Showing 6001 words to 9000 words out of 68809 words
Chapter 3 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf
miki makeup din, bari nakaima Khaleel wristwatch din" tafita daga dakin a
tsakar gida taci karo dasu Mama da yayyin ta, kallonta daga sama har kasa Mama tayi tace "ina
zaki haka" Kaman zatai kuka tace "Mama abu zanbama Khaleel a waje plzz" Mama zatai
magana Yarta dasuke Kira da inna asabe tace "tafi kinji Eesha" ta kalli Mama tace "kibarta
mana daga yauma gidan mijinta zata koma tabarmiki gida, tunda yana kiranta aisaitaje" da sauri
tafice tana dariya dan tasan Mama da hanata zatayi, hango su Baba tayi a barander waje hakan
yasa taja gaban hijabin ta dan karsu ganeta tazo ta wuce tafita sadaf sadaf daga gate din, da
sauri take tafiya hartakai bakin titi, yana tsaye a shagon ya hangota zata tsallako kasan cewa
kofar glass ne a shagon, murmushi yayi yacema Yusuf "am coming my queen wanna see me"
hararan shi Yusuf yayi shikuma yajuya yafita daga shagon, tana hango shi ta sakin mai
murmushi, murmushi yamata sanan ya mata alamu da hannu ta tsaya bari shi ya tsallako,
murmushi tasake yi ta make kafada sanan ta kalli titi ganin babu wani abun hawa yasa ta shiga
titi ta tsallake first lane, hakan yasa shi ya tsaya yafasa tsallakowa yana mata tattausan
murmushi. Kaman ance ya waiga nan yaga wani trailer daya dauko yashi yataho dawani irin
mugun gudu tsaki yayi yace "Wayan nan reckless drivers dinan ko" alamu yakara yima Eesha
da hannu ta tsaya, gyadamai kai tayi Dan trailer kawai take jira yawuce ta tsallake titin nabiyu,
kara taji hakan yasa ta kalli trailer da sauri tayan gaban ne yafashe hakan yasa motar fara
kwana, ganin motar yayo dakalin tsakiyar titin datake tsaye zai fadi akai yasa tai ihu
"subhanallah Wayyo Allah" tai baya da sauri ta fada titin bayan ta, kararrarraaa naji wani irin
kara dayasa gabana bugawa.
[6/7, 11:23 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
6&7...
Dawani irin mugun gudu ya tsallako titin bai damu da babban trailer dayama fadi ba, tsayawa
yayi a akan dakalin tsakiyan titin ganin motoci kusan uku su bubbuge juna, waigawa yayi sanan
yasake waigawa again dan baiga Eesha ba, ahankali yace "kodai taji tsoro ne ta koma gida?"
hanunshi yaji anrike da sauri ya daga kai Yusuf yagani ya rikemai hannu gam, gasu Ibrahim tela
da abokanayen shi yan wajen aiki da suka daura hannu aka suna kallon titin ganin yanda
mutane harsun cika wajen suna ku matsa aciro ta tana numfashi, wani irin fuzge hanunshi yayi
daga Yusuf ya shiga titin, mutane kawai yake turewa kaman zararre yana kutsawa cikin crowd
din, Yusuf da abokanansu ne suka bishi da sauri ture mutanen yayi duka harsaida yakai dadai
saitin wata bakar jeep, kasa yabi da kallo kaman zararre ganin jini nabin wajen, da sauri ya
tsugunna ya leka kasan motar, hango Eesha yayi hakan yasa ya tashi da sauri kaman zararre
yace "ku matsar da motar da sauri masu motocin suka shiga, ahankali aka mammatsar da
motocin, tsugunna nawa yayi ya jawota ya daura kanta akan kirjinshi yana kallon fuskarta yama
kasa magana, murmushi tamai jini nafito wa daga bakinta, kokarin yimai magana take amma
takasa da sauri Yusuf ya tsugunna ya dafa kafadar Khaleel ahankali yace "Aisha kice La'ilaha
illallah Muhammadur rasulullah" bakinta ne ke rawa haka Yusuf ya dinga maimaita mata harta
karba, da kyar ta daga dayan hannunta da ledan agogon ta ke ciki ta daura akan hanun
Khaleel, sanan hanunta yay lagwal.
"Abba Abba" kanin Eesha ne Ibrahim yazo da gudu da farin shaddan anko dinshi ajiki, Abba
dake tare da abokanan aikin shi yace "lafiya Ibrahim" yana haki yace "Abba anyi hatsari sosai
akan titi wlh" subhanallah Abba yafadi shida abokanan shine suka tashi dan zuwa dubawa,
Karo sukaci da Babban Khaleel da wanshi suma zasu dubawa hakan yasa dukan su suka
dunguma zuwa titin.
Salati gabaki dayan crowd din wajen suka dauka, kowa ya kasa motsi barinma mutumin daya
bigeta wanda yake arne yaci suit jikin shi yay mugun sanyi, ahankali Yusuf yakai hannu ya
rufemata idanu, Khaleel ya kalla dayaga kallonta yake kaman zai cinyeta yace "Khaleel Khaleel"
ko kallon shi Khaleel baiyiba har lokacin yana tsugunne da ita akirjinshi. Tashi tsaye yayi
idanunshi sun xhanza launi, hango su Abba yayi kana ganinsu kaga tashin hankali karara akan
fuskokin su, ahankali suka tako zuwa wajen tsugunnawa baban Eesha yayi ya kalleta shiru yayi
yana addu'a sanan ya kalli Khaleel yace "Khaleel" ko dago kai Khaleel baiyi ba har lokacin
fuskar ta yake kallo yay shiru da sauri Ibrahim tela ya koma shago ya dauko wata katuwar
tabarman shi dayake yanka dinki akai, karaso wa yayi yamika ma Baban Khaleel ya karba,
zuwa wajen yayi ya warware, ahankali baban Eesha ya mika hannu zai karbe ta wani irin ihu
yayi yasake riketa yace "karku tabamin matata, bacci take" dariya yayi ya kalli fuskar ta yace
"My Eesha sleep kinji idan kin tashi saimutafi, kitashi kafin karfe daya fa dan lokacin zaa daura
mana aure" Ahankali baban Khaleel yake furta "innillahi wa innailaihi raji'un" ahankali yace "Son
saketa zamu kaita gida amata sutura" ko kallon mahaifin nashi baiyi ba, hakama Baffan shi
Abba babu wanda ya kalla cikin su, Yusuf ne da abokanansu su kusan takwas suka rirrike shi
da kyar aka dauketa akai gida da ita, Khaleel kam ahaka abokan shi da Yusuf suka rirrike shi
yana maganganu dako gane meyake fadi basayi suka taho kofar gidan su Eeshan dashi.
Ance kowani rai mamaci ne, mutuwa bata baka notice, once lokaci yayi you just have to go, mu
kusanci Allah mu nisanci zunubai, muyawaita istigifari bamusan kozamuga gobe ba.
Babu wanda ya yarda Eesha bata, Mama gani take ya'ta da yanzun nan tazo tacemin zata fita
dama ajali ke kiranta?? Khadija kam kasa magana tayi kuka kawai take, su Ihsan dasu Faiza da
kanin Eesha bansan wama ke lallasan wani ba, Maman Khaleel da Umma da Mujiba ma duk
zuwa gidan su Eesha sukayi. Ko alwala ma yima Khaleel akayi sosai yafita hayyacin shi hanunshi damke da ledan da Eesha
tabashi yana wasu irin surutai, haka aka mata Salla aka kaita, aka dawo shikenan fa duniyan.
Yauce Rana uku da rasuwan Eesha, babu wanda zaiga Khaleel dabazai yi kuka ba, koka zo
gaisuwa bakai niyyar kuka ba shiza kagani kai kuka, ko abinci yakici, ruwama saidai abashi
wanda ya shiga ya shiga sauran su zube akasa dan baya zukan ruwan da kanshi, ko wanka
yakiyi balle ma wani abun, bayama kowa magana saidai yay ta maganganu shi kadai, addu'a
ake mai bana wasaba amma har lokacin ba chanji, Maman Eesha duk idan ta kallai saitai mai
kuka, Ammin shi kam baa cewa komai.
Misalin 1:25 na dare kowa na dakin shi, karan fashe fashen abubuwa ne yasa kowa ya mike
daga kan gado dan dama bawani baccin kirki kowa keyiba, afrigice Yusuf ya farka gefen shi ya
duba ganin babu Khaleel dake kusa dashi yasa yay jumping daga kan gado yafito daga dakin,
cin Karo yayi da Abban shi da Umma, Abban shi zaiyi magana saiga Daddy da Ammi sun fito,
su Ihsan ma haka atare suka dunguma suka sauka kasa kitchen sukayi dan nan sukejin karan.
Shiga sukayi da sauri Khaleel suka gani dauke da tabarya a hannu yana faffasa koma me
hanunshi yakai yana ihu yana magana "ba Kaine bakin jeep dinba Kaine my Eesha ke
karkashin ka, ku ku 5 ne" tawarwatsa kwanuka kawai yakeyi, ko kallon su Abba dake kiranshi
baiyiba, Yusuf ne ya fizge tabaryan ya ijiye hakan yasa ya ture Yusuf, da sauri Ammi ta juya ta
koma falo danji tayi wani mugun kuka yazo mata, Ihsan ma fita tayi da sauri jikin Ammi tafada
sai kuka da kyar Umma ta lallashe su, wani irin murmushi Mujiba tayi mai wuyar fassara kafin ta
dawo falon ta zauna. Baban Eesha Abba yakira dan babban likita ne shi, within 2min ya iso, da
kyar su hudun suka iya kama Khaleel dubashi baban Eesha yayi kafin yamai alluran bacci, nan
bacci yay gaba dashi akan dogon kujera.
Ajiyar zuciya Abban Eesha yayi kafin ya kalli Abba yace "I think Khaleel yay developing mental
issues".
[6/8, 5:37 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
8&9...
"But gobe in Allah ya kaimu da safe sai mu kaishi clinic dinmu a dubashi" kowa kasa magana
yay afalon da kyar Abba yace "mungode" Sallama yamusu yatafi zuciyar shi cike da tausayin
Khaleel, Aisha bata amma Khaleel kai Allah gamu gareka, girgiza kai yayi yatafi kawai. Gabaki
dayan su a falon suka kwana dan sosai Khaleel ke surutai cikin bacci. Around 8 baban Aisha yazo shirye cikin suit bakake da kyar Yusuf suka fito dashi suka sashi
amota sanan aka tafi asibitin wani babban likita daya kware a bangaren mental Baban Eesha ya
kaisu wajen shi, nan yazo gaban Khaleel ya tsaya ya dudduba shi sanan ya Kalli Daddy dayay
shiru yana kallon ikon Allah yace "Ya sunan shi?" Abba ne ya iya yay magana yace
"Muhammad Khaleel" rubuta wa Dr yay a file din daya shigo dashi ya maida duban shi ga
Khaleel daketa motsi da bakin shi, "Khaleel" Dr yakira sunan shi, shiru kaman ma bada shi
akeba, Yusuf ne ya matso wajen ahankali yace "Dr tun randa abin yafaru bai kara mana
magana ba, is as if baima sanmu ba" rubuce rubuce Dr yayi, ya dauko wani abu kaman bindiga
ya daura akanshi nakusa 1min sanan ya cire, rubuce rubuce yayi sanan yamika musu
prescription sheet yace "asiyo mai wanan magungunan" Ahankali Abba yace "meke damunshi?"
murmushi Dr yayi yace "post traumatic stress disorder, but zai dinga zuwa therapy bayan kwana
bibbiyu, and zan sashi a medication, bayan 2 weeks inhar babu improvement sai musan abin yi"
godiya sukamai sanan Yusuf yatafi siyo maganin suka tafi gida.
Yau kimanin 2 weeks kenan gidan nan babu wanda bai rame ba sabida Khaleel, babu wanda
yake yadda dashi baya wanka, baya ma kowa magana abinci ma ko Ammi tasamai abaki
wanda yaga damane zai hadiye sauran akasa, har yanzu Baffa da Family shi basu komaba dan
bazai taba iya tafiya yabar kaninshi da wanan wahalar ba yasan yanda kaninshi keson Khaleel,
bashi kadai ba duka familyn ma akwai wanda bayason Khaleel ne.
10 a office din Dr yamusu ajiyar zuciya Dr ya sauke kafin ya Kalli Abba yace "Sir Khaleel yaki
responding to treatment, inda acema ya yarda yay magana ne ko awajen therapy dinshi ne it
would have been a great difference dakomi yazo mana da sauri" "to to Dr yaza ayi yanzu?"
cewar Abba "Alhaji yanzu is time for the second treatment abinda nakeso daku shine ku cire,
kokuma ku fitar dashi daga environment din incident dinan, inma da hali yabar Abuja for now, ai
zaku iya daukar mai excuse a wajen aiki na medical leave ni zanmai recommending, duk wani
abu dazai dinga tunama kwakwalwan shi Aishan ku nisan tashi daga abin, kana ganinshi ahaka
kome daya dangan ci Aisha yasani so ku nisan tashi daga memory and ku dinga cheering
dinshi up now more than ever he needs love da pampering kome yakeso kumai koma menene
shizai sa yay healing fast" godiya sosai suka mai sanan suka tafi.
Koda suka kai gida kwantar da Khaleel sukayi a dakin shi Yusuf ya zauna dashi, Ammi dasu
Umma Abba ya kalla yace "kubiyo ni" falo suka fita suka zazzauna Abba ne ya Kalli Daddyn
Khaleel yace "inason na wuce da Khaleel yola kaman yanda Dr yabamu shawar anisan tashi
daga nan koya kagani achan saimuga Yaya zaiyi healing idan babu improvement saimu fita
dashi waje koya kagani" gyada kai Daddy yayi ahankali yace "to Yaya nima nafison hakan, ke
Amina saiki hadamai kayan shi ko" gyada kai Ammi tayi da sauri, Ihsan da hawaye ya cika mata
ido tace "Abba nima zan biku" Ammi ne ta kalleta tace "exam dazaku fara next week fa? Don't
worry duk lokacin dakukai hutu saikuje ku dubashi" murmushi Umma tayi tace "addu'an ku
Khaleel yafi bukata yanzu bawani abuba, Alhaji tun jiya Gwaggo ke kirana tana tambayana
yaushe zamu dawo bansan mezan cemata ba" "banason na tada mata da hankali ne, idan
mukoma ma fadi mata meya faru" wani irin murmushi Mujiba tayi tana kallon fuskar Daddy
Khaleel tana kada kafa.
Washe gari jirgin Rana sukabi suka koma yola, haka gidan ya dawoma Ammi da kanen Khaleel
wani iri, ba karamin wani iri Ammi takeji ba da kyar ta lallaba kanta ganin zazzabi nason kama
su Ilham.
Yau kusan watan shi daya kenan a yola, yana zaune a dakin Goggon wacce ta hadamai fura
take bashi abaki, yana sanye da farin t-shirt wacce ba karamin dambe suka sha da Yusuf ba
kafin yabari asamai, ahankali Goggo ta ijiye kofin furan, tadau handky ta share mai bakin shi da
rigar jikin shi dan gabaki daya fura zubewa yake wanda ya shiga bakin shi ne yake lashewa,
Abba dake tsaye akansu ta kalla tace "Sama'ila ni ni wlh jikan nan nawa tausayi yake bani, ace
yaro yafita daga hayyacin shi baima sanmuba yanzu" kecewa tayi da kuka sosai ta kwance
bakin zani tana share fuska zama Abba yayi yace "to Mama idan kina kuka haka mumuce
mene, namayi magana da baban shi dazunan, jibi zamu fitar fashi waje saudiyya zamu, akwai
wani likita dana sani a wajen yace mukawoshi in sha Allah zai sami lpy har magana zai fara" da
sauri Goggo tace "dagaske Sama'ila" gyada mata kai Abba yayi tace "Alhamdulillah" shafa kan
Khaleel din tayi tace "Allah nagode ma, dazaran ya warke zan nemo yarinya yar kirki mai
hankali da natsuwa na auramai hakan zaisa ya wartsake" tashi Abba yayi yace "bari nadan fita"
"adawo lahiya" part din Mujiba yatafi a uwar daki ya sameta tana kan gado tana watsapp baiko
kalleta ba ya bude wardrobe babban rigar shi ya dauka yasa sanan yace "kihada min kaya jibi
zamu fita da Khaleel waje" adan zabure ta kalli Abban tace "Alhaji maisa zaka wani kashe kudin
ka Yaron nan yariga ya haukace bazai taba warke wabafa" wani irin kallo dayamata yasa
tadanyi murmushi ta kwantar da murya tace "bahaka nake nufi ba, ni gani nayi tayaya treatment
din zaiyi progressing bayan baya cewa uffan balle asan meke mai ciwo daka bari yafara
magana tukun, duk kawani damu saikace Yusuf ne baida lpy" wani irin kallo ya watsa mata ya
nunata da yatsa cikin fushi yace "ki kiyaye ni Mujiba, ki kiyayeni fa, and Yusuf da Khaleel basu
da bambanci awurina duk yayana ne, baki isa kiraba kan family naba kinajina ko" fita yay daga
dakin ranshi abace, sosai abin ya konama Mujiba rai, ai wlh yanda naso kaninka yakini,
dasonshi nake wahala da dawainiya, bankara ganin farin ciki ba, haka danshi ma zai wahala
bazai taba samin farin ciki ba arayuwar nan ba, ko Allah ma nabaya na, ai saisa ya kashe
yarinyar batare danai komiba, warke wa dai bazaiyi ba bi'iznillahi, koma ya warke farin ciki
yakare mai arayuwa. Tsaki tayi ta wurgar da wayar ta tashi ta shiga bayi.
Saudiyya.
Ba karamin cigaba aka samu a treatment din Khaleel ba, dan yanzu dazaran yaji kiran salla zai
tashi yay alwala yayi, magana ne idan anmai saiyaga dama zai amsa, gabaki daya ya chanza
ya dawo shiru shiru kaman ba Khaleel mai rahan nan ba, idan Ammi tabashi abinci zaici kadan
ya ijiye mata, idan yagaji ya kwanta ya daura kanshi akan cinyar ta ya lumshe ido, sosai aka
dage damai addu'a dudda haka sunji dadin yasoma samin cigaban nan. Dr yahana amai
maganan Eesha ko kadan. Ganin cigaba sosai yasa Dr ya sallame su suka dawo Nigeria Ammi
da Daddy suka wuce Abuja, Baffa da Yusuf suka wuto dashi nan yola.
[6/8, 5:37 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
10...
Da sallama ya shigo dakin Goggo, ganinshi dayayi kwance akan katuwar dogon kujera ear
piece akunenshi ya lumshe ido yana sanye da white t-shirt sai dogon black jeans yasa yakarasa
shigowa dakin, hannu Yusuf yasa ya cire earpiece din daga kunenshi ya jawo hanunshi ya
zaunar dashi bude idonshi yayi ahankali yadaura akan Yusuf yay shiru as usual batare dayace
komi ba yana kallon shi da idanunshi masu kama da madara, hanunshi Yusuf yaja yana kokarin
tadashi tsaye yace "zomuje karakani jor let's go out" kaman marason yin magana yace "am not
going" fitowa daga uwar daka Goggo tayi hanunta rike da goro tace "waye yanzu yatada min da
Babana" baki tarike tana hararan Yusuf tace "shine kadatashi Yusufa? Yaro na hutawa abinshi
dan bakin ciki" wajen Goggo yaje yace "goggo tayani mai magana please kicemai ya rakani
mufita" zama kusadashi Goggo tayi tace "Babana katashi mana kabi dan uwanka kufita, yau
kusan wata shidafa kenan baka taba fitaba banda masallaci, jibi kanka kaki aski iye, aya aya
tashi kabishi kafin kadawo zan dafama dambu dakaina kaji Dan'nan" ahankali shima Yusuf yace
"please Bro for my sake" shiru yadan yi sanan yay musu murmushi yace "okay" sabida murna
Yusuf saida ya rungume Goggo suka tafa, tashi sukayi Goggo tarakasu har wajen mota tana
musu adawo lafiya kafin sufita tadawo cikin gida.
Dukan glass din window Mujiba tayi zuciyar ta nazafi wani irin ihu tayi ta cire dankwalin kanta
tayar "no.. No ooo" kaman mahaukaciya taje wajen fridge ta bude goran ruwa ta dauko ta bude
tasha sanan ta ijiye, jin har lokacin zuciyanta bai dena zafiba yasa tace "nooooo nooo yaushe
har yawarke daga haukan?? Yaushe, dahar zai fara fita" wani irin ajiyar zuciya ta sauke tace "I
have to do something bazan taba bari ka warke daga haukan dakake ba, banason nataba ganin
koda digin farin ciki a fuskan iyayenka khaleel, inaso mahaifinka ya daddana azabar dayasani
na shiga" goran ruwan takara dauka tasha ruwa sanan ta ijiye tace "Khaleel nadau alkawari
bazaka taba samu farin ciki da haske arayuwan kaba har abada, yanda mutuwar Aisha yasa
kasami ciwon hauka kashiga kunci da bakin ciki ahaka rayuwar ka zata kare harka koma ga
ubangijin ka wanan alkawari nane ni Mujiba agareka" tawani fashe