Showing 21001 words to 24000 words out of 59226 words

Chapter 8 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

ba amma
sai Salimat tayi biris da shi. Lokacin da Hantaru ya tabbatar da
cewar Salimat ba za ta saurareshi ba sai ya mike tsaye ya shiga
cikin dakinsa ya bude wata katuwar akwati ya dauko ajiyarsa ta
takobin Saiful Lujara wacce ke lullube a cikin mayafi. Hantaru
bai sake daukar komai ba a cikin dakin kawai sai ya fice daga
cikin gidan ya kwanto doki guda daga cikin bargar dawakai ya
hau kansa ya kama tafiya ba guzuri babu tanadin komai.
HANTARU YA NAUSA cikin daji ya rinka tafiya ba ji ba gani, dare
da rana
ko yaushe takobin Saiful Lujara na rataye a bayansa.Duk
sa'adda ya gaji sai ya yada zango a duk inda ya ga dama, idan
kuma yaji yunwa sai ya yi farauta a cikin daji ya samo abin
kalaci.
Haka dai Hantaru ya ci gaba da tafiya yana ratsawa ta cikin
dazuzzukan masu mugun hadari,amma bisa mamaki sai
Hantaru ta ga ko sau daya bai hadu da wata muguwar dabba da
ta durfafeshi,kai ko aljanu idan suka hangoshi daga nesa sai su
tarwatse su kama guje-guje suna neman maboya.ldan kuwa
riskarsu ya yi tsulum sai su kama yi masa sujjada suna tuba da
neman gafara tamkar sun ga mutum a gabansa. Al'amarin da
yai matukar bashi mamaki ke nan.
Abin da bai sani ba shi ne, ba komai ne ya janyo hakan bs face
wannan takobi ta Saiful Lujara ds ke ratayea bayansa. Sirrinta
shi ne, in dai mutum na tare da ite duk irin halittar da ganshi sai
ta ganshi firgice te razana ainun walau mutum ko dabba ko
dodo.
Sannu-sannu darare na shudewa rana na wucewa har Hantaru
ya shafe wata uku yana tafya har ya iso birnin Kisra. Da
shigarsa cikin garin sai ya sauko daga kan dokinsa ya daure
dokin a jikin wata bishiya sannan ya cire takobin saiful Lujara
daga cikin mafiyafinta kuma ya zareta daga cikin kufenta ya
ruketa tsirara ya nufi gidan boka
Ardusa kai tsaye fuskarsa a murtuke har tana yatsina saboda
fusata,kuma jikinsa na tsuma. Duk inda ya ratsa jama'a suka
ganshi sai ka ga ana tashi ana rugawa izuwa cikin gida ana
kulle kofofi saboda ganin Hantaru a cikin mugun yanayi, kuma
ga babbar takobi mai daraja a hanannsa.
Boka Ardusa na kwance a cikin turakarsa yana faman shara
barci abinsa, kawai sai yaji turakarsa ta cika da hayaniye. A
firgice ya farka ya mife zaune domin wannen ne karo na farko
arayuwarsa da ya taba jin hayaniya a turakarsa.Boka Ardusa na
bude idanunnsa sai ya yi arba da dukkanin hadimansa na aljanu
sun cika dakin jikinsu na kyarma kamar ace kyat! su tsure da
gudawa.
Cijin fushi boka Ardusa ya daka musu tsawa ya ce, "Ina delilin
shigowarku nan turakata ba tare da izinina ba? Lallai gaba
dayanku sai kun dandana kudarku domin kun sa na farka a
lokacin da na ke cikin yin barcina mai dadi".
Koda jin wannan batu sai shugaban hedimansa ya zube a Kasa
gaban boka Ardusa ya ce, "Ya shugabana ai yau mu da kai duk
muna cikin mummunan bala'i ne. Mun zo gareka ne domin ka
gaggauta nemo mana wajen buya har kai kanka kuwa, ka sani
cewa a halin yanzu ga jarumi Hantaru can ya durfafo wannan
gida naka dauke da takobin Saiful Lujara. Kuma ya taho ne
domin
ya hallakaka bisa cin amanar sarki da kayi ka
kwanta da matarsa aka sami cikinsa."
Koda jin wannan batu sai boka Ardusa ya daka tsalle sama ya
tumu da kasa. ldanunsa suka zezzaro,kawai sai ya ruga da
gudu izuwa cikin dakinsa na halwa domin ya duba wadansu
ababan dogaronsa na tsafi. A wannan lokaci ne wadannan
hadiman aljanu nasa da ya baro a turakarsa duk suka tarwatse
suka tashi sama suka rinka tsala gudu cikin dimauta ba tare da
sanin inda suka dosa ba.
Boka Ardusa ya yi sauri ya debo dukkanin guraye da layu na
tsafinsa sannan ya dauko kayan yakinsa ya rugo waje da gudu
daga cikin dakin da nuim shima ya tashi sama, kawai sai ya ga
Hantaru tsulum! A gabansa.
Boka ardusa ya yunkura da nufin ya shafi weta laya da ke
wuyansa, sai Hantaru ya sa takobin Saiful Lujara cikin zafin
nama ya sare kan boka Ardusa. Kan yai tsalle sama ya rabu da
gangar jikin, kawai sai hantaru ya daga daya hannun nasa ya
cafo gashin kan Ardusa a lokacin da gangar jikin ta sulale kasa
ta fadi.Kawai sai Hantaru ya juya juya ya fice daga cikin gidan
ya durfafi gidan sarki Kusaidu.
Sarki Kusaidu na kwance bisa gado yana jinyar rashin lafiya,
kawai sai wani hadiminsa ya
shigo cikin turakar da gudu yana haki, ya fadi Kasa ya ce, "Ya
shugabana gari fa babu lafiye".
Cikin Karfin hali Sarki ya dubeshi ya ce Yaki ne ya taso mana
yanzu-yanzu?". Hadimi ya ce, "Ai abin da ya taso yanzu yafi
karfin yaki domin danka ne Hantaru ya dawo rike da takobin
SAIFUL LUJARA, har ma yaje gidan boka Ardusa ya yanko
kansa.
Kode jin wannan batu sai sarki Kusaidu ya mike zumbur! Cikin
tsananin farin ciki tamkar bai tabe yin wani ciwo ba ya ruga
waje da gudu yana mai bude hannayensa yana kwalawa
Hantara kira A wannan lokaci gaba dayan Dakarun gidan sun
dimauce sai guje-guje suke da iface-iface suna neman inda za
su shiga su buya domin sun san cewa basu issa su tari Hantaru
ba bare har su hana sh�� y��n abin da ya zo yi.
Shi kuwa sariki Kusaidu ko kadan bai damu da wannan hali da
dakarunsa suka shiga ba kawai burinsa shi ne ya ga ta inda
Hantaru zai 6ullo ya tareshi su rungume juna yaji dumninsa
kirjinsa.
Sarki Kusaidu ya ci gaba da gudu a cikin gidan sarautar ya
shiga wannan sako ya fita ya shiga wancan loko yana ta
Kwalawa Hantaru kira,amma bai ganshi ba.
Shi kuwa Hantaru lokacin da ya shigo ciki
gidan sarautar sai ya ruga lzuwa cikin wani surfuki inda babu
wanda zai yi zaton shigarsa wajen sannan ya rikide ya zama
gashin dawisu ya nufi dakin gimbiya Zarifa Duk wannan hayaniya da ke faruwa a cikin gidan sarauta Zarifa
bata san da ita ba, domin tana can cikin kewayenta a cikin baho
tana wanka a cikin ruwan kumfa mai kamshi.
Tana cikin wannan hali ne ta ga wani gashin dswisu mai kyau
ya shigo cikin turakar. Koda ganin gashin dawisun sai ta tsaya
cak ta kura masa idanu, daga can sai ta bushe da dariya ta ce,
"Lale marhabun da dana na cikina wanda ya zo domin ya sare
kaina ya kaiwa matarsa".
Kode jin wannan batu sai wannan gashin dawisu ye rikide ya
zama Hantaru sai gashi tsaye a gabanta rike da kan boka
Ardusa a hannun hagu jini na diga a jikin ken. A hannunsa na
dama kuwa takobin Saiful Lujara ce sai sheki da walwali take ta
haskake bandakin gaba dayansa tamkar an kunna fitilu a
cikinsa guda dubu.
Cikin sanyin jiki da matukar mamaki Hantaru ya dubi Zarifa a
lokacin da hawaye ye zubo masa ya ce, "Ya ke Ummina ina
dalilin da ya sa kika ci amanar sarki Kusaidu kika sadu de
bokansa aka samu cikina? ya ya aka yi kika ganeni a yanzu da
na shigo cikin wannan kewaye a cikin
siffar gashin dawisu?"
Koda jin wadannan tambayoyi guda biyu sai Zarifa ta sake
bushewa da dariya a karo na biyu sannan ta tsuke fuska ta ce,
"Ya kai dana ina son ka sani cewa in dai don biyan bukatar rai,
mutunci da dukiya ba a bakin komai suke ba, saboda bukatar
cika burin zuciyata ne na ci amanar sarki na sadu da bokansa
aka sami cikinka kuma na bashi kai a matsayiin dan cikinsa har
ya soka fiye da komai a duniya. Tabbas burina ya cikan tun da
na sami nasarar kawar da 'yar uwata Marifa domin na mallaki
dukiyar da mahaifinmu ya bar mana ni kadai.Sai dai kash! Har
yanzu ban mallaki dukiyar ba, bakin cikin hakan ne ya sa naji
bana tsoron mutuwa don haka idan ka kasheni a yanzu zan
kasance a cikin farin ciki tum da burina bai gama cika ba a
duniya. Abin da zan sanar da kai shi ne, kaima baka isa ka shiga
kogon da aka ajiye wannan dukiya ba domin ka debota ka
kaiwa matarka Larziya domin a lokacin da na fahimci cewa ba
zan iya mallakar dukiyar ba face na samo takobin Saiful Lujara
sai hankalina ya dugunzuma na baza manzanni a duniya suka
rinka ziyartar manyan bokaye
akan yadda zan iya kona wannan dukiya gaba dayanta yadda
har abada babu wanda zai moreta. Sai da manzannina suka
shekara goma sha biyar suna wannan aiki sannan suka samo
mini sihirin da na sami damar kona dukkan wannan dukiya ta
zama toka. Yanzu haka idan ka shiga inda dukiyar take za ka
iske babu komai a ciki face toka.
Game da tambayarka ta biyu kuwa, ina son ka sani cewa komai
sammakonka wani a tafe ya kwana. Saboda tsananin yawo na a
cikin duniya wajen bokaye sai da na mallaki dukkan sihirin tsafi
na duniya wanda ban samu ba kawai shi ne wanda ke jikin
takobin Saiful Lujara. Ka ga ke nan a duk matsafan duniya
yanzu babu wanda ya fini karfin sihiri face kai,don haka duk irin
yanayin da mutum zai juye izuwa wata siffar da na kalleshi sai
na ganshi a zahirin siffarsa ta gaskiya. Yanzu gashi a
matsayinka na dan da na haifa a cikina baka kaunata ka tsaneni
kamar yadda ka tsani mutuwarka. Dukiyar da na ke ta hankoron
mallaka tafi karfina ina ji ina gani, mijina da yake mutuwar sona
fiye da komai a duniya na hainceshi na ci amanarsa kuma ya
san duk abin da na aikata amma saboda tsananin son da yake yi mini ya
danne komai a zuciyarsa ko a fuskarsa bai ta6a nuna mini ba".
Sa'adda zarifa tazo nan a zancenta sai idanunta suka ciko da
Kwalla hawaye ya fara zuba sannan ta ci gaba da kallon
Hantaru tana mai cewa,"Ya kai dana yanzu mene ne amfanin
zamana a duniya? Ina ribar da na samu tun da har yanzu abin
da na shuka ban girbi komai ba? Hakika nayi nadama tun daga
lokacin da 'yar uwata Marifa ta fada mini maganganun cewar za
ta rabu da ni ba a son ranta ba duk da cewa bama son juna
saboda ko babu komai ni jinin ta ce.
Duk sa'adda na tuno da kalamanta sai nayi kuka na zubar da
hawaye, yanzu ne na gane cewa duniya ta rudeni na bi son
zuciyata nayi biyu babu don haka yanzu bani da sauran buri a
duniya wanda ya fi na bi 'yar uwata Marifa izuwa inda ta tafi. Ina
tabbatar maka da cewa idan ma ka tafi yanzu baka kasheni ba
sai na kashe kaina. Bakin cikina shi ne na ri ga na lalata maka
taka rayuwar domin kaima ba za ka taba samun sukuni ba da
kwanciyar hankali."
Lokacin da Zarifa ta zo nan a zancenta sai jikin Hantaru ya yi
sanyi, yaji ba zai iya sare kanta ba, kawai sai ya fashe da kuka
cikin tsananin bakin ciki.
Zarifa ta dubeshi ta ce, "Maza ka yi abin da ya kawoka domin
wannan kukan ba zai fishsheka ba. Idan kuma ba za ka iya
kashe ni ba to ni ka bani takobin Saiful Lujara na sare maka kai
sannan na kashe kaina.!
Kafin Hantaru ya ce wani abu sai Zarifa ta fito daga cikin bahon
wakan ta fisge takobin Saiful Lujara daga hannunsa ta daga
sama za ta sare masa kai. Cikin zafin nama Hantaru ya cafki
takobin ya Kwace takobin sannan ya datse ma ta wuta, sai ga
kanta na lilo a hannunsa.
A dai-dai wannan lokacin ne sarki Kusaidu ya banko Kofar
kewayen ya shigo. Da shigowarsa ya yi arba da kan Zarifa a
hannun Hantaru jini na zuba sannan ya ga gangar jikinta
kwance a Kasa faca-faca da jini. Koda ganin wannan al'amari
sai sarki Kusaidu ya hadiyi zuciya nan take ya fadi kasa
matacce.
Hantaru ya kwarara uban ihu ya fadi kan gawar sarki Kusaidu ya
rungumeta kuma ya
fashe da matsanaicin kuka.
Sai da aka kwana goma sha bakwai ana kuka da bakin cikin
mutuwar sarki Kusaidu a cikin birnin Kisra. Shi kuwa Hantaru
saboda tsananin bakin ciki ma kasa zama ya yi ayi jana'izar
Sarki da shi. A wannan rana ya shirya ya tafi kogon da mahaifin
su Zarifa ya 6oye wannan dukiya.
Bisa tarihi tun bayan mutuwar mahaifin su Zarifa ba a taba
samun wani mahaluki da ya shige shi ba walau mutum ko
aljana, amma a wannan rana sai ga shi Hantaru ya sa takobin
Saiful Lujars ya sare wata bakar kofa ta karfe a jikin kogon.
Take kofar ta rufta ciki ta fadi Fasa.Duk da cewa kogon a can
bayan gari yake sai da aka jiyo karar faduwar kofar a can cikin
bimin Kisra, saboda girman kofar da nauyinta domin inda Kartin
aljanu majiya karfi guda dubuc casa'in za su hada karfi ba za su
iya banke kofar ba har su kaita kas. Kai sabods karfin sihirin da
ke jikin kogon ko fara ce ta gifta ta kusa da kogon sai ta fado
kasa matacciya bare mutum ko aljan.
Bayan Hantaru ya banke kofar ta fadi kasa sai ya kunna kai
cikin kogon ba tare da fargabar komai ba. Duk da cewa kogon na da tsananin duhu ko
tafin hannu mutum ba ya iya gani amma da shigar Hataru cikin
kogon sai ya haskake gaba daya albarkacin hasken takobin
Saiful Lujara.Kawai sai ya ga babu komai a cikin kogon face
bakar toka tuli a ko ina, sama da kasa. Koda ganin wannan
al'amari sai Hantaru ya durkusa kasa bisa guiwoyinsa ya fashe
da kukan bakin ciki. A sannan ne ya gasgata maganar Zarifa
cewar ta gama kona dukiyar gaba dayanta amma a sa'adda ta
gaya masa sam bai yarda ba.
Sai da Hantaru ya dade a durkushe a kasa yana kukan takaici
da bakin ciki. Abin da ya fara fado masaa zuciya shi ne ya ya
Larziya za ta karbeshi idan ya koma gareta babu wannan dukiya
sai kan mahaifiyarsa Zarifa?"
Haka dai Hantaru ya ci gaba da tunani mai zurfi a zuciyarsa ya
tuna cevwa shi fa yanzu ya rasa babban masoyinsa a duniya
wato sarki Kusaidu, wanda ya rage masa kawai mutum biyu ne,
daga Salimat wacce ta shayar da shi ta reneshi a matsayin dan
cikinta sai kuma matarsa Larziya wadda take kuma take
&matsayin 'yar uwarsa ta jini ta hanyar haduwar
jini tsakanin mahaifiyarsa Zarifa da
mahaifiyarta Marifa.
Idan Salimat taji cewar Sarki Kusaidu ya mutu sakamakon
ganin gawar Zarifa da wane matsayi za ta dubeshi? Kawai sai
Hantaru ya aiyana a ransa ya ce, "Lallai ba zan baiyana ma ta
gaskiyar al'amari ba har sai ta dawo birnin Kisra da kanta taji
abin da ya faru".
Bayan Hantaru ya gama Kulle-Kulle a zuciyarsa sai ya mike
tsaye cikin sanyin jiki da tsananin damuwa da bakin ciki ya fice
daga cikin kogon gaba daya ba tare da bata wani lokaci ba ya
hau dokinsa ya ci gaba da tafiya ba sassauci ya durfafi birnin
Darul Mahabul.
KAMAR YADDA ya shafe watanni yana tafiya a lokacin zuwansa
birnin Kisra haka ya sake shafe wadannan watanni ya dawo
birnin Darul Mahabul, kuma a wannan karon ma takobinsa bata
sha jini ba, domin babu wani abu da ya kawo masa farmaki
walau mutum, aljan ko dabba har ya iso kofar birnin Darul
Mahabul.
Da zuwansa bakin kofar birnin sai ya ja
linzamin dokinsa ya tsaya cak! Yana tunani.Abin da ya fara fado
masa a rai, ina ya kamata ya fara zuwa? Shin wajen
mahaifiyarsa Salimat zai je ko kuwa gidan sarki zai wuce domin
ya ga masoyiyarsa abar begensa dare da rana wato matarsa
kuma 'yar uwarsa Larziya?
Nan take Hantaru yaji zuciyarsa ta cika da tsananin farin
ciki,domin ya san cewa a yau ne zai more amarcinsa da Larziya,
amma da ya tuna cewa a cikin abubuwa guda biyun da Larziya
ta ce ya zo ma ta da su guda daya kacal ya zo da shi, wato kan
mahaifiyarsa Zarifa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun yaji
zuciyarsa ta fara bugawa da karfi kamar za ta tsage ta fado
kasa ba don komai ba sai don tunanin cewa ba lallai bane
Larziya ta amince da shi ba kuma za ta iya kashe kanta bisa
bakin cikin rashin cika burin mahaifiyarta.
Hantaru ya tuno da batun Salimat, take yaji kijin nasa ya ci
gaba da daka da sauri da sauri duk da cewar ya yanke shawarar
ba zai gaya ma ta ainahin gaskiyar al'amarin da ya faru ba.
Sai da Hantaru ya shafe rabin sa'a a tsaye akan dokinsa yana ta sakar zuci, fargaba da
tunanin abinda zai fishsheshi sannan daga karshe ya yanke
shawarar ya fara zuwa gidan Shurem domin ya sadu da Salimat
saboda ya san cewa ya tafi ya barta a cikin tsananin fishi da
bakin ciki, bai san halin da take ciki ba yanzu. Lallai ya zamo
wajibi a gareshi yaje gareta ya nemi gafararta kuma ba zai
yarda te san da mummunan bamar da ya aikata ba a can birnin
Kisra har reyuka uku suka salwanta.
Lokacin da Hantaru ya fara tafiya ya nufi hanyar de za ta kaishi
gidan Shurem, sai ya tuna cewa ai yana dauke da kan
mahaifiyarsa Zarifa a cikin jakara guzurinsa wanda ya zuba
masa wani ruwan sihiri wanda ya hanashi rubewa. Nan take
Hantaru ya ratse hanya ya shiga cikin daji ya isa har karkashin
wani tsauni mai duhuwa ya saula daga kan dokinsaya tsaya
cak! Ya dubi gabas da yamma,kudu da arewa bai ga kowa ba
kuma bai ji motsin komai ba. Har tsawon lokaci yana tsaye a
hakan. Koda ya tabbatar da cewa babu mai ganinsa sai ya haka
rami a gaban wata siririyar bushiya ya binne wannan kai na
Zarifa sannan ya koma da baya ya kau kana dokinsa ya durfafi
gidan Shurem.
Tun dage nesa Hantaru ya hango kofar gidan Shurem a ciko
makil da zuriarsu ta makera, jama'a na tsaitsaye sun yi tsit ba a
jia muryar kowa face sautin numnfashinsu.
Koda ganin haka sai zuciyar Hantaru ta buga da tsananin karfi
irin bugawar da bai tafa ji ba a rayuwarsa. Cikin tsananin
fargaba ya iso cikin taron, ai kuwa jama'a na hangoshi sai aka
dare aka bashi banya ya kutsa ta tsakiyarsu bisa dokinsa ya iso
tsakiyar harabar gidan. Koda ya yi arba da abin da aka shimfide
a agabansa sai ya tsandara uban ihu ya fado kasa tim! Daga
kan dokinsa ya fashe da mataanaicin kuka yana mai buga
kansa a jikin dirkar gini, har kan nasa ya fashe jini ya ringa zuba.
Cikin sauri wasu karti majiya karfi su uku suka kamashi suka
rirrikeshi don kada ya ci gaba da buga kansa a jikin dirkar ginin
wacce ita ma kanta ta fara tsattsagowa tana barazanar
rugujewa.
Ba wani abu Hantaru ya yi arba da shi ba face gawar Salimata
shimfide idanunta a Kafe kamar za a yi ma ta magana ta amsa.
Hantaru ya ci gaba da rusa kuka da ihu tamkar mahaukaci
sabon kamu har ya zamana
cewa gaba dayan jama'ar da ke wajen sun tsorata ainun sun
fara watsewa don tsoron kada ya zare takobinsa ya hausu da
sara.
Shaulat da ke tsaye a kansa tana ta faman zubar da hawaye ta
kasa cewa da shi komai,sai ta sa hannunta cikin aljihu ta dauko
wata guntuwar wasika ta mikawa Hantaru. Hannun Hantaru na
karkarwa ya karbi wasikar ya budeta ya fara karantawaa fili,
kamar haka;
Ya kai dana Hantaru,kayi sani cewa ka bani kunya, kuma ka bani
mamaki, domin a zatona za ka janye mugun nufin da ka tafi da
shi izuwa birin Kisra, amma sai gashi soyayya ta sa idanunka
sun rufe ka manta da muhimmancina a rayuwarka
Ka tuna cewa babu wani mahaluki da nake so a wannan duniya
sama da Sarki Kusaidu,gashi ka kashe matarsa Zarifa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login