Showing 3001 words to 6000 words out of 68809 words
Chapter 2 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf
izinin shigowa wata kakkyawar baby ce ta shigo office din wacce akallla zatai 26 tana sanye da
daoguwar riga ta yafa gyalenta idanunta a cikin black shade kallo daya yamata ya dauke kanshi
akanta yacigaba da abinda yakeyi, ahankali taja kujeran gaban table din ta zauna tareda ajiya
handbag dinta akan table ta cire dark shade din ta ijiye kan table idanunta har sundan kumbura
sunyi ja alamun taci kuka sosai take kallonshi bataki suyi ta zama ahakaba har karshen
rayuwan su at least yarage mata wahalan da take ciki. Kusan 20mins yayi kafin yagama report
din yatura head quarter dinsu na Lagos sanan ya kashe laptop din batare daya kalleta ba yace
"what brings you here Zainab?" da kyar ta iya tattaro courage din dayadan rage mata ahankali
tace "nazo nabaka hakuri I know I shouldn't have picked d call, please forgive me khaleel"
takarashe maganan tareda ciro tissue daga jakanta tana goge hawayen daya zubo mata sosai
ta bashi tausayi shiya rasa mesa Zainab ke sonshi haryau bai tabajin koda digon sonta aranshi
ba. Ahankali yasauke ajiyan zuciya yace "am sorry too Zeenat I shouldn't have acted d way I did
jiyan, Zeenat you are too good and Charming soul, banason kiyi wasting precious time dinki
akaina, u know dis, duka duka bikina baifi two weeks ba, am sorry to say but my heart belongs
to Aisha kadai, please move on and kimanta dani kinji Zee" sosai hawaye ke bulbulo mata ita
kadai tasan yanda takeji ahankali ta mike tsaye tadau jakanta da shade dinta tafita daga office
din da gudu. Lumshe ido yayi tareda fuzar da iska ba karamin tausayi tabashi ba sosai yamata
addua Allah yahada ta damai sonta haka, ganin 5 tayi yafara shirye shiryen tafiya gida
[6/7, 11:23 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
3...
Around 9 yakirata ringing uku ta dauka cike da damuwa yace "my Eesha ya muran?" cikin wata
irin siririyar murya tace "Alhamdulillah yadena" da sauri yace "are u sure kodai you are just
scared ne Kisha maganin daren ki" dan dariya tayi tace "am serious fa, yaragu sosai nasha ma
ginger tea dazu Mama tamini" dan ajiyar zuciya ya sauke yace "okay" shiru suka danyi ahankali
yace "My Eesha inaso nadan fita" shiru tadanyi kafin tace "ina zakaje?" "just wanna hang out
with some friends, colleague dina na birthday yau" kaman mara lafiya tace "okay" kara sassauta
muryanshi yayi yace "what? Menene saheeba" girgizamai kai tayi tace "babu komi kawai zanyi
kewanka ne" murmushi yayi yace "don't worry khaleel naki ne my Eesha and I promise dazaran
nadawo I will call u is dat okay?" gyada mai kai tayi tace "uhm" "okay I love you bye" ajiye wayar
tayi ta tashi tafita jin Mama na kiranta dakin Mama ta shiga ta zauna akan gado tace "Maman
mu gani" spoon Mama tacire acikin cup din dake hanunta tace "gashi shanye" karban cup din
tayi tana yatmuse baki ita wlh tagaji da wayan nan abun da Mama kebata daga mai bauri, sai
mai gishiri da mai daci, gashi ba halin zubarwa agaban ta kesata tasha, ajiye cup din tayi tadau
ruwan dake gaban mirror tasha da sauri tana yatsine fuska tace "haaaa Mama daci wlh"
hararan ta Mama tayi tace "gulmamma ashe keda Khaleelu so kuke ayi auren dazaran kin
gama exam ran Friday nan ko, oh ni ya'su wanan wasu irin yaran zamani ne" Mama tarike baki,
zaro ido tayi waje dan bama tagane inda zancen Mama din tadosa ba tace "ni Maman mu"
Mama dataji kaman ta make ta tace "eh kefa, to ai bukatun ku yabiya Abban ki yace dazaran
kingama final exam dinki dis Friday upper Saturday bikin ki, Kinga yau saura kwana 9 kenan
happy?" arude ta dafa kirji tareda zubewa nan kasa afalon tafara rantse rantse cikin kuka "wlh
Maa nidai abari sai nan da 4 weeks din, Mama I don't know wanna leave you please" yanda
tadage tana kuka yasa Mama sakin salati da tafi da hannu tace "da jiya kuka gama shirya
abunku bakisan zakiyi kuka ba, keda naso immediately bayan kin gama exam natura ki Sudan
amiki gyaran jikin 3 weeks shine kukai hadahaden kuko, ai bari Khaleelu yazo Shima jiranshi
nakeyi marasa kunyan yara kawai" sosai tafashe da kuka hakan yasa Mama tafita daga dakin
tace "inkin gama kije ki dafama auta indomie" nan tabarta sosai taci kukan ta sanan tabar dakin
tareda yin kwafa.
koda yadawo yakira yakira taki dauka yasan bata bacci saisunyi waya da kyar ya iya yay bacci
batare dayaji muryan taba, da safe ma haka yakira taki dauka karshen ta ma kashe wayar tayi.
11 a makaran tar su tamai yay parking yana jiran tafito daga exam hall sabida 12 zasu gama,
11: 45 tafito tana sanye da milk color Hijab har kasa da bakin flat shoe karasowa yay gabanta
ya karbi handbag dinta as usual bata hanashi saidai taki bari suhada ido hakan yasa yagane
tana fushi dashi, bude mata gaba yayi saida ta zauna ya rufe sanan yakoma ta dayan bangaren
Shima ya zauna yay facing dinta yace "are u happy now kin hanani bacci jiya sanan kuma kin
hanani zama nai aiki" wasa tacigaba dayi da yatsun ta batare data kalleshi ba hakan yasa yace
"My Eesha menayi talk to me I can't take dis punishment" shiru tasake mai hakan yasa yace
"please" kwallan daya zubo mata ta share da sauri tace "mesa kasa aka maida bikin upper
Saturday" takarashe maganan tareda rera mai wani sabon kuka ahankali, dan murmushi yayi
tareda shafa kanshi yace "to everyday u keep driving me crazy nakosa ki zama tawa"
yakarashe maganan yana dan dariya ciki ciki hakan yasa tasake harzuka takara narkemai da
kuka kama bakin shi yayi yay shiru yadan daure fuska ya dafa kanshi tsayar da kukan tayi ta
kalleshi cikin shagwaba tace "what?" kaman zaiyi kuka yace "bakomi yaune na gane cewa am
just wasting my time amma baki taba sona ba my Eesha, I feel like hanging my self nahuta, no I
feel like na shiga beach ruwa yatafi dani, no I feel like namaida kaina kifi kawai asoyani aisaiki
huta ko" yakarashe maganar tareda kifa kanshi a sitiyari mota dan inyacigaba da kallon ta
dariya zaiyi sabida yanda yaga tashin hankali karara akan fuskarta, ta tsani ta ganshi cikin
damuwa hankalin ta tashi take. Dawata irin calm voice tace "am sorry" girgiza kai yayi batare
daya kalleta ba yace "No my Eesha u are not, kawai ki barni naji dakai na" kaman mara gaskiya
tace " kayakuri to na yarda" murmushi yayi ya dago kanshi ya kalleta tareda kara narke mata
yace "a'a abarshi in four weeks time din kinsan bazan iya jure kina fushi dani ba, I can manage
myself tunda baki damu daniba" da kyar ta shawo kanshi sanan suka shirya yay parking agaban
gidansu ya kashe motar dago da kanta tai ta kalleshi ganin ita yake kallo yasa ta sakinmai
murmushi tace "infadama wani secret?" da sauri yace "yes my Eesha" bakin hijabin ta tarike
tana dan murmushi hakan yasa yace "ha'an tell me nakosa" shiru tadanyi tana dan waswasi
kafin tace "kasan mesa at first I was angry danaji an matso da bikin kusa?" "No" kaman zatai
kuka tace "naga wani agogo" tadanyi shiru tare da juyar da kanta ta kalli window motar tace
"dama tara kudin dinkin danake yi nakeyi har kudin yacika in saima, ranar bikin mu agogon
nakeso kasa, but kaga yanzu bangama tara kudinba kuma kasa anmatso da bikin kusa" jin yay
shiru baice komiba yasa ta juyo da kanta ta kalleshi tsantsar sonta tagani kwance akan fuskar
shi hakan yasa tamai murmushi wani irin gauron ajiyar zuciya ya sauke tareda lumshe ido danji
yake kaman yajawota ya rungume iska yaji anhuramai a fuska hakan yasa ya bude ido ya
saukesu akan kakkyawar fuskarta cikin tsantsar kauna dawata irin calm voice yace "incika miki
kudin kisaimin my Eesha?" girgiza mai kai tayi tace "I want to use my hard earned money, da
gumina nakeso nasai ma dashi inda bahaka ba danai amfani da kudin da Abba da Ammi keban
tuntuni, nasan zan sami dinki I will be able to complete the money" hannunta yakai zai kama da
sauri ta janye tana hararanshi ahankali tareda murguda mai baki ta bude kofar motar tafita ta
bude gate ta shiga gida.
Hannu shi ya daura kan kirjinshi dake bugawa very fast ahankali yace "Ya Allah kabani Eesha"
kunna motar yayi yabar anguwan.
Bude ido yayi afirgice ya kalli agogo zaro ido yayi yace "wat those girls will kill me today"
agurguje yafada bayi yay wanka yafito ya shirya cikin farin shadda gizna dayay mugun karban
shi yadau turare ya feshe kanshi dashi sanan yadau waya da car keys dinshi yafita daga dakin
da sauri dakin mum ya shiga yace "morning Ammi" ajiye littafin Azkar din dake hannunta tayi ta
kalleshi tace "ango in the next seven days antashi lafiya" murmushi yayi kaman baijiba yadau
mug din tea daya gani akan stool din dake gaban Ammi ya kwankwande sanan ya ijiye mug din
yace "Ammi ina su Ihsan" tabe baki tayi tace "nizaka tambaya kasan kunyi alkawarin yau
asabar karfe tara zaka kaisu shine yanzu ake ganinka ai sunce sunfasa zuwa hanyar kofa yayi
zai fita Ammi tace" Son" juyowa yay yace "Na'am Ammi" mayar da kanta tayi kan littafin
hannunta kafin tace "anjima yan uwan babanku da babar ka zasuzo yau za'akai akwatin"
takarashe maganan tareda dago kanta tana kallon fuskar shi wani kunyar Ammi yaji yakamashi
hakan yasa yafita dakin da sauri ya shiga dakin su Ihsan. Dariya Ammi tai kawai ta kada kai
babu wanda yasan halin dan nata kaman ita.
[6/7, 11:23 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
4&5...
Dankakaren falon gidan su acike yake dam da yan uwa dan yau Alhaji Ismail wan baban
Khaleel wanda suke kira da Abba ya iso daga Yola tareda yaranshi da matayen shi biyu, Hajiya
Amina wacce itace babba yaranta uku Mustapha babban danta da yanzu yay aure matar shi
bata haihuwa, sai Yusuf shine na biyu shine saan Khaleel tare suka taso sun shaku sosai, sai
autar su Fa'iza wacce ke SS3 a boarding school. Amaryan Abban Kuma Mujiba yarta daya
wacce takeda shekara daya aduniya, gabaki daya falon ya kachame da hira idan ka gansu
gwanin ban Sha'awa.
Yusuf ne ya kalli Khaleel dake danna waya yana shan tea yace "kai tashi muje mu amso dinkin
mu, and su Shareef na jiran mufa a barrack dinku" yatsine fuska yayi sanan ya maida wayar
aljihu ya harare shi yace "muje" tashi sukayi Yusuf yace "Abba zamudan fita" da sauri Ihsan
tace "Ya Yusuf ku dawo dawuri fa, 4:30 daidai ne walimar babu afircan time" ta kalli Fa'iza da
Ilham tace "ku tashi muje gidan su Aisha ma, nasan amma fara lallen tanata min flashing" Car
key Khaleel ya dauka suka fita dukan su tare.
Karfe 4 aka fara tafiya da kawayen amarya wajen event din ganin su Eesha basu fitoba yasa
Mama ta shiga dakin nasu, su Ihsan ne da wata kawar Eesha wacce suke aji daya anan
University Abuja. Kasa magana Mama tayi ganin yanda Eesha tai mugun kyau abunka da
wacce bata saba kwalliya ba, murmushi su Ihsan sukayi, Ilham tace "Mama tai kyau ko, Fa'iza
ce tamata makeup dinan" murmushi kawai Mama tayi tajuya tabar musu dakin, ahankali Aisha
ta dago kanta ta kalli fuskar ta a madubi murmushi tayi sabida taga tama kanta kyau, Khadija ce
ta dagata tace "tashi muje, yau idan Khaleel ya ganki na tabbata hmmm" dariya sukayi
bakaramin kunya taji ba ta turesu tafita daga dakin da gudu, binta sukayi nan suka shiga motar
da aka barmusu driver ya jasu zuwa wajen venue walimar.
Wa'azi aka musu mai ratsa jiki, mai sanyaya rai mai kara Imani, sosai kowa yay hawaye,
barinma amaryar, bayan angama aka rarraba kyaututtuka akai ciye ciye sanan aka fara kawo
motocin komar dasu gida. Gaban wata babar jeep Khadija ta kaita kirar Brabus, bude marfin
motar tayi ahankali ta shiga sanan ta mayar da kofan ta rufe juyawa tayi da sauri ta wuce ta
shiga wata motar daban. Kin dago kanta tayi dudda taji yanda kamshin turaren shi ya bude
motar, cikin wani irin calm voice taji yacema driver mutafi. sundan jima suna tafiya kafin ahankali
ta dago kanta ta kallai karaf suka hada idanu hakan yasa ta juyar da kanta da sauri tana
murmushi.
Parking motar taji anyi anbude gaban motar anfita matsowa yay kusa da ita kadan dawani irin
murya chan ciki yace "wife" duk yanda taso karta kallai hakan ya gagara samin kanta tayi da
juyowa ta sauke mai kyawawan idanunta akanshi, ganin kallon dayake mata yay yawa yasa ta
huramai iska a fuskar murmushi yayi, ahankali tace "Mesa kake kallona haka?" takarashe
maganan tana turamai baki, murmushi yasakin mata kafin yakara matsowa kusa da ita, da sauri
tai yunkurin matasawa hannunta yarike yana wani irin kallon fuskar ta, jikinta ne yafara rawa ta
bude baki zatai magana, dayan hanunshi ya daura akan lips dinta yana girgiza mata kai da
idanunshi dasuka xhanza launi kaman basuba, ahankali yadaura goshin shi akan nata lumshe
ido yayi jin yanda take numfarfashi, dawani irin murya yace "ina sonki sosai my Eesha" Ahankali
ya dago da kanshi hannu yasa yay cupping fuskar ta sauke idanunshi yay akan lips dinta dake
shining sabida Jan bakin dasuka ji wani irin abu ke fizgar shi ahankali yakai bakin shi zai daura
da sauri ta kawad da kanta kirjinta na mugun bugawa dan tunda take dashi baitaba mata
hakaba, wani irin hawaye ne ya zubo mata tai sauri ta share sanan tadan kalli fuskar shi wanda
ita yake kallo da idanunshi dasuka kankance kofa ta bude da sauri tafita ta bude gate ta shiga
gidan su. Yafi minti uku a zaune kafin ya bude kofar ahankali yafito front sit yakoma ya kunna
motar yaja yabar wajen.
Gaishe da kawayen Mama tayi dake falon a kunyace ta wuce sama, su Khadija da Ihsan ne ke
gwada kayan ankon su da aka kawo musu, zama tayi a gefen gado tana yatsine fuska tace
"wash Allah wlh nagaji" dariya duka yan matan sukayi Khadija ce tace "ai dole sannu kinji"
yanda tai maganan yasa Ilham ta kwashe da dariya tace "ai Yaya Khaleel shegen naci shi
bazaima bari gobe tayiba yawani..." hararan ta Eesha tayi tace "yan sa ido Yaya Khaleel dina
baida naci duk cikin sone" kama baki dukan su sukayi suna kallonta cike da mamaki, Ihsan ne
tace "iyye kike karemai muma Allah bamu mai sonmu" dariya tayi tareda cire doguwan rigan
jikinta ta yarage saura shimi da dogon sket, ta ninke ta ijiye akan gado, murmushi tayi ganin
fuskar Khaleel namata gizo, hannu tasa ta cire dan kunnen kunnenta ta ijiye agaban mirror
sanan ta juyo ta kallesu ganin duk ita suke kallo yasa tasake murmushi tace "bazaku gane
yanda nakeson yayan nan naku bane, inama Ya Khaleel son da ina ganin ko bayan namutu
banjin son zai mutu ba, Ya Khaleel namijin tal da har yau banga irinshi ba, mutum ne mai
tausayi, kirki ga amana da addini, nasan yanada matsalan zuciya da yawan fushi but alkairan
shi sun mamaye wanan, sabida Ya Khaleel ne Auta ke raye da yanzu ya mutu, kuntuna randa
gidan mu yakama da wuta duk anfito damu but Auta na ciki, Ya Khaleel was d one daya koma
duddu uban wutan nan yaje ya dauko Auta, saida ya kone a hannu garin hakan, haryau tabon
na jikin shi" share dan guntun hawayen daya zubo mata tayi ta mikama Ilham da Ihsan hannu
tace "Yaya Khaleel dina is my everything bazan taba son wani sama dashi ba" murmushi tayi ta
sake su ta wuce bayi danyin wanka.
Banjin daga Khaleel har Eesha wani daga cikin su yay wani bacci mai kyauba, Eesha su Ihsan
da Khadija ne suka tasata agaba wai takosa, shiko Khaleel abangaren shi Yusuf da friends
dinshi ne suka tasashi gaba wai yakosa yaki bacci dariya yay yaki musu magana.
Misalin 9:30 nasafe na ranan bikin mutane sun cika gidan makil, Aisha ce zaune akan gadon
dakin ta tasa wata atampa English wax da aka mata stone work yay kyau sosai, wayarta ta
dauka tai dailing number Khadija ringing daya ta dauka, tace "Eesha am coming back yanzu na
siyo agogon, gama ninan nafito daga Dunes Abuja taxi nake nema nahau" murmushi Eesha tayi
daya mugun kara mata kyau tace "nagode Tawas, kiyi sauri please inaso nabashi yasa kafin
lokacin daurin auren ne" katse wayar tai tana murmushi tun jiya bai kirata ba tasan hala fushi
yakeyi, murmushi tayi tadau wayar Flashing tama su Ihsan dan sun tafi gidan su dauko kayan
makeup din Faiza sunki dawowa.
Wuraren goma da rabi Khadija ta dawo da sauri Eesha ta karbi ledan da akwatin agogon ke ciki,
ciro agogon tayi ta bude daga box din wow tace, agogo ne mai kyau Rolex wanda tasaimai da
kudin ta 75,000 naira, gashin golden color rufewa tayi ta dau wayarta dailing number Khaleel
tayi saida takusa katsewa sanan ya amsa. Murmushi tayi kafin yay magana tace "am sorry Yaya
Khaleel" Ahankali ya lumshe ido danji yayi wani sanyi ya ratsa zuciyar shi, dawani irin murya
tace "kana ina kana gida ne?" dan murmushi yayi sanan yace "a'a muna bakin layi shagon dinki
Ibrahim tela, kayan dazamu sa gabaki daya fashion designer damuka bama dinki yamana
wandunan sunyi tsawo sosai shine muka kawoma Ibrahim yarage mana, Mesa kike nemana
Kuna bukatan wani abune, nazo?" girgiza kai tayi tace "a'a kabarshi bari nina zo, I want to give
you something, something special" da sauri yace "kina amarya kifito akalle min ke lallai to naki,
bari am coming" dan dariya tayi sanan tace "ni to ai kofar gidanmu da mutane banaso su ganmu
tare ne saisa, Kuma su daddy ne da friends dinshi, saisa nakeson nazo am coming" katse
wayar tayi tadau dogon hijabin ta har katsa tasa, Khadija dake shiryawa tacema "Ina zuwa, insu
Ihsan sunzo afara