Showing 1 words to 3000 words out of 68809 words
Chapter 1 - JARABTA Book Complete Document by Maman Abdul Shakur.pdf
[6/7, 11:23 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
....... 1
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Wanan novel din kirkirarren labari ne.
"au Khaleel ne shine kawani tsaya a bakin kofa bazaka shigo ba" murmushi dake kara fito da
kyanshi yayi ya shigo dakin da gudu yaron dake jikin matar yatashi yayo kanshi da muryan shi
irin ta yara yace "Uncle Khaleel" tsalle yayi hakan yasa kakkyawan matashin dake sanye da
Shadda sky blue wacce akamai dinkin 3quater daya kara amsan cikakken jikin shi yadau yaron
ya shilla shi sama yace "my boy" sanan ya sakko dashi ya zauna akan kujeran dake falon yana
sunnar dakai ahankali yace "ina yini Mama" tashi matar da akalla zatakai 45 tayi tareda daukan
plate din data gama bama auta abinci aciki tai murmushi tace "Khaleel manya bazadai mubar
yar kunyan nan bako, ai shikenan bari naturo ma ita" ya kalli Auta wanda tuni ya maida jikin
Khaleel din filin wasa tace "Oya Auta kadai san ba wajen ka Khaleel yazo bako, tashi mutafi
ciki" noke kai yayi yaron yace "oh'oh" tabe baki tayi ta wuce sama abinta. Khaleel ya kalli yaron
saida yafara jujjuyawa ya tabbatar daba kowa adakin sanan ya kalli yaron ahankali yace "My
Boy where is Anty Aisha?" sauka yaron yay daga jikinshi yafara tafiya sanan yace "cana dacinta
cana cifan citso" shigowan wasu yara kyawawa guda uku mata biyu sai namiji daya yasa yay
shiru da sauri suka yo wajen Khaleel atare suka gaidashi "Ya Khaleel welcome" murmushi
yamusu yaja kumatun wacce tafisu girma yace "Hello my fatty Fatima" sanan yaja kumatun
dayar wacce ita kebi mata yace "Hello my skinny Maryamu" sanan yaja kumatun dayan namijin
yace "Hello my Hafiz Ibrahim how was the madrasa today?" kasan cewa islamiyan su 3 narana
ake zuwa ataso su 8 nadare achan suke sallar la'asar, magrib, da issha'i atare yaran sukace
"Fine Uncle Khaleel" suna mugun son Khaleel Shima haka yake sonsu, Chocolate din daya
kawomusu ya basu nan sukamai godiya cike da murna suka tafi sama dan nunama mummy.
Yaye labulen dakin Mum tayi hakan yasa ta juyo da sauri, wata faran budurwa ce dabazata
wuce 22 ba, doguwa ce sosai amma batada kiba, zaune take akasan dakin su tana tsifan gashi.
Haba Mama tarike tace "eyye yau iskanci naki ne yatashi ko meye kin bar bawan Allah shikadai
har yanzu a falo" dan turo baki tayi a shagwabe batare datace komiba, kwafa Mama tayi tace
"yo ai shikenan bari nacemai yatafi abunshi" da sauri ta mike tsaye tace "uhmm damafa umm"
Mama ta juyo tace "dama me?" shiru tayi tana wasa da yatsar ta dan murmushi Mama tayi tace
"will u get out of this room my friend" dogon hijabin ta dake kan gado taja tafita daga dakin
tsayawa tayi anan corridor tasa hijabin sanan ta wuce, kada kai Mama tayi tace "andai kusa nan
da 4 weeks ne mumuku auren kowama ya huta fitinan nun yara" ta shiga dakin Ibrahim rike da
hannu auta dan jimai haddan dazai bayar gobe.
Tunda take sakkowa daga stairs yake kallon ta harta karasa sakkowa ko kallon inda yake ba
tayi ba ta wuce kitchen abinta fridge ta bude ta ciro zobon data hadamai da yamman nan mai
sanyi wanda yaji cucumber da water melon, ta daura jug din akan tray sanan tasa karamin
glass cup akan tray din tadau tray din tafito ahankali take tafiya kaman batason taka kasa
wanda dama haka tafiyan nata yake karasowa gaban shi tayi da sauri ya mike ya karbi tray din
hannu nata wanda dama haka dabi'an shi yake, tunda tasan shi bata taba kawomai abu ta ijiye
da kanta ba dan da sauri yake tashi ya karba. Ganin ya karba yasa ta dauko table ta ijiye
agaban shi ahankali hannu tasa ta karbi tray din, hannu shima yasa ya sake karban tray yayi
yana kallon kakkywar fuskarta wanda kwayar idonta yake kasa dan taki yarda su hada ido, cikin
wata irin murya wanda ita kadai yakema muryan nan aduniya yace "My Eesha" kin amsawa tayi
saima sakinmai tray din datayi. ahankali yadan tsugunna ya ijiye tray din still yana kallon fuskar
ta tashi tayi fuuu zatabar wajen hakan yasa ya rike gefen hijabin ta chak ta tsaya batare data
juyoba hakan yasa ya sauke ajiyan zuciya tareda yin taku biyu yazo gaban ta, sakin Hijabin yayi
yay folding hanunshi a kirjinshi yana kallon fuskarta dahar lokacin taki kallon shi, cikin wani irin
tattausan murya irin na lallashin mai fushi kuma karamin yaro yace "My Eesha" kin dago kanta
tayi saima yatsun ta datake ta wasa dashi, kallon upstairs yayi ganin babu kowa a saman yasa
yakara matsowa dab da ita ahankali yace "My Eesha please look at me" saida tai kusan 10
seconds sanan tadago idanunta dake kyalli sabida yanda hawaye ya cika su tam, hakan
bakaramin tadamai da hankali yayi ba Kara tausasa murya yayi yace "am sorry" ajiyan zuciya
ya sauke kaman shima zaiyi kukan sabida yanda hankalin shi yatashi "My Eesha nabar wayana
a office ne nadan fita waje just to come back na tarar da Zainab tai picking call dinki, wlh trust
me I don't have anything to do with her please am sorry Saheeba" hawayen ne suka shiga
gangarowa sosai lumshe idonshi yayi ahankali kafin ya budesu ya kalleta sosai idanunshi sukai
jaa cikin wata irin karamin murya yace "please ki share hawayen ki okay" ahankali tasa bayan
hanunta ta goge hawayen tas, ajiyan zuciya ya sauke sanan yace "kin yafemin my Eesha?"
gyadamai tayi hakan yasa yay murmushi sosai yace "to adan kalleni mana" ahankali ta dago
manyan idanunta ta kallai tareda sakin mai murmushi daya lobar da dimple dinta ciki sosai wani
sanyi yaji har karkashin zuciyan shi ita tafara yin gaba sanan yabita a baya tsugunnawa tayi ta
tsiyaya mai zobon a cup sanan ta koma ta zauna akan kujeran dake facing nashi daukan cup
din zobon yayi yakai bakin shi yasha wani irin sanyi da zobon yayi ga dadi mai sanyaya rai
lumshe ido yayi ya kwankwade duka yasake karawa ya shanye yasake karawa hakan yasa ta
ware ido cike da mamaki, daga mata gira yayi yace "my Eesha bazan iya forming ba gaskiya is
too sweet" kyalkyacewa tayi da dariya Jin horn din mota yasa ta tashi da sauri yana kallon
agogo karfe goma harda minti biyar cikeda rashin Jin dadi yace "oooohh wai su Abba harsun
gama hiran dawuri haka ne" dariya tamai tareda mai gwalo ta tashi da saurin tayi kitchen hakan
yasa yaciro car key din shi daga aljihu yarike a hannu daidai lokacin tafito da baban goran Eva
dake cike da zobo tasamai a ledda binta yake da kallo harta karaso gaban shi ta ijiye akan table
sanan ta dago batare data kalleshi ba tace "good night" dadan gudun ta tayi sama saida takai
karshen stairs sanan ta juyo ganin ita yake kallo har lokacin yasa ta wara ido tace "go" make
mata kafada yayi hakan yasa tasake murmushi tace "go" kara make kafada yayi yaki tafiya
bude baki tayi zatai magana daidai lokacin anbude kofa ta arce da gudu ta shige dakin su.
Daukan ledan goran zobon shi yayi ya sunnar dakai yana dan sosa keya kaman mara gaskiya
yace "welcome Abba" kallon shi mutumin yayi from head to toe sanan ya girgiza kai yay gaba
abunshi hakan yasa kaman wanda aka hankada yay hanyar kofa "Khaleel" yaji muryan Abba
hakan yasa adan firgice ya juyo yace "naam Abba" Hawa stairs Abba yafara yi sanan yace "tell
ur Dad sun chanza time din meeting din daga 9 zuwa 11 :30" ahankali yace "to Abba sanan ya
bude kofa yafita, motar shi ya shiga gate man ya bude mai yafita daga gidan. Gidaje uku ne
duka tsakanin su yay horn aka budemai gate, parking yayi ya shiga ciki babu kowa a parlor
hakan yasa ya wuce sama, direct dakin Mum ya wuce bata ciki hakan yasa ya kwanta kan gado
ya lumshe ido fuskar Eesha ke mishi yana, bude kofa da akayi yasa yadan bude ido kadan yace
"Ammi" batare data kalleshi ba ta zauna agaban madubi tana share ruwan dake fuskarta,
ahankali yasake cewa Ammi juyowa tayi ta harareshi tace "look Khaleel please kabarni nai
bacci nariga nasa Ilham ta kaima abincin ka daki, ka girma amma wlh kafi kaninka fitina" dan
yatsine fuska yayi yace "Ammi I don't want food I want another thing" ajiye cream din da Ammi
ta dauko tayi ta juyo fully tana facing dinshi sai a lokacin ta lura da damuwan dake kan fuskar
shi hakan yasa tace "mekake so to?" dan murmushi yayi sanan ya sosa kai kaman mara
gaskiya yace "Ammi kinsan u are d best, u always brings me first, my one and only sweet
Mama" murmushi Ammi tayi tace "Khaleel bangane wanan sweet mouth dinnaka ba just tell me
wat do u want" kara sosa kai yayi tareda noke murya yace "please Ammi kima Dad magana
Yama Abba magana please, Ammi nidai gaskiya arage tsawon bikin nan tunda dai next week
zata gama exam basai ayi bikin upper week ba" yakara she maganan yana kallon fuskar Ammi
data kafeshi da ido baki sake. Ahankali yasake cewa "Ammi naaaaa" ahankali yaga Ammi takai
hannu tana kokarin ciro slippers din kafanta hakan yasa yay jumping daga gadon da gudu yay
waje yakucan cin karo da Dad da sauri ya matsa yace "sorry Dad" ya bar wajen da sauri ya
shiga dakin shi yana haki.
Visit mamanshakur.wordpress.com for all my write-up
[6/7, 11:23 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
2...
Shiga dakin Dad yayi yabi Ammi da kallon tambaya murmushi kawai tayi tadau man shafawan
ta tsayaya a hannu tace "wlh Alhaji dan nan naka baida kunya cewa yayi wai nacema tunda
Aisha zata gama exam next week wai please ayi bikin upper week he is tired of waiting"
murmushi Abba yayi tareda daukan news paper shi dake kan gado yace "Zan sami baban Aisha
da maganar gobe" da sauri Ammi ta kalleshi tace "what?" bude jaridan Dad yayi yace "I said
zan sami Baban Aisha da maganar" da sauri Ammi tace "haba Alhaji kuwai maza maisa tunanin
ku daban ne, mu bangaren mu mata bamu gamaba fa ina aka gama shirya yarinya eyeh" tabe
baki Alhaji yayi yace "ke yanzu baki gaji da ganin katon matashi a gidan nan ba, abin dadi ne
ma yaran sun kosa suyi auren gwara mumusu kafin shaidan ya shigo lamarin" yatsine fuska
tadanyi tace "ai shikenan".
Saida yay shafa'i da wuturi sanan ya kwanta a kan makeken royal bed dake dakin shi, wayarshi
ya jawo tareda kashe bedside lamp din dailing number dayay saving da heartbeat yayi saida
wayar yakausa katsewa sanan ta dauka batare datace komiba, shiru shima yayi hakan yasa ta
lumshe idonta shima lumshe idonshi yayi sanan yace "my one and only Eesha" cikin siririyar
muryarta tace "kana gida?" murya Chan kasa yace "yes dear, tell me how are was your day?"
ahankali tace "my day was bad" da sauri yace "why? Maisa my Eesha?" shiru tadanyi nayan
sakanni kafin chan kamar wacce zatai kuka tace "I don't wanna talk about it" lumshe ido yayi in
so much pain yace "maisa baki yarda daniba, there's nothing going on between me and her, my
Eesha I love you don't you get it? Zuciyata taki ce kadai, I don't think wanan zuciyar nawa zata
taba son wata mace aduniyan nan sama dake, my Eesha trust me please or kinason nafara
miki kuka ne?" da sauri ta girgiza mai kai kaman yana wurin murmushi yadanyi sanan yace"
don't worry bayan bikin mu zan lallasheki da kyau okay" make kafada tayi tareda cewa "oh'oh"
dan murmushi yayi mai kara yana kara jin wani irin zafin sonta na ruruwa a rashin, ahankali
yace "wani paper kukeda shi gobe?" cikin sanyin muryanta tace "GNS221" "hope you read very
well?" ahankali tace "eh" "wat time is the exam" murya chan kasa tace "afternoon paper ne 2 to
4" ahankali yace "okay" shiru sukadan yi na kusan 5 min ahankali yace "My Eesha" murya chan
kasa tace "uh" kara kwantar da murya yayi yace "ina sonki dayawa, I love you so much my
Eesha" murmushi tayi tasa hannu ta rufe fuskarta dashi murmushi yasakeyi yace "bazaki cemin
you love me ba" turomai baki tayi tace "su Faty fa na nan" ware ido yayi yace "nizakima wayau
yaran da tuntuni sunyi bacci" murguda mai baki tayi tai shiru kara kwantar da murya yayi yace
"haba babyn khaleel yakuri to fadamin kodan kadanne that you love me please my Eesha" shiru
tadanyi hakan yasa ya lumshe ido yana jira ahankali da dan karamin muryanta tace "I love you
Ya Khaleel" dip ta kashe wayan wani irin dadi ne ya lullube shi da sauri yasake dailing number
amma bata dauka ba yasan dama bazata daukaba text ya tura mata "good night my Eesha, I
love you" yay sending sai bayan ta karanta message din sanan ta rungume wayan tareda yin
addu'an bacci.
Shirye yake da uniform dinshi na navy bakaramin kyau dan farin rigan yasake haska bakin fatar
shi, dining ya karaso ya gaida Dad da Ammi dasuke cin abincin su wayar shi ya ijiye da car key
akan dining yay sama dakin kanenshi ya bude ganin suna gaban mirror Ilham nama ihsan
makeup yasa yawani ja dogon tsaki yace "wlh if I count 3 baku tafi dining ba yau saida kuje
school da kafa, one two" da gudu suka tashi suka dau jakunkunan su ta gefenshi suka fito ajiye
cup din tea Ammi tayi tace "da kyau haba Yara sai sufi awa uku ana shafe shafen banza" zama
sukayi daidai lokacin ya karaso dining Shima ya zauna ihsan tai serving nasu, Abba ne yafara
gamawa yaciro 5k yabama Ihsan yace "gashi nan kuyi amfani dashi a school" ya kalli Mum nina
tafi, godiya sukayi sukamai da addu'an Allah kiyaye. Shiya fara mikewa hakan yasa Ilham ta
langabar dakai tana kallon Ammi, Ammi tace "Son kadan jirasu su gama nasu break din mana"
hararan su yayi yace "Mum sunsan zasuyi break suka tsaya fentin fuskan su, my friend will u
get up ko na tafi abina" hakanan suna kunkuni suka tashi sukama Ammi sallama. A bakin gate
din Baze university yay parking kaman zasuyi kuka suka ce "Yaya Khaleel dan Allah ka shiga
damu daga nan zuwa lecture hall danisa wlh" wani yar dariyar mugunta yayi bayan ya kalli
kafafuwan su yace "gashi anci uban hill fa" yakara fashewa da dariya Ilham sarkin kuka harta
fara matsar kwalla Ihsan tace "kai Yaya Khaleel bazamu kara batama lokaci ba" saida yagama
daddana wayar shi sanan ya kunna motar ya shiga dasu sabida sundan bashi tausayi abakin
lecture theater ya ajiye su tareda basu 5k sanan ya wuce aiki dan yay latti.
Tun daga nesa ya hangota tana sanye cikin sky blue hijab mai hula fuskarta fayau ba makeup,
lips dinta sunyi jaa sosai hakama hancin ta, ahankali take tafiya tanadan yatsine fuskarta fitowa
yay daga motar ya jingina da motar tareda rungume hannayen shi a kirji bata lura dashi ba
hakan yasa ta cigaba da tafiya, dan yatsine fuska tasakeyi tareda cire Jakarta data rataye a
kafadar ta bude tissue ta ciro tasa akan hancin ta ta rike sabida atishawa takeji ahankali yafara
tafiya harya karasa inda take a tsaye muryan shi kawai taji akanta "My Eesha meke damunki"
dago idanunta tayi ta kalleshi yana sanye da uniform alamun daga office yake idanunshi boye
cikin black shade wani sassanyar murmushi ta sakin mai, hannu ya mika mata ya karbi jakan
hanunta har lokacin yana kallon fuskarta yace "baki da lafiya ne?" yatsine fuska tasake yi tace
"am fine just mura nake yi" ganin yanda yan school din ke ta kallonsu wanda apparently shi
suke kallo yasa ta gimtse fuska tace "mutafi" bude mata front seat yayi ta zauna sanan ya koma
mazaunin driver ya zauna ya tada motar suka fita daga school din ganin yanda taketa atishawa
yasa yay parking agaban wani pharmacy, maganin mura yasiyo mata da bottle water sai kuma
cold farm fresh yogurt, bude side dinta yayi ya tsaya ahankali ya bude kwalin maganin ya ballo
guda biyu yabata tareda bude marfin goran ruwa ya mika mata yatsine fuska tayi kaman zatai
kuka murya chan kasa yace "please my Eesha for my sake" hakan yasa tasha da kyar kaman
zatai amai da sauri ya karbi goran ruwan sanan ya bude mata yogurt din yabata yace "take this
sabida karki amai" karba tayi ya maida kofan ya rufe mata sanan ya koma mazaunin driver ya
tada motar, batawani sha dayawa ba ta rufe ta ijiye, ahankali yace "are you okay?" gyada mai
kai tayi kafin ta lumshe ido within one minute bacci yay gaba da ita, murmushi yayi dan yasan
tana tashi cikin dare tayi karatu ahankali yake tuki haryakai anguwan su, abakin gate dinsu yay
parking ya juya yana kallon ta yanda take baccin ta hankali kwance hancin ta yay ja sosai
abunku da farar fata, hakama lips dinta wani irin sonta yaji nakara shigan shi ahankali yakira
sunan ta "My Eesha, My Eesha" bude ido tayi kadan kafin tabude su duka magungunan da
yogurt din ya dauka yasa acikin Jakarta yabata, ahankali tasa hannu ta karba yace "ko muje
hospital ne?" da sauri ta girgiza kai ahankali tace "am fine idan naje gida zansha ginger tea I will
be fine" dudda baiso ba hakanan yace "okay on ur phone to, I will call you later" gyada mai kai
tayi ahankali ta bude kofa ta juya zata fita da sauri yace "My Eesha" juyo dakai tayi ta kalleshi
murmushi yamata yace "I love you" murguda mai baki tayi tafita da sauri, dan murmushi yayi
tareda girgiza kai saida ta bude gate dinsu ta shiga sanan ya kuna motar yay reverse office
dinsu ya wuce dan excuse ya dauka yafita dama.
Zaune yake akan kujera yana rubuta report da laptop dinshi knocking akayi hakan yasa yabada