Showing 48001 words to 51000 words out of 140774 words

Chapter 17 - MATAR DAMISA Complete Novels By Asmeetah.doc

Asmeetah   

23 Sep 2025

2289

kan Ayush yana faWin "idan kin gama koke-? nakin inaso zan kwanta bacci..

?aga kanta tayi tana kallon fuskar sa cikin rashin fahimta ta mi?e tsaye murya ciki-? tace "mommy tana nan ne?"
Shi sai lokacin ma ya tuna shin ta dawo ne daga asibitin ko kuma tana can har yanzu, yasan halin mom yanzu sai tace zata zauna a gurin Dr. Hasheem!

Bin ta gefen Ayush yayi yana faWin "let me check her.."
Itama bin bayansa tayi da kallo har ya fice daga Wakin, zuciyarta fari sol ita kaWai sai murmushi take yau jin kanta take kamar ba ita ba!
a ranta take faWin "yanzu zan samu damar aiwatar da aiki na akan Junaid, zan cika burin mahaifiyata, haba yanzu ka fi kyau wallahi amma mutum koda yaushe fuska a Waure kamar wanda aka aiko wa sakon mutuwa."
Maganar zuci take kamar wanda take magana a gabansa!
Gaban mirror taje ta tsaya tana kallon kanta a ciki, ga light Win Wakin green colour, fuskar nan sai she?i yake...

"?ingel! ?ingel!! ?ingel!!! kada ki wahalar da zuciyarki akan abun hari na kuma ma?iyina,
Junaid ba mijin Aure bane domin bazamu taSa barinsa yayi Aure ba indai yana raye!
Ke sarauniya ce, kuma gimbiya, kada ki ?as?antar da kanki akan Wan masa?ina wato shalelen damusa na,
Hahaha! Hahahah!! Hahahaha!!! "

Ayush tayi matu?ar tsorata da jin waWannan maganganun a ta cikin madubi,
Bayan ya kammala wani irin dariya yake yi har saida glass Win madubin ya tsage....

Jaa da baya tayi tana furta "Innalillahi wa inna ilaihi raju'un, wanene kai"
Ji tayi an ?ara tintsirewa da dariya sannan yace "yau zan sanar miki ko ni waye ne, amma inaso ki fita daga cikin rayuwar Junaid domin kina hanani rawar gaban hantsi, idan kina tare da shi damusa na jinya yake baya samun lafiya har sai kin bar gurin da Junaid yake.."

Jin hakan yasa Ayush ?ara matsowa dab da jikin madubin a hankali ta furta "Abbah!".

Wani irin haske ne ya bayyana a jikin madubin ya soma she?i ga taurarin da suka bayyano suma ta cikin madubin,
Ita ma Ayush haske ne ya bayyana a jikinta sai wal-wali take, wannan hasken ne ya janyeta cikin madubin ta Sace Satt...

Tsintar kanta tayi a cikin wani sansani wanda ko bishiya babu a waran balle Wan adam ko tsuntsu babu, ?asar gurin fari sol sai feshin ?an?aran da ake yi!
gurin ya yi matu?ar burgeta sanyi ne yake ratsa duk ilahiriin jikinta, weather yayi matu?ar yi mata daWi sosai,
Duba kanta tayi taga abun mamaki an canza mata kayan jikinta zuwa gown doguwar riga fara sol, daga saman rigar ya matse ta zuwa kunkumin ta kuwa rigar ya baje sosai ta bayan har jan ?asa take, rigar dogon hannu ne na net ga wani irin takalmi a ?afar ta mai shegen tsini shima farin ne tas, sai gyaran gashi data sha an tuttu?e gashin sannan aka sanya mata hular sarauta na gold mai she?in bala'i,
Anyi mata makeup sosai wanda duk wanda ya ganta sai ya suma tsabar kyan data yi!
Ga wasu zobina na gold suma yanda aka jera mata su a duk yatsun hannun ta, sai warwaraye suma na gold sai she?i suke,
Sai kuma sar?ar wuyanta mai Waukar ido ya kame wuyanta gam shima sai bada kalar hasken sa yake,
Hatta ?afarta sai da aka jera mata sar?o?i wanda tana tafiya suna bada kalar sauti...
*MASHA* *ALLAH* Ayusher fa ta fito sai wanda ya ganta zai bada labari kamar dai Asmeetah domin har musabaha mukayi =??=??

Kallon kanta take yi da gasken gaske fa itace abun ya yi matu?ar bata mamaki, kanta ne ya Waure tana cigaba da kallon wajen da take
"Wai aina nake nam? ko dai mutuwa nayi ne aka kawoni nam! Ga kuma feshin ?an?arar da akeyi ba ruwa kuma, ?asar gurin laushi ga kuma fari tass...."
Magana take a fili tana ta waige-? ..

?arar gudun doki taji daga nesa ana nufan gurin da take tsaye, idonta akan yanda zataga Sillowar mai tafo wa!

Wani mutumi ne fari tas dogo ne sosai ga ?iran jiki kamar basamude duk jikinsa a murmurWe gashi da ?irar ?arfi,
Ba riga a jikinsa sai wasu tarukucan sar?o?i a wuyansa da kuma dantsen sa duk sar?o?i yanda ya WaWWaure su a ?atoton dantsen sa!
Suman gashin sa kuwa har gadon bayan sa ga laushi, sai wandon buzaye dake jikinsa,
Yana gudu da doki wanda shima yasha kwalliya, ta ?asan sa kuma wani ?aton damusa ne shima yake ta ti?ar gudu shima har da sar?ar sa a wuya...

Sai da yazo daf da Ayush sannan ya tsaya tare da sau?owa akan dokin,
Tsayawa yayi a gaban Ayush yana kallon ta da murmushi a saman fuskar sa.
Yace
"?ingel na gaisheki gimbiya mai sarauta a hannu" sai da ya sunkuyar da kansa ?asi alamar girmamawa sannan ya mi?a mata takobi mai shegen masifar kyau ga she?in da yake yana wal-wal, hannu tasa ta karSa idonta akan mutumin mayar da tokobin tayi cikin gidansa
Tana faWin "godiya nake...."

Shima damusan dur?usawa yayi ya gaishe da Ayush sannan ya mi?e,
Sake baki Ayush tayi tana kallon ikon Allah, a cikin ranta tace "ni kuwa a duniya nake?"

Kamar wanda yaji abunda tace sai ji tayi ya katseta da cewa
"Ha?i?a keWin gimbiya ce, kuma a duniya kike nan Win bayan masarauta ta ce! ba mai zuwa nan sai ni da kuma shalele na ya nuna damusar sa da hannu...."

Ayush baki na motsi kaWan-? tace "waye ne kai?"
Murmushi yayi yana kallon ta yace "Singel, ni mahaifinki ne wanda kika daWe kina son gani amma hakan baiyu ba sai yanzu gani ga ki Singel"

Zaro ido waje tayi cike da mamaki take kallonsa bata san lokacin da wani irin farin ciki ya ziyarce ta ba tana faWin "yau ni ce a gaban mahaifina" lokaci guda kuwa ta fashe da kuka....

Tallafo kanta yayi yana faWin "gimbiya bata kuka amma kin mayar da kuka abun sana'ar ki, hakan yana ?ona mun rai Singel,
Inaso ki zama jaruma, idan ana ri?e da takobi kuka ?ai?ashewa yake!!!
Goge mata hawayen da ya zubo mata yayi da hannayensa masu laushin gaske...

(ikon Allah! A tunani na zanga wani dattijon tsohon boka sai kuma naga akasin haka,
Kyakykyawan mutum mai siffar jaruman bahindiye,
A tunani na zanga ?azamin boka amma sai naga fashion man, a ?alla shekarun sa bazasu wuce 45 ba, Ayushh kuma tana da 20years a duniya....)


"?ingel nasan kin tsaneni a cikin zuciyarki, sakamakon labarin da mahaifiyarki ta baki akaina, wanda hakan ba gaskiya bane,
Mahaifiyarki bata san komai a kaina ba, ni ba mungu bane, ni ba azzalumi bane, ni kaina nasan dalilin daya sa nake wahalar da Junaid wanda sirri ne a gareni, zaki san wannan sirrin amma ba yanzu ba akwai lokaci!
?ingel ki daina Waukar kanki cewa ke bakida ?anci,
Ke ?a ce kamar kowa ni mahaifinki ne, kuma ta hanyar Aure aka sameki, amma sai dai mahaifiyar ki bata san da hakan ba,
Ni na sanar miki ne domin ki sakawa ranki nutsuwa, ki kwantar da hankalin ki a matsayinki na ?er masarauta gimbiya *MAYUSHERT* asalin sunanki kenam!!!
Sannan mahaifiyarki tana nan da ranta bata mutu ba, akwai lokacin da zakii ganta ba yanzu ba...
Kece AYANAR JUNAID hakan yasa damusa na baya iya motsi idan kina tare da Junaid domin duk wani motsin sa yana a tattare da Junaid,
Rashin motsawarsa kuma illa ne hakan yasa banaso kina kusantar shi saboda damusa yana cutuwa motsinsa kuma zaisa Junaid cutuwa,
Makaryar wannan tsafin kuma yana tattare da ke, hakan bazai yuba saboda zaki iya cutuwa, kuma zan iya rasa duk wani ?arfin ikona...."

Ajiyar zuciya yajaa yana kallon Singel Winsa wacce itama kallon mahaifin natan take..

LeSenta ne yake motsi da ?er ta iya cewa "meye abun dake jikina na makaryin tsafin?.."

Dariya yayi short har sai da dimple Winsa ya lotsa yace "bazan sanar miki ba Singel, saboda nasan idan soyayya tayi nisa zaki iya cutar da ni,
Amma inaso ki sani cewa bazaku taSa yin Aure ba a tsakaninku ke da Junaid,
Har sai an karya wannan tsafin jikinsa, idan kuma ba haka ba
*DAMUSA* *BAZAI* *AURI* *GIMBIYA* *MAYUSHERT* *BA*...

Kafin ta furta wani abu ya kuma katseta da cewa "ga wannan duk wani ?undin tarihi na yana ciki, kada ki bari wani ya gani"
Wani ?atoton littafi ne ya mi?a mata a bayan littafin an zana masarauta.....
Ya kuma cewa "duk wanda ya Wauki littafin nan bazai taSa buWe shi ba, sai wanda yake da ala?a da masarautar kamar ke...
Na barki lafiya ?ingel.."

Juyawa yayi yahau saman dokin sa,
Ayush kuwa tana ri?e da takobi da kuma littafin da aka bata
Baki na rawa tace "shin menene sunanka?"

Murmushi yayi sannan yace " *SARKI* *RAAMAD*..

Ya kamata ki rage tsoro domin ke jinin Jarumi ne....
Sannan ni ba Boka bane sai dai na kasance ni matsafi ne, kuma ni musulmi ne! kada kuyi mun mummunan fassara..."

Yana kaiwa nan yayi tafiyarsa.
Ita kuwa Hasken daya kawota shine ya kuma Waukar ta....
Sai tsintar kanta tayi a cikin toilet ga ruwan shower yanata zuba..
Jikinta ta duba taga jallabiyan Junaid aka maido mata dashi, ga kuma hannunta ri?e da littafin tarihin mahaifinta da kuma takobin da ya bata...

Bata ankara ba taji ance "Yushert wai mekike a toilet haka since."
Muryar Junaid ta jiyo yana magana..
Wanda tin Wazu shigowar sa room Win bai ganta ba sai zubar ruwa yake ji,
A tunaninsa wanka take sake yi, bai yi tunanin babu kowa a ciki ba...

Rasa yanda zatayi da abubuwan da suke hannunta ta yi, da sauri ta buWe drower cikin toilet ta a jiye su a ciki sannan ta rufe..
Ta kashe ruwan dake zuba sannan ta fito,
Zuba mata eyes yayi yace "daman ba wanka kike yi ba tin Wazun? to me kikayi kenan?"

kiWimewa tayi ta soma ?in?ina tana faWin "daman daman da daman nayi ne"
Kallon ta yake cike da mamaki yace "kinyi mai?"
Gaba Waya ta rasa mai zata ce, sai kawai zuba masa ido tayi...

Tashi yayi daga zaunen ya nufi toilet ya buWe ya gama dube-dubensa
Yakai idonsa kan drower yasa hannu zai buWe da gudu Ayush tayo kansa tana faWin "na wanke toilet ne kar ka Sata shi," ta kuma ri?e hannunsa wanda yakai zai buWe gurin ma'ajiyin ta.

"Mtsw kuma shine ina tambayarki kika yi shuru?.."
Sunkuyar da kanta tayi ?asa ta kasa Wagowa,
Jan hannunta yayi suka fita daga cikin toilet,
Kai tsaye haurawa saman bed Winsa yayi
Ya kwanta tare da janyo mayafi ya rufe jikinsa
Tsayawa tayi Ayush, yace "ke bazaki kwanta bane?"

Murya ciki-ciki tace "ni bazan iya kwanciya a tareda kai ba"
"For what?"
Ya tambaya a takaice.
"Saboda bazan iya juran yanayin da zan shiga ba!"
"Ban ganeba? What do you means?"
Yayi tambayar yana kallon fuskar ta.
Sunkuyar da kai tayi ta kasa cewa komai...

Tashi yayi daga kan gadon
Yace "toh kwanta na bar miki gadon tinda bakyason kwanciya da ni"
?aukar pillow yayi yaje saman sofar Wakin ya kwanta...
Itama bin kan gadon tayi ta mimmi?e tareda rufe kanta da mayafi..

Maganganun mahaifinta ne suka soma dawo mata kwakwalwar ta,
Tayi matu?ar yin farin cikin jin abu biyu daga gare shi
Mahaifiyarta tana raye, da kuma ita ba ta hanyar fasi?anci aka sameta ba,
Wannan abun yayi mata daWi a ranta
Bugu da ?ari kuma taga mahaifinta face to face tinda aka haifeta bata taSa ganinsa ba.....

A ranar da farin ciki ta kwana.......!


*MASHA* *ALLAH*
yaaa Allah kamar yanda ka bani damar rubuta littafi na Allah ka bani ikon kammalawa =?O?=?O?



*>?? SDEENDTM DATA SERVICES>??*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ? 300. 1GB = ? 350
2GB = ? 600.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login