Showing 12001 words to 15000 words out of 68809 words

Chapter 5 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf

M Shakur   

07 Oct 2025

1813

da tray hakan yasa ya karba tace "ina zaka haka?"
komawa dakin yay da tray din tana biye dashi abaya yace "inaso nai aski ne" washe hakora tayi
danba karamin dadi tajiba tace "toai saikayi break ko, kaga dakaina fa a hadama, ina Yusufa"
muryan Yusuf sukaji daga bedroom cikin bacci yace "tsohuwar nan kidena batama mutum suna,
niba Yusufa aka yanka rago aka samin ba" hanyar bedroom din Goggo tayi tace "uwar kace
tsohuwa, katambayi Sama'ilan koni saida na yanka maka rago da aka haifeka" da sauri Yusuf
yaja bargo ya rufe kanshi jin ta shigo bedroom din, duddu Goggo ta zubamai Abaya tace "dan
kan uba" ihu sosai Yusuf yayi abin yabama Khaleel dariya, cup din shayin ya ijiye yadau one
slice bread ya shafa cheese spread dake dakinsu yaci, da tissue ya share baki yay murmushi jin
Goggo da Yusuf nata daru yadau wallet dinshi yasa a aljihun bayan wandon shi yafita daga
dakin.
Wani babban barbing saloon yaje aka mai aski da gyaran fuska ba karamin kyau yayiba sanan
yabiya kudin yabar shagon, ganin he is running out of fuel gashi baida enough cash atare dashi
yasa yay parking agaban wani ATM ganin akwai 2 people infront of him yasa ya tsaya ya jingina
da motar shi yana kallon titi, ihu yaji hakan yasa ya juya da sauri, wata yarinya yagani ta fashe
da kuka tana nuna wani guy dake gudu ga jakar ta a hanunshi tana cewa barawo ya kwacemin
jakana.
[6/11, 9:19 AM] Maman Jedda: *JARABTA*


Maman Abd Shakur

14...
Tashi tayi tazo gabanshi da sauri, hawayen dake zubo mata ta share cikin muryan kuka tace

"please help, ya kwance min jakana, credentials dina and everything are inside" baice mata
komiba ya koma cikin mota ya kunna motar yabi guy din daketa gudu yana kokarin shiga wani
layi gaban shi yasha da mota ya fito da sauri Guy din yajuya zai kara guduwa, taku biyu yay ya
riko guy din ranshi abace da daga hannu zai wanka mai mari da sauri yaron yabashi jakar yace
"dan Allah mallam kayakuri wlh yunwa yasa nai hakan, kayakuri dan darajan Allah" shiru yayi
dan yaron yabashi tausayi duka duka bazai wuce 22 ba, anatse yace "idan kanajin yunwa
kamata yayi kaje kafita ka nemi aiki kasamu kaci abinci stealing daukar abun wasu ba kyau,
hakki zai bika" wallet dinshi yaciro daga aljihun bayan wando ragowan cash din dayake dashi
yaciro yabashi sanan yabashi card din Abba yace "kaje address din company nan zansa abaka
aiki kaji" tsugunnawa yayi yaron yanamai godiya murmushi yamai yace "tashi katafi don't worry"
daidai lokacin ta iso wajen dan tun dazu take tsaye tana kallon abinda yafaru. Tafiya yaron yayi
shikuma Khaleel ya mika mata jakar tareda bude mota ya shiga, yana kokarin tada motar ne
tace "thank you so much, am grateful, ammm by the way am Farida Maikano and you?" dago
kanshi yayi ya kalleta sai alokacin ma ya lura da fuskarta black beauty ce yarinyar tana sanye
da doguwar riga na lace orange dakeda rantsin baki, ta yana black gyale akanta, murmushi
tasake mai tace "u really help me wlh credentials dina duka suna ciki nagode ko" murmushi
yadan mata batare dayace komiba ya kunna motar zai tafi da sauri takara matsowa jikin motar
kaman zatai kuka tace "baka fadamin name dinka ba and u are going is dat fair?" murmushi
yasake mata ganin yanda takeda surutu sai ta tunamai da Ihsan ahankali yace "just call me MK"
kaman mai tunanin tace "MK, MK Mk?" tasake kallonshi alamu tambaya ahankali yace "zaki iya
kirana Muhammad" murmushi tamai tace "wow MK nafiso, Muhammad na tsofaffi ne" murmushi
yasake yi dan dukta cikashi da surutu yace "bye" girgiza kai tayi tace "please dan tsaya kaji dan
Allah" Jakarta ta bude taciro wani memo ta rubuta number ta da sauri ta yagi paper ta mikamai
tace "please please ka kirani this is my number kaji, dan Allah" ajiye mai tayi ajikinshi ganin yaki
miko hanunshi sanan tamai bye, tafiya yayi haka tabi motar da kallo baki abude saida motar
yabace sanan tace "gosh he's so handsome, jibi muscles dinshi bumbum, awwwn my
superman" Ta wani lumshe ido.
[6/12, 1:16 AM] Maman Jedda: *JARABTA*


Maman Abd Shakur

15 &16

ATM gallery din yakoma yaciro cash sanan yawuce gida.
Wuraren 4 suka shigo gidan, dawani irin gudu Farida taje ta fada jikin Mum tace "oyoyo Mummy
na mundawo" murmushi Mum tayi tace "wanan murnan na lafiya ne" ta kalli Islam dake kokarin
bude bottle water tasha dan kishi takeji tace "Ya school din Islam hope kunbama Olayinka
credentials dinku danace" gyada mata kai Islam tayi sanan takafa goran abaki, tashi daga jikin
Mum Farida tayi tace "Mum yunwa nakeji sosai" tai hanyar kitchen taji andaka mata tsawa "my
friend will you leave there! wuce sama kije kafara wanka ki canza kayan jikin ki kafin kinemi
abinci, yara duk anbi anbata su" takarashe maganan tana huhhura hanci tana kallon Mum dako
daga kai batayi ba, saima marking scripts din dake gabanta da takeyi, turo baki Farida tayi ta

juyo tai stairs hakama Islam tabi bayan ta sum sum sukazo suka wuce ta sukai dakinsu.
Dakinsu suka shiga duk ransu abace, suka zauna akan gado, murmushi Farida tayi tafada jikin
Islam tace "no Anty Hindun nan bazan bari tai running mood dina yauba am so so happy" baki a
sake Islam ke kallonta irin lafiyan ki lau, dariya tayi sosai sanan tasa hannu ta Fizgo Islam suka
fada kan gadon a kwance tace "Islam yau I met my superman, wlh Islam yanada mugun kirki,
kinsan nasauka daga mota a bakin ATM ba ke Bala ya wuce dake school ba, shine fa bayan
naciro kudi wani barawo ya fizge jakana ya gudu, haba saiga giant huge gallant superman dina
ya kwatomin jakan, and ko, baima barawon komiba saima kyauta dayamai ya bashi card wai
yazo address din zai bashi aiki" ajiyar zuciya ta sauke tace "Sis kingan shi wlh kyakkyawane
sosai, black arab, gashida kirki, he is so cute" ba karamin mamaki abin yabama Islam ba tace
"Auwal dinki fa Faree?" tsaki taja tace "please karki karamin maganan shi nidai" murmushi
tasake yi sanan ta bude ido ta kalli Islam daketa kallonta cike da mamaki tace "gist me jor dazu
ina hall Fahad yakirani wai yanaso yazo gida kin hanashi, mesa kika hanashi yazo yaga Dad?"
kaman zatai kuka ta tashi tana zage zip din sket din dake jikinta na material tace "kinga Anty
Hindu tazo banason anything dazaisa tasani agaba wlh banason masifar ta" da sauri Farida
tace "to shikenan saiki hanashi zuwa?" turo baki tayi batace komiba ta zame sket din ta ninke,
tashi Farida tayi tace "shikenan karki gayamin gaskiya zurfin ciki saiya miki illa wataran" tai
hanyar bayi da sauri ta rike hanunta hawayen datake kokarin boyewa ne yadan zubo da sauri ta
share cike da damuwa Farida tace "talk to me Islam" ahankali ta zauna abakin gado tissue ta
dauko ta share fuskar ta sanan tace "yasami wani job offer ne a Dubai kuma in two months time
akace yay resuming yafara aiki, shine yake damuna yanaso yazo gida ya gaida su Dad, shiwai
so yake muyi aure yatafi dani chan, so yake ai auren nan da 2 months, and because nace
karyazo shine yaketa fushi jiya ko kirana baiyiba text kawai yamin jiya wai yatafi Abuja yin some
papers zai dawo ran monday" "and all this while baki fadamin ba kikai shiru tun jiya nake lura
dake kaman abu nadamin ki nadaiyi shiru, wai mesa kike hakane why are you my sister idan
nima zaki dingamin zurfin cikine" girgiza kai tayi ahankali tace "am sorry Faree bansan tayaya
zan fara fadan miki bane" hugging dinta Farida tayi ta shafa kanta tace "stop crying" share
fuskan tayi sanan ta saketa ahankali tace "tun muna SS3 kuke soyayya da Fahad, baki taba
bari yazo gidaba kibarshi yazo yaga Dad koma mezai faru ya faru" girgiza kai tayi tace "yanzu fa
muka fara University sai kawai nai maganan aure, Anty Hindu da Dad zasuce dama aure
nakeso maisa nabari ya kashe min kudi a school, am scared" tureta Farida tayi tace "banza
kekika sani sabida tsoro zakije kiyi asaran love dinki, bari naje I will tell mum" tai hanyar kofa da
sauri Islam tarike mata hannu tace "dan Allah karki fadama Mum, we will sort it out ran monday
idan ya dawo, zance yafara aikin tukunna nan gaba sai muyi auren" sosai ta mugun bama
Farida tausayi hakan yasa tace "okay shikenan amma karki bari abin yaja muku matsala" gyada
mata kai tayi tadanyi murmushi sanan ta wuce bathroom da gudu jin Anty Hindu ta kwalla musu
kira.

Tun jiya da daddare duk ringing din da wayar ta zaiyi da gudu take dubawa taga ko bakuwar
number ne amma duk wayanda tasani ne, babu sallan dazatayi da bazatai addu'a Allah yasa ya
kirata ba, ko bayi zata shiga wayar na hanunta dan Karya kira yaga baa dagaba. Koyau da safe
data tashi saida tai mafarkin shi hakan yasa tana bude ido ta duba wayarta bataga any miss call
ba tsaki taja duk ranta adagule.

Batai niyyar zuwa Saturday lecture da aka samusu ba amma sabida yanda duk taji batajin dadin
komi ne yasa ta tashi tai wanka ta shirya cikin wani brown Abaya da aka bishi da stones ba
karamin kyau yamata ba gyale ta yana akai Islam dake nannade cikin bargo tace "ina zaki?"
turare ta fesa sanan tadau jaka ta kalli Islam tace "inada Saturday lecture ne, bye baby girl"
ahankali Islam tace "bye" tafita tayi dakin Mum ta shiga tamata sallama sanan tafito Bala driver
ne ya dauketa suka fita, jakar ta tabude tasake ciro wayar ganin har yanzu babu miss call yasa
ta ijiye wayar akan cinyar ta ta dafe kai dan bakaramin daci taji zuciyar ta namata ba, sun kusa
kaiwa school ta tuna bata dauko calculator ba sabida bakin ciki gashi calculation course zasuyi
hakan yasa tacema Bala "malam Bala please danyi parking agaban super market dinan bari
nasiyo abu" gaban wani babban super market Bala yay parking purse dinta da waya kawai ta
riko tafito ta shiga ciki, bangaren littatafai taje nan taga calculator ta dauka, wajajen su
ice-cream tayi tadanyi tsaki maybe zata dan rage zafi da ice-cream din, fridge din tabude ta ciro
ice-cream ta juyo zata tafi wajen biya kaman ance ta daga kai ta hango Khaleel tareda Yusuf
sunci sky blue shadda gizna da aka musu dinki half jumper ga wata hula kube sun kafa akai sai
kace zasuje biki suna kwasan su snacks da littafi dan zasuje ma Fa'iza visit a boarding school
ne. Wani irin farin ciki ne ya lullube zuciyar ta ajiye abubuwan tayi a kanta din accounter tace
"am coming" da sauri tai wajen su da murmushi akan fuskarta tace "Hi MK" Yusuf ne yafara
juyowa saikuma Khaleel daya dago kai ya kalleta yana kokarin tuna fuskar, kamar zatai kuka ta
kalli Khaleel tace "shine baka is kirani bako MK" sai alokacin ya tunata, dan murmushi yay yace
"how you?" har cikin ranta takejin muryar shi da yanda yay maganan tace "fine" Yusuf ta kalla
sanan ta kalli Khaleel din tace "dan uwanka neko" gyada mata kai yayi Yusuf ta kalla tace "ina
yini" cikeda fara'a yace "Lpy Lau sis, yasu Mum nd Dad" purse din hanunta taketa wasa da
igiyan sanan tace "suna lpy" dan kallon Khaleel dake kokarin dauko gwangwanin Milo tayi tace
"shine baka kirani bako MK" ajiye milon yay a cart sanan yace "sorry battery na was flat jiya ne
saisa" murmushi tamai har cikin zuciya sanan tace "okay" Yusuf ne yace "how about nabaki
number shi dan ya iya mantuwa kina ganinshi haka, incase ya manta baikirakiba sai kimai
flashing ko" kama rigar Yusuf yayi tabaya yanda bazatai ganiba hanunshi Yusuf ya bige ya
shiga karanto mata number tana saving sanan ta kallesu tace "okay kayana nachan bye" ta
daga musu hannu cike da fara'a, bye suka mata sanan tawuce tatafi, turashi Yusuf yayi yace "at
least be a gentle man kabiya mata kudin abinda tasiya" zaiyi magana Yusuf yakara tureshi
hakan yasa yajuya yatafi badan son ranshi ba, murmushi Yusuf yay ya dunkule hannu ya saki a
iska yace "yess".
ATM card taciro tana shirin biya da POS ya mika nashi, ahankali ta kalli gefenta ganin shine
yasa wani dadi ya lullubeta, samata akai a leda aka bata ta karba sanan ta juyo cike da dan
kunya tace "thank you, am going to school karnai latti, bye" hannu yadaga mata yana mata calm
murmushi dake melting heart tai hanyar fita security ya bude mata kofan. [6/12, 1:16 AM] Maman Jedda: *JARABTA*


Maman Abd Shakur

17...
Hararan shi Yusuf yayi daya dawo yace "shine ko abani labari, who is she?" dan yatsine fuska

yayi yace "a girl I met yesterday" da sauri Yusuf yace "and??" tsayawa da tafiya Khaleel yayi ya
kalleshi yace "and wat, nace jiya muka hadu I just helped her out ne da wani guy ya kwace
jakarta shikenan" murmushi Yusuf yay suka cigaba da tafiya chan yace "she is nice" ahankali
yace "yea ga shegen surutu ba" dariya Yusuf yayi batare daya kara cewa komiba sukaje suka
biya kudin kayan sanan suka wuce school dinsu Faiza.
Tsabagen farin cikin daya mamaye zuciyar ta batamasan me aketayi a class ba dan murmushi
kawai take tana kara kallon special number Khaleel datai saving da my superman.

Haka tai wasting 4 hours lecture dinan tunanin Khaleel barinma yanda yawani zo ya mika ATM
card yabiya kudin nanne yafi tsumata.
Koda daddare Islam bacci tayi ta barta ido biyu sabida jira take Khaleel ya kirata ganin har 11
bai kirata ba yasa ta dialing number shi har tagama ringing bai dauka ba, sake kira tayi nanma
bai daukaba wani iri taji sosai ahankali ta ijiye wayar taja bargo ta kwanta ta rufe ido da kyar
bacci ya dauketa.
"Goggo jikan ki yay kawa fa" ajiye maficin datake fifita musu wani dan kasko data daura ruwan
shayi akai anan tsakiyar falon ta tayi tace "kai da gaske Yusufa" kallon Khaleel dayay kaman
bejishi ba yayi yace "gashi nan ki tambaye shi, wlh Goggo yarinyar badai hankali ba, ai in sha
Allah watarana zan kawo miki ita ki ganta" sosai Goggo taji dadi, batace komiba ta sauke shayin
daketa uban kamshi ta zuzzuba musu a cup, dauka yayi yay sipping kadan sanan ya ijiye saida
yadanyi sanyi sanan ya dauka ya shanye ya goge baki ya tashi ya Kalli Yusuf yace "zanje Gym"
kafin Goggo takirashi yafita daga dakin da sauri dan bayason surutun su, part dinsu ya wuce ya
shirya cikin kayan gym, wata gym singlet ne dake kama jiki mai ruwan toka tadan budemai kirji
sosai yasaka, sai dogon wandon shimin, yasa sport shoe na Nike, yadau wani dan madaidaicin
towel ya daura akafada yadau car key da wayar shi, da sport bottle dake cike da warm water na
glucose and lime yafita.

"ke Farida, Farida, wai bataji nane" tana zaune a dining itada Islam suna hira taji Anty Hindu na
kwala mata kiran nan kaman ana yaki, da sauri ta tashi tana amsawa, sama tayi tai sallama
tabude dakin Anty Hindu dake zaune da Dad suna magana, kudi Anty Hindu ta mika mata tace
"ki kira bala ya kaiki inda nake siyo fruit a kasuwa yasan wajen kisiyo, babu fruits agidannan
yau" karban kudin tayi tajuya tafita daga dakin, dayake tariga tai wanka tunda sassafe yasa
Hijab dinta kawai ta dauko da wayarta ta sakko, dining tazo tasami Islam na taya Mum yanka
kubewa ta kalli Mum tace "Mumy Anty Hindu ta aikeni kasuwa plz Islam tarakani" Mum ta kalli
Islam tace "zaki?" gyada kai tayi "tashi kutafi to, amma kuyi sauri" da gudu Islam tai sama Hijab
ta dauko milk daya kai mata gwuiwa tadaura akan atampa dayake jikinta tabita suka fita waje
bala ya dauke su suka tafi. Suna zaune a motar takara dailing number Khaleel saida wayar ta
kusa katsewa ya dauka, ajiyar zuciya ta sauke mai kara har saida Islam ta kalleta, dawani irin
calm voice tace "good morning Mk" ahankali yace "ya kk" murmushi tayi daya bayyana fararen
hakoran ta tace "Alhamdulillah" "gud" yafada tareda yin shiru itama shiru tayi, hayaniyar dataji
ata bangaren shi ne yasa tace "ina kake haka da ake hayaniya sosai?" wlh kawai dan bayason
wulakanci ne saisa amma dis girl is really disturbing him, kaman bazaiyi magana ba chan dai
yace "gym" da sauri tace "wani gym?" shiru yayi hakan yasa ta kalli wayar ganin yana kan line

har yanzu yasa ta mayar kunne tace "hello are you there" batare daya amsa ba yace "infinity
gym, bye gat to go now" Ya katse wayar. Bala ta kalla tace "dan Allah Bala dan kaini infinity
gym" da sauri Islam ta kalleta tace "ba kasuwa aka aikemu ba" yarfe hannu sama tayi tace
"dalla forget kasuwa, I wanna see my superman face tukun" tabe baki Islam tayi ta juya ta
cigaba da kallon hanya, agaban wani babban building da aka rubuta infinity gym ajiki bala yay
parking. Hannu Islam ta daura akan kirjinta sabida yanda taji yana bugawa.
[6/13, 8:48 AM] Maman Jedda: *JARABTA*


Maman Abd Shakur

18...

Bude motar Farida tayi ta zagayo ta bangaren Islam ta bude kofar tace "zomuje ku gaisa da
superman dina" girgiza kai Islam tayi tace "sabida Anty Hindu ta hadamu ta mana rashin
mutunci ko, nidai ban kudin Bala ya kaini na siyo" wani dadi ne ya kama Farida takama
kumatun Islam taja sanan tamata peck tace "luv u Islam dina, idan kun siyo ko, kubiyo ku
daukeni saimu koma tare" karban kudin Islam tayi tareda mata murmushi taja kofan motar ta
rufe sanan ta kalli Farida yanda take washe baki yasa tace "at least adan rufe bakin ko ta
superman" murguda baki tayi sanan tajuya security dake bakin wajen ya budemata ta shiga
tana waige waige, babban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login