Showing 57001 words to 60000 words out of 68809 words
Chapter 20 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf
yayo wanka ya fito daure da
towel ya zauna akan kujera yaja laptop dinshi booking flight yamusu dazai tashi gobe dan shima
jitayi duk ya gaji da garin gwara ya koma Abuja kawai yafara aikin shi, karfe 11 nadare jirgin
nasu zai tashi gobe mayar da laptop din yayi yarufe ya dauko mai ya shafa sanan yadau kayan
dazaisa yafita daga dakin yakoma dakin Ihsan yay kwanciyar shi.
Karan dataji yasa ta bude ido ahankali tana karema falon kallo, a kitchen ta ganshi tsaye yana
kokarin daukan heater kettle yana sanye da farar singlet dayar 3 quarter kafarshi cikin slippers,
tashi tayi daga kujeran tazo wajen kitchen din yanajin ta amma yaki kallonta hanunta yaji ta
daura kan nashi cikin sanyin murya tana kokarin karban kettle din tace "kawo nasama, mekake
so nama?" batare daya kalli fuskarta ba yasa dayar hanunshi yacire hanunta dake kan nashi ya
bude tap yatara kettle din yana diban ruwan, saida ya dibi daidai wanda yakeso sanan ya kashe
tap din yarufe kettle din yajona shi da igiyar shi, dan juyowa yay ya kalleta yace "i can manage"
ta gefenta yazo zai wuce tariko hanunshi da sauri muryan ta har rawa yake tace "am sorry, dan
Allah kayakuri idan kaji haushin abinda nace jiya ne, babu yanda zanyi ne Farida yar uwata ce,
my only sister kaji" takarashe tana wani rera sabon kukan dan juyowa yay ya kalleta hakan yasa
tadan tsagaita kukan datake yi, hanunshi ya fizge daga nata yakara mata wani kallo sanan yace
"nasani i know she's ur only sister" ya maimaita mata maganar da tamai na karshe yawuce
wurin kettle din ganin yana tafasa ya kashe ya dauko mug zai juye ruwan aciki da sauri ta
tsayar da kukan datake yi tazo wurin tace "kawo natayaka" daukar kettle din yayi ya tsiya ya
ruwan aciki batare daya kalleta ba yace "zan iya da kaina" ajiye kettle din yayi ya dauko nescafe
ya zuba aruwan da honey sanan yadau spoon yafita daga kitchen din yawuce falo ya barta
anan, yana gamasha anan falo yabar cup din ya shiga ciki ya chanzo kaya zuwa Jean da t-shirt
daya daura jacket akai yazo yafita daga gidan, wani irin abu taji ya tsaya mata arai hawaye
kawai taji yana fita ta dinga goge wa ranan hartai bacci bata ganshi ba, da safe ma data tashi
bata ganshi ba tadai ga note a gefenta kan gado daya rubutu ta hada kaya yau zasu tafi wani
dadi ne taji ya lullube ta zataje taga Farida, bayan sallan Isha ya shigo gidan afalo ya sameta
zaune da doguwar riga ja ajikinta ga akwatin su babba data hada kaya ta fito dashi falo, baiko
kalleta ba ya shigo yaja jakar yafita da ita waje sanan ya dawo duk tana tsaye, tashi jakar yafito
dashi batare daya kalleta a yace "muje" bayanshi tabi jikinta duk asalube suka fito ya kulle gidan
yabama Raymond dake waje key da wasu kudi Yaron yarakasu har wajen mota suka shiga
yana daga musu hannu suka wuce airport. Bayan sunyi checking in suka zazzauna suna jiran
afara boarding, goma dayan kai aka fara boarding suka shiga jirgin nan jirgin ya tashi jarida
yake ta karanatawa abinshi chan yaji kanta akan kafadar shi Jaridar yarufe yadan kalli fuskarta
bacci yaga tanayi hakan yasa yadan gyara mata kwanciya tareda sauke ajiyar zuciya shima ya
lumshe ido.
Karfe tara da minti arba'in jirgin su ya sauka a airpot din Abuja, ahankali take bude ido harta
bude su duka hada ido sukayi hakan yasa ya dauke kai da sauri, daga kanta tayi daga kafadar
shi tana zare ido, fara fita akayi daga jirgin hakan yasa yatashi itama ta tashi sauka sukayi wata
mota tazo ta dauke su ta ijiye su a gaban luggage claim nan suka jira akwatinan su suna zuwa
ya kwasan musu ya gungura tana bishi abaya suka fita daga arrival din wani driver sune da
Ammi ta turo musu yazo ya karbi akwatinan daga hanun shi yana gaidasu cikin fara'a, Khaleel
ne ya amsa suka shiga motar sukabar airport din. A wuse gaban wani babban gida driver yay
horn aka bude musu suka shiga ahankali tafito daga motar mai gadi yazo ya cicciro akwatinan
daga bot shikuma driver yakoma cikin mota yamusu sallama yabar gidan, kofa ya bude ya shiga
haka yasa tabi bayanshi duk agajiye wani hadadden duplex ne, falon anmai fentin brown da
milk, furniture din cikima kalan su kenan, upstairs dataga yayi yasa tabi bayanshi dadan sauri
wani falon tasake gani a upstairs din sanan ga dakuna uku, wani daki taga ya shiga kasa binshi
tayi tabude dayar dakin akwatin ta da tagani adakin yasa ta gane nanne natama, karasa shiga
dakin tayi tana karema dakin kallo anma dakin fentin baby pink ga akwatin ta da aka jera
asaman wardrobe kaya tacire ta shiga bayi tai wanka Koda tafito abinci tagani lafiyayyen white
rice da stew ga farfesu agefe duk anjera mata a tray, salla tafara yi sanan tazo ta zauna taci iya
cinta ta ijiye sauran akan drawer gefen gado ta kwanta sabida ta mugun gaji within 2min bacci
yay gaba da ita.
Koda tatashi da asuba tai salla tai karatun al Qur'ani sake komawa bacci tayi sai wuraren 7: 30
ta farka bayi ta shiga tadan kuskura bakinta tafito tasaka hijabi, ahankali tabude kofa tafito
daidai shima yafito sanye da uniform dinshi na navy bakaramin kyau yayiba, dauke kai yayi da
sauri daga kallonta, harda dan saurin ta takarasa gaban shi ahankali tace "good morning"
batare daya kalleta ba yace "morning" juyawa yay zaibar wajen ta bishi da saurin ta ahankali
tace "uhmm dan Allah kadan kiramin Abba inaso inyi magana da Farida ne" batare daya kalleta
ba ya cigaba da sauka daga kan stairs din sanan yace "bazan kiraba" da kyar ahankali tace "to
yaushe zamuje yolan?" baiko kalli fuskarta ba yace "babu inda zaki" wani irin kuka ne taji yazo
mata, fita daga gidan yayi da sauri, ta dade tsaye a wurin tana hawaye sanan takoma dakint.
Saida taji yunwa na neman mata illa sanan ta sauko kasa tana neman kitchen sallama dataji
yasa ta amsa wata ma tace da zatai 29 haka tanadan murmushin ta tashigo tace "sunana
kande nice mai tayaki aiki mai gidan ne ya turo ni, ai tunda akazo akai jere nike zuwa kullum Ina
gyara gidan, yau da safe ya kirani yacemini kun dawo nazo natayaki aiki" dan murmushi tai ta
gaishe da Matar, tare suka shiga kitchen suka dafa abinci mai rai da lafiya sai kallon yar torch
light phone din matar take ahankali tace "indan ari wayar ki?" da sauri Kande tace "eh gatanan"
ta dauka ta mika mata karban wayar tayi tafita daga dakin taje parlor ta zauna number Abba
tasaka tai dailing ringing biyu Abba ya daga da sallama da sauri tace "Abba Ummi ce"
murmushi Abba yayi yace "Ummi dazuko nake tambayan mijin ki ke yake sanar dani yana
wajen aiki toya kuke ya karfin jikin naki" ahankali tace "Alhamdulillah Abba ya Farida" ajiyar
zuciya ya sauke yace "ga Farida nan sai addu'a batama San wanda ke kanta ba" wani kuka ne
taji yazo mata hakan yasa ta taushe bakinta "amma muna ta addu'a in sha Allah zata sami lpy
so karki damu kanki ki kula da kanki kinji kinsan kema baki dade da samin lpy ba, Allah muku
albarka duka" kasa amsawa tayi ta katse wayar tafashe da kuka sosai, kande tafito daga
kitchen din da gudu tana lpy, kasa amsawa Islam tayi saima kukan datake yi da kyar tai shiru
ganin yanda Kande dukta damu ta mika mata wayarta dadan murmushi tace "Ya tace batada
lpy" Kande tace "to ai addu'a zaki mata ba kukaba Allah bata lpy" ahankali tace "Ameen
nagode" share idonta tayi tace "dan Allah tayani diban abinci kibama su mai gadin, kema ki
diba" murmushin dadi kande tayi sanan tace "to" diba tayi ta kaima su mai gadi Sanna itama
tazo tadiba a yar kula tamata sallama ta tafi.
Har dare haka ta wuni tana kuka, bayan tai sallan Isha tashiga bayi tai wanka tafito daure da
towel, yunwar dataji tana addabar cikin ta yasa tafito daga dakin ta sauko kasa, kitchen ta shiga
ta bude warmer ta dibi dan rice a bowl karami tadau spoon tafito daga kitchen din tareda kulle
kofar, karan anbude kofar sitting room yasa ta daga kai hada ido sukayi yana sanye da uniform
da sauri ya dauke kai yazo yafara hawa stairs da sauri ta ijiye abincin akan dining tabishi sama
harya bude dakinshi ya shiga itama tabude dakin ta shiga wani kamshi ya bugi hancinta, dakin
tsaf tsaf komi fari, ko kallonta baiyiba saima kokarin bude boturan rigar shi dayake yi, ahankali
tace "Ya Khaleel dan Allah yaushe zamuje duba Faridan?" ko kallonta baiyiba saima karasa cire
rigarshi yayi ya ijiye agefe ya tsugunna yana kokarin kwance igiyar takalmin kafarshi, duka ya
kwance ya ijiye agefe yatashi tsaye yana kokarin cire dogon wandon uniform din jikinshi, tadan
matso kusa dashi jikinta nadan rawa tana gyara towel din jikinta adan tsorace tace "eh yaushe
zamuje" bai kalleta ba saima zame wandon dayayi yace "babu inda zaki" sosai tafashe mai da
kuka hakan yasa yabude bayi ya shiga abinshi kuka take sosai tasa hannu tanata murza idanu
tace "dazu dana kira Abba yacemin batasan wake kanta ba, Farida is suffering, tun ina yarinya
mu biyu Mummy ta raine mu tare, Farida ita ke tare min fada a school, ita ke bani snacks din
break, itake rikemin hannu, she is my best friend, so kake karaba mu yanzu?" tacigaba da kuka
sosai kaman yanda yara suke suna kuka suna magana, da kyar tai shiru tana sauke ajiyar
zuciya tace "tun ranan da ka karbo mata jakanta Farida take sonka, Farida loved u so much,
Allah ne ya jarabce ta da wanan son and ni take fadama komi, yanzu she is seriously sick
bazaka sakeni ka aure ta ba, wlh idan wani abu yasa meta bazan taba iya yafema kaina ba"
takara fashewa da kuka harda shesheka, cikin kukan tace "kaki kiramin su nai magana da ita,
sanan kuma bazaka barni naje naduba taba rabamu kake so kayiko hmmm" tacigaba da rera
kukan sabida yanda abun ke mata ciwo, ya dade tsaye abakin kofar bayin daure da towel yana
kallonta sabida ta juyama kofar baya, wani irin cije lips dinshi yayi sanan ya fuzar da iska sabida
yanda ranshi ya mugun baci, rufo kofar bayin yayi da karfi har saida tai kara hakan yasa ta juyo
a firgice ta kallai, ganin idonshi yasa ta tuna marin da tasha ranan da sauri tai hanyar kofa zata
bar dakin ya fizgo hanunta ihu mara kara tayi, jijjigata yay rai abace yace "bazaki yolan ba, and
saki kikeso ko baza'a sakekin ba, barima kiga" towel din jikinta ya fizgo ya yar arude tafara
kokarin tsugunnawa tace "na shiga uku dan Allah ka yakuri Ya Khaleel, wlh bazan karaba"
jefata yayi kan gado.
[7/2, 9:28 AM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
73 & 74
Bakaramin wahala Khaleel yabata ba dan wlh ta gurzu, tun tana iya rokonshi daya ya hakuri
har takasa magana sai ajiyar zuciyar wahala take tana kuka, wuraren 3 ya saketa tafashe da
kuka kasa kasa tana saukar da numfashi juyowa yay ya kalleta fuskar nan adaure yace "get
out" da sauri ta dira daga gadon dan wani irin mugun tsoron shi taji tanaji anan kasa ta
tsugunna tadau towel dinta ta daura tana goge hawayen dake zuba, sanan tafita daga dakin
tanadan dingishi ta shiga dakinta bayi ta wuce direct.
Runtse idonshi yayi da karfi sabida yanda kukan ta ke taba rashin shiya rasa wanan wace irin
jarabta ce, da kyar yatashi ya shiga bayi yadan dade sanan yafito ya tsane ruwan jikinshi da
towel yasaka jallabiya yahau kan dadduma yafara salla. Da aka tada salla asuba ne yafito
yawuce massallaci saida gari yay haske yadawo yawuce dakinshi ya shirya cikin shirin zuwa
aiki yafito kofar dakinta yabude da sauri ta tashi zaune kan gado jikinta har wani bari yake
sabida yanda taji wani irin tsoron shi daya shigeta bakinta har rawa yake tace "in ina kwana" bai
amsa taba saima harara daya jefeta dashi yace "ki tashi ki shirya ina jiranki amota" barin wurin
yayi so yake ya kaita gidan su ko tadan walwala, yasan idan ya barta a gida haka zata wuni
tana kukane. Yakai kusan 15 minute amota ta glass ya hango ta tafito sanye da riga da zani na
brown and yellow atampa tasaka brown hijab da takalmi da brown jaka fuskarta dadan hoda da
kwalli sosai tamai kyau tana tafiya ahankali, bude kofar gaban tayi ta shiga ta zauna hakan yasa
yaja motar batare daya cemata kala ba har gidan su, parking yayi ababban compound dinsu
yafito hakan yasa tafito tana biye dashi har suka shiga gidan da sallama su, Ihsan dake falo dan
dama yariga yakira Ammi yace suna zuwa suka taso da gudu suka wuce shi suka rungumeta
suna ihu Ammi da Abba dake sakkowa dan rakoshi tayi zai tafi aiki tace "karku karyamin
daughter bafa hankali cikakke gareku ba Ilham" sakin ta sukayi suna dan turo baki, murmushi
tayi tazo gaban su Ammi kanta akasa dan bakaramin kunyan su takejiba tace "ina kwana Abba,
Mummy ina kwana" dagota Ammi tayi tace "daughter ya jiki" Abba yace "kun iso lpy" murmushi
tayi tace "Alhamdulillah" Ilham ne tazo tace "muje dakin mu Amaryan Bros" dan murmushi tayi
suka riketa Ammi tace "kujata ahankali mana" shidai yana zaune a dining yadau apple yanaci
yabisu da kallo dan ajiyar zuciya ya sauke ganin murmushi akan fuskarta, tareda Abba suka fita
yacema Ammi zai biyo ya dauketa idan yataso daga aiki. Abinci Ammi tahada mata sanan takira
Ilham ta sakko ta dauka ta kai mata sai nannan suke da ita sai wajen karfe sha daya sanan
suka shirya badan sunso ba suka tafi school shima sabida test din dasuke dashi ne. Ita kadai
suka bari adakin hakan yasa tai shiru tana tuna jiya wani zazzafan hawaye ne taji sun fara zubo
mata, kofar dataji anbude da sallama yasa ta share hawayen da sauri amma Ammi tariga tagani
tashi tayi ta zauna akan gadon Ammi kuma ta shigo ta zauna a gefenta tana kallon idonta tace
"lpy daughter kike kuka menene?" girgiza kai tayi tareda kakalo murmushi tace "bakomi Ammi"
hanunta Ammi ta rike tace "menene karki boyemin komi, ni mahaifiyar kuce un menene
daughter fadamin wani abin yamiki?" girgiza kai tayi da sauri tana kokarin tsayar da wasu
hawayen dake shirin zubowa ahankali tace "Farida ne batada lpy Mummy" da sauri Ammi tace
"subhanallah tun yaushe?" "tun muna chan" cike da tausayi Ammi tace "oh Allah meke
damunta?" fashewa tayi da kuka hakan yasa Mum ta shafa bayanta tace "bansani ba amma
tanata tarin jini Abba yace bama tasan wanda ke kanta ba" "shine baisan ya kaiki tun jiya kuje
dubiya ba, zaizo ya sameni ne, in sha Allah gobe goben nan zansa shi ya kaiki kuje ku dubo ta,
dena kuka kinji tashi muje dakina kin zauna ke kadai awanan dattin dakin nasu" dan murmushi
tayi dan ba tawani ga dattin da Ammi ke fadaba banda kayan sawan su dasuka tara akan
gadon, tashi tayi suka fita daga dakin tareda Ammi sosai tasaki jiki da Ammi ganin yanda taketa
janta jiki tabata wasu magunguna tasha sanan tahada mata wasu aleda dazata tafi dasu ta
dinga sha da yogurt, Ammi ta kunna mata kallo wai dukdan tasaki jiki.
Bayan sallan magrib ya shigo gidan afalo yasameta dasu Ihsan suna bata wani labarin novel sai
dariya take dan bama ta lura dashi ba, hada ido sukayi da sauri ta hadiye dariyar ta janye idonta
daga nashi ganin yanda yake kallonta, daure fuska yayi dukan su suka gadaishi bai amsa suba
yawuce dining dan yunwa yakeji sosai, warmer yabude yadebo potato porridge dayaji nama ya
zuba a plate yasa spoon, Ihsan tace "Ya Khaleel Ammi na kiranka" daukan plate din yayi
yawuce sama dashi, da sallama ya shiga dakinta ya zauna akan gadonta yanacin abincin,
kallonshi tayi ta daure fuska tace "mesa bakakai Islam ta gaishe da yar uwarta ba" plate din
abinci ya ijiye agefe baice komiba hakan yasa Ammi ta sassauta murya tace "haba son koma
me Farida tayi yariga yawuce ai, so kake karaba su danka auri wanan, karka manta fa tare suka
taso koma me yar uwarta tamata bazata taba dena sonta ba eh son, kai yanzu idan aka cema
Ihsan ko ilham basu da lpy basuma san inda kansu yakeba yazaka ji eh?" shiru yayi hakan yasa
Ammi tai murmushi tace "don't be selfish, inaso gobe kubi jirgin safe kutafi yola" ahankali yace
"Ammi aikina fa" "nadai goben, gobe ai Friday basai kudawo ran sunday ba, haba Son" dan
murmushi yayi yace "shikenan naji" abincin shi ya dauka ya cigaba daci ya cinye, fridge dinta
dake nan daki ta bude ta daukomai ruwa agora tabashi ya karba yasha sanan ya sauka kasa
wanan karan basa falon massallaci yawuce yaje yayo Isha sanan yadawo tareda Abba suka
shigo, afalo suka sami Ammi suka zauna sunata hira sai wuraren goma sanan Abba yacemai
oya yatashi yadau matarshi sutafi, Ammi ta tashi tawuce sama, dakinta takira Islam din tabata
abubuwa dayawa aleda sanan tamata addu'a suka fito har wajen mota suka rakata, Abba
dakanshi yabude mata gaban motar ta zauna yarufe duk suka daga musu hannu jitayi kaman
karta tafi sukabar gidan, amota shiru dukansu sukayi har suka kai gida tabude mota zata fita
batare daya kalleta ba yace "ki shirya gobe da safe zamu yola" yafita daga motar batare
dayajira cewarta ba bayanshi tabi ta shiga dakinta wanka kawai tayi ta kwanta.
Wuraren 8 suka tafi airport din bata wani dau kayaba banda hadadden lace din dake jikinta
orange da black shikuma shadda ce ajikinshi fara gizna sai uban kamshi yake, karfe goma da
arba'in jirginsu ya sauka a yola driver su daya kira yazo ya dauke su dayake Abba yafadi mai a
general hospital suke