Showing 15001 words to 18000 words out of 68809 words

Chapter 6 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf

M Shakur   

07 Oct 2025

1810

wajene da sanyin ac ya cika ko ina, bangare daya gym ne sai dayan
bangaren da ake saida any type of fruit salad da smoothies and fresh veggies da coffee. Waige
waige tadinga dan wajen da dan mutane ga wani calm music dake tashi kadan kadan, hangoshi
tayi akan treadmill machine yana gudu, karasawa wajen tayi ta zaga ta gabanshi ta tsaya
ahankali tace "good morning Mk" saida yadanji tsoro daya ganta agaban shi kaman anjehota
daga sama, wanan wace irin yarinya ne, murmushi kawai yamata batare dayace komiba
yacigaba da gudu abinshi, wasa takama yi da bakin hijabin ta fuskar ta yay wani iri, yanda take
wasa da bakin hijabin saiya tunamai da Eesha, ahankali yasa hannu ya kashe machine din
sanan yadau towel dake kan kafadar shi ya share zufan dayayi sanan ya sakko yadan wuce ta
ya dauko dumbell yadawo ya zauna akan kujera, kujeran dake kusa dashi ya nuna mata yace
"sit" murmushi tamai ta zauna shikuma yacigaba da daga dumbell din da hannu, baki tasaki a
bude ganin yanda jijiyoyin muscles dinshi ke tashi. Ajiye dumbbell din yayi akasa ganin yanda ta
kafeshi da ido kaman zata hadiye shi yay folding hanunshi a kirji yana kallonta wani irin kunya
taji hakan yasa ta kawad da kanta tace "dama nazo na gaishe kane kawai, naji kace you are
here and I know dis place very well" murmushi kawai yamata batare dayace komiba yadau
bottle dinshi yabude yana shan ruwan tace "Mk wai mesa bakason min magana ne?" cire bottle
din yayi daga bakin shi da sauri ya kalleta, murmushi tasake yi tace "kagani bakason yima
mutum magana, tell me about your sef to, kaman family, career and everything about you, I
wanna know u more" wani waiter ne yazo wucewa yakira shi yazo sanan ya kalleta yace "me
kikeso aka wo miki" wani irin dadi ne ya lullubeta tawani langabe kai kaman baby tace "anything
of your choice" maida duban shi ga waiter yayi yace "bring one avocado smoothie and one
strawberry smoothie" juyawa waiter yayi yatafi ganin yana daddana wayarshi kirar IPhone Xmas
yasa tai wani iri kaman zatai kuka tace "Mk" dago kai yay ya kalleta tace "tunda you don't

wanna go first ni I will tell you about my self" ajiye wayar yay daidai lokacin waiter yakawo musu
smoothies din a wasu cups masu kyau da straw aciki, daukan na strawberry yayi yabata
shikuma yadau na avocado, wani irin murmushi tayi tace "yamasan fevorite dina" kaiwa
bakinshi yayi ya zuko kadan sanan ya kalleta ganin shi take kallo yasa yace "am listening" wani
dadi ne yakamata tana mugun son yanda bakinshi keyi idan yana magana, ajiye smoothie tayi
akan tray sanan tace "my family name is maikano, Babana dan asalin Fulanin nan yola ne,
yanada one sister yayar shice amma, mai suna Anty Hindu, Anty Hindu Allah yay mata baiwar
masifa, abinda ma yarabata da mijinta kenan bata taba haihuwa ba. So daddy na nada two
wives but tafarkon yanzu she is late, tarasu lokacin I think I was either 13 ko14 years old, yara
biyu ta haifan ma baban mu Yaya Abdallah wanda yanzu yagama mechanical engineering yayi
applying short service na soja, yama samu yanzu haka yana can kaduna suna training, sai yarta
tabiyu mai suna Islam wacce muke age mate" murmushi tasake mai ganin yay paying attention
yana jinta tace "amma fa na girmi Islam dinfa ni kaga an haifeni March itakuma December but
the same year kagani ai na rigata shan iskan duniya ko?" gyada mata kai yayi, tace "mum dina
itace second wife we are three, yayana Ibrahim yanzu yana hostel a zaria dan ABU yakeyi, saini
saikuma my 5 year old brother mai suna Sameer yana basic 1 yanzu, so My mum ita tai training
dinmu dukan mu ta lura damu sabida Mumyn Islam was always sick sikla ce, thank god Islam
da yaya Abdallah ba sicla bane suba, anata fita da ita abroad ana mata magani" shiru tadanyi
ahankali yace "sorry Allah jikanta" murmushi tamai tace "Ameen, so tareda Islam muka taso
tundaga nursery ajinmu daya saiyanzu damuka shiga University ne nake Mass com ita kuma
tana Home economics, kasan difference dinmu? Ni am free minded, am very free and friendly,
Islam is friendly oo idan tasaba dakai but tanada zurfin ciki, she is my only friend and sister and
am her only friend and sister, I love her so much and she loves me so much, my mum yar yola
ce itama fulani, tana aiki lecturer ce anan AUN, tana koyar da yan food and nutrition, Mumyn
Islam kuma yar Sudan ce daga chan dadyn mu ya aurota. So this is my story tell me yours"
murmushi yamata daidai lokacin wayarta yay ringing, ganin Islam ne yasa tai picking "okay
tace" fuskarta ya nuna alamun rashin jin dadi ahankali tace "I have to go su Islam na waje
sunzu daukana, bye but next time is your turn u will have to tell me about yourself and your
family too" murmushi yamata yace "okay" harta fara tafiya ta dawo da sauri tawani langabe mai
kai tace "bazama karakani ba?" wayarshi ya dauka ya ijiye cup din smoothie dake hanunshi
yace "okay" ita ke gaba yana biye da ita abaya.
[6/13, 8:48 AM] Maman Jedda: *JARABTA*


Maman Abd Shakur

19 & 20

Harsuka kai wajen kofa security ya bude musu sosai yaji kirjin shi yabuga hakan yasa ya tsaya
tareda shafa wuyanshi, waigowa tayi ta kallai tace "why did you stop bazaka zo ku gaisa da
Islam ba?" murmushi yamata ya girgiza kai yace "nah, next time ma gaisa bye" bye tamai
yajuya yatafi, ahankali tajuya tafita cike da farin ciki ta bude mota ta shiga Bala yaja sukabar
wajen.

Cikin gida suka shiga Bala kuma yabiyo su da fruits, da Miemie taci karo a falo tanata wasa da
toys din Sameer da gudu Islam ta dauketa ta shillarata sama tana mata wasa, Farida Kuma ta
wuce sama dan kaima Anty Hindu sakkon ta. Daukar Miemie tayi ta wuce kitchen Mum da
Maman Miemie ne suna yanka nama gaidasu tayi tareda cire hijab ta ijiye akan kofa ta kalli
Mum tace "mum ni zanyi" tashi Mum tayi tace "sarkin son aiki bari to na wanke hannu saina tafi
da Miemie" hannu ta wanke a tap sanan tadau Miemie suka fita, naman tarike ma Maman
Miemie suka dinga yankawa har suka gama, ta tayata suka gama hadadden girki tare, fried rice
sukayi da pepper meat sai fruit juice dasuka hada suka jera a dining sanan Islam ta wuce sama
dayin wanka.

Wuraren 9 Farida ta tashi afirgice ta kalli agogo a rude tace "na shiga uku Islam shine baki
tashe niba dan kinga yau bakuda lectures ko" bude ido Islam tayi cikin bacci tace "sorry nima
bacci ne ya kwasheni bayan nagama azkar" daka mata duka Farida tayi abaya ta shige bayi da
gudu, ihu Islam tayi tareda buga kafa ta rike bayanta tace "wlh kinci bashi saina rama" leko
dakai Farida tayi ta kalleta tamata gwalo tace "kindai san baki da karfi ko I will break ur borns,
ragagagga" pillow Islam ta dauka ta jefa mata hakan yasa ta fashe da dariya ta koma cikin
bayin da sauri ta rufe kofa Islam ta daga murya tace "Allah sama kiyi latti muguwa kawai" dan
bayanta har yanzu zafi yake mata Farida badai zafin hannu ba. (name ur friend dake da zafin
hannu, hahah nidai Humi ne wlh). Agurguje tai wanka tafito ta tsaya agaban mirror tana
shiryawa tana hango fuskar Islam yanda take turo baki, ajiye hodan hanunta tayi tawani zo ta
rungume Islam tace "haba tawas sorry to daga wasa, wayyo nasan da zafi ko muga bayan"
kokarin tabamata baya take hakan ya mugun bata dariya, dariya dukan su biyu sukahauyi,
Islam ne tafara dakatawa tace "wai bazakisa kayaba sai kinyi latti" da gudu ta tashi taje gaban
wardrobe ta dauko simple material tasa tadau gyale ta tsaya gaban madubi tana rolling tace
"yau Fahad zaizo ko?" gyada kai tayi tace "eh yama dawo jiya wai, yace muhadu a quiks cafe
bayan sallan la'asar" pin ta dauka ta kama gyalen sanan ta rataya bag tace "kici gayu sosai fa
idan zaki, haka akema maza su haukace akanka, idan superman dina ya ganni har kasa
magana yake sabida kyan dayake ga inamai wlh" tai wani fari da ido, kama baki Islam tayi tace
"you with this ur superman Faree, wlh kinyi nisa" tace "Islam saima kin ganshi wlh black Arab ko
inhar kinsansu he is just like one of them, anyways ki lallaba Fahad fa, idan kuma yaki yarda
call me zanzo na same ku awurin na sasan taku u know am good at dat natafi kimin addu'a dan
wlh tunanin superman yahanani yin karatu bansan komiba Allah" tabude kofa tafita, girgiza kai
Islam tayi tace "Allah shiryeki, gud luck anyway".

Tun kafin la'asar tazo ta shiga wanka ta dauro alwala tafito, jin ana kiran sallan la'asar yasa ta
shimfida dadduma tai salla. Bayan ta idar ne ta zauna agaban mirror ta tsantsara kwalliyar ta
very light hoda ta shafa tasaka kwalli daya kara bayyana hasken idanunta, sanan ta gyara
giranta da brush haka nan taji tanajin sa jan baki, red janbaki ta dauko tasa hakan yakara fito da
kyan fuskarta leben yakara kankancewa kaman na jaririya, body splash da body spray ta dauko
ta fesa sanan taje gaban wardrobe ta tsaya tana tunanin kayan dazata saka wani black lace
dinta dake dauke da small small design din red flowers ta dauko doguwar riga akama dinkin
A-Shape, sanya kayan tayi ba karamin kyau yamata ba yafito da shape dinta sosai, gaban

madubi ta koma tadau brush tai brushing dogon gashinta dashi sanan takama da ribon ta
nannade ta cusa a tsakiyar ribon din, jan plain gyale ta dauko mara stone ta yafa tadau flat
takalmin ta channel mai igiya ta baya shima red ba karamin kyau baki da ja dressing din yamata
ba, phone dinta kawai ta dauka da dan karamin coin purse dinta tarike, humuran da xoxo ta
hadamata ta tsiyaya ta shafa kadan a hanunta dan badai kamshi ba sanan tawuce tafita daga
dakin, sanin Anty Hindu ne kadai agidan yasa tai sallama tabude kofa ta shiga dakinta, dan
tsugunnawa tayi kadan tace "sannu da hutawa Anty Hindu" kallonta tayi daga sama har kasa
tana hura hancin nan nata as usual tace "ina zaki ba kince anyi canceling lecture ku nayau ba?"
gyada mata kai tayi tace "eh, dama zandan je gidan su yar ajinmu na karbo handout dina ne"
saida Anty Hindu tagama nazarin ta sanan tanuna mata kan drawer tace "dauko car key dina na
aiki Bala, kidaiyi tuki ahankali" murmushi tayi harda juya kai tace "thank you Anty Hindu" key ta
dauko tafita daga dakin cike da murna. Gaban wata Toyota camry taje ta shiga kunnawa tayi
taja motar cike da kwarewa mai gadi ya bude mata gate tafita abinta, 20 min yakaita quiks cafe
parking tayi tafito tana takunnta daidai ta shiga, wani waiter ne yazo yace "are you Miss Islam
Maikano?" gyadamai kai tayi yace "Mr Fahad yamuku reserving table please come with me"
binshi tayi ya kaita wani hadadde table dake zagaye da kujeru biyu, zama tayi yace "meza
akawo miki Hajiya?" girgiza mai kai tayi tace "don't worry inyazo" juyawa yayi yatafi, wayarta ta
dauka tai dailing number Fahad bai daukaba harya katse, text dinshi ne ya shigo ta bude da
sauri "princess am sorry please give me 20-30min Abba ne baida lpy muna hospital but yanzu
nan zan fito nazo" reply tamai "Allah bashi lpy, take your time". Kunna data tayi ta shiga
watsapp tana duba messages wanda yawanci na groups ne, ganin Khaleesat tai posting Noorul
Huda yasa ta gyara zama tana karanatawa ba karamin dadi novel din kemata ba harta gama
karanatawa baizo ba, agogo ta kalla taga biyar da rabi saura minti biyu, number shi tafito dashi
zatai dailing message dinshi ya shigo tai maza ta bude "am sorry my luv bazan iya zuwaba, jikin
Abba yay tsanani an kwantar damuma. Luv u" reply tamai "Allah yaba Abba lpy, please take
care of him, Luv u 2" ta senda mai sanan tadau car key da purse tafito ta shiga mota tabar Cafe
din, tadanyi tafiya mai nisa kafin ta shiga wani uban traffic dan tsaki tayi tasa hannu ta kunna
radio.

Hakanan yau yaji yanason yabuga kwallo hakan yasa ya shirya cikin jersey ya sanya takalmin
kwallo yadau key mota yafita, yadanyi tafiya mai nisa dan stadium yakeson yaje yahadu da
traffic dukan kujeran motar yay sabida haushi dan bayason afara bugawa bashi, kashe motar
yayi ya bude yafito dan yaga maiya kawo traffic haka gashi ko moving motoci basayi, wata mota
yagani babba tafadi gashi ankawo wata babbar mota dake daga mota ana kokarin cireta daga
hanya sabida motoci su samu su wuce hakan yasa yadawo mota ya zauna, wani mai saida
ayaba ne yazo ta bangaren glass din haggu yace "mallam ga ayaba sun nuna sosai gasu da
shegen dadi" alamu yamai da hannu cewa bayaso hakan yasa mai ayaban ya wuce tareda
barin jikin window hango Islam yayi tadaura waya a kunne tana magana, da sauri ya goge
idanunshi sanan yasake kallon wajen, sosai yaji heart dinshi na racing kaman zai fita gani yayi
ta ijiye wayar ta kunna motar ta tafi, wani wawan horn ya danna ma motar gabanshi ganin
anfara tafiya, dawani irin mugun gudu yabi bayan motar Islam ganin tamai dan nisa, haka
yadinga binta abaya hartakai layinsu, horn tayi agaban gate dinsu kusan sau uku gateman bai
budeba hakan yasa tai parking ta bude kofa tafito daidai shima yay parking yafito daga motar

shi, batama lura da motanba tadan duka ta mika hannu tadauko purse dinta dake kan sit ta
maida kofar motar ta rufe ta juyo kadan yarage bata fada jikinshiba sabida yanda ya tsaya
akusakusa da ita, atsorace ta jingina da motar tana kallon fuskar shi, wani irin kallonta yake
kaman zai cinyeta, idanunshi data kalla yasa ta tuna fuskarshi a rude tace "innalillahi, wayyo
Allahna, you again!" atsorace ta bangaje shi ta ruga da gudu ta bude gate din gidansu ta shiga,
da gudu shima ya bude gate din yabita ciki.
[6/13, 10:55 PM] Maman Jedda: *JARABTA*


Maman Abd Shakur

21 & 22

Kafin takai tsakiyar compound ya cimmata yasha gabanta, chak ta tsaya tana waige waige duk
ta rude dan kar wani ya gansu barinma Anty Hindu, arude tahada hanunta biyu tace "dan
Allah karabu dani, waikai ajjani ni" sosai idanunshi suka xhanza kala ga heart dinshi dake wani
irin mugun racing yana duka fat fat fat, gabaki daya yanda take magana yasa yaji kanshi yafara
juyawa, ahankali yakai hanunshi daya yadafe kan, da wata irin murya ya kalleta yace "are you
my Eesha" girgiza mai kai tayi arude yace "then who are you? Mesa idan na ganki bana iya
hakura?" sake girgiza mai kai tana waige waige tace "wlh ni ba wacce kake nema bane, plz go
karka sani a wahala" cire hanunshi yayi daga kai yay folding hanun a kirji yana wani irin
kallonta, sosai jikinta ke rawa tace "na shiga uku, mallam inkana ma Allah katafi karabu dani"
ganin ko gezau baiyi ba har lokacin kuma ita yake kallo kaman wani sabon maye yasa tace "kaji
dan Allah katafi bani bace wacce kake nema ba, wlh in aka ganni dakai anan yau na shiga uku"
takarashe maganan tana yarfe hannu idanunta sun cicciko da hawaye, ajiyar zuciya ya sauke
da muryarshi datai mugun rauni yace "please don't cry kinji" yay maganan kaman zaiyi kuka
ahankali yace "naji zantafi but on one condition" ware ido tayi tana kallon shi, ajiyar zuciya
yadan sauke sanan yace "gobe by 4 zanjiraki a bakin layin nan, magana nakeso muyi, inhar
bakizo ba zan biyoki har gida" gyadamai kai tayi tana waige waige tace "eh na yarda, naji
please katafi Abbana yakusa dawowa" kallon fuskar ta yay nayan sakkanni kaman mai nazarin
wani abu ahankali ya tako zuwa gabanta da sauri ta matsa baya, kallon kwayar idonta yayi da
sauri ta kawad dakai ganin ya cikamata ido, ahankali yace "please karki kara fita ahaka" yay
maganan yana nuna gyalen data yafa, kaman mai rada yace "I don't like it" yanzu dai tayarda
mutumin nan baida lpy me ruwan shi da gyalen ta, "bye" taga ya daga mata hannu, yana fadin
haka yawuce ta gefen ta yafita daga gidan yana tafiyan nan kaman Boss.
Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke ta dafa kirji, tafi minti 5 tsaye a inda take da kyar ta iya daga
kafa tafara tafiya ta bude kofar falo ta shiga, hamdala tayi dataga babu kowa sadaf sadaf take
tafiya harta kai dakinsu ta bude kofa ahankali dan bataso Anty Hindu ma taji tadawo.

Gab da magrib Farida tashigo gidan a gajiye, Islam tace "Ya lectures yau, sannu yan mass com
kunajin jiki" yatsine fuska tayi tace "ni wlh duk am not happy yau lectures yasani yau banga my
superman ba" tabe baki Islam tayi tareda kwanciya ta lumshe ido dan har yanzu bata dawo
daidai ba, wai wayeshi ne? tsaki tayi ta tashi ahankali tai bathroom dan dauro alwala.

Atare da Farida yau duk suka tafi school dan itama tanada lectures yau.
Wuraren 3 tagama lectures dinta Farida ta kira tace mata ta wuce ita bata gamaba hakan yasa
tafara tafiya har tafito bakin gate, Keke napep takeson ta tare tahau. "Assalamu Alaikum my
Princess" daukar mai muryan yasa ta juyo murmushi kwance akan fuskarta, wani dogon guy ne
mai farar fata, yanada jiki ga saje daya yawaita a fuskar shi, ya sanya wani lallausan yadi brown
sai kamshi yake, baki ta bude zatai magana ya girgiza mata kai yana hararan ta dawasa yace
"karma kifaramin wanan dadin bakin naki, shall we" Ya nuna mata motar shi, murmushi kawai
tayi ya bude mata gaba ta zauna sanan ya zaga ta dayan bangaren ya shiga ya zauna hakan
yasa yace "Ya jikin Abba?" wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login