Showing 21001 words to 24000 words out of 68809 words

Chapter 8 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf

M Shakur   

07 Oct 2025

1812

ajiyar zuciya Khaleel ya sauke ya bude takardar shiru yay ganin tambayar, Fa'iza tace
"karanto muji question dinka Yaya" ahankali yace "wakake so?" shiru yadanyi kafin ahankali
yace "My Eesha" sosai maganar ta daki Farida, hawaye ke kokarin zubo mata da kyar tai
controlling dinsu tadanyi murmushin yake daidai kiran Bala na shigo wayanta dan biyar da rabi
ya wuce har da kusan minti goma, tashi tsaye tayi ahankali tace "natafi anzo daukana" "dawuri
haka ai bamu gamaba" cewar Ilham murmushi tamusu tace "zan dawo wataran" hanunta Ihsan
ta kama tace "muje ki gaisa da Umman mu da Goggo mu fita daga dakin tayi tana dan waigen
fuskar Khaleel, sosai Umma taji dadi barin ma Goggo sai addu'a take mata saida suka fito Ihsan
tace "sis Eeshan dayake magana fa ta rasu, saisa dakika shigo rayuwar shi yanzu muke murna
sosai in sha Allah dake za'ayi" batasan Sanda ta sauke ajiyar zuciya ba, ta share kwallan daya
zubo mata murmushi Ihsan tamata sanan tarike mata hannu tarakota har waje, Khaleel ta gani
da Yusuf jikin motar Bala suna jira su fito, dan murmushi Khaleel yamata yace "thanks for
coming" murmushi tamai back yadaga mata hannu ta shiga mota suka wuce.

Yau Monday bata da lectures amma sabida Farida data kirata tamanta da presentation dinta
dake cikin file akan table Kuma yau zasuyi yasa ta tashi ta shirya tana tsaki.
Sauka falo tayi tadau presentation din akan table tafito Bala ne ya dauketa suka fito daidai yay
parking motar shi a kusa da gidan su batama lura dashi ba suka wuce, ajiyar zuciya ya sauke
sanan ya kunna motar ya bisu har AUN. Parking Bala yayi a parking lot tafito hanunta rike da
file dakuma waya data kara a kunne, kasa dauke kanshi yay daga kanta bata lura dashiba
sabida glass din motar shi tinted ce. Maida wayar tai cikin jaka tadan jingina da wata mota tasa
kumbanta abaki tanaci dan taga yadanyi tsayi, Farida data hango tadan taho da gudu gudu,
yasa ta karasa wajenta file din tabata ta karba ta bude tagani murmushi tayi sanan ta mikama
Islam hannu suka tafa tace "bari nai sauri an fara amma ba'akai group dinmu ba" tana fadin
haka tama Islam bye ta wuce ta tafi dadan sauri dawowa motar Islam tayi ta shiga Bala ya
kunna sukabar wajen. ba karamin mamaki yayiba dayaganta da Farida, wayar shi yaciro da
sauri neman number ta yafara dan baitaba kiranta ba, da kyar yagane number yay dailing,
Farida data kusan class dinsu tanajin ringing ta duba wayarta ganin superman ne wani farin ciki
ya rufeta da sauri tai picking, "Hello Mk" ahankali yace "how you" murmushi tayi tareda yin wani
fari ta cigaba da tafiya tace "fine, yasu Ihsan" shiru yadanyi kafin yace "inaso nadan tambaye ki
wani abu" baki tawani washe tace "ok" yace "ina parking lot din school dinku.." "school dinmu?"
ta katse shi yace "yeah, naganki da wata, I think kaman tabaki wani folder ne, who is she?"
"Farida Maikano" taji ana kiranta is time for her presentation kenan da sauri tace "Mk I will call
you later, zanyi presentation ne bye".

*JARABTA*

Maman Abd Shakur

27...

Sai yamma ranan tabar school tana komawa gida taci abinci bacci yay awon gaba da ita, Islam
bata tasheta sabida tasan bata salla.
Atare yau suka fito Bala ya dauke su waige waige tadinga yi awaje ganin yauma bata ganshi ba
tabe baki tayi tace "hala yagaji ya hakura ne" ahaka suka kai makaranta kowacce tai
department dinta.
Misalin 11 Mum na zaune adakin ta wayar wata baban kawarta senior lecturer ce itama ta kirata
dauka mum tayi tace "Hajiya hope baki shiga school bayau?" "ahh'ah ban shiga ba yau banda
lectures" matar tace "kin ganni nan ma fitowa ta kenan driving ma nake wlh wani good student
of mine yazo yake cemin nabar school din now, wai student zasuyi protesting sabida party
dasukaci SUG wai cuwa cuwa sukayi, an kinsan yaran nan Allah kadai yasan mesuka shirya"
arude mum ta mike tsaye tace "Hajiya sadiya yata na makaranta" katse wayar tayi tadau car
key dinta dake kan carbod tadau hijabi tafita arude, taja mota dawani irin gudu tafita, number
Farida tai dailing cikin sa'a ya shiga tana dauka tace "kina ina?" murmushi tai tace "gani nan
mum nama fito daga massallaci ne zan koma class" da sauri mum tace "Kifito yanzun nan kizo
baki gate, right now" yanda Mum tai magana yasa tace "Mum lpy?" tsawa Mum ta dakamata
"nace kifito bakin gate yanzun nan am coming right now" juyawa Farida tai da sauri tadinga
tafiya harta kai bakin gate tafita, tsayawa tayi abakin titi daidai lokacin Mum ta iso, wining glass
down mum tayi tace "get in" bude kofa Farida tayi ta shiga tana kallon fuskar Mum, kunna motar
mum tayi sukabar wajen ta kalli Mum tace "Mum lpy mesa kika kirani lectures gareni fa" batare
data kalleta ba Mum tace "riot students zasuyi i just got d information yanzun nan saisa nazo
daukar ki dakaina" da sauri Farida tace "Mum Islam fa? Turn d car muje mu daukota tana
lecture theater department dinsu sunajiran lecturer" tabe baki Mum tayi ta cigaba da tuki abinta,
"Mumm" Farida ta kirata dawani irin murya, ahankali tace "she always considered her mum"
mum ta harareta tace "and nikuma yata mace dayane which is u, Kuma kimin shiru anan wlh
kona wanke miki fuska da mari" wani hawaye mai zafine ya zuboma Farida tace "Mum I tot
kinason Islam, inhar bazaki koma mu daukota ba to ki saukeni nakoma koma menene
yasamemu tare" wani mugun kallo mum tamata tace "waya cemiki bana sonta?? Kawai dai
danka danka ne" sosai Farida taji kuka yazo mata da kyar ta hana kanta yi wayarta ta ciro daga
jaka Mum tace "wlh inkika kirata saina bata miki rai, ita yarinya ce once anfara riot din she will
find her way out so karki sake ki kirata, I know wat am doing" sosai taji tanajin haushin uwartata
ahankali tace "ni dama ba kirama zanyi ba, watsapp zan shiga" wani irin kukan zuci ta dingayi
tayaya yanzu zata taimaki Islam? Mk ne yafado mata rai, text yes text zatamai, da sauri ta shiga
massage tafara typing
"Mk zaka iya tuna fuskar wacce kace kaganmu jiya tare? If yes please help me get her out of
the school now, riot students zasuyi, please nasan wat am asking is a bit much but you are my
superman, taimakon mutane is ur periorty, tana theater din Home economics department, thank
you" ta turamai.
Yana kwance akan gado yana danna wayar sakon ya shigo mistakenly hanunshi ya danna
sakon ya bude dan baiyi niyyar budewa ba. "subhanallah" yafada bayan yagama karanta text
din da sauri yadau car key yafita daga dakin.

Zaune take achan sama, last roll din sit din lecture theater, bata sami gaba ba sabida taje

massallaci tai salla bata shigo ajin dawuri ba, sai hayaniya ake chaaa ana jiran malamin, Class
chairman dinsu daya fita siyo kati dan yakira lecturer awaya ne yaleko ta window yana
numfarfashi sama sama yay ihu yace "everybody run yaki sukeyi, wlh teargas zasu wurgo
yanzun nan" dudda yan ajin basu gane kan zancen shi ba amma numfarfarshin da akaga
yanayi yasa aka tattashi tsaye ana gudu, tashi tsaye Islam tayi tana Kalle kalle, ta window
sukaga wasu students dasuka fenfenta fuskokin su dan kar aganesu sun wurgo teargas ta
window yafado ajin, fuuufuufuu yafara wani irin popping yana fitowa yana hayaki, ihu yan ajin
suka fara, ture ture ake kawai kowa na neman takanshi ga waje yan protests din na dambe da
securities, hijabin ta tasa ta taushe hancin ta dan batama gani da kyau sosai tana sakkowa
daga matattakalan tsakiyar ajin, tari tafara yi sosai idanunta na juyawa, bangajeta akayi hakan
yasa tai gefe zata fadi wasu students dasuma sun haukace suna neman hanyar fita sabida tarin
dasuke suka kara bigeta luu taji hannunta yay kasa tai dayan bangaren, hakan ya bayyanar da
hancin ta ta shaka, ga idanunta dake wani azaban yaji ga hayaniya ga tarirrika Kala Kala, ga
ihun mata daban daban, tsugunnawa tayi anan tsakiyar stairs tafashe da kuka zuciyar ta kaman
zai fito sabida tsoro da fargaba, gawani irin tari datake yi tace "wayyo Allah Mamana" wayansu
student da basa ganine sukazo wucewa tuntube sukayi da ita hakan yasa dukansu kusan su
bakwai suka fada kanta duka kowa na tari.

Ba lallai nai typing gobeba sabida yau nakuma da mugun yawa lol😜
[6/16, 8:30 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

28 & 29

Da kyar ya iya gane department dinsu dan duk student din daya gani zai tambaya gudu yake, a
parking lot din department dinsu yay parking yafito yana waige waige, few people kawai yadan
gani suna gudu dan duk an watse, saikuma wanda yagani sunyi fenta jikin su suna dambe da
securities wasu kuma na faffasa windunan aji wasu na kona taya gadai sunan. Da dan gudu
gudu yake tafiya yana zagaye wajen da kyar yagano theater din, hayakin dayaga yana fitowa ta
windunan yasa yakarasa wajen da gudu, hanunshi yasa ya taushe hancin shi ya shiga baya
gani hakan yasa yaciro wayar shi daga aljihu ya kunna yana haskawa some student ya gani sun
faffadi ta gaban ajin harda maza suna tari, tadasu yafara yi yana kamasu yana fitar dasu waje,
tsayawa yay awaje yana dan fifita idonshi sabida wani irin azaban yaji dayake mai na teargas,
bude boturan shirt din jikinshi yay yacire rigar ya kulle hancin shi dashi, haka yadinga fififto da
students dayaga sun zuzzube yana hashaska fuskokin su amma bai gantaba, saida yagama fito
dasu sanan yafara hawa stairs din yana hashaskawa ga idanunshi dake mai zugi, wasu group
din student yagani again anan tsakiyar stairs din wasu akan wasu daddaga suna tari duk sun
kasa tashi, daddaga su yay yana kaisu waje, mai Hijabin daya gani a karkarshin su ta kife yasa
yaji kirjin shi ya buga dim! ahankali yadan juyo da ita, ganin fuskar Islam jini nabin goshinta
idanunta a kulle yasa jikinshi yafara rawa, jakarta data rataya ta wuya yay maza ya cire mata
yarike jakan a hannu sanan ya dauketa ya fara sakkowa daga matattakalan, wani kusa kujera
ne yaji yawani kece shi acinya saida wandon shi ya yage, bai damuba tafiya kawai ya cigaba

dayi yana sakkowa, fitowa yay daga ajin yana kallon fuskar ta, tunawa yay da randa Eesha ta
rasu, jijjigata yayi arude yace "dan Allah karki barni, please stay with me" harda gudu yahada
yay inda yay parking da ita, bude bayan motar yayi ya kwantar da ita ya rufe, rigar shi daya rufe
hanci dashi ya cire ya yar ya bude gaba ya shiga ya zauna tareda ajiye jakarta a kusa dashi, ya
kunna motar yabar school din dawani irin mugun gudu, wani hospital yagani akan hanya
Salama Clinic da gudu ya shiga yay parking daidai lokacin yaji wayarta dake cikin jaka na ruri
bude jakar yayi ya dauko wayar, yasaka a aljihun shi batare dayama kalli screen dinba yafito,
bude baya yayi ya dauko ta chak idanunshi sunyi jajir ya shiga cikin hospital din da ita, nurses
din dake reception ne suka tashi ganin yanda jini kebin fuskarta, wani gado suka turamai ya
kwantar da ita, daya daga jikin su ta ruga da gudu kiran Dr, daya Kuma ta cire mata hijabin
jikinta ta mikamai ahankali ya karba yana kallon fuskarta, Dr ne yafito ya karbi handglove yasa
yafara kokarin tsayar da bleeding din forehead din yadan waigo yace "maiya faru?" tari yadanyi
sanan yace "school dinsu ke zanga zanga shine akasa teargas" Dr yace "okay tana bukatan
madaran ruwa kaima haka" sanna sukai cikin wani daki da ita da sauri yabisu Dr ya nunamai
kujera yace "calm down sit and relax, zamuyi aikin mune, kaje ka kawo mana madaran" yajuya
ya shiga dakin ya rufo kofa, ahankali yakoma ya zauna akan kujera hijabin ta dake hanunshi ya
daura akan fuskan shi jin hawaye na neman zubomai, ringing yakara ji wayarta nayi ahankali
yacire hijabin daga fuskarta yaciro wayar ya kalli screen din "Abba" yagani, kasa picking yayi
harta katse, sake kira Abba yayi hakan yasa yay picking yakai kunne, "Ummi dafatan komi a
school lpy, hankalina yaki kwanciya sai tunanin ki nake?" shiru yayi baice komiba, Abba yasake
cewa "are u there Ummi?" da kyar ya tattaro courage yace "Abba muna asibiti?" yacigaba da
tari adan rude Abba yace "Asibiti? Wani Asibiti? Ina Ummi? Wake magana?" da kyar dan
muryan shi ta dinshi makogwaran shi har yaji yakemai yace "salama clinic, riot akayi a school,
tadan sami injury, muna asibiti" "innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ganinan zuwa" kashe wayar
Abba yayi, kasa hakura yay yatashi yaje gaban kofan yadan leka glass din, oxygen yaga an
mata fixing, sanan Dr na dressing ciwukan data samu a goshi da gwuwowinta da hannu,
komawa yay ya zauna idanunshi sunyi jajir ya dafe kanshi dayaji yana wani irin mugun sarawa.
Wani list wata nurse takawo mai tace "ga abubuwan da ake bukata, kaje ka siyo a pharmacy"
ahankali ya karba yafita yaje pharmacy ya siyo harda madaran ya kawo ya bata yasake zama
dan kanshi bala'in ciwo yake, ringing wayar Islam tayi hakan yasa ya amsa, Abba yace "ina
reception din asibitin a ina kuke?" Daidai Abba ya bude kofa ya shigo reception din sanye da
manyan kaya, tashi yadanyi tsaye dan baijin zaima iya tafiya ba sabida yanda kanshi ke
sarawa, Abba nagani shi yagane shi ganin wayar Islam a hanunshi yakara so inda yake yana
kallon kafar shi ganin yanda kafan ke jini yace "subhanallahi basu duba ka bane jibi yanda kafar
ka ke jini, nurse" ya kwalama nurse kira, wata nurse data fito daga dakin da aka shigar da Islam
ta karaso inda yake tace "thank God kakawota da wuri mun samu mun tsayar da bleeding din
she is out of danger, bacci take yanzu sabida duk wanda yasha teargas need sleep sabida
system dinshi yay relax" murmushi yama nurse din dan sama sama yake gane mema take
cewa sabida yanda yaji kanshi ke juyawa, ahankali yaji jiri na dibar shi yay baya zai fadi da
sauri Abba ya rikeshi yace "subhanallahi" turo gado nurse din tayi Abba ya kwantar dashi tace
"ai namaga mugun kokarin shi yasha uban teargas dinan har ya iya tuki ma yakawo ta ba
abinda ya samai, and I told him yasha madara fa" shigar dashi wani daki sukayi dan bashi
kulawa, fitowa Dr yayi yace "Kaine mahaifin ta?" Abba yace "eh, zaka iya zuwa ka ganta she is

fine amma bacci take" shiga dakin Abba yayi ya zauna akanta kumatun ta ya shafa tareda
sauke ajiyar zuciya yace "Alhamdulillah, banason wani abu yataba samin ki Ummi ke kadai
nake gani dakike tunamin da mahaifiyar ki" wayar shi ce tai ringing da sauri ya dauka ganin
Anty Hindu ce yace "Yaya ina asibiti fa, Salama clinic Islam ce duk taji ciwo wai students ne ke
riot a makaran tarsu, shine wani bawan Allah yakawota shima gashinan ba lpy".

"Maman Ibrahim Islam na asibiti fito fito mutafi" arude Mum da Farida data fashe da kuka suka
fito daga daki, Mum tace "meya faru?" Anty Hindu tace "baban su yake cemin wai zanga zanga
ake a makarantar su, Islam duktaji ciwo mutafi" Hijab Farida ta dauko zata bisu Mum tamata
tsawa tace "yanzun nan Sameer zai dawo daga school dawa zai zauna idan yazo? Wuce ki
zauna my friend" fashewa ta karayi dawani irin kuka Anty Hindu tace "yi shiru jeki zauna ai
zamu dawo, saike kije yanzu dai kar Sameer yadawo ba kowa gidan" fita sukayi sukabarta.

Abba ne ya shigo dasu sukaje dakin Islam sosai jikin Mum yay sanyi bata taba zatan abinda tayi
zaiyi resulting to this ba. Tashi Abba yayi yace "bari naje naduba bawan Allah daya taimaketa"
Anty Hindu tace "muje nima nagode mishi daga nan" Mum suka bari tareda Islam dake bacci
suka fita daga dakin, dakin da aka kwantar da Khaleel Abba ya bude ya shiga, bacci yake, Anty
Hindu ne ta kallai sanan ta kalli Abba tace "kaga shine yaron danake fadama ranan nan". Sake
kallon fuskar shi Abba yayi daidai lokacin wayar Khaleel dake gefenshi akan bed yay ringing
dauka Abba yayi yaga an rubuta Abba ajiki, Anty Hindu tace "waye?" "baban shine?" Anty
Hindu tace "to kadauka mana ka fadamai dansu na asibiti yakamata su sani" fita Abba yayi dan
yadau wayar. Bayan yagama wayar ya wuce ya biya kudin komi both ba Khaleel da Islam sanan
yadawo ciki, Abba ne yasake kira hakan yasa yafita dan shigo dasu, ba karamin mamaki yayiba
dayaga dan Aminin kasuwancin shine, musabaha sukayi tareda kara jajanta lamarin sanan
suka shiga ciki.
Tareda Abba da Yusuf Babban Islam suka shigo dakin da sauri Yusuf ya karasa kusa dashi ya
zauna Abba yay ajiyar zuciya yace "Allah sawake, ya yartaka dafatan dai babu wata matsala
babba" Abban Islam yace "a'a Alhamdulillah bacci ma take, kampanin nanko sun kiraka?
abubuwa sunsa na manta ban kirakaba" kafin yay magana Anty Hindu tace "kunsan junane"
murmushi dukansu sukayi Abban Islam yace "amini nane muna kasuwanci tare" gyada kai tayi
tace "masha Allah" Abba yace "muje ko mudubata" tashi dukan su sukayi harda Yusuf suka
shiga dakin da aka kwantar da Islam, ba karamin mamaki Yusuf yay ba dayaga yanda Islam ke
kama da Eesha ko wanan ce wacce Khaleel yataba cewa yagani? Ajiyar zuciya yadan sauke
yace "bambamcin su kawai shine wanan tafi Eesha jiki kadan" . Gaisawa da Mum Abba yay
yamata ya jiki sanan suka baro dakin.

*JARABTA*

Maman Abd Shakur

30...

Da magrib yatashi yana karema dakin kallo Yusuf daya gani akan kujeran dakin yana kallonshi,

yace "wat happen?" dan murmushi Yusuf yamai yace "kasha uban teargas ne ka sume ma
mutane" tashi yay ya zauna yana dan yatsine fuska sabida yanda ciwon kafarshi kemai zafi,
Yusuf ya nunamai wata white t-shirt daya fita ya siyomai yace "ga riga kasa ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login