Showing 33001 words to 36000 words out of 68809 words
Chapter 12 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf
tai lamo abayan shi duka
hannayenta nakan kirjinshi dan rungumoshi tai tabayan, daure fuska yay tamau yace "mekika
zoyi anan?" yana maganan ne tareda daukar rigar Islam dake kan kujeran yana bata da sauri ta
karba ta saka, kasa cire ido tai akanshi ganin cikakken kirjinshi gawasu six packs dasukai layi
gwanin ban sha'awa, jijiyoyi sun fiffito a muscle dinshi "mekekazo yi agidan mu nace?" Ya daka
mata tsawa hakan yasa Islam tadan leko da kanta daga bayanshi bayan tagama saka rigar
bakinta har rawa yake tace "Faa.. Faree" wani irin kuka ne da kishi yakawo ma Farida wuya da
kyar ta iya kakalo murmushi tace "am sorry nazo gidan ku bada izinin kuba, dama damaa"
takasa karashe maganan sabida wani irin kuka dataji yazo mata, da sauri Islam ta sakko daga
kan kujeran zataje wajenta riketa yayi yasa hannun shi abayanta ya zuge mata zip din rigar,
hakan yasa Farida taji wani sabon kuka yazo mata da kyar ta share idonta tace "dama nazo na
roki gafarar kune akan duk abinda nayimuku, zan tafi Umara gobe, anjima zan tafi Abujama, so
I just tot nazo sabida mu shirya, shine nace Bala yakawo ni tunda yace yasan gidan yataba
kawo Anty Hindu" takarashe maganan tana kuka dan takasa daurewa yanda tagansu yasa taji
kirjinta namata zafi, fizge jikinta Islam tayi daga nashi taje da gudu ta rungume Faridan hakan
yasa ta fashe da kuka sosai tace "Islam am sorry, please kiyafe min abubuwan dana miki kinji
kema naji Anty Hindu tana cewa gobe zaku tafi ko please forgive me" girgiza mata kai tayi tace
"am sorry too Faree, please kiyafe min" girgiza kai Farida tayi tace "bakimin komiba, please
kiyakuri da duk abinda nayi" tai maganan tana kallon Khaleel, rigarshi dake kan kujera yadauka
ya saka sanan yazo wajen kamo Islam yay ya share mata hawayen datake ya girgiza mata kai
yace "is okay, stop crying Baby" ture hanunshi tadanyi ganin yanda Farida ke kallonsu ahankali
yace "bari nadan baku wuri to" yadan matso da bakinshi wurin kunnenta yace "zanje gida, but
idan nadawo zamu cigaba daga inda muka tsaya" dan tureshi tayi tana kallon fuskar Farida
murmushi yay ya saketa sanan ya kalli Farida ahankali yace "make your self at home bari naje
gidanmu bye" tunda yake maganan takasa dauke idonta akanshi, fita yay yana kallon fuskar
Islam ya rufo musu kofa.
Rungumeta Islam tasakeyi sanan taja hannunta suka zauna akan kujera tana kallon fuskarta
tace "Faree da gaske kin yafemin dan Allah?" dan murmushi Farida tayi tace "how about nadafa
miki wanan sweet Indomie dana ke miki agida kici kawai dan ki yadda komi yawuce awurina"
cike da murna Islam tace "to tashi muje mu dafa" ta mike tsaye harda jan hanun Farida tashi
Farida tayi tace "ki zauna abinki, nizan dafa miki gawayata nan ki karanta Soyayyar mu yau Fati
Teejay tai posting" da sauri ta karbi wayar sabida tana mugun son littatafan faty, Farida ta
kalleta tace "inane kitchen din? " nunamata tayi da hannu tareda kwanciya dan ta karanta novel
din, Farida tajuya ta shiga kitchen din, Indomie biyu ta ciro da Kwai tafara dafawa, komawa tayi
ta kulle kofar kitchen din sanan tadawo gaban gas din ahankali ta bude jakarta ta ciro sniper
tabare ledan tabude sanan ta zuba acikin ruwan Indomie, tai maza tai grating attarugu da yawa
da albasa ta zuba aruwan sabida ya kashe warin sniper, saida tagama dafa Indomie dayay
mugun kyau a indo ga egg agefe ta bare sanan taje gaban fridge ta dauko sabon exotic dayay
sanyi sosai ta bude ragowan sniper ta zuba aciki ta jijjiga sosai sanan tahada komi a tray tadau
fork da glass cup tasaka sanan wurgar da goran sniper a bin dake kitchen din, tadawo tadau
tray tabude kofa tafito falon, table taja ta ijiye mata tace "tashi tashi kici" ta mika hannu ta karbi
wayarta takoma ta zauna wurin ringing tone ta shiga ta danna hakan yasa wayar tai kara ta
mike da sauri ta kalli Islam da ita take kallo tace "Abba nakirana bari natafi zaikaini airport ne
saisa yake kirana nadawo" Islam tadan tabe fuska tace "to Indomie mufa bazaki tsaya muciba"
hararan ta tayi tana murmushi tace "sabida nai missing flight dina ko" tashi Islam tayi tsaye da
sauri Farida ta maida ita ta zauna tace "dalla kekuma sai Indomie yahuce, I cook it with luv so
kici da kyau bye" murmushi Islam tayi tace "Allah kiyaye hanya, I love you Faree bye" fita Farida
tai daga dakin tana daga mata hannu.
Komawa Islam tayi ta kwanta ta lumshe ido danji tayi hankalin ta ya kwanta yanda Farida
tadena fushi da ita, jin kamshin indomie ya ishi hancin ta yasa ta tashi ta zauna fork ta dauka ta
debo ahankali takai bakinta dan yatsine fuska tayi tana tunawa tace "kaman wari warin kalanzir"
hadiye wa tayi dan ba karamin dadi Indomie yayi ba, ahankali ta sake debo na biyu takai
bakinta hadiye wa tayi tana yatsine fuska tace "kodai akwai kalanzir agidan nanne" exotic din ta
dauka ta jijjiga sanan tabude ta zuba a glass cup takai bakin ta tana sha, cire cup din tayi tana
jujjuyawa tana shinshina jikin cup din, kodai hancin tane kejin warin kalanzir dinan tasake
tambayan kanta, sanyin da exotic din yayi yasa takarashe kwankwadewa ta ijiye cup din, sanan
ta tashi taje gaban TV tai plugging ta kunna, remote ta dauka tasaka zee world sanan tadawo ta
zauna akan kujera takara daukan fork tadebo Indomie zatakai bakine taji cikinta yadanyi wani
irin kara tareda tsukewa kadan, dan zabura tayi tareda yamutse fuska but tagama period
mekuma cikinta ke haka, batare data kawo komi ba takara kai Indomie bakin ta ta hadiye da
kyar, tashi tayi tana shahshafa cikinta sabida yanda taji kaman hanjinta na vibrating.
[6/23, 1:42 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
43 & 44
Parking Abba yay yafuto yazagayo ta inda take ya budemata kofa, tama kasa tashi tana
mamaki mekuma sukeyi anan ga Khaleel, inane ma nan, hannu Abba ya mikomata yace
"sakko" ahankali ta sakko da kafarta dake sanye cikin flat shoe dinta black, maida kofar Abba
yay yarufe sanan yafara tafiya tana biye dashi abaya dan dukar dakai kadan Khaleel yayi yace
"sannu da zuwa Abba" murmushi Abba yamai ya shiga gaba Abba da Islam na biye dashi
abaya ya bude musu kofa suka shiga wani babban falo dayasha kujeru ash color ansa labulaye
masu kyau baki da ash, dakin sai kamshi yake ga sanyin ac dayakara karama dakin dadi, ga
babban tv bango dake aiki saidai babu kara, zama Abba yay akan kujera har lokacin yana rike
da hanunta ya zaunar da ita a gefenshi, karasa shigowa Khaleel yayi yaje zai zauna akasa
Abba ya nunamai dayan gefenshi ahankali yazo ya zauna yanadan satan kallon fuskar Islam
wacce kanta ke kasa.
Gyara murya Abba yayi sanan yafara da addu'oi ya kalli Islam yasa hannu yaciro bandir din yan
dubu daidai a aljihunshi ya ijiye akan jikinta yace "Ummi ga sadakin kinan, dazu aka daura
aurenki da Khaleel" da sauri ta dago kai ta kalli Abba jikinta har bari yake murmushi Abba
yamata yace "nariga nasan komi, yanzu dai abinda nakeso dake shine kibi mijinki sau da kafa
karki manta aljannarki na karkashin kafarshi, Koda wasa karki batama mijinki rai ki kasance
mace mai addini, ibada hakuri da jarumta dakuma tsafta, har mahaifiyarki ta koma ga Allah
bazan iya tuna randa ta taba batamin raiba" murmushi yadanyi sanan ya mike tsaye, ahankali
Khaleel ya mike, hannu Abba yasa ya dagota sanan yarike hannunta ya kamo na Khaleel
yasaka hanunta aciki ya Kalli Khaleel yace "ga amanar yata nan nabaka Muhammad ka kular
min da ita, Allah ya baku zaman lpy Allah ya albarkaci auren, Abban ka yacemin ran Sunday
zaku wuce Abujan ko" Ahankali yace "eh Abba sati daya kawai zamuyi anan" murmushi Abba
yay yace "to shikenan ubangiji Allah ya kiyaye yakuma baku zaman lpy ka kular min da
amanata na yarda da tarbiyanka Khaleel" murmushi yay yace "in sha Allah Abba" "to masha
Allah nabarku lpy" yajuya zai tafi sai alokacin taji wani mugun kuka yazo mata fizge hanunta tayi
daga hannu Khaleel da gudu taje ta rungume Abba tabaya tana kuka sosai tace "Abba dan
Allah karka tafi kabarni, dan Allah" dan juyowa Abba yayi danba karamin karyarmai da zuciya
tayi ba, ahankali ya dagota ya sharemata fuskar tareda sumbatar goshin ta ya girgiza mata kai
yace "ai auren kenan Ummi, kiyakuri kinji dole natafi ki zauna da mijinki, haka iyayenmu duk
aka musu, take care daughter" alamu Abba yamai da hannu ya riketa hakan yasa ya rikota
Abba yajuya yatafi, sosai tafashe da kuka harda majina tureshi tayi ta zube a wajen tana kuka.
Farida takira Khaleel yayi sau goma baya dauka, daga bayama saitaga bata iya kiranshi dan
kaman ma yay adding dinta a black list, mutanen dazasu kai Amarya sun gaji da jira suka fara
watsewa dai dai yarage daga Mumy sai wasu kawayen ta guda biyu da ita Faridan dake sanye
da lapaya ajiki duk tai sukusuku gabanta sai faduwa take idanun nan sun fiffito waje.
Shigowan Abba yasa Mum da Farida suka mike batare daya kallesu ba yace "kusame ni afalo
na" yay gaba suna biye dashi abaya, zama yay a babban kujeran shi ya nuna musu waje, kofa
Anty Hindu ta bude ta shigo dakin cike da murmushi ta kalli Abba tace "harka kaita kadawo?"
gyada mata kai yayi tareda cire hular dake kanshi ya ijiye a saman kan kujera Mum ce tace
"Alaji naga kana cire hulane, kiran mutanen nan fa yakamata kayi azo atafi da amarya wanan
wani irin abune, ko sai gobe zasuzo ne" wani irin kallo Abba yamata sanan yace "ai anriga ankai
amarya tun dazu" batare daya sake kallon Mum da fuskarta ya nuna alamun tambaya ba
yacema Farida "zonan" tashi tayi jikinta a sanyaye taje gaban Abba ta zauna, ahankali yasa
hannu a aljihun shi yaciro ticket din makka dakuma car key yabama Farida yana murmushi yace
"kinga wayan nan duk nakine mota sabuwa, ga ticket din makka wanda ranan lahadi mai zuwa
jirginku zai daga ko Faridan babanta" murmushi tama Abba tace "nagode Abba" gyara zama
Abba yayi yace "Farida yanda nake sonki haka nakeson Ummi, saisa nake kokarin yin adalci
atsakaninku, kinsan hadarin auran mijin dabaya sonka kuwa? Ai yaro kodan gidan kirki ne inhar
baya sonka gwara ka hakura dan duk yanda zuciyar shi take dole saiya cutar dakai dan zuciyar
nan dakike gani bata da Kashi Farida, ko yayyinki maza Abdallah da Ibrahim wlh bazan taba
bari su auri wacce basaso ba sabida nasan zasu cutar da itane" ajiyar zuciya ya sauke sanan
ya dafa kanta kaman yanda ake lallashin yaro yace "Farida nariga nasan komi, Khaleel bake
yakeso ba Islam yakeso saisa nahada auren shi da ita bawai da wani abu ba, saidan shine abu
mafi alkairi agareki, amma yanzu ga ticket dinki idan kinje Umarah kiyi addu'a in sha Allah
mijinki na nan zuwa, and Koda banma hadasu aure bayau one way or d other saiya aureta dan
Matar mutum kabarin sa, kiyakuri kinji karki bari komi ya tsaya miki arai, aure lokaci ne, wani
rashin alherine kinji" gyadama Abba kai tayi tana hawaye, Mummy da duk ranta ya dagule
yanzu mezatace ma kawayen ta ta kalli Abba tace "gaskiya Alhaji anzuba sonkai awajen nan,
kirikiri shikenan kanuna kafison Islam, yarinya tama Farida kwacen saurayi Kuma ka auramata
ha..." tsawa Anty Hindu tamata tace "kwace saurayin gidan ubanwa eh? To bari kiji jiya yaron
nan saida na aika aka kiramin shi bayan kun watse kun tafi walimar ku, har cikin falon nan na
Abba ya shigo saida nasa shi yafadiman gaskiya, ni tun bayau ba nasan Islam yakeso, Islam
yafara haduwa da a garin nan, sanan maganar so baitaba hadashi da Farida ba daga taimako
ta likemai, ai har labarin haukan datayi nacin shinkafar bera saida nasamu" takalli Farida
dawani mugun ido tace "ba shinkafar beraba ko taliyar bera ce kije kisiyo kici dan uwaki kezaki
mutu kafira kinji ko walakiri ya narkeki ehe mara hankali kawai" da gudu Farida ta tashi tafita
daga dakin tana kuka, tsaki mum taja tamike tabi bayan yarta, Anty Hindu ta kalli Abba tace
"tana dawowa daga Umarah kanemi Yaron kirki mumata aure kafin tajawo mana abin kunya
tunda dai zuciyar uwarta ta dauko" ta wuce tafita daga dakin tana masifa, Abba ya girgiza kai
wanan yayar tashi hmmm ba'a cewa komi.
Ahankali ya tsugunna agabanta yadaura hannayen shi akan gwuiwarta ta turemai hannu cike
da masifa, murmushi yamata yace "stop crying to kinji" make kafada tayi ta cigaba da kukan ta,
murmushi yamata yace "okay" tashi tsaye yayi ya cire babbar rigar shi ya zauna agabanta ya
lankwashe kafa yay tagumi yana kallon yanda take kukan, hararan shi tayi sanan ta janyo hular
hijabin ta tacigaba da kukan, dan dariya yayi ya sanya hannayen shi biyu ya maida hijabin baya
hakan ya bayyana fuskar ta, turo baki tayi ta daga hannu kaman yanda yaro yake idan zai daki
mutum tana kuka, murmushi yayi ya sanya hannayen shi ya rike kunenshi tareda langabar
dakai ahankali yace "am sorry plzzzzzzz" kawad da kanta tayi tacigaba da gunjin kukan ta,
ahankali yadawo ta inda fuskarta yake murya chan kasa yace "please stop crying ya isa haka,
zomuje kiyi wanka let's have dinner" yay maganan yana rikemata hannu, fizge hanunta tayi tace
"bazan yiba" murmushi yasake yi ganin masifa takeji yau, matsowa yasake yi kusa da ita yakai
bakinshi saitin kunnenta ahankali yace "oh are u shy? Okay bari ni naje nafara yi" kin kallonshi
tayi saima goge goge hawayen datake yi, ahankali ya mike tsaye yawuce ya shiga wani yar
corridor dazai sadashi da bedroom din, tashi tayi tsaye da kyar jin yanda cikinta ke ciwo waige
waige ta dinga yi kozata ga wani abu dazata iya rubutu dashi, akan dining table ta hango wani
leda dataga an rubuta thanks for coming ajiki, dama ya taho dashi ne danyabama mai gadi,
budewa tayi taga memo da byro da goran bottle water da duk anrubuta sunanta da nashi ajiki,
memo ta dauka da byro dan tsaki tayi dan wlh Allah yagani bayanda zatayi yine bude marfin
byro tayi sanan ta rubuta "please I, I, please I need pad" sosai taji wani irin kunya nakamata
ajiye byro tayi akan dining din sanan ta dawo cikin falon, ajiye memo tayi kusa da wayarshi
tabar page din datai rubutun abude yanda dazaran yazo zai gani, ta koma kan kujeran ta
kwanta tana tunanin gida da Farida.
Alamun tafiyar shi dataji yasa ta lumshe ido da sauri yana sanye da farin jallabiya sai kamshi
yake, shigowa falon yay yana kallon fuskarta ganin memo kusa da wayarshi yasa yakarasa
wajen dan yasan babu komi akan kujeran daya shiga ciki, daukan memo yayi ya duba, dago kai
yay ya kalleta yana murmushi, daukan key din motar shi yayi dake kan center table da wallet
dinshi yasa a aljihun ahankali yazo gaban kujeran datake ya tsugunna ba karamin bugawa
kirjinta yayi ba jin ya daura hanunshi akan nata data daura akan cikinta yana shafa fatar hanun
nata, dayar hanunshi kuma a saman kan hijabin ta ahankali yace "am coming bari naje nasiyo
miki" dan dukowa yayi yamata peck a kumatu ya mike tsaye yana kallon yanda jikinta ke rawa
murmushi yayi yafita daga dakin.
Abunku da GRA gabaki daya shagunan duksun kulle tsaki yayi yadau wayarshi sako yaturama
Ihsan kanwarshi sanan yay kwana yadawo, agaban gidansu yay parking dayake tsakanin gidan
da inda akakai Islam baifi gida uku bane tsakani, yana zaune a car Ihsan ta bude gate tafito
sanye da Hijab hanunta rike da Leda tana kallon fuskar Khaleel tana murmushi, daure fuska
yayi ya mikamata hannu tasaka mai tana dan dariya ciki ciki tace "ka gaisheta Ya Khaleel"
harara ya zuba mata yace "nidan aiken kine" eh din tace taruga da gudu tashiga cikin gida
murmushi yay ya kunna mota yabar wajen yay horn agaban gidansu mai gadi ya budemai yay
parking motar yafito, bude kofa yay dayar sallama tana kwance inda yabarta idanunta a lumshe
takowa yay inda ya barta ya ijiye ledan a gefe ahankali yakai hanunshi waist dinta hakan yasa
ta firgita ta bude ido da sauri tareda ture hanunshi, murmushi yamata yasaketa sanan yadau
ledan yabata ahankali ta karba tareda kawad dakai, hanunta ya kama yace "to tashi kije ciki kiyi
wankan" uhn tace tareda turemai hannu folding hannayen yay a kirji ya tsaya yana kallonta
ganin gabaki daya duk a tsorace take yasa yay hanyar kitchen yace "am going to the kitchen,
jekiyi wankan ki" saida taga ya shiga kitchen din sanan ta wuce hanyar dataga yabi dazu, daki
dayane tak a corridor hakan yasa ta bude dakin ta shiga babban gadone royal yaci hadadden
zanin gado, sai wardrobe din bango sai yar center carpet a tsakiyar dakin kofar bathroom din
tagani yabari abude ta wuce ta shiga tarufe. Takai kusan 10min atsaye tana tunane tunane wai
yanzu shikenan haka dama ake aure, shikenan ta auri wanda Farida ke mugun so bayan tai
rantsuwa bazata taba auren shiba yanzu ya hukuncin rantsuwarta?.
Jiki asanyaye tacire hijabi da doguwar rigar ta ijiye a gefe sanan tafara wanka, sai bayan
tagama wankan tarasa yanda zatayi gashi ko kaya daya bata dashi kuma doguwar rigan yadan
yi staining balle tamaida, hijabin ta dauka tasaka sanan tadan bude kofa kadan ta leka dakin
hada ido sukayi daidai yana ijiye tray din abinci akan drawer dan murmushi yay ya dauke kai
ganin she's so uncomfortable, batare daya kalleta ba yace "am coming" ajiye tray din yayi
yakoma gaban wardrobe ya bude wani dan madaidai cin akwati ya dauko ya kawomata nan
gaban bayi ya ijiye batare daya kalleta ba ganin ya zauna abakin gado ya juya mata baya yana
daddana waya yasa ta tsugunna ta bude akwatin wani doguwan rigan bacci ta dauko mai dan
mutunci da undies sanan tadan dago kai ta kallai ganin