Showing 39001 words to 42000 words out of 68809 words
Chapter 14 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf
Son?" da kyar ya iya cewa "Ammi wai kekika cema Goggo karta bari Islam tabini anan zata
dinga kwana" Ammi taso tai dariya da kyar ta saita kanta sanan ta kallai tace "eh nafiso kawai
ran Sunday idan duk mun tafi Abujan basai ta tare wajenkaba, yanzu ga duka family anan
mezataje tai ita kadai achan gidan kadaici zai isheta mana" zaiyi magana tace "ka bacemin
daga nan I have alot of things to do" tashi yay yafita daga dakin duk ranshi acinkushe ta gefen
ido yaga Yusuf ya ijiye Indomie hanunshi yanamai dariya ciki ciki haka yay kaman bai ganshi ba
yana zuwa dai dai inda yake yadau plate din Indomie yace "wlh bazaka ci shiba" Yusuf ya
kwalama Ammi kira yace "Ammi kinga wai akaina zai huce takaicin shi" da sauri Khaleel yafita
yay part dinsu ya kulle kofa ya ijiye Indomie anan kan kujera yawuce bedroom yafada kan gado
kasa bacci yayi sai juye juye yake daga baya yatashi ya shiga bayi kawai ya dauro alwala yazo
ya kabbarta salla.
Bari muleka Faridan mu.
Idan kunga Farida saikun tausayamata ta rame sosai, da kyar Mum kesata taci abinci, bata da
aiki sai daukar waya taita dailing number superman da baya shiga ko kadan, Abba kullum
wa'azi yake mata da fada, Mum dai duniya yay mata zafi hakan yasa wani zubin idan Farida
tafara kuka itama jonata takeyi suyi tayi tare, ba irin Allah ya isan da basuma Islam ba sabida
bakin ciki.
Hakanan yau Wednesday taji tanajin fita kotadan ga rana, doguwar riga baka tasaka ta yana
gyalen ko hoda bata shafaba tafito daga gidan danko Mum bata fadimawa ba, keke napep ta
tare tace "yakaita Infinity gym" ta shiga ciki yaja har wajen yana ijiyeta ta ciro kudi ta bashi,
sucurity ya bude mata ta shiga ciki, wani kukane yazo mata ganin treadmill din data taba ganin
superman dinta akai, da kyar ta hadiye hawayen ta karasa wajen eatry din, order strawberry
smoothie tayi ana kawomata ta karba tareda bada kudin tanata kallon smoothie din tana tuna
ranan da superman dinta yasaimata yabata ahankali tace "menama Islam haka datamin irin
wanan abu? Mesa nakasa cire sonshi araina why, please God inaso na manta dashi please"
share da kwallan daya zubomata tayi tadau smoothie zatakai baki da sauri ta ijiye ta kife kanta
akan table din tana wani irin kuka mai cinrai, "hey is everything okay" dago kai tayi suka hada
ido da Yusuf dake sanye cikin sport wears hanunshi rike da cold bottle water, share ido tayi ta
juya da sauri ta duba ko suna tareda superman dinta ne taga shikadai ne, juyoda kai tayi ta
harari Yusuf tace "wat are you doing here?" kujera Yusuf yaja ya zauna yana kallon fuskarta
yace "nothing banmasan kebace" tashi tsaye tayi tajuya zata bar wajen dan wani irin haushin
Yusuf takeji da sauri yabita juyowa tai cike da masifa tace "kadena bina harda kai aka hadu aka
yaudaran, Islam Islam" takira sunanta saikuma tajuya tafita daga wajen da sauri jin wani kukan
ke zuwan mata suna fita Yusuf yasha gabanta yace "hear me out, kidena blaming sister ki wlh
batada laifi, Allah kuwa trust me" bakin gyalen ta tasa akan fuskar ta tafashe dawani kukan,
jitake kaman zuciyata zai fashe, ba karamin tausayin ta Yusuf yaji tabashi ba ya tsaya kawai
yana kallonta da kyar tai shiru ta kalli Yusuf da rinannu idonta tace "koma menene at least for d
sake of ni yar uwartace, tasan yanda nake sonshi saitaki auren shiko" ta dago kai ta kalli Yusuf
tace "kataba son wata?" girgiza mata kai yayi alamun a'a hakan yasa tadanyi murmushi tace
"bazaka taba iya gane wat am going through ba, Islam" tasake kiran sunan Islam tana wani irin
dafa kirjinta da sauri tajuya tabar wajen akan bakin titi ta tare napep ta shiga tana goggoge ido
da bakin gyale. Sosai Yusuf yaji jikinshi yay sanyi wanan wani irin sone, yanda take haukan son
Khaleel dinan shikuma haka yake haukan son Islam, oh Allah kayaye ma wanan baiwar naka
wanan son maso wanin, ahankali ya juya ya shiga ciki.
Islam dai sai gyaran jiki ake mata in and out, Goggo yanzu kulle kofa take idan baka
kwankwasa ka fadi sunanka ba bazata taba budewa ba duk dan kar Khaleel ya ganta take
wanan.
Dayake yau asabar yasa anata shirye shirye kowa na hada kayanshi dan gobe zasu tafi,
Wuraren 11 Khaleel yafito daga part dinsu yana sanye da jeans black da blue t-shirt mai gajeren
hannu, fuskar nan tashi adaure har wata yar raman dole yayi sabida rashin ganin Islam, dakin
Ammi yayi yasameta zaune kusa da Dad datake hadama tea gaishe su yayi suka amsa, Dady
ne yace "mekake so son" kallon fuskar Ammi yayi hakan yasa ta dauke kai ahankali yace
"dama Dady inaso Ammi tasa Islam muje ta tayani hada kayan mune nachan gidan tunda gobe
zamu tafi" Dady ya Kalli Ammi yace "kiramai matarshi tazo sutafi ta tayashi mana" Mum zatai
magana Daddy yace "ki kirata nace banson jin komi" murmushi Khaleel yayi hakan yasa Ammi
ta watsamai harara sanan ta wuce tafita tai dakin Goggo saida tai magana sanan Goggo tabude
ta shigo Islam dake sanye da riga da sket nawani soft material mint green dake zaune rike da
wayar Ihsan tana karanta wani novel tace "dauko Hijab dinki kizo Islam" ajiye wayar tayi tadau
hijab Goggo tace "ina zata?" "Kiranta Alaji yake" black hijab tadaura akan kayan tabi bayan
Ammi har falo, tunda ta shigo yake kallonta ganin yanda fatarta har wani kyalli take takara
haske, dudda tasaka hijabi bai hanashi ganin yanda tawani kara cikowa ba tai fresh like honey
wine, gaida Abba tayi cikeda girmamawa tana kallon Khaleel ta gefen ido dudda tadanyi
kewanshi amma taki Koda kallonshi balle ta gaidashi, Abba ya nuna mata Khaleel yace "kuje
kuhado kayanku na dayan gidan dan gobe da safe zamu tafi" ahankali tace "to daddy" fita
Khaleel yayi batare daya kalleta ba hakan yasa tabi bayanshi kirjinta nadan bugawa, mota ya
shiga hakan yasa ta bude gaban motar ta shiga ta zauna tarufe, kunna motar yayi suka fita
daga gidan su aranta tace "nan da nanne bazai iya zuwa da kafaba, lazy fellow" horn yay mai
gadinsu yabude yay parking yafito ya shiga ciki saida tai kusan 2min a motan sanan tafito jiki
duk asake, ahankali ta bude kofar ta shiga falon, da kyar ta iya daga kafa takai tsakiyar falon ta
tsaya ganin bata ganshi ba, tabaya taji anrungumeta hakan yasa saida tai yar kara sabida tsoro,
tsamtsam ya rungumeta yakawo kanshi ta wurin kunnenta yace "I miss you" juyo da ita yay
yakai hanunshi yay cupping fuskarta ya kalli cikin idonta yace "did you miss me" dan murmushi
tai sabida yanda yay maganan ta dauke kai, zama yay ya daurata akan cinya yana kallon
fuskarta yace "waye lazy fellow?" adan rude ta kallai ta dafe kirji, ganin yanda yake kallonta
yasa ta tashi da guda tana dariya tai hanyar bedroom tace "bafa dakai nakeba" harta zauna
akan gado taji yabude dakin da gudu ta tashi zata shiga bayi ya rikota tabaya tareda cire hijabin
jikinta ya matseta yana kallon idonta yace "Wana kama?".
[6/23, 2:07 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
49 & 50
Dan dariya taji yazo mata, kawad dakai tayi sanan tace "sorry" ahankali, kamo hanunta yay ya
zauna akan gado ya daurata akan jikinshi yana kallon fuskarta murya chan kasa yace "did you
miss me?" daura kanta tayi akan hanunta akunyace tace "uhm" bakinta tarufe da sauri dan wlh
batasan lokacin da maganan yafito ba, hade kansu yay wuri daya ya hade hannayenshi biyu ta
bayanta yana dan jijjigata akan kafarshi, murya chan kasa yace "banjiki da kyau ba" dan dago
kai tayi ta kalleshi suka hada ido batare data cire idonta daga kanshi ba ta sanya hanunta ta
baya ta bige hanunshi ta tashi da gudu ta tsaya abakin kofa sanan ta juyo ta kallai ta gyadamai
kai kaman yanda yara suke sanan tace "yea I miss yhu" bude kofa tai tafita da gudu tai
kwanciyan ta afalo akan dogon kujera tareda daura filon kan kujeran akan fuskarta. Alamun
tahowar mutum dataji yasa tadan zame filon kadan daga kan fuskarta ta kalleshi maida filon tayi
da sauri ganin sun hada ido kirjinta na bugawa sosai, zama yay ya dauki kafafun ta ya daura
akan cinyarshi yana mata waiwayi akafa, motsi ta dingayi tareda kara rike filon ta danne
fuskarta aciki, jin bakinshi datayi akan babbar yatsar kafarta yasa taji wani yarr batasan lokacin
data saki filon yafadi akasa ba, kasa daure yanda yake sarrafa yatsun nata yake ta mirgina ta
kifa tareda daga kafafun nata sama hakan yasa sket dinta yay kasa kafafun suka bayyana ta
lumshe ido tana cuccusa fuskar ta acikin kujera, ahankali ya kamo kafafun ya kwantar sanan ya
kwanto ta bayanta yakai bakinshi saitin kunen yakira sunanta "Islaaam" yanda yaja sunan yasa
takasa daurewa saida tabude idanunta dasuka kankance ta kallai, tashi yay ya zauna ya sanya
hannu ya dagota itama ta zauna tana lumlumshe ido, hanunta yakama yarike gam ahankali
yace "ina sonki dayawa Islam please don't ever leave me, I love you sama da yanda kike tunani,
u know something" kai ta girgiza mai tareda kwantar da kanta kan kafadar shi, kanshi ya daura
akan goshin ta yasanya hannayen shi yay cuddling nata very tight sanan yadan sauke ajiyar
zuciya yace "are you fine?" gyada mai kai tayi, ahankali yasake sauke ajiyar zuciya yace "nai
mafarkin kine jiya saisa nasa Abba yace kiboyini nan, I just wanted to know idan kina lpy"
lumshe ido tayi akan kafadar nashi tana kara shakan kamshin dayakeyi datake mugun so cikin
siririyar muryarta tace "mafarkin mekayi?" murmushi yay tareda kissing forehead dinta yace "it
doesn't matter now, all I want you to know is I love you very much Islam" da sauri ta maida
kanta kirjinshi tareda lumshe ido sabida yanda yakesa takejin kunya, ahankali yaciro kanta daga
kirjinshi yana wani irin kallon fuskarta bude ido tayi kadan ta kallai da sauri ta kankame idon
ganin ita yakema wani irin kallo, saukar bakinshi dataji akan lips dinta bazato ba tsammani yasa
ta bude ido da sauri tana kokarin kwace bakin matseta yay ajikinshi yana mata wani irin
zazzafan kiss, hanunshi taji abayanta yana shashafawa batare daya raba bakin nasuba zip din
rigarta taji yaja kasa kokarin tashi tai daga jikinshi hakan yabashi damar cire rigar da kyau ya
ijiye gefe, kankame idonta tayi sosai cike da kunya ganin yanda yake kallonta, ahankali yasaki
bakinta da idanunshi dasuka soma ja yana kallon yanda take kakkare kirjin da hanunta, hanunta
yakama yanadan murmushi yana wani irin kallonta ganin yanda taki bude ido, jin hanunshi akan
bra dinta yasa tadanyi ihu ta shige jikinshi sosai jikinta na rawa ta fashe da kuka tace "please
sto... " bai bari takarasa maganar ba yasake hade bakinsu wuri daya ya kwantar dasu akan
kujeran ya shiga wasa da ita da zafi zafi gashi yaki bata daman yin magana hawaye kadai take
iya zubarwa, bude kofa akayi aka shigo dakin kai tsaye hakan yasa ya dago kai tareda maida
Islam bayanshi itama bude ido tai atsorace jin anshigo dakin tai lamo abayan shi duka
hannayenta nakan kirjinshi dan rungumoshi tai tabayan, daure fuska yay tamau yace "mekika
zoyi anan?" yana maganan ne tareda daukar rigar Islam dake kan kujeran yana bata da sauri ta
karba ta saka, kasa cire ido tai akanshi ganin cikakken kirjinshi gawasu six packs dasukai layi
gwanin ban sha'awa, jijiyoyi sun fiffito a muscle dinshi "mekekazo yi agidan mu nace?" Ya daka
mata tsawa hakan yasa Islam tadan leko da kanta daga bayanshi bayan tagama saka rigar
bakinta har rawa yake tace "Faa.. Faree" wani irin kuka ne da kishi yakawo ma Farida wuya da
kyar ta iya kakalo murmushi tace "am sorry nazo gidan ku bada izinin kuba, dama damaa"
takasa karashe maganan sabida wani irin kuka dataji yazo mata, da sauri Islam ta sakko daga
kan kujeran zataje wajenta riketa yayi yasa hannun shi abayanta ya zuge mata zip din rigar,
hakan yasa Farida taji wani sabon kuka yazo mata da kyar ta share idonta tace "dama nazo na
roki gafarar kune akan duk abinda nayimuku, zan tafi Umara gobe, anjima zan tafi Abujama, so
I just tot nazo sabida mu shirya, shine nace Bala yakawo ni tunda yace yasan gidan yataba
kawo Anty Hindu" takarashe maganan tana kuka dan takasa daurewa yanda tagansu yasa taji
kirjinta namata zafi, fizge jikinta Islam tayi daga nashi taje da gudu ta rungume Faridan hakan
yasa ta fashe da kuka sosai tace "Islam am sorry, please kiyafe min abubuwan dana miki kinji
kema naji Anty Hindu tana cewa gobe zaku tafi ko please forgive me" girgiza mata kai tayi tace
"am sorry too Faree, please kiyafe min" girgiza kai Farida tayi tace "bakimin komiba, please
kiyakuri da duk abinda nayi" tai maganan tana kallon Khaleel, rigarshi dake kan kujera yadauka
ya saka sanan yazo wajen kamo Islam yay ya share mata hawayen datake ya girgiza mata kai
yace "is okay, stop crying Baby" ture hanunshi tadanyi ganin yanda Farida ke kallonsu ahankali
yace "bari nadan baku wuri to" yadan matso da bakinshi wurin kunnenta yace "zanje gida, but
idan nadawo zamu cigaba daga inda muka tsaya" dan tureshi tayi tana kallon fuskar Farida
murmushi yay ya saketa sanan ya kalli Farida ahankali yace "make your self at home bari naje
gidanmu bye" tunda yake maganan takasa dauke idonta akanshi, fita yay yana kallon fuskar
Islam ya rufo musu kofa.
Rungumeta Islam tasakeyi sanan taja hannunta suka zauna akan kujera tana kallon fuskarta
tace "Faree da gaske kin yafemin dan Allah?" dan murmushi Farida tayi tace "how about nadafa
miki wanan sweet Indomie dana ke miki agida kici kawai dan ki yadda komi yawuce awurina"
cike da murna Islam tace "to tashi muje mu dafa" ta mike tsaye harda jan hanun Farida tashi
Farida tayi tace "ki zauna abinki, nizan dafa miki gawayata nan ki karanta Soyayyar mu yau Fati
Teejay tai posting" da sauri ta karbi wayar sabida tana mugun son littatafan faty, Farida ta
kalleta tace "inane kitchen din? " nunamata tayi da hannu tareda kwanciya dan ta karanta novel
din, Farida tajuya ta shiga kitchen din, Indomie biyu ta ciro da Kwai tafara dafawa, komawa tayi
ta kulle kofar kitchen din sanan tadawo gaban gas din ahankali ta bude jakarta ta ciro sniper
tabare ledan tabude sanan ta zuba acikin ruwan Indomie, tai maza tai grating attarugu da yawa
da albasa ta zuba aruwan sabida ya kashe warin sniper, saida tagama dafa Indomie dayay
mugun kyau a indo ga egg agefe ta bare sanan taje gaban fridge ta dauko sabon exotic dayay
sanyi sosai ta bude ragowan sniper ta zuba aciki ta jijjiga sosai sanan tahada komi a tray tadau
fork da glass cup tasaka sanan wurgar da goran sniper a bin dake kitchen din, tadawo tadau
tray tabude kofa tafito falon, table taja ta ijiye mata tace "tashi tashi kici" ta mika hannu ta karbi
wayarta takoma ta zauna wurin ringing tone ta shiga ta danna hakan yasa wayar tai kara ta
mike da sauri ta kalli Islam da ita take kallo tace "Abba nakirana bari natafi zaikaini airport ne
saisa yake kirana nadawo" Islam tadan tabe fuska tace "to Indomie mufa bazaki tsaya muciba"
hararan ta tayi tana murmushi tace "sabida nai missing flight dina ko" tashi Islam tayi tsaye da
sauri Farida ta maida ita ta zauna tace "dalla kekuma sai Indomie yahuce, I cook it with luv so
kici da kyau bye" murmushi Islam tayi tace "Allah kiyaye hanya, I love you Faree bye" fita Farida
tai daga dakin tana daga mata hannu.
Komawa Islam tayi ta kwanta ta lumshe ido danji tayi hankalin ta ya kwanta yanda Farida
tadena fushi da ita, jin kamshin indomie ya ishi hancin ta yasa ta tashi ta zauna fork ta dauka ta
debo ahankali takai bakinta dan yatsine fuska tayi tana tunawa tace "kaman wari warin kalanzir"
hadiye wa tayi dan ba karamin dadi Indomie yayi ba, ahankali ta sake debo na biyu takai
bakinta hadiye wa tayi tana yatsine fuska tace "kodai akwai kalanzir agidan nanne" exotic din ta
dauka ta jijjiga sanan tabude ta zuba a glass cup takai bakin ta tana sha, cire cup din tayi tana
jujjuyawa tana shinshina jikin cup din, kodai hancin tane kejin warin kalanzir dinan tasake
tambayan kanta, sanyin da exotic din yayi yasa takarashe kwankwadewa ta ijiye cup din, sanan
ta tashi taje gaban TV tai plugging ta kunna, remote ta dauka tasaka zee world sanan tadawo ta
zauna akan kujera takara daukan fork tadebo Indomie zatakai bakine taji cikinta yadanyi wani
irin kara tareda tsukewa kadan, dan zabura tayi tareda yamutse fuska but tagama period
mekuma cikinta ke haka, batare data kawo komi ba takara kai Indomie bakin ta ta hadiye da
kyar, tashi tayi tana shahshafa cikinta sabida yanda taji kaman hanjinta na vibrating.
[6/23, 2:07 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
51 & 52
Da kyar ta iya ta zauna akasa ta daura kanta akan kujera tana wani irin numfarfashi da baki
tana cije baki tana jujjuya kafa sabida yanda taji kaman ana jajjage acikin nata, wasa wasa abu
sai gaba yakeyi wani irin barje dataji cikin nata nayi yasa tawani irin buga kai akasa tana
mukurkusu ahankali tace "wayyo Allah na, cikina na shiga uku" kokarin kamo kujera take ta
tashi tsaye hala cikin yadena, da kyar ta iya janyo filo daga kan kujeran ta tusa akarkashin cikin
nata ta, ji tayi kaman takara azaban datake jine, nukurkushewa ta dinga yi a wurin tana jujjuya
kai tana dukan kasa da awahale tace "Ya Khaleel" tafara kokarin jan jiki dantai wajen kofa
amma takasa ta kife kanta anan kasa tana dukan tiles din wajen da hannu, kofa taji anbude an
shigo tsabagen azaban datake ji tama kasa dago kai ahankali ya tsugunna yana shafa kitson
kanta daya mugun