Showing 45001 words to 48000 words out of 68809 words

Chapter 16 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf

M Shakur   

07 Oct 2025

1808

wasu
hawaye dasuke gangarowa ta gefen idon, da sauri ya kwanto da kanshi daidai saitin fuskar ta
yasa hannu ya share hawayen ahankali yace "u don't want me to go" daga kai tayi wanan karan
tana kuka sosai, "okay nafasa tafiya" yafada tareda zama ya riko hanun nata data rike shi dashi
yana shafawa kadan kadan, dayan hanun Kuma yana share mata hawayen datakeyi sanan ya
ijiye hanun agefen filon yana shafa gaban goshin ta, ahankali tasanya fuskarta cikin hanun
tareda sauke ijiyan zuciya sanan ta lumshe ido within 3min bacci yay gaba da ita, numfashin ta
dayaji yana sauka ahankali ahanunshi yasa yagane tai bacci, ahaka wata nurse ta shigo dakin
cikin harshen turenci tacemai lokacin tafiya yayi yatashi yatafi itace mai kula da ita, kallon
fuskarta yayi kafin ahankali ya zare hanunshi ya mike tsaye tareda sanya hannayen acikin aljihu
ya tsaya yana kallonta kara komawa yayi ya tofeta da addu'a sanan ya juya yafita daga dakin
yana leken fuskarta. A reception yasami Ihsan sanan suka fito daga asibitin taxi yatare musu
suka shiga, tafiyan kusan 20min sukayi sanan sukai parking agaban wani dan madaidaicin gida,
kofar ya bude ya shiga Ihsan na biye dashi Yaron dazu suka tarar yanata mopping kasan dakin
murmushi yamai yace "weldone Raymond" zama akan daya daga cikin kujerun yay yana kara
karema gidan kallo, babban falone da akamai penti off white irin dakunan turawan nan saita
bangare daya kuma kitchen ne wanda komi yake a gyare, sai dan corridor da dakuna biyu ne
awajen kowanensu da bayi aciki, saida Raymond yagama yamusu sallama yatafi shikuma
yatashi ya shiga daya daga cikin dakunan hakan yasa Ihsan ta tashi itama ta shiga dayan dakin
dan yin wanka tai salla saita fito tadan sama musu abinci.

Zaune yake shida Anty Hindu suna magana akai sallama jin muryan su Abban Khaleel yasa
yatashi tsaye yana murmushi tareda basu izinin shigowa ganinsu tareda Farida idanunta sunyi
zuru zuru yasa ya daure fuska ya nuna mata kofa "fitan min daga gida, fita nace" fashewa tai da
kuka ta tsugunna jikinta har wani barbar yake tace "Abba dan Allah kayakuri kayafe min" Su
Abban Khaleel ne suka saka baki suna tausasa shi da kyar ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Anty
Hindu gyadamai kai tayi hakan yasa ya kalleta ya gyara murya yace "shikenan na hakura amma

inada sharadi daya kifito da miji nan da sati biyu kokuma nahada ki daduk wanda naga dama
namuku aure" sosai take kuka tana share ido, Anty Hindu sai wanke ta da harara take tace
"tayaya ma Farida har kikasan da sniper kika bama yar uwarki, Farida bamu baki irin tarbiyan
nanbafa, maisa kika bama yar uwarki guba?" shiru tayi tana matso kwalla Anty Hindu tace
"badake nake magana ba" da sauri ta share hawaye da kyar tace "ranan da Bala ya kaini gidan
tun kafin yay parking akofar gidan mukaga wata mata a tsaye baka tanada dan jiki, yana
parking nafito zan bude gate na shiga sai kawai naga takira sunana Farida, nace mata Na'am,
na tambayeta ya akayi kikasan sunana, murmushi tamin tace ai taganni randa nazo gidansu
get-together, shine tacemin wai yanzu na yarda kanwata ta aure wanda nakeso bazan yi
komiba niba mace bace, shiru nayi bance mata komiba, shine tacemin Ina sonshi? Ahankali
nace eh, tace amma ai nasan idan kanwata ta mutu zai aureni nace mata eh, shine tabude jaka
tabani sniper tace gashinan nasan yanda zanyi nabata idan tamutu ai shikenan zan auri wanda
nakeso" shiru tadanyi tana goge hawaye kowa na falon na kallonta ahankali tace "wlh Abba
banyi niyyan bata ba, nidai kawai na karba ne dan kaman tamin asiri tana bani na karba nasa
ajaka na shiga cikin gidan, to Ina ganin fuskar Khaleel dinne shine shine wlh bansan meya
shigeniba shine na a.. " takasa karashe maganan tana kuka sosai da kyar tai shiru Abban Yusuf
ne yace "matar tafadi miki sunanta?" girgiza kai tayi tace "a'a tadaice taganni randa nazo get
together, ni bansan taba" shiru kowa yay na falon Kafin Abban Khaleel yay dan murmushi yace
"komi yawuce Allah ya yafemana gabaki dayan mu, tashi kitafi abinki" Ahankali ta tashi tafita
daga dakin dakin Mum ta shiga ta rungume Mum tana kuka, tureta Mum tayi ta harare ta tace
"Farida kinsan kai, haba Farida a ina kika koyo wanan mugun halin, tausayi kawai kikabani
saisa na rokesu ayafe miki amma da wlh bazan yiba, haba wanan bakin hali har ina" shiru Mum
tayi jin tasake rungume ta tana kuka kaman zata mutu hakan yasa tashiga bubbuga bayanta
tana bata hakuri tace "bakomi zakaso ka sameshi ba Farida, Allah ya jarabce ki dason bawan
Allah nan amma hakanan zaki dau dangana danba mijinki bane" tai maganan tana share mata
hawayen dake zuba.

Daga Abban Yusuf harna Khaleel jiki asanyaye suka dawo gida kowanne su na zargin mutum
dayane amma kasancewa babu proof yasa kawai suka share suka dawo gida.
Da sallama ya shiga part dinta, dakinshi direct yay niyyar wucewa ganin bai ganta a palour ba,
daidai ta kofar dakin ta dake rufe yazo wucewa dariyar dayaji tanayi yasa ya mika hannu zai
bude handle din tsayawa yay chak batare daya bude kofan ba jin tai dariya tace "ai ingaya miki
shinai niyyan kashewa amma na rasa ta yanda zan shiga gidan, kinsan ba shiri nake dashiba
idanma na shiga nace mene, saiko ga kanwar matan, kinsan ko lokacin datazo gidanmu nazaci
itace yakeso ashe ba itabane kanwartane yakeso, dan naji lokacin dasu Ihsan suke labarin
yanda yar ke sonshi kazakaza kaza, shine Ina ganin yar nai instigating dinta sosai, na bata abin
nace tabama kanwar tasha kinga ai idan tamutu zai aureta" dariya tasake yi sosai sanan tace
"wawiyar ta yarda not knowing fully dat kaina nake taimaka nasan dai yanda yakeson mai kama
da Eeeshan nan tunda bansami daman kashe shi ba idan na kasheta kinga ai za'a koma gidan
jiya" wani dogon uban tsaki taja tace "ke bata mutu bafa, amma dai rai a hannun Allah dan
mutum mutumin ce yanzu, batada amfani" Ahankali yaji tace "hmmmm bazaki gane bane
takano, wlh Allah ya jarabce ni dason kaninshi ne tun randa yazo dashi tadi wajena, na fadinma
kanin amma shi yama tsaneni haka na auri wanshi Ina dawainiyar sonshi kirikiri sabida ni

yadena zuwa yola yanzu ma badadan bikin danshi ba da bazai zoba Kuma wlh bakigani ba ko
kallo ban isheshiba saisa nace zan dandanamai azabar rayuwa, zanso yasan yakake ji idan
karasa abinda kake mugun so, Kuma Kinga yanda yakeson yaronne shikadai ne namijin shi, ai
kinga idan na kashe Yaron koya karashe rayuwan nashi a haukace sabida mutuwar mai kama
da Eeshan ainaci riban abinda mahifin shi yamin, yanzu ma idan bata mutuba zansan abinyi"
dan dariya tayi tace "to shikenan ki gaidamin dashi idan yafita ki kirani, takano tawa kenan" tai
wani uban shewa. Shirun dayaji yasa ya bude kofa ya shiga dakin adan firgice ta kallai tanadan
murmushi tace "harkun dawone Alaji?" yafi minti biyu yana kallonta sanan yace "na sakeki saki
biyu, ba wanan kadai ba zanje nai filling complain akanki a police station ba Khaleel kadai ba
koma waye awanan family wani abu yasake sama keza'azo akama, kije keda Allah" yana fadin
haka ya rufomata kofar bam yabuga yawuce, da gudu tabiyoshi har tsakar gida tana bashi
hakuri amma ko sauraronta baiyiba saima sake juyowa dayayi yace "kifara tattara yinaki yinaka
kibar min gida, karki sake kitafin min da ya" yana gama fadin haka ya shiga mota yabar gidan,
ahanya ya kira Abban Khaleel yace "maisa baka taba fadamin halin Mujiba ba, abinda tama"
dariya yadanyi sanan yace "Yaya nazaci yarinta ne" murmushi Abba yayi yace "kazo kasaman a
office muyi magana".
[6/25, 2:17 PM] Maman Jedda: *JARABTA*


Maman Abd Shakur

59 & 60

🇬🇧
Taxi yatare ya shiga motar suka fara tafiya wani shago ya hango da ake saida teddies masu
kyau cema mai taxi din yayi ya tsaya ya shiga shagon wani jan teddy yasai mata mai kyau da
taushi yabiya kudin yadawo mota ya shiga ya zauna yana kallon teddy din yanda yarike flower.

Ahankali yatura kofar ya shiga dakin bata kangadon ma hakan yasa ya ijiye teddy akan gado,
maganar nurse dayaji tana cewa gently raise your head yasa yaja kujera ya zauna yana kallon
kofar bayin, wajen 3 min da zaman shi sanan nurse din tabude kofa ta gunguro ta akeke an
chanza mata rigar asibiti zuwa pink amma desame design ne fuskar ta dadan ruwa ga nurse din
rike da karamin farin towel a hanunta saida takawo ta bakin gadon sanan nurse din ta gaida
Khaleel daya kasa cire idonshi akan Islam dan gani yay bakin yadan sabe jan dayayi ya ragu
sosai, tsugunnawa nurse din tayi zata share mata ruwan fuska da towel din hanunta ya tashi
tsaye yana tattare hanun doguwar rigar dayasa yace "may i" yay maganar tareda mika ma
nurse din hannu murmushi tai tace "sure" tabashi towel din tsugunnawa yayi yana kallon fuskar
ta yakai towel din kan fuskar yana share mata ruwan ahankali, lumshe ido tayi tadan saukar da
ajiyar zuciya wuyarta ya share sanan ya dauketa ahankali daga kan kujeran sabida karya fama
mata ciwo ya mike tsaye yana kallon fuskarta, ahankali tadan bude ido takallai kara gyara kanta
tayi akan kirjinshi tasake sauke ajiyar zuciya, kwantar da ita yay akan gado ya rankwafo yamata
runfa batare daya dagoba yace "good morning wife" hanunshi dayaji ta rike yasa yadan dago ya
kalli hanun, murmushi yamata sanan ya zauna yakai hanunshi kan filon ya budemata yana

kallonta, ahankali tasake matso da fuskarta tadaura kan hanun sanan ta lumshe ido tareda
sakin ajiyan zuciya takara kankame dayan hanunshi data rike within 1min bacci yay gaba da ita,
batare datamaga teddy ba.
Murmushi Nurse din dake tsaye tana kallonsu tayi cikin turenci tace "her mind is at ease
anytime u are around, inhar tana ganinka haka kullum zaiyi helping recovery nata" murmushi
yamata batare daya dena kallon fuskarta ba hakan yasa nurse taje ta bude wardrobe din dakin
ta ciro wani ruwa dake cikin farin gora ta ijiye akan table din gefen gadon tace "wanan ruwan
zata sha dazaran ta tashi, bari naje inta tashi ka danna mana alerm" tana fadin haka tajuya
tafita daga dakin, yadade yana kallonta kafin ya daura kanshi agefen gadon shima bacci yay
gaba dashi dan jiya kasa bacci yayi sabida tunanin ta.


Yau kwana su sha bakwai a asibitin, sosai condition din Islam ke improving dan bakin tass ya
warke babu kumburin babu zubar yawu tana iya hadeye magani yanzu, cikin ne yanzu ake kai,
kullum Khaleel na tareda ita abinda ke dagashi daga dakin salla ne kokuma idan zaije siyo
magani a pharmacy hospital, shima idan zaije to Ihsan na wurin, Ihsan taita karanta mata novel
tana murmushi kadan kadan, idan kaga yaci abinci to coffee ne yadan sha, baya iyacin wani
abinci ko Ihsan ta girka saidai yay wasa da abincin kawai yatashi yabarshi, jiyake kaman ciwon
yadawo jikinshi.

Zaune suke adakin itada Ihsan dake karanta mata wani novel tana kwance kan gado suka bude
kofa suka shigo hakan yasa ta dago kai ta kallai shida Dr Om ne suna dan magana, murmushi
Dr yay ya kalleta suna karasowa jikin gadon yace "how's my patient doing" dan murmushi tamai
tana kokarin gyara kanta akan filo, ya makala mata wani abu kaman camera karama a hannu
sanan yace "Gud, I need you to do something for me, inaso kitashi ki tsaya naga" karamin tablet
din hanunshi ya daddana sanan ya kalli Khaleel yace "dago min kanta" ahankali Khaleel ya
dago kanta ya zaunar da ita, kafarta Om yanunamai hakan yasa ya sauko da kafarta kasa yana
kallon fuskar ta, kallonta Dr yayi yace "now try and stand on your feet" dan dafa bango tayi
Khaleel ya tsaya kusa da ita dan karta fadi ya sakin mata murmushi tare da nunama ta thumb
dinshi alamun good, ahankali take daddafa bango harta dan tsaya amma aduke tana dan ciccije
lebe sabida zafin datake ji, dadi Dr Om yaji yace "gud now try and raise ur head, stand straight,
inaso naga inda yarage dabai warke bane acikin" fuzar da iska tayi tareda karasa mikewa
ahankali ahankali Khaleel yace "sorry wife" Dr Kuma na duba tab din hanunshi, kasa daurewa
tayi jin zafin yay yawa tacire hanunta daga bango tai luuu zata fadi Khaleel yatare ta da sauri
hakan yasa ta fado kanshi wani irin shocking yaji tunda ga yatsar shi har brain dinshi sabida
yanda hanunshi yakama kirjinta mistakenly, itama wani iri yarr taji duka karfin ta tasa tadan juyar
da jikinta ta yanda abin ya sauka daga hanunshi ta lumshe ido tana sauke numfashi, yafi
3minute ahaka sanan ya kwantar da ita ahankali yaja bargo ya lullubamata yana kallon idonta
dasuke alumshe, maganar Om ce yadawo dashi daidai yace "Khaleel zokaga" zuwa yay ya kalli
tab din yace "kaga wanan mucus dinne keda inflammation dazaran ya sabe shikenan zata iya
tana mikewa tana komi saimuyi focusing kuma a dawo da maganarta" rungume shi Khaleel yayi
cikeda murna yace "Alhamdulillah, Dr am grateful" fita Om yay daga dakin yanata dariya.
Cikin sati daya cikin ya warke fess, takan tashi tai tafiya ahankali ta shiga bayi da kanta tai

alwala tai salla, kuma takanci abincin dan har tuwo ranan nan Ihsan tamata Kuma taci sosai
danyamata dadi, Khaleel ko babu wanda ya kaishi murna harda yima nurses kyauta.

Zaune suke adakin yana bata tea abaki kiran Om daya gani yasa ya dauka ahankali yace
"okay" sanan ya katse wayar Ihsan yamika mug din tea yace "zoki bata am coming Om nason
ganina" fuskar Islam ya kalla dake kallonshi da idanunta masu kama danamai jin bacci yace
"am coming wife" fita yay yawuce office din Om shiga yay ya zauna, Om ya bashi wayansu
hotuna yace "kaga wanan hoton damukama wuyan tane, babu any damage a vocal dinta so Ina
suspecting infection ne awuyan dake hanata magana, yanzu abinda zanyi shine zan bata
magunguna sanan zan sallameku inyaso every every week zaka dinga kawota chech up tunda
for now ai babu wata matsala saita maganan ko" kasa boye murnanshi Khaleel yayi hakan yasa
Dr yafara rubutu akan paper asibiti yace "ko aje ai amarce hmm" yagama rubuce rubucen ya
mikamai yace "your discharge letter, I will be expecting you guys next week Thursday" ahankali
ya karba yana murmushi sanan ya mikamai hannu sukai musabaha tareda kara godemai sanan
yafita daga dakin, dakinsu ya shiga Ihsan dake zaune agefen gado tana nunama Islam wani
hoto yazo ya daga yana jujjuya ta yana murmushi dariya tayi tace "Ya Khaleel menene wai?"
murmushi yamata yace "an sallamemu" yay maganar yana kallon fuskar Islam ahankali yaga
taja bargo ta rufe fuskarta tana murmushi dan wlh tagaji da asibitin sosai itama. Ihsan ya kalla
yace "tashi kitayata shiryawa bari naje nakira taxi" fita yay daga dakin yana Satan kallonta,
shiryawa tayi cikin dogon black skirt din kanti na jean tasa shimi fari tadaura sweater akai pink
dan garin da sanyi sanan Ihsan tamata rolling black gyale sanan tasamata flat slippers, tahade
yan littatafai da kayansu dasu tea dake dakin ajakan trolley ta kulle ta daga, shigowa dakin yay
yana kallonta tana zaune akan gado kanta akasa hanunta rike da teddy daya saimata kallon
Ihsan yayi yace "fita da jakan taxi din na waje" jan jakan tayi tafita shikuma ya karasa cikin dakin
har gaban gadon ahankali ya daura hannayen shi akan nata ya dagata tsaye ya karbi teddy ya
ijiye akan gado kasa daga kai tayi ta kalleshi, jinta tayi kawai ajikinshi ya rungumeta tsamtsam
tareda kissing gefen wuyanta.
[6/25, 2:22 PM] Maman Jedda: *JARABTA*


Maman Abd Shakur

55 & 56

Ya sakin mata light kiss gudun karya ji mata ciwo sanan ya dago kai ya kalleta murmushi
kwance akan fuskarshi, jiyay duk wani ciwon kan da yakeji yabace, sake kai hannu yayi ya
share hawayen daya gangaro mata tareda girgiza mata kai yace "am here for you now, koma
inane I don't care saina kaiki koda bangon duniya ne inhar zaki sami lpy, zakiji sauki in sha
Allah, stop crying..." dan kwankwasa kofa akayi Anty Hindu ta shigo takaraso inda suke ta kalli
Khaleel sanan tace "Dr nason ganin ta, za'a wanke mata bakinne, kaga yanzu ma yadan warke
tadan iya hadiye tea mai sanyi yau, amma tunjiya babu abinda take iyaci da bakin danyay jajir
kaman kuna, bari nakaita" da sauri yatashi yakoma bayan keken yace "zankai ta Hajiya" dan
hararan shi Anty Hindu tayi tace "banason gardama Muhammad, ba gamunan ba duka, salla

yakamata kayi tukun yanzu sai asan abinyi, oya shiga bayi ka dauro alwala saika wuce
massallaci, idan ka Ida aisai kazo kasamemu a dakin nata" tana fadin haka ta gungurata suka
fita daga dakin, zama yay akan gado ya dafe kanshi tareda fuzar da iska shikadai yasan yanda
yakeji, wayarshi ya dauko dake gefen gado yay dailing wani number yafi minti biyar yana
magana aharshen turenci sanan ya katse wayar ya shafa kanshi yana fuzar da iska, ahankali
yatashi ya shiga bayin dakin ya dauro alwala sanan yafito yafita daga dakin baiga su Abba
awajen ba hakan yasa yawuce massallacin dake cikin asibitin.

Saida ya gama salolin dasuka hau kanshi sanan yafito daga masallacin yana tafiya ahankali
dan yay nisa acikin tunani, mutum yagani yasha gabanshi ya tsugunna hakan yasa yadan tsaya
yana kallonta ba karamin ramewa tayiba tai duhu sosai idanunta duksun fada ciki, fashewa tai
da kuka sosai ta hade hannayen ta tace "dan girman Allah kayafe min, wlh shirin shaidan ne
saida nayi sanan hankali na yadawo, am very sorry Mk, dan Allah na tuba kayafemin" tunda
take maganan yake kallonta harta gama kara daure fuska yayi kaman baitaba murmushi ba ya
matsa zai wuce takara tasowa tasha gaban shi tace "dan Allah, kaga Abba yakoreni daga gida
idan kaima baka yafemin ba dame zanji, am very sorry, dan Allah inaso naga Islam na roketa
gafarta please"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login