Showing 27001 words to 30000 words out of 68809 words
Chapter 10 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf
kadan ya sassauta
murya kaman me lallaba yaro yace "plzzzzzzz" yanda yaja plz din haka tajishi har cikin ranta
ahankali ta mika hannu zata karba girgiza kai yayi batare dayay magana ba ya nuna mata
bakinta da yatsa yace "haaa" wai mutumin nan magic yake minne dudda yanda taso tahana
kanta kasawa tayi ahankali ta bude bakinta kadan, murmushi yayi yakai chocolate din bakinta
yana kallon fuskarta Islam! Farida takira sunanta dawani irin murya da tunda suke bata tabajinta
dashi ba, adan rude ta juyo dan yanda Farida takira sunanta saida ta firgita shima ita ya kalla,
gyara zama yay sanan yace "Hi how u?" dan wlh yamanta sunan ta, da kyar ta iya kakalo
murmushi tace "fine" murmushi yamata sanan yace "don't tell me u two are sisters" Ya kalli
Islam sanan ya kalleta ya nuna Islam yace "itace dama Islam din dakike ta bani labari" gyada
mai kai tayi tana kokarin danne hawayen dake barazanar zubomata, yay murmushi yana wani
irin kallon Islam kaman ya cinye ta yace "I see" dan murmushi tamai sanan tace "bye" tajuya
tafara tafara hawa stairs, tashi Islam tayi zata bita dawani irin murya yace "ina zaki My Ummi,
we are not done yet baki karbi Chocolate dinba" wani irin hawaye ne mai zafi ya zuboma Farida
da sauri sauri tai tawuce dakinsu jin yanda Superman kema Islam muryar dabata sanshi da ita
ba, dama yanama magana haka?.
Zama Islam tai ahankali ta kallai dauke kai tayi sanan tace "dama ka San Farida ne?" gyada kai
yayi yace "yea I helped her once haka dawani thief ya kwace mata jaka and daga nan I think
mun sake haduwa twice ko I think, ashema sisters neku, Kinga ko Allah ma wants me to marry
u tunda har yasa nasan yar uwarki" tashi tayi tsaye tace "bye" da sauri shima ya tashi yace "but
I don't wanna go now" hawaye ne yacika idonta tadan kalleshi sanan ta dauke kai, ahankali
yace "okay I will go, Plz don't cry" dan matsowa yayi ya tsaya a gabanta ya mika mata
chocolate din yay murmushi yace "u have to eat it before i go" bakinta yakai hakan yasa ta
kawad dakai, tsayawa yay yana nazarin fuskarta kaman something is wrong ahankali yace "Are
you okay?" murmushi tayi tadan bude baki hakan yasa yay wani murmushi daya bayyana
fararen teeth dinshi yasaka mata chocolate din abaki ta gutsiri kadan sanan ya cire yana
murmushi, dadan sauri tabar wajen murmushi yayi saida yaga tai sama sanan yafita daga dakin
tareda kai sauran chocolate din bakinshi.
Ahankali ta bude dakinsu jikinta yay mugun sanyi ganin Farida tsaye a tsakar dakin idanunta
sunyi jajir alamun taci kuka, ahankali ta maida kofar ta rufe ta shigo dakin tace "Faree wlh ban.."
hannu Farida ta daga mata tace "banason naji komi daga gareki" nuna kanta tayi in so much
pain tace "nizaki yaudara? Ni Islam ur own blood, ur only sister, daga nace yaje ya taimaka miki
ranan a school shikenan har kin nunama su Abba shi aka samuku rana ko" share hawayen
daya zubo mata tayi tace "no wonder ko waya zakiyi dashi bakiyi agabana, ko dazuma bayi kika
gudu sabida karnaji mekuke cewa, duk idan nai maganar shi saidai kiyita cemin na manta
dashi, na shareshi, my God u fooled me Islam" sosai Islam ke kuka tana girgiza kai tace
"bahaka bane wlh" ta matso kusa da ita zata tabata wani tsawa Farida ta daka mata tace " don't
touch me you cheat! Mara Imani, mai bakin hali, trusting and liking u sune biggest mistake din
danayi arayuwata wlh, mai bakin hali kawai kamar uwarta" tsayar da kukan datake tayi ta kalleta
tace "Faree dan Allah karki kara zagin min mama kinga tariga tamutu ba kyau" nunata Farida tai
da yatsa tace "an zagadin, ance uwarki kika biyo da wanan bakin halin" mari Islam ta kaimata
abaki hakan yasa Farida ta taba bakinta jini tagani hakan yasa wani zuciya ya dauketa da
haushin kwace mata superman datayi ta chakume Islam, da sauri Islam data mugun tsorata dan
ganin idanun Farida ta rike hanun Farida inda ta chakumeta tace "yakuri dan Allah bada gangan
na mareki ba" buga Islam tayi da bango, Islam tai wani wahalallen kara, duk iya karfin ta takasa
ture Farida, kara Fizgo Islam tayi daga bangon tawani nakata akasa kan center carpet din
tsakiyar dakin ta finciko gashin Islam tanaja, azaban da Islam taji yasa ta dana mata cizo a
hannu da sauri Farida tasaki gashin nata tana duba hanunta, azabure Islam tamike zata gudu
waje Farida ta tadiyota da kafa jikake dimm tafadi tai kara, Farida da zuciya tariga ta debeta ga
shaidan daketa zugata tai kan Islam tahau ruwan cikinta tana kima kaman ta sami kayan wanki,
da kyar Islam ta iya kai hannu tana kokarin kama gaban rigar ta.
[6/18, 10:30 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
40 & 41
Wani mugun kallo ya watsama Faridan batare daya damu da maganan mutanen wajen ba ya
juya zai tafi, kafarshi Islam ta rike gam gam tareda daura fuskarta akan gwuiwar shi tafashe da
mugun kuku harda shesheka tace "bakace kana sona ba, inhar kanasona son gaskiya, so
sabida Allah to ka yarda ka auri Farida, dan girman Allah do it for me" fincike kafarshi yayi
yakara juyawa zai tafi da sauri tabishi da gwuiwa ta kama kafarshi again gam sanan ta dago kai
ta kallai suka hada ido, ahankali ta saki kafarshi tahada hannayenta tace "inhar kanasona da
gaske, ka aure ta karta kashe kanta, yar uwata ce bazan taba yafema kaina ba idan wani abu
yasa metaba, dan darajan Allah am begging you" yanda take kuka tana rokanshi yasa ya
tsugunna ya dagota sama kallon cikin idonta yay yace "stop crying" ahankali ta tsayar da kukan
tana kallon fuskarshi yace "abinda kikeso kenan na auri Farida?" Ya tambayeta "jama'a zataci
shinkafar fa" da sauri Islam ta juya ganin Farida na kokarin kai shinkafar bakinta ta daga hannu
tace "stop, stop Faree ya yarda, zai aureki" kallon ta Farida tayi sanan ta kalli Khaleel din tana
goge hawaye, Islam ta kallai tace "please tell her ka yarda" yadade yana kallon fuskar Islam din
kafin ahankali ya juyo ya kalli Faridan da kyar ya iya cewa "yea na yarda I will marry u"
murmushi Islam tayi tana goge hawayen dataji ya zubo mata, Farida takara goge hawayen
dasuka ki dena zuba tace "and kayarda dazaran na sakko zamuje gida direct ku fadama Abba
kun yarda" yadade yana kallon fuskar ta sanan yace "yea, now come down" yasa hannu ya
danne mata ladder, murmushi Farida tayi ta kabar da shinkafar rice din dake hanunnata tafara
sakkowa saida ta sakko kasa ta fada jikinshi ta rungumeshi tana kuka sosai tace "I love you so
much Mk, wlh Ina mugun sonka, Allah ya jarabceni da sonka, I love you my superman" ihu
mutanen wajen sukeyi suna tafi da sauri Islam ta sanya hijabin ta tarufe fuskarta jin kuka yazo
mata sosai, da sauri ta juya zatabar wajen karaf taji anrike hanunta hakan yasa ta dago da
rinannun idanunta taga Khaleel ne wanda Farida ta shige jikinshi tana kuka yana kallon kwayar
idonta, fizge hanunta tayi da gudu tabar wajen tai bakin titi Keke napep ta tare ta shiga ciki
tacemai suje sosai take kuka mai Keke na tambayan ta lpy.
Cireta daga jikinshi yayi batare daya kalli fuskarta ba yace "mutafi" yana gaba tana biye dashi
suka karasa har wajen motar ya shiga itama ta bude gaba ta shiga sai murmushi take tana
kallon fuskarshi kaman yau tafara ganinshi, kunna motar yayi sukabar wajen, a kofar gida suka
ganta zaune akan bencin mai gadi, parking yayi suka fito ta kalli Farida tace "dama kunake jira
mutafi wurin Abban" da sauri ta bude gate ta shiga batare data kalleshi shiba Farida ta kallai
tace "muje my superman" Atare suka shiga cikin gidan direct falon Abba sukayi suka shiga da
sallama, yana zaune tareda Mum dake tayashi arranging some business papers. Daga Abba
har Mum din binsu sukai da kallo ganin yanayin idanun yaran nasu.
Gaban Abba Islam taje ta tsugunna ahankali tace "Abba dan Allah kahada Farida da Khaleel
aure bada niba please Abba, don't ask me why amma dan Allah kahada su aure ni banaso"
tunda take maganan Khaleel yay folding hanunshi akirji yana kallonta idanunshi sunyi jaa, with
so much confusion Abba ya kalleta sanan ya kalli Farida da Khaleel dake tsaye sanan yadawo
da kallonshi ga Islam yace "wai meke faruwa ne Ummi, wanan wace irin magana ne kikazomin
dashi haka, meke faruwa?" gyara zama Mum tayi tace "Alaji zan fadama" dan shiru tayi tana
kallon fuskar Islam sanan ta kalli Alhajin tace "ni dama ban fadamaka bane sabida banason
kaga kaman na tsangwami Islam ne, ka tuna fadan da ita da Farida sukayi kwanakin baya, to
ashewai Islam ce bayan Farida tagama bata labarin soyayyar ta da Khaleel shine Islam taje ta
kwacema Farida dake son Khaleel sosai Khaleel" shiru Abba yayi yana nazarin maganar Mum
sanan ya kalli Islam yace "haka abin yake Ummi?" ahankali ta gyada kai ganin yanda Abba ke
kallonta yasa tace "am sorry Abba" batare daya kalleta ba yakira Farida, ahankali Farida tazo
gabanshi ta tsugunna Abba yace "haka zancen yake?" gyada kai tayi sanan tace "Abba inason
Khaleel sosai shine ta kwacemin shi" tafashe da kuka tareda daura kanta akan cinyar Abba,
shiru Abba yayi sanan ya kalli Islam ahankali yace "kinason Khaleel ko baki sonshi, tell me the
truth?" ahankali ta juya ta kalli Khaleel da ita yake kallo sanan ta kalli Mum data jeho mata wani
uban hararan, kallon Abba tayi sanan ta girgiza kai tana kokarin hadiye kukan dake zuwan mata
tace "a'a bana sonshi" da sauri Abba yace "dama kinyi hakane dan ki bakan tama yar uwarki rai
ko?" da sauri ta girgiza kai, dago kai Abba yayi ya nunama Khaleel kujera, kasa zama yay
akujeran ya zauna akasa, ahankali Abba yace "Wakake so cikin su wazaka aura? Banason
tauyema kowa hakkin sa, yaran zamanin nan kuncika matsala wlh, ka fadamin gaskiya Khaleel
wakake so acikin su wazaka aura?" kallon Islam yayi hadamai hannu tayi sanan ta girgixamai
kai tana hawaye da sauri ya dauke kai, ya kalli Farida dake kallonshi kirjinta na bugawa
idanunta sun cicciko da hawaye ahankali yace" "Farida" murmushi Abba yayi yace "shikenan
Allah Sanya albarka, Allah muku albarka dukan ku saikaje ka sanar da iyayenka" Ahankali
yatashi yafita daga dakin, sauka yayi yafita daga gidan ya shiga mota ya daki sit din motar yafi
sau dari, wani bakin ciki mara misultuwa yaji yanaji da kyar ya iya tuka kanshi yakai gida.
Abba ya kalli Islam yace "mesa kika aikata irin abin nan Islam?" Mum tace "Alaji bawanan ma
kadai ba da Farida tamata magana shine fa takifa mata mari ranan harda fasamata baki, haba
haka ake abu a duniya, daga yar uwarki tabaki labarin saurayin ta saikibi takasa kije ki kwace
mata shi, kasan shi namiji wawane hala saisa lokacin ya biyemata ya yarda har aka turo, yanzu
dai alhaji tunda komi yay daidai basaika hukuntata ba nariga na yafemata, faridama ta yafe
mata shikenan magana ta wuce a cigaba da shagulgulan biki zamu aurar da ya" Ahankali Abba
ya sauke ajiyan zuciya yace "hakane kutashi kutafi" fita sukayi daga dakin Farida ta bangajeta
ta shige dakin Mum binta tai da kallo kafin ta wuce dakinsu a daddafe ta fada gado taci kukanta
tai bacci.
Manya manyan hajiyoyi masu gyaran jiki Mum ta daukoma Farida nan fa aka fara gyara
amarya ciki da waje idan kunga Farida en tai mugun kyau bakin fatarta har kara walkiya take,
ko tak baya hadata da Islam idan Islam zata wuni tana mata magana bazata kulata ba hakan
yasa kullum Islam na daki, Maman Miemie nema idan tazo aiki takan dan kawomata Miemie ta
dauketa suyita wasa, Khaleel bai kara zuwaba, Farida bata damuba tunda wani zubin yanadan
picking call dinta suyi magana daya biyu ya katse.
Yau saura sati daya biki yaune aka kawo akwatin Farida saitin goma sha biyar, su Umma da
Mujiba datai kini kini da rai dawasu kawayen sune suka kawo inda Mum da kawayenta lecturers
suka tarbesu akaci akasha, akasha guda, dazasu tafi aka basu tukuici. Da daddaren ranan Anty
Hindu tadawo daga dubai da kayayyakin daki data siyo anata murna Koda Islam tazo gaishe ta
kallonta tayi daga sama har kasa tace "ke ciwo kikayine haka wanan rama" murmushi tayi tace
"eh amma naji sauki" tsaraba Anty Hindu tabata sanan ta wuce dakinsu ta kwanta.
Washegari da safe Abba yafita da wurin kasancewar yanada aiki, Mum ce ta turo akwatinan
Farida ta shigo dasu dakin Anty Hindu one by one tace "ga akwatin Farida nan Anty?" kallonta
Anty Hindu tayi cike da mamaki tace " Farida Kuma wace Faridan?" kama haba Mum tayi tace
"au Abban su bai fadamiki ba, ai Anty Kwai ne yafashe gaskiya ta futa, ashe fadan nan da yaran
nan sukayi kan Khaleel ne, wai Islam kwacema Farida Khaleel fa tayi, shine da kanshi Khaleel
din yay tattaki yazo yafadi ma Abba shifa Farida yakeso ba Islam ba" tunda take maganar Anty
Hindu ke kallonta tace "Khaleel din yace hakan" "eh" murmushi Mum tayi tace "ga akwatin ki
duba kisa mana albarka" tabe baki Anty Hindu tayi tace "nayafe fitanmun dasu daga daki" tabe
baki mum tayi tafita dasu tana kunkuni tace "yar bakin ciki kawai" sosai Anty Hindu taji ranta ya
baci da zancen, wanan wani irin abune.
Family Khaleel kodaya fadan musu abinda ke kasa basu wani damuba kasancewa sunsan
Faridan dama.
Yau thursday da kyar Yusuf ya tirsasa Khaleel yatashi suje gidan su kaima Farida kudin fati, da
wasu yan abubuwa, da kyar yatashi ya shirya dan wlh bayason yamaje gidan balle yamaga
Islam shiryawa yay cikin shadda Light brown shadda daya mugun amsan shi ba karamin kyau
kayan sukamai ba sai uban kamshi yake, fara tsayawa sukayi sukai isha'i sanan suka tafi. Farida taci uban lalle dan gobene walima tasanya wata atampa da tasha uban stones, kallon
Sameer dake kusa da ita tayi ganin kiran Khaleel ya shigo wayarta tace "jeka cemusu su shigo
falo Ina zuwa" fita yay da gudu, ta zauna agaban mirro tana shafa hoda.
Ahankali take sakkowa daga stairs sanye da doguwar riga na atampa jada baki ta daura gyale
black akai, so take taje kitchen ta dafa Indomie kamshin turaren dataji yasa ta daga kai hada ido
sukayi daidai suna shigowa falon hanunshi rike da Sameer tsayawa yay chak yana kallonta
hakan yasa Yusuf ya Kalli inda yake kallo, da sauri takarasa sakkowa ta shiga kitchen, jingina
tai da fridge ta dafe kirjinta jin wani abu ya tsayamata awuya, tayi kusa 20 sec ahaka sanan ta
shiga store ta dauko Indomie guda daya da egg daya tafito, kamshin turaren shi taji da sauri ta
daga kai ta kallai suka hada ido ganin ya kulle kofar kitchen din yasa ta ijiye kwan da Indomie
akan fridge tajuya da sauri ta bude kofar dazai satada da backyard tafita, babu haske sosai a
backyard din dan kwan fitilar wajen ya mutu hasken wata ne kawai ke haska wajen, tafiya ta
soma yi da sauri zata zaga, hanunta taji ankama da sauri ta juyo fizgota yayi da karfi fuskarshi a
daure yasata abango yana wani irin kallon fuskar ta, ahankali yake matsowa har ya matso kusa
da ita sosai wanda gab din tsakanin su baifi tsawon yatsa ba dan tanajin saukar numfashin shi,
sosai kirjinta ke bugawa hakan yasa ta kawad da kanta gefe, ahankali yakai hannu ya kama
habarta ya juyo da kanta kin kallonshi tayi ta saukar da idanunta kasa, hanunshi daya ya daura
a bangon wajen dayan kuma na habar ta murya chan kasa yace "look at me, kin kasa kallonane
sabida kinsan u are forcing me to do dis?" sosai kirjinta ke bugawa, lumshe ido yayi sanan ya
budesu akanta ahankali yace "bakyacin abinci ko, look at your neck" yasa hannu yana shafa
kashin wuyarta buge hanunshi tayi hanun nata ya kama da sauri yadan matse hakan yasa tai
yar kara tana yatsine fuska yace "it hurt ko?" gyadamai kai tayi, dan murmushi yayi yace "zuciya
hurt more than this sau dubu dabara sabida abinda kika sata tayi" yakarashe maganan tareda
sakin hanunta yana nuna mata zuciyar shi da yatsa, dan shiru yayi yana kallon fuskar ta dan
har yanzu taki yarda suhada ido, hannu yakai yarike habarta yadaga kanta kaman mai rada
yace "kinfiso na auri yar uwarki ina dawainiya da sonki araina ko" shiru tamai, kasa daurewa
yayi ahankali yahada goshin su yana kallon idonta, hakan yasa itama ta dago idanunta dasuka
cika da hawaye ta kallai bakinshi taga yay motsi yace "I love you Islam" fashewa tai da kuka
sosai, hannu yakai ya share hawayen dake zubowa batare daya cire forehead dinshi daga nata
ba, ahankali ya saukar da yatsar tashi akan lips dinta, shafa su yayi yana kallon idonta,
hannunta tasa ta bigemai hannu, lumshe ido yayi ya maida fuskar shi ta gefen kunnenta ta,
goga mata sajen shi akumatun ta yayi wani yarrr tajj yabi kowani gashin fatarta sabida yanda
gashin sajen suka tattaba fatar, kokarin tureshi tafara yi hakan yasa ya cigaba da gangaro da
sajen nashi har wajen lips dinta, ahankali ya juyo da kanshi daidai ta wajen hakan yasa lips
dinshi yahadu da nata.
Wlh kun daman saisa namuku typing. Gaskiya Naga Farida tafi fans, lol.
I love guys.
[6/22, 7:53 AM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
47 & 48
Yakamo hanunta yarike gam yana yar dariya, turo baki tace "kasaken" make mata kafada yayi
yaja hanunta har gaban wardrobe, wani madaidaicin black hijab yaciro ya warware yasaka mata
sanan yarike mata hannu ya kalleta yace "banason ana kallon mu goody bag dina muje naraka
ki" akunyace ta dauke kai, tare suka fita daga dakin suna zuwa dining tafara kokarin kwace
hanunta sabida mutanen datagani su kusan five ga manyan kuloli kusan