofa yay ya shiga ciki Anty Hindu da Maman Miemie ne suke dan hira
ya gaidasu yace "hajiya dama wanine yake neman hajiya Islam, gashi nan ma" zama Anty
Hindu ta gyara tace "okay shigo dashi" fita mai gadin yay yace "ance kashigo" sosai yaji kirjinshi
nabugawa ahankali yabude kofar ya shiga mataye biyu yagani Babbar daya gani wacce daga
gani kasan tama girmi Ammin shi yadan duka kadan yace "ina yini Hajiya" murmushi Anty Hindu
tayi tace "Lpy Lau" ta kalli Maman Miemie dake zaune gefenta tace "jeki kirata" ta kalli Khaleel
dake tsaye har lokacin kanshi akasa dan wani irin kunya yaji yakamashi tanuna mai kujera tace
"bismillah zauna mana" ahankali ya zauna itakuma ta bude newspapers dake kan table din
gabanta ta cigaba da karanatawa.
Bude kofar dakin tayi Islam dake gyangyadi ta shigo ta tabata tareda kiranta tace "Islam Islam"
Farida cikin bacci tace "maman Miemie kuna damuna plzz" maganar Farida ne yatada Islam
Maman Miemie tace "Anty Hindu na kiranki tana palo" da sauri ta mike tsaye, da dan gown
dinan iya guiwa da gashin ta datai parking yana lilo tafito daga dakin, dayake daga sama Anty
Hindu kadai zaka iya hangowa danshi yana kan kujeran dake ta ciki sakkowa tayi ta shigo falon
kai tsaye tazo gaban Anty Hindu ahankali tace "gani Anty" rufe jaridar Anty Hindu tayi tace
"banike neman kiba game neman kinan" ta nuna mata Khaleel da tunda ta shigo idanunshi ke
kanta, juyowa tayi ganinshi yasa numfashin ta ya tsaya chak zazzaro idanu tayi tana kallon shi
unbelievably, wawwaigawa tayi hijabin Maman Miemie data gani akan stool din dake kusa da
Anty Hindu ta dauka da sauri ta saka dan juyawa tayi ta kalli fuskar Anty Hindu ganin ita take
kallo yasa ta daburce cikin inda inda tace "uhnn dama dama" ta nunama Anty Hindu shi da
hanunta tace "uhn, dama brother yar ajinmu ce, ta turoshi ne yakawo min note ko" ta kallai ware
ido yay ya kalleta zaiyi magana tai sauri tace "yauwa ina note din data baka ka kawomin din?"
kasa magana yayi dan baima san mezece fa, kara kallon Anty Hindu tayi ganin ita take kallo har
yanzu yasa tace "ahhh yana mota? Muje na amsa saika tafi ko" tai hanyar fita daga dakin
ahankali ya tashi ya kalli Anty Hindu yace "sai anjima Hajiya" murmushi tamai tace "daga zuwa
ka tsaya kasha drinks mana" da sauri Islam tace "yana azumi ko, yau Monday" ta kalleshi
gyada kai yayi yana dan murmushi, murmushi itama Anty Hindu tamai tace "to shikenan mun
gode agaida su Mum" bude kofa Islam tayi tafito yabiyo ta abaya yana wani irin murmushi.
[6/16, 8:26 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
23 & 24
Saida takai bakin gate sanan ta juyo ta kallai cikeda masifa tace "wai wat is ur problem with me
ne eh? Dan Allah ka rabu dani" "I can't" yafada tareda folding hanunshi a kirji yana kallonta,
kwafa tayi tace "okay shikenan duk randa nama kara saka ka a idona sainai reporting dinka to
police station" dan murmushi yayi dan baiso tadena magana ba, ta gefenshi tazo zata wuce
yariko bakin hijab dinta da sauri ta dawo tana waige waige ko akwai wani a tsakar gidan ta
kalleshi tace "na shiga uku wanan wai kai dan Allah wani irin mutum ne, wlh wlh kaga na rantse
sau biyu niba nice wacce kake nemaba, Allah zan hadaka da Abba nafa this is not norm...al"
hanunshi dayasa akan bakinshi yamata alamun tai shiru yasa takasa karasa maganan da kyau
kirjinta nawani irin mugun bugawa gashi yaki sakin bakin hijab din nata balle ta gudu, ahankali
yadan zo kusa da ita kadan, sosai taji kirjinta ya cigaba dawani irin mugun racing gashi takasa
magana kaman yay mata magic dawani irin murya yace "will you marry me plz?" jin maganan
tai daga sama da sauri ta kalleshi danta tabbatar shiya fada inko dai shiya fada to mutumin nan
baida lpy, dawani irin murya yace "plzzzzz" wani karfi taji yazo mata ta fizge hijabin ta tana wani
irin hararan shi da manyan idanunta, batare datace komiba tazo zata wuce ajiyar zuciya yadan
sauke yace "at least kifada min sunan ki to kafin kitafi" juyowa tai ta kalleshi taja tsaki ta wuce
fuuuuu, yafi minti uku a wajen da kyar yadaga kafan shi ya bude gate yafita kanshi nawani irin
ciwo, shi kadai yasan me yakeji.
Ahankali ta bude kofa ganin Anty Hindu bata falo yasa da gudu tai sama ta shiga dakinsu,
Farida tagani zaune tanacin abinci tace "waye yazo wajen ki Fahad ne?" tsaki tadanyi tacire
hijabin Maman Miemie ta ijiye tace "wani unwanted guest ne" tai tsaki tawuce bathroom dan
tadan wanke fuska jin har yanzu kirjinta na bugawa.
Yau dasafe takeda lectures while Farida Kuma sai 11, da wuri ta shirya cikin atampa ta daura
Maroon hijab akai dayay mata kyau Bala ya dauketa a mota aka bude musu gate suka fito,
hada ido sukayi da Khaleel dake sanye cikin sport wears kafarshi cikin Nike sport shoes yana
jogging agaban gidan su, gadan towel dinshi akafada yana goge zufa idan yayi, wani heart
melting murmushi ya sakar mata daya fito dayar wushiryar shi, ya daga mata hannu alamun Hi,
sanan ya cigaba da jogging abinshi kaman da gaske, dauke kai tayi daga kallonshi ta turo baki
tacema "Bala mutafi" samun kanta tayi da kallonshi ta mirror mota taga ya daga mata hannu da
sauri ta dauke kai.
Around 3 tadawo kaman jiya Fahad ne ya sauke ta abakin layinsu ta dandaro da kafa, a kusa
da gidan su ta ganshi tsaye ya rike wani katoton balloon da aka hura an rubuta I love you ajiki
murmushi kwance akan fuskar shi yana kallonta, dauke kai da sauri tayi ta cigaba da tafiya.
Biyota yay da sauri yasha gabanta wani dan Kati mai kyau pink yaciro daga aljihun shi ya bude
an rubuta "please tell me your name" . Fizge katin tayi tayar ta kalleshi masifa tai niyyar mai
amma saitakasa ahankali tace "please leave me alone" da sauri ta wuce shi ta shiga gida
tabarshi nan tsaye.
Wuraren Magrib Farida tashigo gidan dakinsu ta shigo ta zauna akan gado batare datacema
Islam dake rubutu komi ba, kallo Islam tabita dashi sanan tace "Faree wah happen a school
why are you like this?" hawaye ne yazubo sharr daga idonta, ajiye biron dake hannunta tayi
tadawo kusa da Faridan ta dafata tace "meya faru me aka miki" fadawa tayi jikin Farida tafashe
da kuka da kyar tai shiru duk hankalin Islam yatashi tace "baki da lpy ne?" girgiza mata kai tayi
sanan tace "tun jiya bayan mun rabu nake kiran my superman yaki dauka, wlh har Gym dinan
saida naje yau amma bayanan ban ganshi ba, nakasa komi ko lectures ma babu wanda
nagane, I don't know why he is not picking my calls" tafashe dawani kukan, ba karamin
tausayinta Islam tajiba hannu tasa ta share mata hawayen tace "stop crying hala baya kusa da
wayan ne kokuma ansace mai wayan, please stop crying in sha Allah zai kiraki kokuma kuhadu"
gyada mata kai Farida tayi, murmushi Islam tayi tace "oya cire kayanki bari naje nakawo miki
abinci ta superman".
Washegari zazzabi ne yarufe Farida hakan yasa Anty Hindu tace ta zauna kartaje school yau
Abba Kuma yakira Dr.
Bala ne ya dauketa a mota ana wangale gate ta ganshi yana jogging yauma, baki ta tabe ta
dauke kai abinta suka wuce shi dudda haka saida ya daga mata hannu.
Da yamma ma data dawo haka ta ganshi zaune shida mai gadi suna hira murmushi yamata
yace "welcome" dauke kai tayi da sauri dan duk inta kalleshi heart dinta bugawa yakeyi ta shige
cikin gida da sauri.
Ba karamin murna yay ba da Ammi ta turo mishi su Ilham da Ihsan suzu suyi hutu, ga Fa'iza ma
sun suma mid term break hakan yasa gidan yacika da hayaniyan su.
Zaune suka dukan su a katoton falon Goggo wanan Karan ma harda Umma duk sai hira ake shi
kadai ne ke kwance ya lumshe ido kawai yana jinsu. Yusuf ne yace "why not mu dan hada get
together gobe Saturday da yamma" ihu Ihsan tayi harda tsalle tace "Ya Yusuf wlh is gonna be
fun to a ina zamuyi?" shiru yadanyi yana tunani sanan yace "anan falon Goggo but zamuyi
decorating, and zaku iya inviting anyone, kawai games zamu buga sai Kuma drinks and have
fun shikenan" ya dakama Khaleel duka yace "Ya kagani" batare daya bude ido ba yace "yea"
finciko hanunshi yayi yace "bawai Yea ba ATM dinka zaka basu suje kasuwa su siyo abubuwan
decorating dakin tsohuwar nan" hararan shi yayi yace "kai maiya sami ATM dinka" dariya Yusuf
yayi yace "ai am d organizer ni zanyi handling inviting guest, kai a cash aspect din kawai anan
muke bakatan ka, dan ban wayar kama" mikamai wayar yayi ya amsa yace "mezakai dashi?"
tashi Yusuf yayi saida yakai bakin kofa sanan yace "I want to invite your Farida" yafita da gudu,
da sauri Khaleel yatashi ya bishi yana kiran shi Yusuf Yusuf.
Part dinsu Yusuf ya shiga kafin Khaleel yazo ya kulle yana jinshi yana kiran shi amma yay
bedroom ya rufe kofa, zama yay akan gado ya bude wayar dan dama babu key, duba contact
dinshi yayi yaga babu wani suna Farida, wajen kira yaduba nan yaga wani number daketa
kirashi baya dauka hakanan yaji ajikin shi wanan ne number yay dailing ringing daya ta dauka
da sauri tace "Mk" dan dariya Yusuf yayi yace "ba MK bane Yusuf neto" ahankali tace "ina Mk
inata kiranshi baya dauka" yace "eh baida lpy ne saisa yasani na kiranki ma, dama munada
family get together ne yace he will be happy idan you come" wani murmushi tayi tace
"dagaske?" "why not ai yanzu u are part of the family, anyways karna cikaki da surutu gobe ne
4pm sharp, zan miki forwarding address din" da sauri ya kashe wayar jin Khaleel kaman zai cire
kofar da bugu ya tura mata address din gidan su sanan ya ijiye wayar yazo ya bude kofan ya
ruga da gudu yana kiran Goggo.
*JARABTA*
Maman Abd Shakur
25 & 26
Gayu Farida taci sosai kaman zataje gasar Islam Kam tanata dariya dan tasan wajen superman
dinta zata Bala ne ya kaita har kofar gidan tacemai 5:30 yadawo ya dauketa yace mata to
sanan yatafi. Wayar Khaleel dake hannu Yusuf ne tai kara dan tun safe ya dauke wayar ya boye
a wurin shi dan yasan Khaleel zai iya yaki daukar wayar idan tazo, tashi yayi yaje wajen Khaleel
yace "Bros tana waje fa jeka shigo da ita" wani kallo yamai danji yake kaman ya bindige shi,
ganin baida niyyar magana yace "tariga tazo wulakanci ba kyau please ka shigo da ita naji na
yarda koma me zakamin inta tafi Kamin please" wani kallo yamai sanan yajuya yafita daga
dakin Goggo ahankali, juyowa Yusuf yayi suka kashe da kanin nasu dukan su suna rawan
murna Fa'iza tace "wlh nakosa naganta" kara gyaggyara decorations din flowers din dakin
sukayi sanan suka zazzauna akan baban lallausan carpet din dasuka shimfida akan tiles.
Gate ya bude yafito tunda yake takowa take kallonshi tafiyar shi kadai gusar mata da tunani
yake kayan turawa ne ajikin shi white shirt ne yadan bude boturin saman sai dogon jeans blue
daya saka, wani irin murmushi takemai tace "barka da yamma Mk" dan murmushi yamata yace
"shall we" yana gaba tana biye dashi abaya cike da kunya har part din Goggo, wani ihu da tafi
su Yusuf dasu Ilham suka dingayi hakan yasa Farida ta labe abayan Khaleel tana kukkule fuska
dan ba karamin kunya tajiba, wani irin kallo yakema Yusuf dako ajikin shi saima wani dadi
dayake ji, Ihsan ne taje bayan Khaleel din ta kalli Farida dake rurrufe fuska cike da kunya,
tabata hannu tace "am Ihsan his sister nice to meet you" hanunta Ihsan ta rike ganin taki bude
fuska, tajata takaita wajen su sunata ihu sunajin dadi, da gudu Fa'iza ta kunna music suka hau
tika rawa, Yusuf yazo gaban Khaleel dake kallonshi yana wani irin kwaso mai shoki harda
gwalo, Farida kuma dasu Faiza sun sata a tsakiyar su sunata rawa abinsu. Gabaki dayan su
dadi sukeji Khaleel yay budurwa, sosai sukasha rawa abinsu shi waje ma yasamu ya zauna
yana kallon su, Farida sai satar kallonshi take, sunyi kusan 15 minutes suna rawa sanna Yusuf
ya rage karan music din Ilham ta tashi ta kwaso drinks da chicken kebab din dasuka hada.
Juice kawai Farida ta iya sha sabida yanda suke nan nan da ita duk tadinga jin kunya bayan
sun gama ne Yusuf yace "okay once again atafa ma our special guest Farida... Daaaa" yawani
kara gunna, suka wani kwashe da tafi, sanan yace "oya time for our game" yan matan suka
mimmike suna yeee. Akan carpet suka zazzauna sukai circle Yusuf yakamo hanun Khaleel
batare daya kalli fuskar shi ba ya zaunar dashi, sanan ya dauko wani bowl dake dauke da
papers da akai folding ya daura ma kowa one one paper ajiki harda Farida sanan ya ijiye bowl
din ya zauna kusa da Khaleel yay folding leg kaman yanda kowa yayi yace "papers din nan
each of them contain a question da dole saika amsa mana ka fadi gaskiya so starting from me
bari na duba Naga wats my question" budewa yayi sanan ya karanta "who is your best friend?"
murmushi yay yanuna Khaleel yace "dis dude shine best friend dina"
Fa'iza ta bude nata tace "what do you hate most" dan dariya tayi tace "wanke wanke wlh" daka
mata duka Yusuf yayi yace "lazy girl" Ilham ne tabude nata tace "izifi nawa kika haddace?"
gwalo Ihsan tamata dauke kai tayi tace "ashirin, suratul Ankabut zuwa Nas" Ihsan ta karanto
nata "meke saki kuka?" shiru tadanyi tace "ciwo, idan ina ciwo" sai Farida ahankali ta bude nata
ta karanto "who do you love?" shiru tayi Yusuf yace "answer now is ur turn" ahankali ta kalli
fuskar Khaleel da sauri ya kawad da kai murya chan kasa tace "him" wani murmushi dukan su
sukayi Ihsan ne tace "him, waye him?" juyo dakai tai ta kalli Ihsan a kunyace tai murmushi taki
magana, Yusuf ne yace "barta tamayi kokari ai, ya kalli Khaleel ya daga mai gira yace" Mk is ur
turn"